Showing 204001 words to 207000 words out of 296192 words
idan ina raye ba a isa an yi auren nan ba, idan kuwa ka dage sai kayi ba da yawuna ba sai dai ka nemi wata uwar Khalil. Shashasha mara zuciya ko kallon abin da ubanka yayi mini baka yi, ke kuma munafuka kin aure mini miji, shine kika saka ya aurawa ɗana 'yar matsiyata irinki ko, ai ina tsaye ina jinku, idan har ni na haifeka Khalil ban lamunci auren nan ba ba da yawuna ba".
AYSHERCOOL
08081012143GABA DA GABANTA
NA
AISHA ADAM AYSHERCOOL
64
Gaba ɗaya jikin Khalil yayi sanyi, ya waiwaya yana kallon Hajiya Zainab.
Daddy ya ce "Wannan aure babu abin da zai hana shi yiwuwa, babu biyayya ga abin halitta, wurin saɓawa mahalicci, auren Khalil yana kan tsari da koyarwa ta Addinin Musulunci, dan haka babu gudu ba ja da baya ba abin da zai hana wannan auren muddin ina raye".
"Wallahi baka isa ba, ba za ayi shi ba, idan har aka yi auren nan ba da yawuna ba kuma sai dai ya nemi wata uwar bani ba"
Amina ta jinjina kai ta ce "Taɓ"
Mummy ta mayar da kallonta kan Amina ta ce "Ke kuma baƙar algunguma tashi ki bar wurin nan, ina magana da mijina da ɗana"
Hararta Amina tayi, ta murguɗa baki, ya cigaba da kaɗa ƙafa.
Daddy ya kalli Khalil ya ce "Khalil, tashi kaje ba abin da zai hana aurenka albarka da yardar Allah" Jiki a sanyaye Khalil ya tashi ya bar falon.
Ya kalli Amina ya ce "Meenalina, kije ki kwanta kinga dare yayi" Amina ta miƙe tsaye ta ce "Ok, sai da safe ma ƙarasa maganar kenan?"
Ya ce "Eh, but i hope baki ji haushi ba?"
"No ba damuwa, good night dear"
Ya kashe mata ido ɗaya, tayi gaba tana wani rausayawa kamar ana mata kiɗa, Alhaji Ahmad ya bita da kallo, wanda hakan ya fusata Hajiya Zainab ainun.
"Wallahi Ahmad kaji kunya, 'yar tatsitsiyar a bar nan kake bi da kallo, 'yar cikinka Allah wadaran halinka wallahi".
"Kema da zaki yi mini hakan kallonki zan yi, ke kika watsar kika daina, dan na samo mai yi mini ai ba laifi bane, ke a wurinki na tsufa ko? To ita a wurinta ban tsufa ba, ina sake gargaɗinki a kan wannan ɗaga hankalin naki da kike yi, kuma auren Khalil yana nan babu fashi, sannan Fadila idan har iyayen wancan yaron ba su zo ba, ita ma zan yi abin da ya dace a kanta".
Ji take kamar ta shaƙe shi ta huta da baƙincikin da yake ta dan ƙara mata sinƙi-sinƙi.
"Mu zuba ni da kai Ahmad, shege ka fasa"
"Daga ni har ke babu shege duk 'yan halak ne"
Ko a mafarki idan aka ce Alhaji Ahmad zai yi mata haka, zata ƙaryata ɗari bisa ɗari, amma ɗan tahalikin nan ya rufe ido yana ta surfa mata rashin mutunci yadda yake so.
Malam Khalil kuwa ɗakinsa ya wuce, yayi sallar isha'i, dama cikinsa a cike yake, ya ɗau wayarsa ya haye gado, ya kira lambar Hafsa, cikin ikon Allah yana kiranta ta ɗaga, suka cigaba da yin wayarsu cikin soyayya da kewar juna.
