Showing 180001 words to 183000 words out of 296192 words

Chapter 61 - GABA DA GABANTA

a idon duniya? Ka haɗa jiki da wannan kucakar ƙazama jahila 'yar ƙauye ka dawo ka haɗa jiki da ni Ahmad?.
Ashe shiya sa kake ta nan nan da ita, na kaɗa na raya ka canza mata makaranta kaƙi, ka dinga tsiro mini da rashin mutunci da wulaƙanci kala kala, ashe wannan 'yar abar ka samu ka liƙewa kake bibiya"

Amina dai ta kashingiɗa tayi shiru da ita, jin Hajiya Zainab ta kirata da 'yar aba ne ya sanyata yin murmushi a ranta ta ce 'Lallai 'yar aba ta baki mamaki ai GABA DA GABANTA'.

Fadila da bata riga ta gama barin falon gaba ɗaya ba, ta zube a ƙasa ta toshe bakinta tana kuka, wannan wane irin abu ne Daddy ya janyo musu, su basu ɗauko masa magana ba sai shi da girmansa da komai zai yi mus haka?.

Ya kalli Mummy ya ce "Zainab ko me zaki kirani da shi, ba zan ji haushinki ba, amma ki bari nayi miki bayanin komai"

Cikin tsabar bala'i ta ce "Kai har akwai wani bayni da zai fito daga bakinka in tsaya in saurara? Me zaka gaya mini munafukin Allah wata'ala, wallahi kaji kunya Ahmad, 'yar wannan yarinyar 'yar aikin gidanka, ina ka baro manya manyan karuwan da ke tsakanin Lagos da Abuja da kake zuwa, manyan karuwai da suk ji da kansu, da ka gaza nemansu yadda zanniya gogawa da kowace 'yar bariki kake bi, amma saboda tsabar rashin ta ido irin naka ka rasa wadda zaka bi sai wannan"
Ta mayar da idonta kan Amina ta ce Tsinanniya munafuka, dama shi ne wanda yake da alaƙa da cikin ko? Zan nuna miki ƙarshen iskanci da alama baki san wacece ni ba, sai na yi miki abin da ke da ƙara ganin wani ɗa namiji ya burgeki balle ki bibiyeshi har abada, ai ƙaryar iskanci kike yi, zaki san mijina kika bi. Wallahi saina yi miki illar da ko a bola aka yasar da ke ba zaki moru ba".

Ƙarar buɗe ƙofar da aka yi ne, ya sanya suka waiwaya suga mai shigowa.

Baba ne ya shigo sanye da ash ɗin yadi,yayi kyau sosai, ya shigo bakinsa ɗauke da sallama.

"Dakata a nan! Kar ka kuskura ka shigo mini falo, tsohon banza da na wofi. Ashe haɗa kai kayi da 'yarka ka kawota karuwanci gidana take bin mijina wallahi sai nayi maganinku"

A fusace Amina ta yinƙura za tayi magana, amma Daddy ya dakatar da ita, ya kalli Baba da jikinsa yayi sanyi ya ce "Malam Hassan ƙaraso mana"

"Wallahi ya shigo mini falo, sai nayi masa lahani ya fita ya bar mini gida, kan nayi masa illa"

"Zainab wai meye haka ne?"

"Ban sani ba, ai ka taro bala'i da masifan da ba zaka iya tarewa ba, son zuciyarka da budurwar zuciyarka sun ranto maka abin da ba ka da yadda zaka biya" ta faɗa tana kumfar baki cikin bala'i.
Amina ba ta taɓa zaton bala'in Hajiya Zainab ya kai har haka ba sai yau.

Baba dai ya takure a jikin ƙofa, yana kallonsu, Amina kuwa duk ta sha jinin jikinta ta sunkuyar da kanta ƙasa.

Wasu dattijai ne suma suka yi sallama a falon.

Daddy ya amsa musu, ya na musu sannu da zuwa.
Hakan ya bawa Baba damar biyo bayansu ya shigo shima, saboda yadda yaga alamar jikin Hajiya Zainab yayi sanyi da ganin wannan mutanen.

Ɗaya daga dattijan ya bisu da kallo, ya ce "Lafiya tsayuwar me kuke yi haka ne? Kai kuma ka taso mu babu shiri" yayi maganar yana kallon Alhaji Ahmad.

Amina da ke gefe a zaune a kan Carfet ta ce musu "Ina kwananku?"

