Showing 315001 words to 318000 words out of 332834 words
masa baki.
“Sultan zamu je gida ko?”
Ya lake kafada, ya juya baya alamar ba zai je ba. Ramla ta yi dariya har sai da dimples dinta suka lotsa.
“Ga ma baya son zuwa, amman ka takura masa sai ya ji, yanzu ma fa sai da na yi masa wayo ya fito”
“Kawai dai ba ki ce kin sace min zuciyar da, gashi nan kin hada shi da chocolate ai dole ya ce ba zai zo ba”
“Aa ba dan chocolate ba ne, ka yi masa laifi ne kuma baka ba shi hakuri ba, kuma da alama baka iya rikon yara ba, da wahala yara su saba da kai”
“Ke suna saurin sabo da ke?”
“Sosai ma, ga zahiri kana gani”
Ta masa alama da ido tana nuna masa Sultan.
“To ai kin ga ta kwana gidan sauki, zuwa zuwa sai ki koya min ni ma su suka saurin sabo da ni”
Ta yi murmushi ta duka gurin Sultan tana magana da shi, hakan ya bawa Faruk damar bawa idanuwansa abinci, tana da kyau da haiba ta fuska, sai a halin yanzu ba kyau fuska ne abun da yake bukata ba, kyau hali.
“Idan ba zai je ba, ka bar shi a nan ya kwana mana”
Ta fada tana dagowa ta kalleshi.
“Yaron nan da kika gani, shi kadai na mallaka fa, ba zan iya ba ina gari daya da shi”
“Aiko wata rana sai na lallaba na bi sawunka ma sace shi, farat daya ka nemeshi ka rasa”
Ya daga kafadunsa.
“Shikenan ai, sai na dawo kofar gidan nan na tare nai ta kuka, da an tambaye ni miye sai na ce Ramla ce.... ”
Kyakyalewa tai da dariya, domin yanayin yadda yai maganar abun dariya ne. Shi kansa dariyar yake, yana kallon yadda nishadi ke kawata fuskarta. Sannan ya mika hannu ya riko Sultan.
“Zo nan, mu tafi gida Mama Rukaiya tana jiranka”
Daker ya yarda Faruk ya dauke shi, sannan ta mika masa jakar hannunta mai kyau irin ta biki wanda ta saka masa chocolate din ciki.
“Dan Allah ka gaida min Rukaiya sosai, da Mama na ma manta ban tambayi jikinta”
“Ta ji sauki sosai gaskiya, Rukaiyah ma tace na karba mata numberki”
“Ka fadawa Rukaiya Number ta mai tsada ce”
“Please”
Ya roka yana bata fuska kamar zai mata kuka.
“Shikenan ka tafi zan kirata”
“Ai bata da waya, daman a wayata ne tace ki saka mata number”
“To zan kira ka”
“Ina zaki samu number”
“Babu ruwanka, kai baka san duk abun da nake so da na yi haka da hannu zan samu ba”
Ta fada tana nuna masa da hannunta da take budewa ta rufe. Sai ya wara ido.
“A takaice ce da aljana na yi arba”
Ta yi murmushi ta juya ta shige ciki, sai ya bita da kallo yana murmushi, sannan ya fice dauke da Sultan din. Kamar wasa yana isa gida ta kira shi ta ce ya bawa Rukaiyah wayar, ba karamin mamaki yai daya daga kiran ya ji muryarta. Sai dai be musa ba ya bawa Rukaiya suka gaisa kamar yadda ta bukata, kuma ya bawa Mama.
Tun daga lokacin sai wani irin shakuwa da alaka mai karfi ta shiga tsakaninsu, cikin kwana biyu suka koma kamar wadanda suka san juna shekaru da yawa, sai dai be yarda ya nuna mata yana sonta ba, Ko muma yana son fadada alakarsu zuwa wani mataki ba, karantar halinta da rayuwarta yake ta yi a hankali. Kamar yadda ita ma take kara fahimtarsa, ga son Sultan da Allah ya dora mata saman can Ramla mace ce mai son yara balle kuma Sultan da take jin kamar ba sonsa ne kadai ke dawainiya da ita ba.