Amma ƙasan zuciyarsa yana jinjina masa yiwuwar abin nan, bayan Mummy ta riga ta nuna bata so.
Shirye shirye suka yi nisa.
Daddy ya canza furnitures ɗin gidan, amma banda na Hajiya Zainab, saboda ta ce ba ta so ya riƙe tsiyarsa.
Zakka kuwa da ya fitar, 'yan dangin Amina wasu sun samu, nasa dangin ma haka, da kuma 'yan unguwa.
Tuni ya bugo invitation na gayyata walimar kammala karatuk Sakandire, da tariyar Amina, ya bawa Amina nata, saboda neman rigima ya kaiwa Hajiya Zainab ma.
Aikuwa ta yayyaga ta watsa masa abin sa a jikinsa, bai damu ba ya ce "Zainab, duk wannan lallaɓakin da nake, dan nayi miki adalci ne, amma tun da haka kika zaɓa shikenan.
Dama kuɗin da kika karɓa a wurina, ki riƙe su, sune na faɗar kishiya da zan baki.
Ko kallonsa ba tayi ba, ta shareshi.
Amina kamar sabuwar amarya, tayi kyau sosai tayi shar da ita, har ƙauye taje ta kai musu invitation na tariya da walima.
Daddy ya so ya saiwa Baba gida a birni, amma ya ce ba zai iya barin ƙauye cikin danginsa ba ya koma birni gaba ɗaya ba, dan haka a nan ƙauye aka saiwa Baba gida, suna ta shirin tashi da zarar an kammala tariyar Amina.
Ya saiwa Baba rumfar kasuwa, ya bashi jari ya zuba kayan awon Abinci.
Amina kuma kuɗaɗenta da ta samo, da kuɗin Aurenta da sadaki, Daddy ya cika aka saya mata ƙatuwar gona a ƙauye.
Baƙi ciki kamar ya kashe su Kawu Bala, duk da suna cin arziƙin su Aminan, ba su taɓa zaton babban mutum ne mai kuɗi ya auri Amina ba.
Ƙarin baƙin ciki sai da Amina ta kai invitation, yadda ta yi ƙiba, kwananta ɗaya washegari aka kawo mata kayan lefe.
Kaya na gani na faɗa, da ba a taɓa makamancinsa a garin ba, Hajiya Maryam ta saiwa Amina kaya na alfarma.
Ammi da su aka karɓi lefen Amina, aka ce walima da tariya kwana goma.
Mutane suka dinga sintirin zuwa ganin kayan lefe, kwanan Amina uku, Ammi ta ce Lallai ta koma Kano, saboda a cigaba da yi mata gyaran jiki.
Da ta koma Kano, gidan su Azima ta tafi, Ammi ta ce sai ranar tariya zata koma gidan.
Khalil gaba ɗaya zaman gidan baya masa daɗi, dan haka a wurin Abdul yake wuni, da yamma ya tafi wurin Hafsa sai dare ya koma gida.
Dangin Alhaji Ahmad, da suka sami labarin 'yar aikin Hajiya Amina ya aura, kamar su zuba ruwa a ƙasa su sha, mussaman ma su Anty Fauziyya da suka je gidansa, Amina ta karrama su.
Alhaji Ahmad yayi ɓarin kuɗi a shirin walimar Amina kamar babu gobe, da ta ce za ayi kaza zai ɗau kuɗin ya bayar, danginsa da abokanansa suka dinga ba ta gudunmawa.
Hajiya Maryam taji daɗin haɗuwa da Ammin Azima, dan a nan ne ma Hajiya Maryam take sake bata labarin halin rashin mutunci na Hajiya Zainab.
Duk baƙin da suka zo, a ɗayan gidan Daddy suke sauka, Abinci kala kala haka aka dinga shiga ana fita da shi.