Suka amsa mata cikin sakin fuska.

Daddy ya ce "Eh na kira ku ne, domin a samu a warware matsalar da nayi muku bayani tun a waya."

Dattijon ya kalli Hajiya Zainab ya ce "To ki zauna mana, ayi maganar da za ayi"

"Wace magana za ayi, ai babu wani abu da wani zai gaya mini a kan abin Kunyar da Allah wadai ɗin da ya aikata" tayi maganar babu girmamawa

"Ki zauna dai nace" dattijon ya maimaita mata.

Tana wani irin huci ta nemi wuri ta zauna a kan kujera ɗaya.

Ɗaya dattijon da tun da suka shigo bai yi Magana ba sai yanzu, ya ce "To muna jinka"

Alhaji Ahmad cikin jin nauyi ya kalli Baba  ya ce "Kan nace komai, zan fara da baka haƙuri, a bisa abin da ya faru, na saɓa alƙawari da nayi, amma dan Allah ina neman afuwarka. Ina son zan sanar da abin da ya faru a yanzu kuma Kawu na kiraku ne saboda kune shaida, kuma ga waliyina kuma ga nata na kiraku ne dan kuma ku zama shaida".
Ya mayar da idonsa kan Hajiya Zainab, da take ta huci tamkar zata kama da wuta ya ce "Zainab, ina son ki zama mai adalci a duk abin da zan faɗa a yanzu".




MONTHS BACK.

Bayan malam Hassan ya nemi alfarma a wurin Alhaji Ahmad, na son ya kawo Amina gidan, tayi aiki a dinga biya mata kuɗin makaranta, saboda yana da burin tayi karatu. Alhaji Ahmad ya amince. Akwai wani ɗan garinsu shi ne mamallakin  makarantar Bright future science Academy.
Ya yi masa magana, a kan zai kai Amina, yayi masa lissafin duk abin da ake buƙata.
Haka kuwa aka yi, aka lissfa masa komai kuɗi kusan har dubu ɗari talatin da wani abu ya biya, ya sanar da Khalil cewa idan ya dawo ya kai Amina makaranta.

Bayan Alhaji Ahmad ya koma wurin aiki, ya ma manta da batun an kai Amina makaranta, director ya kira shi a waya.
Bayan sun gaisa a waya ne, Director yake ta koɗa masa irin ƙoƙarin da Amina take da shi, da yadda ta basu mamaki a lokacin da aka kawota.
Daddy ya ji daɗin cewa yarinyar tana da mayar da hankali sosai, dan haka ya cewa Director yayi masa bill ɗin school fees ɗinta na shekara ya biya, saboda yana son yaga yaro na mayar da hankali a kan harkar karatu.

Lokacin da Daddy ya dawo gida, Baba ya dinga yi masa godiya. Ya sa Amina na tayi masa godiya.
Amina ita ma har ƙasa ta duƙa ita ma tana yi masa godiya.
A dawowar da yayi ya fuskanci Amina 'yar drama ce, ga shegen surutun tsiya kamar radio ko gajiya ba ta yi, amma duk lokacin da zai ganta, zai ganta ne da littafinta a hannu, tana aikinta tana duba littafinta.

Abin da ya lura da shi shi ne, a duk lokacin da ta gaishe shi, ya ja mata aji kan ya amsa, sai ta ɗan yamutsa fuska tana tura baki. Abun ya kan bashi dariya wasu lokutan, sai dai ba yayi a gabanta.
Ya kan so ya yaba mata saboda yadda ake gaya masa jajircewarta a makaranta, amma sai ya ga to ina ruwansa ma da ita, dan haka ya shareta.

Abubuwan Amina na burgeshi wasu lokutan, mussman idan ya zo wucewa ta falo, ya ga suna kallo ita da Hajara, tana yiwa Hajara bayni abin da ake yi a film ɗin idan bana hausa bane ba.
Babban abin da ya lura da shi game da ita, shi ne riƙon addininta da kuma dagewa a kan abubuwan da ta saka a gaba, ga uwa uba yadda ƙaunrta ga mahaifinta a baiyane take, tana matuƙar nunawa Baba kulawa.

Akwai ranar da zai fita, ya daɗe a mota yana kallonsu, ta zaune tana yankewa Baban farce da kanta, duk da baya iya jiyo me take gaya wa Baban, amma ya fuskanci hirar ƙuruciya take masa yana murmushi.

