Showing 285001 words to 288000 words out of 332834 words

Chapter 96 - Bakar wasika Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

65651

gansu a daren nan? Kuma ita ta shirya yadda za a dauke Aminatu? And how tana son Talba? Daman duk zaman da take da Leila tana son Talba, amman shi be taba noticed ba? For how long?’
 
Be samu amsar tambayoyin da zuciyarsa take masa ba ya hangota tana kuka tana fadin.
 
“Na jefa kaina a matsala, ban samu biyan bukata ba na shiga wani tasko”
 
Sai da yai hanzarin tattaro natsuwarsa sannan ya samu gwarin guiwar sake yin magana.
 
“Kidnapping wani ba mafita bace Madina, a lokacin da kika dauke ta idan wani abu ya same ta ya zaki yi? And kina tunanin Talba zai so ke saboda kin aikata wannan abun? Sai dai ya kara tsanarki”
 
“A wacan lokacin duk ban ga wannan ba, domin wata haya mai fadi ta rufe min ido wacce ta hanani ganin komai, zuciyata tana raya min idan nai haka zan samu mafita, ashe ina kara jefa kaina a halaka ne ban sani ba”
 
“Idan kin ji kina son Talba, ba wani sabon abu bane, wata kila yana da wasu siffofi da dabi'u da kike so a namiji. Misali kamar ni ba laifi ba ne idan na ji ina son Leila wata kila tana da wasu siffofi da mu'amala da nake son a nace amman ba zan taba yarda son ta yai tasiri a zuciyata ta yarda zai bata alakata da Talba ba, irin wannan abun ya kamata ki yi, and ina ganin laifinki a gurin Leila na son Talba ne kawai bayan shi duk wani abu daya biyo bayan haka bata dauke shi da girma ba saboda Leila tana da sauki kai”
 
Madina ta kalleshi tana girgiza masa kai.
 
“Barazanar da na yi mata ma ta dauke shi da girma, domin Momy ta turo min sako cewar na saurare abun da zai same ni, kuma Wallahi na karshen ba ni na saka shi shi ya aikata da kansa wai kudi yake so sai na bashi miliyan talatin sannan zai rabu da ni”
 
“Shi mutumen da kuka yi aikin da shi?”
 
Ali ya tambaya tana kara nitsawa cikin labarin ta yadda zai fahimci komai da kyau. Sai ta daga masa kai tana kuka sosai.
 
“Ina kika hadu da shi?”
 
“Wani ne ya hada ni da shi, besty amman Wallahi duk wani abu da yake aikawa Leila na Baaba ba ni na saka shi ba, ni dai kawai na fada masa ina son a tsoratata ta yadda hakan zai yi sanadiyar fasa aurenta da Talba, shi ya tsara komai hakora da aika mata shekaran jiya na ba ni na saka shi ba Wallahi ta ya zan ce ya taba gawa har ya ciro hakoranta saboda rashin imani”
 
Wani irin bugawa gaba Ali yai da sauri, take zuciyarsa ta fara raba jini da gudu.
 
“Ina gawar Baaba take? Kin canja mata guri ne?”
 
Ya tambaya yana son kara tabbatar da abun da Talba ya dade yana zargin Leila da shi.
 
“Aa ni ban ce ya canja mata guri ba, idan ma ya canja shi yai hakan a karan kansa amman ni ban saka shi ba, na san akan kuskure Leila ta aikata kisan Baaba, kuma na san be kamata na aikata mata haka ba, sheidan ya rinjaye ni”
 
Ya sauke ajiyar zuciya a hankali, yana jin tausayin Leila na kama shi.
 
“Shikenan, zan yi magana da Leila sai na ga yadda za'ayi mu samu mafita, amman bana son kowa ya san maganar nan bana son kowa ya san na zo nan okay”
 
Ta daga masa kai, sai ya mike tsaye.
 
