Showing 294001 words to 297000 words out of 332834 words

Chapter 99 - Bakar wasika Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

65581

mamaki tana zaro ido.
 
“Kai da kanka Faruk? ”
 
“Mama gashi”
 
Ya mika mata wayar duk kuwa da kasancewar ya san ba zata iya karantawa ba.
 
“Kuma ba yan dafara ba ne? Na ji ana fadar mutane suna damfara ba, balle kai da aka ji ka samu kudin nan”
 
“Yau kwana uku da turo sakon Mama, ba damfara ba ce”
 
“Allahu akbar Allah mai kyauta da kari, Allah mai yadda ya so a lokacin da ya so ga wanda ya so, Allahu Akbar”
 
Mama da fada ita kanta tana hawayen farinciki. Komai ya zo musu kamar mafarki, tsakamin shi da Mama sai ka rasa waya fi wani farinciki.
A daren ranar Faruk kwana yai yana godiya ga Allah ya raya dare da sallah nafila. Washe gari ya tura musu duk wani abu da suka bukata ta mail din. Within a week rayuwar Faruk ya canja ya koma wani mutum na dabam da be taba mafarkin zama ba, balle tunaninsa ya bashi wata rana haka zai faru da shi. Gida suka kamfanin ya bashi a Lagos inda babban branch dinsu yake, da kudi mai yawa da zai wadatace shi ya kimtsa rayuwarsa na wani lokaci. Kwansa biyu a Lagos ya suka masa booking din jirki ya sauka sokoto, daga can ya hau mota zuwa Gusau, yana isowa wanka kawai yai ya shirya cikin wasu tufafin masu tsada da yai kuzurinsu tun daga can ya nufi asbitin gurin Mama, domin har lokacin tana asibitin suna bata kulawa da ya kamata. Tun kamin ya tura kofar dakin ya shiga ya ji dariyar Rukaiya, na fada musu yau zai dawo sai dai be fada musu lokacin da zai sauka ba sai ganinsa kawai sukai kamar daga sama.
 
“Yan Tafiya har an sauka”
 
Mama ta fada, sai Ramla tai murmushi ta dauki kular da ta kawo ma Mama farfesu kamar yadda ta saba kullum sai ta shigo mata da wani abun idan zata zo.
 
“Sannu da zuwa”
 
Ta fada tana kallonsa, sai ya amsa mata da murmushi a fuskarsa.
 
“Sannu Ramla ya aiki”
 
“Alhamdulillah”
 
Ta amsa tana murmushi sannan ta nufi kofa ta bude ta fice, for no reason ya juya yana kallonta har ta fice, sannan ya juyo ya kalli Rukaiyah dake kallonsa tana murmushi, dan hade rai yai gudun kar ta samu wata dama ta yin masa zargi ko wani tunanin.
 
“Sannu da zuwa”
 
“Yauwa”
 
Ya amsa sannan ya zauna kusa da mahaifiyarsa da ita ma kanta ta canja kala. Balle kuma shi da har wani kamshin tsadadden turare yake.
 
“Mama ya jikin?”
 
“Alhamdulillah Wallahi na samu sauki sosai, na ji ma suna maganar sallama ta gobe”
 
“Maa Shaa Allah, haka Rukaiyah ta fada min jiya a waya ai”
 
“Ya hanya? Ina ta tunani da zullumin ashe har ka dawo”
 
“Na dawo, shiyasa ai ban fada miki lokacin da zamu ta so ba na san zaki yi ta jin tsoro, duk da jirgi muka hau da zamu tafi a dawowa ma jirgin muka hawa”
 
“Laaa Yaya jirgi ka shiga?”
 
“Ni kaina na ji dabam, i never thought wata rana zan shiga jirgi zuwa wani gari da sunan aiki, ko gidan da suka ba ni abun kallo ne Mama ga motar kamfani idan ina bukata, amman na fada musu zan siye tawa motar”
 
“Gaskiya kam, kara dai ka siye taka to wai yanzu a can zaka zauna kenan?”
 
“Eh a can zan zauna, amman aikin ana canja zai iyu yuyuwa a canja ni zuwa wani gari nan gaba ko ma zuwa wata kasar, amman for now dai a Lagos zan zauna”
 
Mama ta yi murmushin jindadi.
 