Ranar da yazo ya tarar Hajiya Zainab ta ci mutuncin Baba, wanda hakan ya sanya Amina kuka sai yaji babu daɗi sam.

Ya sami Hajiya Zainab a ɗaki,, cikin hikima ya ce "Dear me Malam Hassan yayi miki ne kike masa wannan faɗan?"

"Ai ni ban san ma me zance maka ba, nayi nayi da kai ka canza mana mutumin nan ka ƙi, shikenan kullum cikin yiwa mutane shirme"

Daddy ya ce "Na ji, amma dan Allah a dinga sassauta masa kinga babb ne, kuma a gaban yarinyar sa ba zata ji daɗi ba, ba zata dinga ganin girmanki ba, kin san iyaye abu ne masu muhimmanci a rayuwar mutum"

"Ban gane ba me kake nufi da ba zata ji daɗi ba!" Tayi masa maganar cikin tuhuma.

"Babu abin da nake nufi, nufina ɗaya dai ki daina wulaƙanta mahaifinta a gabanta"

"Wallahi muddin ba zai daina yi mini shirme ba, nima na zan fasa ba, idan ba zasu iya ba su bar mini gida" girgiza kai kawai yayi ya ƙyaleta, dan idan ya biye mata, sai suyi faɗa.

Kwanaki biyu a tsakani, Amina ta gaisheshi ya ƙi amsawa, tana yin gaba yaji ta ce 'Aikuwa ba zan sake gaisheka ba'
Bata san maganar ta fito fili ba, amma ya ji ta kawai yayi murmushi ya ƙyaleta.

Ba a rufa sati ba, Hajiya Zainab ta sake yiwa Baba wani saukalen rashin mutunci.
Har cikin ransa ya ji zafin yadda ya kuma ganin Amina tana kuka, ya fita da safe, ya dawo da yamma, ya tarar da ita a haraba tana karatu, amma idanunta sun yi ja sosai, alamun tayi kuka har ta gaji.

Har ya zo ya gifta ta, ya ji ta ce 'Daddy sannu da zuwa"

Maimaita Daddy yayi, saboda tun da suke bai taɓa jin ta kira shi da kowane irin suna ba, ranar da ya kamata tana gulmarsa da sassafe a falo, tana yiwa  Hajara kwatance yana ji tana ce mata  maigidan nan, wannan farin mutumin mai gemu, ya fiye iyayi, wai idan a ka kai Abinci dining, sai ya buɗe yana kallon Abincin kamar an ba shi guba, cikin kwaikwayon muryarsa ta ce "A small portion of it" wai dankali za a ɗan zuba masa kamar wani ɗan yaye, kai wannan da saurayi ne za a ga tsari. Wai idan aka kai masa Abinci a flask da safe, wai ba zaki kuma kawo masa shi da rana ba ji fi'ili"

Sai da ya ƙunshe baki yana dariya, kasancewar basu san ya fito ba. Amma yau sai gashi ta kira shi da Daddy, har ta manta da tayi masa sannu da zuwa, taji ya amsa da yauwwa ya wuce.

Tun daga ranar idan har Amina zata gaisheshi, sai ta ce masa Daddy, shi dai haka nan take burgeshi.
Ba in da ta sake burgeshi, sai yadda ta dinga ba shi Abinci da sasafe kan ya fita, idan bai samu damar ci ba, ta bashi ya tafi da shi wurin aiki.
  Babban abin da ya lura da shi shine, ita yarinya ce mai son kyautatawa mutane.

Daga alkhairan da tayi masa, bai manta lokacin da zai tafi Jigawa ba, ta haɗa masa guzuri wai ko zai ji yunwa a hanya, abin ya daɗe yana bashi mamaki.

Danginsa sun yi farinciki da ganinsa, saboda rabonsa da su har sun manta, shima sun san albarkacin ɗaurin Auren da za ayi ne ya zo.
Ƙannnen mahaifin Daddy suka saka shi a gaba, suka dinga yi masa faɗa, faɗan dai an saba yi masa shi, a kan rashin zumunci sannan kuma shi babu wanda ha isa ya je gidansa, saboda wulaƙanci na matarsa. Ba abin da Daddy yake yi sai basu haƙuri.

Cikin family House ɗinsu ya shiga, cousins ɗinsa mata suka sako shi a gaba, wasu na tsokanarsa wata sabon gani, wasu na masa mitar rashin zumunci.