“Zan tafi, wata kila na dawo wata kila kuma wayarki zan kira”
 
Ta daga masa kai, sannan ta rufe fuskarta da hannayenta tana kuka. Fitowa yai gurin cikin rashin kuzari ya nufi motarsa, yana mata key ya danna horn sau biyu, ko kamin yai reverse mai gadin ya bude masa gate din gida. Yar tafiya kadan yai ya hau babban titi babu komai a zuciyarsa sai tausayin Leila, sai a yanzu ya fahimcin kukan da take dazun, da kalaman da take cewar Madina ta butulce mata Daddy da Talba kuma za su tsane ta Momy kuma ta ki ta saurarenta, sai a yanzu ya fahimci dalilin zuwa gurinsa da tai, ta rasa wanda zai fahimce ne.
 
“Idan Talba ya san wannan ba zai raga miki ba Leila, kamar yadda Daddy ba zai saurara miki ba”
 
Ya fada yana shafa kansa zuciyarsa na masa ba dadi.
 
“Daman Talba ya dade yana zarginki komai akai ke yake dorawa Laifi”
 
Ya sake furta yana jin cewar Leila ba zata kashe Baaba da ganganci ba, zai fi yarda da maganar Madina cewar ta aikata hakan akan kuskure kuma kaddara bata wuce kan kowa ba. Tausayinta ya kara rufe shi, domin ya san Talba ba zai mata da sauki ba, a yanzu ya fahimce dalilin da ya saka dazun take cewa tana nadamar komai, domin a yanayin da take ciki a yanzu tana bukatar wanda zai rarrasheta ya kwantar mata da hankali, Allah ka dai ya san abun da take ji a zuciyarta, bayan abun da ya same ta kuma Madina ta kara mata da wani? Ga kuma bakinciki da Talba yai ta cusa mata kala kala.
 
A harabar gidansa ya faka zuciyarsa fal da tausayinta, ji yai yana bukatar yai magana da ita, akwai abun da ya kamata ya tambaye ta, kuma akwai wanda ya kamata ya fahimtar da ita amman ta yaya? Zata yarda tai magana da shi? Zata fada masa komai? Ta ya mai zai fuskance ta? Iskar bakinsa ya busar ya bude motar ya fita ya nufi cikin gidansa, be yi one hour ba a cikin gidan ya fito da shirinsa na office Haulat ta rako shi har gurin tana masa addu'a, sai da ya bude motar sannan ya juyo ya rikota ya sumbanci bakinta.
 
“Sai na dawo”
 
“Allah ya kiyaye”
 
Ta fada tana kallon yadda mood dinsa ya canja, domin fuskarsa ta nuna akwai damuwa kuma ba haka ya saba mata ba idan zai fita, a kofar falo suke sallamarsu, but this time around har sai da ta biyoshi gurin motarsa sannan ya tuna da zancen yi mata kiss kamar yadda ya saba mata. Sai dai bata shirya yi masa magana a yanzu ba saboda ganin zai tafi gurin aiki, hakan yasa ta hadeye abun da ke ranta har sai ya dawo tukuna.
 
Yana fita daga gidansa faka motarsa ya shiga kwararon makotansu, domin gabatar da abun da Talba yai requesting. Be tarar da shi a gidan sai ya karbi number wayarsa ya kira yai magana da shi ya fada masa inda za su hadu. Ko da karfe biyu na rana tai Ali ya kammala komai tare da Bashir ciki har da awon DNA da Talba ya bukata, sai dai an yi fama da Aminatu kamin a dauki jininta domin shi yake ganin yafi sauki kuma Talba zai fi gamsuwa da shi.
 