“Shamsu yana ta hidima yaron nan yana da kirki, duk abun da ya saka a sabon gidan nan sai ya zo ya fada min, wani lokacin har a wayarsa yake nuna min hotuna gida yayi kyau kamar ba naka ba”
 
“Kamar ba na mu ba dai Mama, ni ma yana kirana a waya ya fada min komai da yake, yana kuma turon min hoton komai. Da na yi tunanin a can zamu zauna ashe Allah yana nan yana nasa tsarin na dabam yanzu sai dai mu rika zuwa muna duba gidan ko kuma idan mun sauka”
 
Sanin manufarsa ya saka Mama murmushi ta girgiza kai.
 
“Aa ni kam ina nan, a can kuma sai ka tare tare da matarka, ni kuma nan ya ishe ni har sai na nemi abokan zama ma, tun da wata rana Rukaiya aure zata yi”
 
“Mama ba zaki je Lagos din ba?”
 
“Aa ban dai hana naje ganinku ba, Sultan ma da zaka yarda da ka bar min shi a nan sai a saka shi makaranta mai kyau in ya so idan an yi hutu sai ya je can yai hutu”
 
“Amman Mama zan fi jindadi idan muka zauna a can tare”
 
“Aa ni dai shawarar da zan baka da zaka dauka da ka cire komai a ranka ka natsu ka samu wata wanda ka natsu da ita ka barwa Allah zabi kai aurenka, a ganina zaka fi kima idan kana da aure”
 
Ya dan yi murmushi yana karbar abincin da Rukaiya take mika masa, a kokarinsa na kawar da maganar ya ce.
 
“Ina Sultan?”
 
“Yana gurin Anty a can ya kwana”
 
Rukaiya ta amsa masa, sannan ta koma ta zauna a inda ta tashi.
 
“Yaya yaushe zaka siye motar?”
 
“Sai na karbi certificate na tuki, ina son na samu natsuwa na shiga makarantar koyon tuki, a can lagos domin sati daya suka ba ni na shirya komai nawa na koma can na kama aiki”
 
“Haka ya kamata, Allah ya taimaka maka”
 
Mama ta fada sai duk suka amsa da Ameen. Sannan Rukaiya ta mike tsaye tana fadin.
 
“Bari na karbo maka lemu shagon waje”
 
“Okay”
 
“Idan kuma zai sha Lemun Kwakwa gashi nan wanda Ramla tai min”
 
Mama ta fada tana nuna masa jug din.
 
“Wai ita yaushe zata daina wannan wahalar ne?”
 
“Sai ranar da ka karbi soyayyarta Yaya, kai baka lura duk sabida kai take somai ba”
 
Rukaiya ta fada tana dariya, sai ya tabe baki.
 
“Ashe ko tana da aiki, ni a yanzu babu mace a gabana, Rafi'a ma ina son na samu lokaci tsakanin gobe da jibi, na kai mata duk abun da ya kamata kuma na biya hakkinta data kashe na”
 
“Ni fa sai nake ganin kamar babu cikin nan, domin da akwai shi da yanzu ta zo karbar wani abu, kuma ni ko mutane ban ji ana labarin cikin ba”
 
“Aikuwa da ta ga tijara, ta zubar min da ciki? Hmmm”
 
“To ya zaka yi? Dan Allah ka saka mata ido kawai ko a yanzu ai Allah ya nuna maka mai hakuri mawadaci ne, domin na tabbatar da zata san haka zai faru da kai da bata maka wulakanci ba balle ta guje ka”
 
“Koma dai minene gaskiya ba zan kyale ta ba, idan ta zubar min da ciki”
 
“Allah ya sauwake”
 
Ya amsa da Ameen. Sannan Rukaiyah ta fice ganin alamar ba zai sha lemun kwakwa ba ta fita siyo masa na gora. Tana fita daga ward din ta hango Kabir tsaye yana waya dayan hannunsa sanye a aljihu, ita yake ta kallo har ta karaso kusa da shi.
 
“Ina wuni”
 
Ta gaishe shi ganin yadda yake sakar mata murmushi alamar dake nuna hankalinta na gurinsa. Sauke wayar yai daga kunnensa ya katse kiran.
 