Shi kansa a wani irin nishaɗi ya tsinci kansa, saboda ba abin da ya kai zumunci daɗi.

"Engineer wai kuwa an gaya maka mun zo gidanka kwanaki?" Cewar matar ƙaninsa Hauwa.

Cikin mamaki Daddy ya kalleta ya ce "Yaushe?"

Ta ce "Wallahi mun je, ai mun san babu lallai Hakima ta gaya maka, ni da su Fauziyya mu kusan huɗu, mun zo Kano ka san nan Kano a ka kai 'yar Yayana muka je gidanka, baka nan, muka haɗu da wata yarinya mai aiki, baka ga yadda ta karrama mu ba, da Abinci da kirki amma matar gidan nan na dawowa ba ka ga kallon banza ba da tayi mana, na san yarinyar nan ta sha masifa bayan tafiyarmu, dan ba kaga kallon banza da tayi mata ba"

Daddy ya ce "Ikon Allah,Ni kuwa wace yarinya ce haka?"

"A gidan dai take aiki, wata mai ɗan ƙaramin baki, tana da ɗan jiki dai, na manta sunanta yarinyar ta karrama mu wallahi sosai da sosai"

"Amina" ya furta a hankali ba tare da kowa ya ji ba.

Wata gwaggonsa da ke gefe tana jin hirar ta su ta ce "To ko ita zamu aura masa ne, mu samu wurin zuwa ko ma samu mu dinga ganinsa?" Tayi maganar cikin sigar wasa.

Daddy ya zaro ido ya ce "Rufa mini asiri, yarinya ce ƙarama fa, bata fi shekara sha shida ba"

"Yo to meye, ba aure bane ba?"

"A'a kar ki haɗani da Zainab, aini babu agender na sake ƙara aure ta isheni"

Gwaggo ta ce "Tafi can, kana zaune mace ta shanye ka, me ake da hali irin na matarka, duk wannan dukiyar taka ko a dangi ka kasa neman wata ka ƙara, dan baƙin ciki ta kanainaye komai ita da 'ya'yanta muguwa"

Daddy ya ce "Allah ya baki haƙuri"

"Rufe mini baki, ba wani Allah ya ani haƙuri" suka yi ta yiwa Daddy mita, shi dai haƙuri kawai yake ta basu.

Yayi musu alkhairi sosai, sannan da yamma ya nufo gida.
Kan ya tafi gida, Hauwa ta bawa Daddy turare da nama fal da kaskon turaren wuta, da wasu kayan da aka raba na biki, ta ce ya kaiwa Amina ya ce suna gaisheta.

Daddy ya ce 'Hauwa banda neman rigima, ki bani abu na bawa 'yar aiki baki bawa matar gida ba?"

"Engeener ita matar gidan da wa ta damu? Ai ni wannan yarinya na sani mai kirki"

Haka Daddy ya karɓi kayan, ya yi musu sallama, ya tafi gida.

Ko da ya dawo gida Hajiya Zainab bata nan, Fadila kuma tana makaranta.

Ya shiga sashen sa yayi wanka, yayi salla, ya fito dining ya ci Abinci.

Ya gama ci yana ƙoƙarin barin falo, Amina ta fito da bokiti da mopper, zata gyara falon.

"Daddy ina wuni"

"Lafiya lau, biyoni mota zan baki saƙo" sai da ta ɗan yi sororo, sannan ta bi shi tana tunanin wani irin saƙo ne haka?

Ya ɗan kallta ya ce "Meye ma sunanki?"

"Amina Hassan Shanono" shi da ya tambayi sunanta har da ƙara masa da sunan mahaifinta da garinsu.

Wata babbar leda ya bata Sannan ya ce "Gashi, baƙin da suka zo rannan ne, suka bani kayan biki suka ce a baki"

"Wane baƙin?"

"Matan da suka zo su huɗu, ki ka yi musu girki"

Ta yi murmushi ta ce "Au, na tuna masu yara ko?"

Ya gyaɗa mata kai ya ce "Sunce a baki"

Ta saka hannu biyu ta karɓa ta ce "Na gode sosai, Allah ya saka da alheri"

Kai tsaye daga wurinsa Wurin Baba ta wuce, taje ta nuna masa.
Ya ce an gode madalla, ta ɗebar masa sauran taje suka yi ta ci ita da Hajara. Ta bata abin da zata bata ta ajiye sauran.