Every morning before ta fita aiki yana kiranta ya bata Sultan su gaisa, wani lokacin ma bata magana da shi, iyakacinta ta ji muryar Sultan, wani lokacin kuma Sultan din ne da kansa zai saka Dadynsa ya kira masa ita su gaisa, ya fada mata duk abun da ya faru a gidan, a irin halinsu na yarinta.
_______________________________
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
Kamar yadda suka fada cewar ranar Monday za su turasu zuwa kotu. Ranar na yi aka shigar da su a gaban kotu. Alkali Dahiru Sulaiman ne ya fara gudunar da shari'a. Lauyan gonatin jiha ya gabatar da karar tare da karanta laifinsu, sannan ya umarce alkalin daya tasa keyar Madina a gidan gyara hali, Leila kuma a yanke mata hukuncin kisa.
Alkalin ya dage sauraren karar har zuwa 24 ga sabon watan mai shigowar sannan ya bada umarnin samawa Leila da Madina Lauyer kamar yadda doka ta tanadar, duk kuwa da kasancewar shari'ar ta zama kala biyu ne, domin ta Leila dabam ake ta Madina da dabam.
A ranar Momy ta ci kuka kamar zata mutu, a kotu ta zube kasa ba dan ta zuma ba sai idan kafafuwanta da suka kasa daukarta saboda kuka, Daddy ma ransa be yi dadi ba ganin yadda Leila ke rusar kuka tana kallonsu, musamman da aza wuce da ita a motar gidan yari. Talba da Kabir ma daker suka iya rike hawayensu, Amal ma ta yi kuka kamar wanda akai ma mutuwa. Kamin yadda labarin abun da Leila ta aikata da kawarta Madina ya karade social media. Wani bangaren har an samu hotonsu da basu san an dauka ba.
Ta hanyar Kabir Ali ya samu labarin yadda aka gudanar da shari'ar, domin be hallarci zaman kotun ba, saboda kar ya ga Leila a halin da ba zai iya jurewa ba, sai a yanzu yake ta nadamar fadawa Talba maganar da yai, wata kila da bar maganar a sirrance kamar yadda take da yanzu komai be faru ba, da yanzu babu bakincikin a zukatansu, kuma ya be jefa Leila a wannan halin ba.
Two days da faruwar hakan Ali ya samu Daddy da maganar Lawyer, suka tattauna ya gabatarwa Daddy da wani babban Lauyer da zai daukar ma Leila, Daddy ya yaba masa sosai kuma ya jidadin yadda abotarsa da Talba ta saka ya dauke shi kamar uba. Sai bayan ya bar gidan ya kira Talba ya fada masa yadda sukai da Daddy.
“Allah ya ba mai gaskiya gaskiyarsa”
Shi ne kawai abun da Talba ya fada masa sannan ya kashe wayar, Ali yayi mamaki sosai a zatonsa Talba zai yi murna ya nuna masa jindadinsa akan abun da yai sai ya ga akasin haka, wata kila saboda tana tunanin ina son Leila na aikata ko kuwa saboda baya son Leila ta fito? Ya kasa raba dayan biyu a tunaninsa, shi dai ya san yayi hakan ne kawai saboda Allah da kuma tunanin halin da iyalan gidan suke ciki, ta wani bangaren yana ganin kamar shi ma yana da laifi na fallasa sirrin da yai.
Ana sauran sati daya a shiga kotun Daddy yake tambayar Talba Aminatu sai ya amsa masa.
“Tana nan lafiya kalau”
“Kana zuwa dubata?”
“Eh ina zuwa”
“Tana ina?”
“Gurin Hajiya Laraba”
“Bata maka maganar tarewarta ba?”
Talba ya kalli Daddy da mamaki
"Haba dai Daddy muna cikin wannan halin kuma?”