 
 
AMINATU POV.
 
gaba daya ta kasa sakewa ayau, saboda mutanen da suke zuwa ganin Talba, most of them yan'uwan Daddy ne sai na Momy da kuma makota da abokan arziki sai kuma wasu daga cikin ma'aikatansa. Gashi a dakin ta wuni domin bata da gurin zuwa, Momy bata sake mata fuskar da zata je waje ta zauna ba a cikin, domin ko shigowar da take da mutane masu dubiya, daurewa Aminatu fuska take babu wanda ya san matsayin Aminatu a gurinsu domin bata fadawa kowa, bata ma son a sani. Zuwan Hajiya Laraba ne ya saka Aminatu ta ji sanyi sanyi ta samu sakewa har tana dariya kamar ba ita ba, Hajiya na zaune kan kujera tana nunawa talba rashin jindadinta na kin yarda da yai a fadawa Kaka abun da ya faru.
 
“Idan ta ji zata ji ba dadi, kasan halin tsofin nan sai tace wulakanta ta za'ayi, kuma kai kanka abun farincikinka ne yadda mutane suke ta shigowa ace ga dangin mahaifiyarka amman ace idan ba ni ba babu wanda ya zo kamar wanda ba shi da uwa”
 
“Ke din ma kin wadatar Mama, kuma ina ganin kamar be kamata a fada musu mummunan labari irin wannan ba, kamata yai ace idan na samu lafiya sai na bi na ziyarce su na san kowa kowa kuma ya san ni, idan wani abu ya taso za su sanar da ni nima zan sanar musu”
 
Hajiya Laraba ta kebe baki
 
“Allah ya sa zaka iya, ni din ma daka sani yaushe rabonka da gidana? Sai zuwan Aminatu ka san da wani zuwa gidana yanzu ma kana dauketa yanke zumuncin zaka yi”
 
“Idan ma na yanke, ai ban iya na yanke na tsakaninki da Aminatu ba, kin ga kuwa dole ne na yi zumuncin ko dan ita”
 
Ya karasa yana murmushi.
 
“Ni na san saboda ita zaka yi ai ba san Allah ba”
 
Wannan karon dariya yai.
 
“Haba an taba zumunci ba domin Allah ba, saboda Allah zan yi”
 
Hajiya Laraba ya tabe masa baki.
 
“Gamu gani ai, Allah yasa wannan uwar taka ta barka ka kula dangin mahaifiyarka”
 
Kusan Hajiya Laraba ta yi sara akan gaba ne, domin fadin hakan yayi daidai da turo kofar dakin da akai Momy ta shigo tare da wasu friends dinta. Kana ganinsu kaga manyan mutane sai kamshin tsadaden turare suke dayar idonta sanye da gilashi irin na marasa lafiyar ido. Sosai Aminatu ta sha jinin jikinta ta dawo kusa da Hajiya Laraba ta tsaya ko ido ta kasa dagawa, tsoron Momy take sosai da dai Leila ce ba zata ji komai ba, amman bata da natsuwa a guri idan Momy na kusa. Yanayin yadda Talba yake masa musu ya tabbatar ma da Hajiya Laraba cewar ya san su, suma kuma sun san shi farin sani, ko da wasa Momy bata kalli inda Hajiya Laraba take zaune ba, sai wani shan kamshi take, tana jiran Hajiya Laraba ta fara nata magana.
Hajiya Laraba kuma ta hakimce saman kujera ta kawar da fuska kamar bata san da Momy a dakin ba, irin sai dai ki ci kanki.
 
 
 
 
 
 
 
 
_______________________________
 
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
 
Ganin Momy zata wuce ba tare da sun gaisa da Hajiya Laraba yasa Talba ya kira sunan Momy tana juyowa ya nuna mata yar'uwar mahaifiyarsa.
 