“Matar nan kina da tsada, tun wacan ganin da na yi miki ban sake saka ki a idona ba”
 
“Ashe kana gane ni”
 
“Really? Ni makaho ne da ba zan gane ki ba? Amman yarinyar nan kin sha da ni”
 
Ya fada yana murmushi mai sauti, ita ma murmushin tai ta cigaba da tafiya sai ya juyo ya jera tare da ita yana takawa.
 
“Ya mai jikin?”
 
“Ta ji sauki, ina tunanin ma gobe za a sallame mu”
 
“Okay, ni ma wanda nake zirga zirga a kansa yau aka sallame shi ya samu sauki”
 
“Allah sarki Allah kara lafiya”
 
“Ameen”
 
Rakata yai har wajen asibitin ta siyo abun da zata siyo suka dawo tare suna tafe yana janta da hira, shi yake rike da ledar lemun har suka iso cikin asibitin.
 
“Ina zuwa dan jira ni zan dauko abu a mota please”
 
“Ba matsala”
 
Ta fada, sai ya juya da sauri ya nufi bangaren da ya faka motarsa yana isa ya bude motar ya dauko katinsa ya saka mata a ledar sannan ya rufe motar. Ko da ya iso har ta nemi guri ta zauna kusa da inda ya barta tsaye.
 
“Da alama dai wannan matar raguwa ce, i don't even know your name”
 
“Rukaiya”
 
“Nice name, ni kuma sunana Muhammad Kabir”
 
Ta yi murmushi sannan ta mika hannu ta karbi ledar.
 
“Na gode sosai”
 
“Amman kamin ki sha lemun ki duba gorar da kyau so that ki tabbatar be yi expire ba”
 
“Inshallah”
 
Ta amsa ba tare da tunanin komai ba, ta nufi ward dinsu, shi kuma ya nufi wani bangaren na asibiti. Taba shiga ta samu guri ta zauna ta bude ledar da zimmar duba lemun sai tai arba a katinsa, saurin rufe ledar tai ta ciro lemun cikin hikima ta mikawa Faruk.
Washe garin ranar aka sallami Mama, da kafafuwanta take takawa sam ba zaka ganta ka ce ita ce wanda aka shigo da ita jiki a mace bata iya tafiya ba. A tsohon gidansu suka sauka, wanda hakan ya bawa makota da basu samu damar zuwa asibitin dubata ba sukai ta shigowa wasu na mata ya jiki wasu kuma na mata barka da arzikin siyen gida da danta yai ba ma daya ba. Domin labarin siyen gidan ya karade ko'ina a unguwar. Sai da Mama ta kwana a gidan sannan ta shirya tarewa a sabon gidan da Faruk ya siya musu, bata bukatar zuwa da komai sai dan abun da ba a rasa ba. Shi ma wanda ya zame mata dole ita da Rukaiya, duk wani abu na al'ada sai da Faruk ya ware kudi akai na dafa abincin a rabawa makotan da suka zo rakiya, daman ya fadawa Shamsu cewar ayi karatu a gidan tun a lokacin da yake aikin zuba furnitures a gidan.
Kamar yadda ya fada gidan bangare biyu ne bangaren Mama da kuma nasa bangaren, an gyara bangaren Mama an saka mata komai da take bukata ciki har da kayan kallo. Nasa bangaren kuma katifa ce kawai sai yar kujerar zama da dan abun da ba a rasa ba. Kusan duk wanda ya zo gidan sai yayi mamaki ace gidan Faruk ne, Faruk dai da wasu ke ganin kamar ba zai iya samun wannan rufin asibiti ba, gidan ne madaidaici ba kato can can ba kuma ba karamin gida ba, tsakar gidan interlock ne main house din kuma ko'ina tiles ne har jikin ginar gidan ga shuke shuke da akai ado da su daga cikin gidan gurin gate zuwa bakin kofar falon.
 Washe garin ranar da suka tare a gidan, Faruk ya shiga wata sabuwar super market da aka bude a unguwar Lalan, tare da dansa Sultan ya siye dan abu bukata na yau da kullum da salulai. Bayan ya biya kudin ya fito ya hadu da Fahat wanda shi ma ya fito daga cikin super market, sai dai Fahat din be lura da shi ba, ko da ma ya ganshi ba gane shi zai yi ba, sai dai Faruk ba zai taba manta fuskar mutumen da ya so taimakonsa ba.
 