“To miye a ciki? Idan ka ce zaka dauki lokaci baka tare da matarka ba saboda shari'ar nan ai zaka dauki dogon lokaci, wata kila za ayi shekara uku biyu har fiye ba a kare ba, kuma duk a tsawon lokacin sai kace kana zaune baka tare ba? Ai ko hidima ake yi ta aure, idan akai mutuwa ba a son a dakatar da ita saboda mutuwar, balle wannan da ba mutuwa ba?”
“Amman ba kowa zai fahimta ba, sannan Momy ma zata ji ba dadi”
“Abubuwa da yawa mutane basa fahimtarsa, idan ka biye musu sai ka kai kanka ka baro, kuma mutanen nan a cikinsu babu mai wuta babu mai aljanna babu mai baka ci ko sha, balle ya hanaka, karka damu da wannan, ka samu lokaci ka yi duk abun da ya dace ka tare da matarka karka yarda na sake maka magana a karo na uku”
“In Shaa Allah Daddy”
Ya fada sannan ya tashi ya fice, y amsawa Daddy ne kawai saboda ba zai iya musa masa ba, amman har ga Allah baya ganin ya dace ya tare a yanzu da gidansu suke cikin tashin hankali, musamman Momy. Be karasa part dinsa ba wayarsa tai ringing, ciro wayar yai aljihunsa ya duba sai yai arba da Number Kaka. Sallama yai bayan ya danna gurin amsawar ya kara wayar a kunne.
“Ai da fushi na yi, ina ta jiran sai ka fara kirana amman baka kira ba”
Ya shafa kansa ya juyo yana kallon harabar gidan.
“Kaka tun lokacin da akai auren nan abubuwa suke ta faruwa na rashin kwanciyar hankali, shiyasa ban kira ba, wani abun kuma na hana a fada miki”
“To ai na ji, shiyasa na kira Laraba ta fada min komai, ashe sace yarinyar nan akai? Amman baka fada min ba, kuma ita Leila ance tana gidan maza? Kaga alhaki?”
“Ita wannan maganar har abar yadawa ce da Hajiya zata kira ta fada miki? Ke kuma ki ce alhaki?”
“Kiranta na yi ina ta masifa nace baka kawo yarinya ta gaishe ni ba, kuma kai baka zo ba, shi ne ta fada min abun da ya faru, shine na ce bari na maka jaje”
“Toh na gode, idan abubuwa sun daidaita zamu zo mu gaisheki, amman a yanzu hankalinmu ba kwance yake ba”
“Toh Allah ya kyauta, kara ma da Allah yasa ba a riga an yi auren ba, ita kuma wacan kawar tata bata da tarbiya ita ba”
“Yadda Allah ya tsara haka yake kasancewa Kaka”
“Allah ya sauwake ya tsare gaba”
“Amin”
Ya sauke wayar, sannan ya karasa part dinsa. Keys dinsa ya dauka ya fito ya nufi motarsa. Tafiyar minti talatin da biyar ta kai shi cikin gidan Hajiya Laraba, sai da ya kashe motar sannan ya bude ya fito ya nufi entrance din gidan. Hannunsa ya kai ya murda kofar ya shiga, sai ya samu yaran gaba dayansu a falon daga manya har kanana, idon Aminatu na rufe da karamin da kwali tana laleben mutanen dake falon, tana jin an bude kofar sai ta nufo inda sautin kofar falon take, a zatonta wani ne ya fita ko ya shigo a cikin mutamen da suke yar nikau din da ita. Talba na kallonta har ta karaso kusa da shi yaran kuma suka rufe baki suna mata dariya, hannu ta kai ta fara laleben wanda ta canka kamin kamshin turarensa ya daki hancinsa sai ta saka hannunta da sauri ta bude idonta. Sai tai arba da fuskar Talba, zaro ido tai ta jiya tana kallon yaran Hajiya Laraba da suka shige dakin da gudu suna dariya. Sannan ta juyo ta kalleshi.