“Momy ga Mama Laraba nan”
 
“Na ganta ai”
 
Momy ta amsa a takaice, sai Hajiya Laraba tai dariyar raini ba tare da tace komai ba, haka Momy ma bata ce da ita komai ba ta fice, domin a ganin Momy ita ya kamata ta fara yi mata magana ko dan rainon Talba da tai, kuma a tunaninta matsayinta da nata ba daya ba. Fitar Momy da minti biyu zuwa uku Ali ya shigo dakin, sai da ya gaisa da Hajiya Laraba sannan ya karasa gurin Talba yana tambayarsa jikinsa, duk kuwa da kasancewar be wani dade sosai da ita daga dakin ba haka yake masa a duk lokacin daya shigo sai ya tambayi jikinsa. Har yayi kamar yai masa magana Leila da yalshen nasara, sai kuma wata zuciyar ya hana shi a ganinsa Talba ba zai fahimta ba, ba lallai ne yai ma Leila uziri ba kamar yadda yake yi ma Aminatu.
 
“An gama komai, shi kansa ya matsu ya ganta”
 
“Yeah Lawyer na ya fada min komai, thank you so much”
 
“A shigo da shi?”
 
“Eh mana”
 
Talba ya bada go ahead, ido Aminatu ta gwalo waje tana jin zuciyarta na bugawar dadi. Cike da farinciki take kallon Talba ba dan Hajiya Laraba na gurin ba da rumgume Talba za tai domin ya faranta mata rai a yau. Ali ya kalli Aminatu ta dauke kai shi dai kam jininsa ba hadu sa nata ba, wani lokacin ma sai ya ji kamar tana ba shi haushi domin saboda ita Talba ke yi ma Leila wani abu, wata damuwar kuma saboda saurenta ne da Talba yai Leila ta shiga damuwa.
 
“Bashir din ne?”
 
“Eh”
 
Aminatu ta amsa mata da sauri cike da zumudi tana kallon kofar shigowa, har wani jimke hannayenta take tana matsasu saboda jindadi. Ali ne ya sake turo kofar ya shigo sannan Bashir dake biye da shi ya shigo, da gudu Aminatu ta nufeshi ta rumgume shi sosai tana jin kukan farinciki na sallamo mata, shi kansa hawaye sun cika idonsa ita da shi suka duke a gurin jikinsa sai rawa yake, iyayensu ya tuna da su, ita kamta rayuwarta ta gidansu ta dawo mata.
 Hajiya ma sai da idonta ta cika da kwalla saboda tausayi, Ali kam kallonsu kawai yake, Talba ta ba shi tausayi sosai domin ya karanci farincikin da dukansu su biyu suke ji, musamman ma ita.
 
“Aminatu...”
 
Sai kuma ya kasa magana sai kuka yake, be taba mafarki haduwa da yar'uwarsa ba, kamar yadda tunaninsa be kawo masa cewar tana raye ba, ya dauka ya rasa kowa kenan.  Daga ita jar shi kuka suke aka rasa mai rarrashin wani, banbancin nasa kukan da nata gurin sauti ne, domin nata sautin yana fita, na shi kuma baya fita sai zallar hawaye. Mutuwar Inna da Baba da sauran yan'uwa sai ta dawo musu sabuwa. Ali ya nufi kofar fita ba tare da yace komai ba ya bude kofar ya fito ya fara tafiya ward din yana lasa wayarsa. Can kuma ya kara wayar a kunne yaja ya tsaya gaban wani daki ya jingina da dakin yana kallon mutanen dake kai da kawo.
 
“Hello Leila”
 
“Na'am”
 
Ta amsa masa muryarta na bayyana damuwarta.
 
“Baki shigo asibiti ba?”
 
“Eh zan shigo maybe sai gobe ko anjima”
 
“Magana nake son yi da ke, zan iya tararda ke a gida, ko na jira ki zo?”
 
“Akan me zamu yi maganar?”
 
“Akan Talba ne”
 
“No I'm not ready bana son karin damuwa a yanzu, and i know duk abun da zai zo daga gurin Talba ba abu ne da zai kwantar min da hankali ba”
 
Wannan furucin da tai ya saka shi kara jin tausayinta sosai a zuciyarsa.
 