“Ranka ya dade”
 
Fahat ya juyo ya kalleshi yana murmushi irin na wanda ya ga fuskar sani amman be gane wanene ba. Ya mika masa hannu
 
“Sannu ya gida”
 
“Ranka ya dade baka gane ni ba”
 
“Na dai ga fuskar sani amman na manta sunan da inda na san fuskar Wallahi”
 
“Allah sarki ni ai ba zan manta ka ba, sunana Faruk...”
 
In brief Faruk ya yi masa bayanin inda suka hada har suka san juna, sai Fahat ya washe hakora yana dariya.
 
“An yi haka, tabbas, ka ce ka yi kudi shiyasa baka nemi ni ba, yanzu ai kai ne ranka ya dade ba ni ba”
 
Ya fada yana kallon dress din Faruk na kananan kaya da suka fito da shi. Faruk yayi murmushi.
 
“Ba haka bane, ina da niyar zuwa, kasan tafiyar da na yi ne ya saka ban samu na zo ba, lokacin da na dawo kuma na tarar mahaifiyata ba lafiya, sai hankali ya tafi can muna cikin haka sai ga aiki na fito mun Lagos daya daga cikin wadanda na yi applying”
 
Fahat ya mika masa hannu yana taya shi murna.
 
“Maa Shaa Allah, Allah ya tabbatar da alheri ya bada sa'a”
 
“Amin Amin na gode”
 
“Wannan yaron ka ne?”
 
“Eh Sultan she's my first born”
 
“Maa Shaa Allah, Allah ya raya. Ba dan kar na yi karabanni ba da nace a kafa kake ko da abun hawa?”
 
“Tukuna dai abun hawan muna da biki nan gaba kadan”
 
“Gaskiya ya kamata, ni ma ai sai a labani na samu wata, amman kamin nan mu je na sauke ka”
 
“Aa ka bar shi kawai,mun gode”
 
“Ka raina kenan yanzu ka fi karfina bari na ja baya”
 
Faruk yayi dariya ya kama hannunn Sultan yana fadin.
 
“Ina gudun wahalar da kai ne kawai”
 
A tare suka nufi motar Fahat din da hannunsa ke rike da Arabian Perfumes masu tsada da kamshi. Fahat ya budewa Sultan gidan baya ya shiga Faruk ya shiga Front seat, Fahat kuma ya shiga mazaunin direba ya ja motar suka hau titi. Suna tafe suna dan taba hira can Fahat ya tambayi inda zai sauke shi, Faruk ya fada masa unguwarsu Rafi'ah, wani irin faduwar gaba Fahat ya ji wanda ya haddasa masa ciwon kai. Faruk yana ta kwatancin inda za su bi har suka gisa bakin gate din gidansu Baturiya, ba karamin mamaki ne ya kama Fahat ba, ta madubin motar ya rika satar kallon Sultan zuciyarsa na raya masa shi ne yaron Baturiya, domin sai a yanzu yake ganin kamaninta kadan a fuskar Sultan.
 
“Ka san wata a nan gidan ne?”
 
Fahat ya tambaya yana kallon gate din gidan.
 
“Eh Ex-wife dita na zo gani zan bata hakkinta kuma Sultan yana son ganinta”
 
“So ka rabu da matarka kenan?”
 
“Yeah mun rabu”
 
“That's mean Baturiya matarka ce?”
 
Faruk ya masa kallon mamaki.
 
“Ka santa ne?”
 
“No...”
 
Sai kuma ya rasa mai zai ce. Faruk ya ce.
 
“Karka maida ni yaro mana, ya akai kasan sunanta?”
 
“Abun da nake son sani, kun rabu gaba daya”
 
“Mun rabu ba gaba daya ba, domin akwai cikina a jikinta shiyasa ma nake son bata hakkinta a yanzu”
 
“So duk abun da aka fada min gaskiya ne about her, sai dai ni na so ta ba da sanin ta taba aure ba ma, domin bata taba fada min ba, sai bincike ne ya gano min haka”
 
Faruk ya runtse ido ta bude yana mamakin furucin Fahat.
 
“Ka taba son Rafi'a ne?”
 