“Yi hakuri ban san kai ba ne”
Yayi murmushi yana jin kamar ya rika hannunta yaja jikinsa ya rumgume, domin yayi marmarinta sai dai ba dama kasancewar karamar yad Hajiya Laraba tana falon tana kallonsu.
“Blind man suke yi?”
Ta daga masa kai, sai ya nufi kujera ya zauna yana ta kallon yadda tai free ta kara kyau, atamfar dake jikinta ta fito da shafe din jikinta kuma ta karbe ta sosai domin jar atamfa ce mai ratsin fari.
“Ina wuni”
Ta gaishe shi a kunyace, be amsa ba sai kallonta yake yana murmushi kana ganin yadda idonsa ke yawo a kyakkyawar fuskarta zaka san kallonta na daya daga cikin abun da ke saka shi mantawa da damuwarsa.
“Kawo min ruwa”
Ta dan saci kallonsa sannan ta nufi kitchen, ya bita da ido har ta shige kitchen din sannan ya dauke idonsa ya maida gurin Hajiya Laraba wanda ta fito sanye da Hijab fuska sake tana masa maraba da zuwa.
“Lfy Kalau Alhamdulillah”
Ya amsa sannan ya maida hankalinsa gurin tv.
“Mun yi waya da Hajiya ai”
Ya sake kallonta.
“Eh ta kirani”
“Ta dame ni da maganar ba kuje kun gaishe ta ba ne, shiyasa na fada mata abubuwan da suka faru”
Yayi shiru be ce komai ba, Aminatu ta fito rike da tray ruwa da cup ta aje masa a gabansa, sannan ta mike tsaye ta nufi dakinsu, a nan kam yayi kokarin ganin ya hana idonsa kallonta har ta shige dakin saboda Hajiya Laraba na gurin.
“Dazun Daddy yake min maganar tarewa da Aminatu, na fada masa be dace ayi haka a irin wannan yanayin ba, amman ya kasa fahimta shiyasa na zo nan gurinki wata kila ke idan kika masa magana zai fahimta”
Wani kallon rashin fahimta Hajiya Laraba tai masa.
“Ban gane ba”
A nan ya fede mata tun daga biri har wutsiya, na yadda suka yi da Daddy. Ba karamin mamaki ne ya kama Hajiya Laraba ba hannu ta saka ta rike habarta cike da tsananin mamaki ta ce
“Na dade a rayuwarta ban ga wani mutum mai karamci da dattako da sanin ya kamata ba irin Alhaji Mu'azu, yana daga cikin mutanen da, kuma mutanen da ke wahalar samun a zamanin yanzu, matsalarsa daya be yi dacen mata ba, ya auro matar data gurbata masa iyali”
“Hajiya Abubuwan da suka faru kaddara ce, kuma kowa be wuce kaddara ba”
Ya fada yana jin tausayin Momy. Hajiya Laraba ta tabe baki.
“Haka ne, Allah ya sauwake. Ya kyauta gaba”
“Ameen”
Ya amsa yana bude ruwan ya sha. Hajiya Laraba ta dora da cewa.
“Ni kam ba wata magana da zan masa, ai shi ya fika sanin abun da ya kamata, kuma wannan abun ai kamar shi akai ma, amman nuna maka haka, kamata yai kawai ka bi umarninsa, domin shari'a ba abu ce da za a ce za'ayi yanzu a kare ba, musamman ma irin wannan ta kisan kai sai ka ga an dauki shekaru ana abu daya”
“Amman Momy ba zata jidadi ba, kuma mutane za su ga kamar ban kyautawa Leila ba”
“Ka aje wannan a gefe, ka bi umarnin mahaifinka, idan kuma kana ganin rashin dacewar hakan to ni ba zan cilasta ka ba, sai ka bari har lokacin daka shirya sannan ka tare da matarka, sai dai kamin nan zata shiga makaranta ta koyi karatu dan abun da bata sani ba ta sani, zai fi zaman banzan da zata yi”
Yayi shiru yana nazari, ita da Daddy dukansu suna da gaskiya, sai dai baya ganin ya dace ya aikata hakan a Yanzu, ba dan baya bukatar matarsa ba ko kuma dan matarsa bata bukatarsa ba, sai dan ganin ko wata biyu ba ayi ba da faruwar abubuwa marasa dadi a gidansu kuma ace ya tare da amaryarsa a gidansa? Kamar Hajiya Laraba ta san abun da yake tunani sai ta ce.