Har gida Yusra taje ta samu Fadila, dan yi tayi kamar bata san meyafaru ba, sai da ita Fadilan dan kanta ta sanar mata da abin da ya faru, dan suna gida amma basu san zancen ya yaɗu a gari ba, mussaman Kasancewar sa sanannan mutum.
Fadila na ganin Yusra ta rungumeta tana kuka, Cikin rarrashi Yusra ta ce "Haba girl, kiyi haƙuri mana ki danne zuciyarki"
Fadila ta share hawayenta ta ce "Yusra ba zaki gane halin da nake ciki ba, Yusra 'yar aikin Mummy fa Daddy fa ya aura, kinga wulaƙancin da suke yiwa Mummy, kullum cikin kuka da damuwa take, gashi ya kaiwa Khalil kuɗin aure gidan su wata yarinya talakawa masu awara a titi, gaba ɗaya ta ɓata mana farinciki"
Yusra cikin rarrashi ta share wa Fadila hawayenta, sannan ta ce "kiyi haƙuri, zaku iya maintaning farincikinku, ku amayar da komai ba komai ba, idan kuka yi kamar baku san da zamanta a gidan nan ba, Mummy ta ciresu daga ranta gaba ɗaya"
"Haba Yusra, tsawon shekaru suna tare da mijinta, rana ɗaya yarinya ƙarama ta ƙwace mata shi, dole ta damu"
"Haka ne Fadila, amma idan ta cigaba da damuwa zata iya haɗuwa da wata larurar"
Yusra ta cigaba da kwantar mata da hankali, ta ce suje su duba Mummy, suka tarar da Mummy tana bacci.
Ita ma Yusra taso sanar da ita batun alaƙarta da Abdul, amma ta yi shiru saboda halin da ta tarar da ita a ciki.
Dangin Baba daga Dutse suka zo, haka 'yan uwan su Amina daga ƙauye, Daddy ko a jikinsa wai dan ya auri yarinya ƙarama yana gayyatar mutane walimar kammala karatu da tariyar matarsa.
Rana bata ƙarya, sai dai uwar ɗiya taji kunya. Hall yayi hall yayi kyau sosai.
Amina ta sha kwalliya tayi kyau har ta gaji da haɗuwa.
Amina sai murna take yi, ganin yadda mutane suka taru duk domin ita. Ga ƙawaywnta na ƙauye, ga na birni 'yan makarantarsu, ga dangin Daddy, ga matan abokansa duk a wurin.
Aikuwa sun tara mata kuɗi matan manyan nan. Tun ƙarfe takwas ake abu ɗaya sai sha ɗaya na dare sannan aka tashi.
Su Ammi suka ɗauke Amina sai kuma gobe wurin kai amarya.
'yan garin su Amina da suka zo, sun sha mamaki a kan gidan da aka sauke su kawai, balle Abincin da aka dinga shiga ana fita da shi.
Inno ma tazo, sai dai ba taje wurin walimar Amina ba.
Hajiya Zainab ji take kamar zuciyarta zata buga ta mutu ta huta da tsananin baƙin ciki da damuwa.
Da yamma Ammi ta saka Amina ta shirya, aka yi mata light makeup, sai zuba ƙamshin turaren Hajiya Maryam take yi.
Mota mota aka dinga caikawa da 'yan garinsu Amina, da 'yan Dutse zuwa gidan Alhaji Ahmad.
Suka shiga suka dinga rafsa guɗa, dangin Alhaji Ahmad suka dinga cewa ko anƙi ko an so yanzu dole su zo gidan ɗan uwansu.
Hajiya Turai ta ce "Ji matsiyatan 'yan uwanta wasu gajiyayyu da su, duk a komaɗe kamar 'yan gudun hijira, munafukai talakawan banza"
Suka dinga santin sashin Amina, komai yaji, yayi kyau sosai da sosai.
Suka dinga Addu'a da sanya albarka.