Watarana cikin Daddy yana bacci, ya farka jikinsa babu daɗi, ƙafafuwansa sun yi zafi kamar wuta, sun samu saɓani da Zainab ranar, saboda shegen yawonta dan ko Abincin dare bai ci ba ya kwanta.
Cikinsa da ƙaffauwansa kamar ana hura wuta, ya duba sugarnsa ya ga ya hau, ga kansa yana masa ciwo.

Hannu ya kai ya tattaɓata, ya samu ta farka da ƙyar, ta kalleshi ta ce "Ya dai?"

Ya ce "Bana jin daɗi ne, jikina zafi yake mini, na duba sugana ya hau"

"To Allah ya sawwaƙe, ka sha maganinka Allah ya sawwaƙe" daga haka ta juya ta cigaba da baccinta.

Ya taso ya fito falo, yana zazzagawa saboda yadda jikinsa yayi nauyi, yana nan tsaye yaga Amina ta buɗe ƙofar sashensu ta fito kamar aljana.

Ta dinga tunkaro in da yake tsaye, kasancewar babu haske a falon, bata sani ba, har sai da suka yi karo, za tayi ihu ya rufe mata baki.

Tun daga wannan ranar, da ta sama masa ruwa ya sanya ƙafafuwan sa, wata irin shaƙuwa ta fara shiga tsakaninsu.

Abu kamar wasa, ƙaramar magana na neman zama Babba, Alhaji Ahmad ko wuni yayi bai ga Amina, sai yaji duk babu daɗi, idan ya ganta kuwa ko bata kula shi, gaba ɗaya nishaɗi take saka shi.
  Kasancewar Daddy hutun ƙarshen shekara ya zo, yana shafe a ƙalla watanni uku a gida, dan haka yadda Amina ke kula da Abincinsa, da kirkinta a gareshi, ya sanya suka samu kusanci sosai.

Watarana Daddy ya dawo, ya tarar da Amina tare da Baba, tana ganin ya zo wurin, ta tashi ta bar wurin ta bar shi ita da Baba.


Alhaji Ahmad ya zauna a kusa da Baba, abin da Baban bai taɓa ganin yayi ba. Suka gaisa.
Alhaji Ahmad ya ce "Malam Hassan, na yaba da yadda malaman su Amina suke ta yaba mata, naji daɗin mayar da hankali da take sosai".

Malam Hassan ya ce "Ai bani da bakin yi maka godiya Alhaji, Allah ya saka maka da alkhairi ban taɓa zaton burin Amina zai cika"

"Wane burin kenan?"

"Burin yin karatun boko mana, mu garinmu ba su damu da shi ba, ina nan 'yan uwana Aure suka so suyi mata da wani dattijo, ta biyoni nan, da baka karɓe ta ba ban san ya zan yi ba"

"Aure kuma, karatun nata fa?"

"Ai basu damu da shi ba, ita ma ɗin da take yi, gani suke yi, tamkar wani zunubi ne barinta da nake tana karatun nan"

Alhaji Ahmad ya ce "Amina tana da ƙwaƙwalwa, Yakamata a bata dama ta cigaba da karatunta har gaba da Sakandire"

Baba ya ɗan yi shiru ya ce "Ashsha, wannan ɗin ma na gode, idan na samu dama ta cigaba da karatun, idan ban samu ba, da ta gama na sakandiren ta samu miji sai na yi mata aure, duk danginmu babu wanda 'yar sa ta yi karatu haka, idan na barta sai ya zama abin magana, yanzun ma suna ta surutu a kan zamanta a nan"

Daddy ya ɗan yi shiru ya ce "Haka ne, Allah ya zaɓa abin da yafi alkhairi"

"Ameen yallaɓai, Allah ya saka da alheri"

"Bakomai Malam Hassan"


Daddy kuwa tuni ya yiwa Amina alƙawarin cigaba da karatu, tun bayan da ya fuskanci tana so.


Wasa wasa, Alhaji Ahmad ya kasa gane me yake ji a game da Amina, a hankali ya cigaba da ƙoƙarin samun kusanci da Amina sosai, ya tsiri sawa a kai masa ita gidansa, dan kawai ya samu nishaɗi daga shirmenta.
A haka yayi galaba ta fara shaƙuwa da shi, shi kuma suna ƙara shaƙuwa yana cigaba da shiga damuwa a kan Amina.

Da fari Daddy 'ya ya ɗau Amina, ita ma ta

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login