“Ba biki za'ayi a tara jama'a ba, aa kai kadai zaka dauki matarka ka tafi da ita gidanka, dan abun da Allah ya hore mana ni da yayanta sai mu yi na iya karfinmu a siya mata abun da ba zai gagara ba”
“Idan har zata tare, ni zan mata komai Hajiya zan bada kudi a siya mata duk abun da ake yi ma kowace ya mai gata idan za a aurar da ita, but before that sai idan na yi magana da Momy na ji idan hankalinta ya kwanta da tarewar tukuna”
“Toh Allah ya taimaka”
Ta fada sannan ta mike tsaye, shi ma tsaye ya tashi yana amsawa da Ameen.
“Daman dai na ce bari na zo na gaishe ku”
“Ka kyauta kuwa, a gaishe da Alhaji”
“Zai ji In Shaa Allah”
Ya amsa yana takawa zuwa gurin kofar Hajiya Laraba ta bishi da ido tana kallon yadda ya dan rame. Sai da ya fice sannan ta kwalawa Aminatu kira, sai gata ta fito da Hijab dinta.
“Je ku yi sallama da mijikinki”
Kamar wanda bata son tafiya haka ta fita kofar, tana fito ta hango shi jikin motarsa ya rumgume hannayensa yana kallon kofar kamar mai jiran fitowarta, da gangan tai tsaye tana kallonsa da alama shawarar tafiya take gurinsa ko kuma komawa cikin falon ganin fuskarsa ba yabo ba fallasa, dan murmushin daya saba yi mata babu shi a fuskarsa. Sai gashi ya mika mata hannunsa alamar ta zo gareshi, saukowa ta fara yi a hankali a tsakanin stairs din dake kofar zuwa interlock din gidan, da sannu take takawa har ta isa gurinsa sai ta sauke kai masa tana kallon shoes dinsa. Bude mata back seat yai, yai mata alama data shiga da kai, sannan ya zagaya dayan hannunsa side din ya bude ya shiga, sai da ya rufe kofar sannan ya matsa kusa da ita sosai ya rumgumeta.
“I miss you”
Ya fada yana jinta har cikin ransa, ita ma kanta yi marmarinsa domin ya kwana biyu be zo gidan ba, saboda baya cikin natsuwa.
“Tun da muka yi aure kullum da matsalar dake faruwa, duk yadda nake son damuwa ta nisance mu na kasa samun hakan”
Ya furta yana dora kansa saman nata.
“But komai zai wuce, ya zama labari komai zai zama kamar ba ayi ba, sai dai ban sani ba anan kusa ne ko kuma nesa”
“Kowa ka gani a cikin duniyar nan baya tare da farinciki dari bisa dari, dole akwai inda aka jarrabesa, sai dai ta wani ta fi ta wani kuma wani ya samu riba biyu a nan da kuma can, wani kuma sai ranar lahira, ka saka a ranka Allah yana jarrabaka ne saboda yana sonka, kuma komai zai wuce kamar yadda ka fada”
Yayi murmushi ya dago kanta yana kallon fuskarta kamar ya cinyenta.
“Ban taba kawowa a rana cewar wata rana zan samu karfin hali kamar haka na yi magana da wani ba, an jarraba ni jarabawar da sai dai na kasa gane kaina, amman a yanzu ba kowa zai gan ni yace ina da damuwa ba, na rasa uwa sai Allah ya wani wata uwar da kaka, kuma ya bani kai a matsayin miji kuma uba mai share kukana mai gudun damuwata, abun da ban taba mafarki ba, shiyasa aka ce wanda yai hakuri saboda Allah sakamakon