Sai da suka fito falo, Anty Fauziyya ta dinga "Allah ya kawo alkadarin baƙar daga, ko anƙi ko an so dole muzo gidan ɗan uwanmu. Engineer ai sai yanzu yayi dacen yin aure wallahi, auren haɗi ya zame masa bala'i".
Hajiya Salma ta ce "Ke ki kiyayi kanki, Karki kuskura ki kuma yin gigin cin mutuncin matar gida"
"Matar gidan banza, ai Allah ne ya kawo karshen mulkin mallakar da kika dinga yi tsawon shekaru. An samu wuri an miƙe ƙafa an manta tushe".
Wuri ya kaure da hayaniya, da ƙyar manyan ciki suka tsawatar, sai wajen ƙarfe goma na dare, kowa ya watse, sannan Hajiya Zainab da Hajiya Maryam suka fara kai Amina danginta da dangin Daddy suka yi nata nasiha sosai, sannan suka kai Amina gidan Alhaji Ahmad.
Hajiya Zainab na ganin Hajiya Maryam tayi sak, ta bita da kallo.
Suka ƙarasa falon suka zauna tare da Amina, ta ce "Ya naga kamar kinyi manakin ganina Uwargida? Kwana da yawa, an naɗamu wakilcin kawo miki ƙanwarki, muna fatan Allah ya baku zaman lafiya"
Hajiya Zainab ta ce "Da ke aka haɗa munafuncin auro mini 'yar aikina ko?"
Hajiya Maryam tayi murmushi ta ce "Ni ba ruwana, sai dai kin san hausawa sun ce komai girman gona akwai kunyar ƙarshe. Allah ne ya kawo lokaci"
Turai ta ce "Hmm, gayyar tsiyar banza da na wofi, zata gani ba dai ta shirya kishi da manyan mata ba, gata nan ga gidan ai"
Ammi ta ce "Ai da sunan Allah muka shigo, dan haka ba abin da zai faru da izinin Allah. Ke Amina tashi muje"
Suka tashi suka wuce da Amina sashin Daddy, wurin yayi kyau sosai, an jere mata kayan lefenta a bedroom ɗin, komai yayi kyau sosai da sosai.
Suka zaunar da Amina suka yi ta mata nasiha, da gaya mata abin da ba a rasa ba, suka kira Daddy a waya dan suna son tafiya, Daddy ya ce su tafi bakomai yana cikin gidan.
Suka fita suka tafi, su Hajiya Turai ma sun bar gidan, saboda dare ya fara yi.
Duk wannan wunin budurin da aka yi, Fadila bata zauna a gidan ba, saboda kar ma taga tashin hankali.
Daddy ya shigo, hannunsa da ledoji, ya fara nufar sashin Hajiya Zainab, amma ya tarar ta rufe da mukulli, juyawa yayi ya koma sashin Amina.
Tana kashingiɗe a kan gadon, tana danna wayarta.
Ya kalleta tare da yin murmushi, ya ce "Fitsararriyar amarya, maimakon ma ki jira na zo na buɗe fuskar taki, shine kika yi kwanciyar ki ko?" Ya ƙarasa maganar yana zama a kusa da ita, tare da ja mata hanci.
Dariya tayi ta tashi zaune ta ce "Wace fuskar zaka buɗe? Mhmm me ka sayo mini?"
"Mutuniyarki da madara"
Amina ta ce "Wayyo daɗi"
"Allah ya shirya wannan amaryar"
Amin ta faɗa tana dariya.
Daddy ya tashi ya cire babbar rigarsa, ya wuce banɗaki, ya yi alwala, ya fito ya kalli Amina ya ce "Je kiyo alwala muyi salla"
Amina ta ce "Da muna Lagos ba ka mini wayo munyi ba".
Daddy ya ce "Yanzu kuma a Kano muke ai, kuma satar hanya muka yi wancan karon, yanzu ma sai mu kuma yi"
A tare suka yi dariya, Amina ta tashi taje ta yi alwala, ta dawo suka yi salla, yayi musu Addu'a sosai, sannan ya kalleta ya ce "Yanzu wanda bai sani ba ma ya sani, duniya ta shaida ke matata ce"
"Da basu sheda ba kenan?"