“Maganar tana da muhimmanci Leila”
 
“Okay idan na shigo zan kira ka”
 
Ya sauke wayar ba tare daya sake cewa da ita komai ba. Sannan ya juya ya koma dakin. A lokacin ya samu Aminatu na zaune kusa da Talba har lokacin bata daina hawaye ba, shi kuma yana tsaye kusa da kofa idonsa sun rikide saboda hawayen da yai da kuma bakinciki da bacin rai na tunawa da iyayensu.
 
“Na dauka na rasa kowa, abun nan akwai matukar ciwo da tashin hankali, har abada ba zaka taba manta komai ba, rana guda ace komai naka ya rushe”
 
Bashir ma maganar Talba na kallon Aminatu ita yake tausayi.
 
“Kai da kake namiji kenan balle ita da take mace, and lokacin data rasa kowa nata bata da ni bata da Mama, but she kept going, sannu sannu tana samu farinciki, a lokacin nan bata san kana raye ba”
 
Talba ya fada sannan ya mika hannunsa yana murmushi ya rika hannun Aminatu.
 
“Ka ga irin mutanen nan, suna da wata baiwa da Allah yai musu ta hakuri, wanda ba kowa yai ma domin wani idan ya wayi gari ya samu kansa a yanayin da Aminatu ta samu kanta, zai iya taba kwakwalwarta ko kuma ya saka zuciyarta bugawa. That's why na yi ma kaina alkawarin ba zan taba aikata wani abu da na san zai taba zuciyarta ba, idan har wani bacin rai ya same ta Wallahi ban sani ba ne, ko kuma babu yadda za'ayi na haka hakan faruwa”
 
Ali ya dan tabe baki kadan yana yana kallon Talba, a ransa yana cewa idan Leila ce ba zai mata haka ba. Bashir yayi murmushi yana kallon kanwarsa da yake jin kamar ya bude cikinsa ya saka ta a ciki saboda kaunarta da yake, domin ita kadai ta rage masa a rayuwar duniyar nan, sai yan'uwa na nesa.
 
“Allah sarki, Allah ya baku ikon hada kanku, yanzu sai ka ji sanyi ita ma sai ta ji, ta samu dan'uwa a raye”
 
Cewar Hajiya Laraba tana kallonsu cike da tausayi. Talba ya ce
 
“Ya akai kai ka rayu? Ina lokacin da aka kai harin?”
 
“Ina nan garin, na fada musu zan taho a ranar na tafi da Inna da su Baba, sai Inna ta dage akan cewa ita dai ba zata je ba, ta fi son ko mutuwa ce ta mutu a can, amman hakan be saka na hakura ba saboda ina gudun kar wata rana a zo a kashe su, ashe ban tsira ba kuma ban isa na tsiratar da su daga mutuwa ko kaddara ba, a ranar da na ce zan ta ho a ranar komai ya faru, sai dai ni Allah be kaddara min zuwa a rana ba, wata kila da ni ma wani labarin ake a yanzu ba wannan bane, domin washe garin na ji abun da ya faru a radio, cikin tashin hankali na isa garin a lokacin gawar iyayena da yan'uwana kawai na tarar, kuma mutane suka tabbatar min da barayin nan sun tafi da Aminatu, mun yi ta sauraren ranar da za su aiko sako ko kuma su kira wayar wani su ce suna bukatar kudi amman shiru... Da farko na yi tunanin wata kila saboda bata haddace number na ba ne sai ta Baba shi kuma baya raye, hakan ya saka na dauki line sa na saka a wayata ina ta sauraren kira amman shiru, sai daga baya muka samu labarin cewa sojiji sun kai samame a gurin kuma sun bukutar da mata da yawa, na je can na duba Asbiti ban ganki ba, na zo nan gari na duba asibitocin gwannati ban ganki ba, har wasu daga cikin private hospital na duba, ban ganki ba, daga lokacin sai na sadakar cewar ko dai kin mutu ko kuma kin zauna can har abada”
 
Aminatu ta lumshe idanuwanta hawaye na zubo mata, the pain is unforgettably, kamin ka yi accepting reality kai

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login