“Yeah, amman yarinyar nan ta yaudare ni, shiyasa bana shakkar fadawa kowa I'm sorry to say baka yi dacen mata ba, duk da yake kun rabu amman akwai da a tsakaninku”
 
Ya mikawa Faruk wayarsa da number Baturiya da ya goge ya saka a blacklist yana nuna masa sakwannin da take tura masa. Faruk yayi murmushin takaici.
 
“If na fada maka abun da ya raba ni da ita you will be shock”
 
Fahat yayi murmushi.
 
“Lemme text her yanzu nan zata fito”
 
Kusan a tare suka bude motar suka fito, Fahat ya zagayo bangaren da Faruk yake tsaye da Sultan yana aika mata da sako cewar yana kofar gida, domin baya jin zai iya kiranta ma. Har yanzu akwai sauran sonta a zuciyarsa domin cire so lokaci daya ba abu ne da zai iya yi a take ba, sai dai yafi tsanarta fiye da son ta a yanzu saboda sanin true color ta, musamman alakar dake tsakaninta da mahaifinsa, ko da wani dabam take wannan alakar ba ya ji zan iya zaman aure da ita bayan ta yi masa karya, balle kuma a yanzu da yake jin aure ya haramta a tsakaninsu.
 
 
 
 
BATURIYA POV.
 
Kamar wanda akai wa bushara da daren mutuwarta, haka Baturiya ta rika kuka tun daga kofar gidan har cikin gidan, tsabar bakincikin da ya rufe mata zuciya ya rufe ya tafi har cikin ido ya rufe su, ga hawaye da ya hana ta ganin komai sai lallaben kofa take har ta shiga cikin gidan. Umma na ganinta ta yo kanta da sauri ta rikata.
 
“Subhanallahi lafiya? Miya same ki?”
 
“Umma na rasa Fahat rashi na har abada, na rasa shi Umma, Fahat ba zai taba aurena ba”
 
Ta fada cikin wani irin kuka da bata san ranar da zai tsaya mata ba, kukan da take ne ya bawa Umma tausayi ba wai domin Fahat ya fasa aurenta ba, domin a tunanin Umma Baturiya zata samu wanda ya fisa ma nesa ba kusa ba, amman saboda ta shaku da soyayyarsa ya saka bata ganin komai idon ya rufe har bata iya komai sai kuka kamar wanda akai wa mutu.
Tun daga ranar Baturiya bata sake wani abu wai shi walwala, abinci ma sai Umma ta matsa mata take ci, da zarar ta tuna da Fahat sai ta ji kamar ta cire ranta daga jikinta ta huta.
Cikin kwana biyu ta koma kamar ba ita ba, daman can jiki babu wani dogon afki balle kuma yanzu da damuwa ke son cinyeta. Ba tana bakincikin rabuwa da Fahat saboda fargaban samun wani wanda ya fi shi ba, no soyayyarsa da tai tahiri a zuciyarta ya saka take jin abu ne mai wahala ta sake samun wanda zata so kamar ranta irin Fahat. Gashi a yanzu da ya nisance ta sai sonsa ya kara shiga ranta ya hana ta sukuni, motsi daya da biyu sai ta tuna yadda suke son junansu.
Har yanzu bata fasa tura masa sakon ban hakuri ba, ta kara hakura ta goge number sa balle ta cire shi a ranta, idan ta kira number shi bata shiga saboda yayi blocking dinta, sakonta da kiransa duka ba za su yi appearing a wayarsa sai a block list dinsa. Karya tai ma Umma cewar wai ya bi zabin mahaifiyarsa ya hakura da ita, ba ta yarda ta fadawa Umma komai ba, Umma kuma bata fasa nuna mata gari da yawa maye ba zai ci kansa ba, maza suna nan da yawa, kamar yadda ta same shi haka zata samu wani. Sai dai duk kalaman da Umma take mata na son kwantar mata da hankali, be yi tasiri a zuciyarta ba.
 
As always  da ta sabawa kanta da zaman kadaici a daki, tana zaune dakin ta yi ruf da ciki tana ta karatun jaki, sako ya shigo wayarta, cikin rashin kuzari ta dauki wayar tana duba sunan wadan ya sakon mata da sakon sai ta ji kamar an mata allura, da sauri ta zabura ta mike tsaye ta, a gaggauce ta cire daurin kirjin dake jikinta ta saka zane da riga na atamfa ta rufe jikinta da Hijab ta fito da sauri zuciyarta na

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login