"Da karuwa ce yanzu kuma matata" yayi maganar yana dariya cikin tsokana.
Amina ta ce "Hmm zan rama ne"
Ya ce "Mmmmm, Meenal uwar daru da rikicin tsiya" ya dinga tuna mata tsiyatakun da ta dinga yi masa.
"Kaga miƙo mini kazata in ci"
"Innalillahi wai wace irin amarya ce wannan ne?"
Tayi dariya ta ce "Irin wadda ka aura ka gama yawo da ita a gari, sai ka dawo kuma ka tuba" hirarsu suke cikin nishaɗi da kwanciyar hankali.
Ya dinga bata kazar nan a baki tana cinye kayarta, har sai da ta ƙoshi.
Ya kalleta ya ce "Yanzu ki shirya muje in rarrasheki kiyi bacci"
Noƙe masa kafaɗa tayi, tana tura baki.
Murmushi yayi, ya ɗagata cak zuwa kan makeken gadon ya rungumeta yana rage mata kayan jikinta ya ce "Ba kya son Allah ya bamu wasu twins ɗin? Ina son yara sosai Meenalina, ina fatan Allah ya bamu masu albarka da jin ƙai"
Ɗan lumshe ido tayi ta ce "Daddy ciki da raino akwai wahala, ina jin tsoro sosai"
"Allah zai sauƙaƙa miki, yayi maganar yana shafa ƙananan kitson da yake kanta.
(Sai suka kashe fitila, ni kuma banga komai ba 🚶🚶🚶)
Washegari tun sassafe, Ammi tayi musu aiken Abinci, Amina Kamar wata sabuwar Amarya haka ake ta wani ji da ita, mussaman dangin Daddy.
Da wuri ta tashi suka karya tare, Daddy ya fita saboda baƙi sun fara zuwa.
Sai da ya fara zuwa wurin Hajiya Zainab, amma still ƙofarta a rufe.
'yan garinsu Amina suka zo suka yiwa Amina Sallama, ciki har da Inno, Inno a ranta ta dinga yaba gidan Amina tana faɗin lallai boko tayi rana.
Inno ta yiwa Amina nasiha sosai da sosai, tare da jan kunne a kan riƙe addu'a. Daga nan mota ta kwashe su, zuwa Shanono.
Tafiyar Inno sai da Amina tayi kuka, kamar lokacin ta fara rabuwa da ita.
Babban abin da ya bawa Amina mamaki, wanda bata san da shi ba, shi ne kayan gara da Baba yayi mata, kayan abinci dai-dai ƙarfinsa, ya ce yadda aka ɗauke masa kayan ɗaki, bai kamata ya zauna ba kataɓus ba, dan haka ya yiwa Amina gara.
Dangin Daddy, suka yi ta jinjina karamci na danginsu Amina, a nan suka sake suna hira, a hirar ta su Amina taji labarin Auren Alhaji Ahmad da Hajiya Zainab.
WANENE ALHAJI AHMAD MUSA DUTSE???
Alhaji Ahmad, haifaffen garin Dutse ne, familynsu sanannu ne a unguwarsu, kasancewar suna da rufin Asiri sosai, kasancewarsu 'yan kasuwa. Kusan su suka mamaye unguwarsu gaba ɗaya, ba yadda za ayi ka shiga layi ka fita, babu danginsu.
Mahaifin Alhaji Ahmad, sananne ne sosai, yana ta'ammalli da 'yan siyasa da manyan 'yan kasuwa.
Matansa biyu, mahaifiyar Alhaji Ahmad Hajiya Bilki, sai kuma amaryarsa Hajiya Sadiya.
Hajiya Biliki bata samu haihuwa da wuri ba, sai bayan da ya auro Hajiya Sadiya tayi haihuwa uku mata.
Duk yaran da Hajiya Sadiya ta haifa ba zaka taɓa cewa bana Hajiya Biliki bane ba, saboda yadda ta riƙesu, daga baya cikin ikon Allah ta haifi ɗa namiji aka saka masa suna Ahmad.
An yi shagali sosai da sosai bayan haihuwar sa, haihuwar da tayi bai hanata cigaba da rainon yaran Hajiya Sadiya ba.
Kowa yana girmama Hajiya Bilki, ciki har da Hajiya Sadiya da yaranta, saboda karamcinta da kyautatawarta.
Daga baya Hajiya Bilki ta dinga ɓari, a haka dai bata kuma samu ta haihu ba, sai Hajiya Sadiya da ta haifi yara shida maza da mata.
Sai dai ita ma Hajiya Sadiya tana ji da Ahmad, kamar babu wani ɗa a gidan sai shi.
Bayan sun girma, duk suna ta karatu, 'yan uwan Ahmad maza suka nuna su sun fi son kasuwanci a kan karatu, shi kuma Ahmad ya ce karatu yake so, mahaifinsu ya goya masa baya yake ta karatunsa.
Familynsu suna da matuƙar haɗin kai da ƙaunar juna, suna son junansu kuma manyansu a tsaye suke a kansu, dan haka da wuya kaga wata ɓaraka a tare da su.
Kasancewar mahaifin su Alhaji Ahmad mutum ne mai kyauta, hakan ya sanya gidansa baya rabo da jama'a, ai ta shiga ana fita.
A jikin gidansu, akwai gidan wani mutum Malam Habu mai itace, yaransa na yawan shigowa gidan su Ahmad, duk da malam Habu ba shi da wani ƙarfi, amma sai auri saki, a haka ya auro wata salihar mata, haihuwarta ɗaya amma azabar yunwa da masifar matansa kusan ita ta haɗu ta kashe ta, ta bar 'yar yarinyarta mai shekaru takwas a duniya Zainab.
Ta tashi a tsakanin matan uba, ba kulawa sai azabar wahala, idan ta samu dama sai ta fita tafi wurin babarsu Ahmad wadda suke cewa Gwaggo, Gwaggo ta bata Abinci, idan bata da lafiya Gwaggo ce ke sawa a kaita Asibiti, harkar makarantarta duk ita ce.
A lokacin da Ahmad ya cika shekaru Ashirin da ɗaya, yana shirin tafiya service, ita kuma Zainab na da shekaru goma sha huɗu, tana tsakiyar azabar matan uba, Gwaggo ta zaunar da Ahmad ta ce tana neman alfarmar ya auri Zainab, ko dan ya rabata da wahalar da take ciki.
shi a rayuwarsa ko budurwa ba shi da ita, amma sama ta ka Gwaggo ta zo masa da wani batu mai nauyin da ba zai iya cewa a'a ba, dan haka ya amince. Tayi murna sosai tayi ta saka masa albarka.
Ko da Gwaggo ta tuntuɓi Zainab a kan lamarin sai ta amince, dan Ahmad ya daɗe yana burgeta, duk gidansu babu mai kyansa, gashi ɗan gayu ɗan masu kuɗi.
Ganin duk sun amince ya sanya Gwaggo ta yiwa mahaifinsu Ahmad magana, shima ya amince.
Sai dai mahaifin Zainab ya ce shi ba shi da kuɗin da zai yi mata kayan gado, Gwaggo ta ce zata yi mata.
Haka aka yi bikin nan, Ahmad na da shekaru ashirin da ɗaya, ita kuma shekaru goma sha huɗu.
A cikin unguwar Mahaifin su Ahmad ya bashi gidan da zasu zauna, a lokacin ba shi da wata sana'a, karatunsa ya saka a gaba, saboda haka komai daga gida ake aika