Showing 174001 words to 177000 words out of 332834 words

Chapter 59 - Bakar wasika Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

65656

bincike da kyau please”
 
“Okay, ba matsala, sai na jika”
 
Ya kashe kiran tare da sauke ajiyar zuciya, har yanzu ya kasa daina ganin yarinyar daya ganin dazun a idonsa, hankalinsa ya kasa kwanciya.
 
 
 
AMINATU POV.
 
“Kuka kike yi?”
 
Ta bude ido da sauri tare da tashi zaune ta share hawayen, sai kuma ta kasa cewa komai.
 
“Ko kin gaji da zama a nan ne?”
 
Da sauri ta girgiza kai ta kara sadda kanta kasa.
 
“Aa ina tunanin su Inna ne”
 
“Allah ya musu Rahama, ki daina kewa ke kadai ta so ki fito falo”
 
Ba musu ta mike tsaye tana gyara mayafin lifayarta. Hajiya Laraba na gaba Aminatu na binta a baya har suks fita daga dakin, a inda tafi jindadin zama ta nufa ta zauna ta maida hankalinta gurin tv da suke kallo. Bata juyo ba har sai da ta ji sallamar Hajiya Hadiza Mai Fata, sai da kowa ya gama gaishe ta sannan Aminatu ta mika mata gaisuwa.
 
“Ina wuni?”
 
Cikin far'a Hadiza ta amsa tana kallon yadda komai nata ya canja kamar ba ita ba.
 
“Maa Shaa Allah, Amina an yi kyau sosai, kamar Aminata”
 
Cewar Hadiza kasancewar ita ma tana da babbar ya sa'ar Aminatu.
Aminatu ta sauke kai kasa tana murmushi, domin ita ma kanta ta san ta canja duk wani furuci da za ayi mata a yanzu ba zata yi mamaki ba. Har suka gama gaisawa da kawarta Hajiya Laraba bata dago kai ba har sai da Hajiya Laraba ta kirata.
 
“Aminatu ta so”
 
Ta amsa tare ta mikewa tsaye ta bi bayan Hajiya Laraba suka koma dakin da ta fito. Ko da ta shiga har sun zauna kan gado sai dariya suke yi suna zancen su na matan aure. A kasa Aminatu ta zauna ta sanda kanta kasa. Sai Hajiya Hadiza tai murmushi ta ce
 
“Aminatu sarkin kunya, haka ake son mace da kamun kai da natsuwa”
 
Sai kuma ta kalli kawarta.
 
“Hajiya ya kamata a kai masa matarsa tun da mun gama gyarata, yanzu ma na wanka ne kawai na kawo mata mata, domin ta gama shan komai daya kamata ta sha, bana haufin komai”
 
Hajiya Laraba ta saka dariya tare da bata hannu suka tabe.
 
“Kawata ai na san ki ba daga nan ba, bana shakkar kayanki ko kadan, nan da kwana biyu ai zan a kaita dazun ma Hajiya ta kira tana fada min irin haukar da yai mata akan matarsa nace ta fada masa ya assabar mai zuwa zamu kawo masa ita”
 
“A gaskiya ya kamata, kam in ma ba dan yana auren kauye ba yaushe za ayi aure har wata uku da wani abu ba a kawo maka mata ba”
 
“Hana dai, ai ke ma kin san idan aka kai masa ita haka nan ba tare da wani gyara ba, wulakanci zai iya biyowa baya, amman kalleta ki gani yarinya ta kara kyau ga jiki ta yi sai shining take kamar yar waje, bakin ma duk ya ragu kamar ba ita ba, jiya na Ogana zolayata yake wai mun ci amanar ango mun rike masa mata, wai yana da hakuri da shi ne kotu zai maka mu”
 
Kusan duk a tare sukai dariya, sannan Hajiya Hadiza ta ciro wata kwalba a jakarta ta mikawa Aminatu.
 
“Wannan idan zaki yi wanka ki rika zubawa, idan ya kare sai ki kara ruraren ki barshi ya dan jika sai ki cigaba da amfani da shi”
 
Aminatu ta saka hannu biyu ta karba, sannan ta mike tsaye ta fice daga dakin.
 
 
 
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazo maku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
 
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
 
 
“Ke Uwani karbi kira min Mu'azu, na fada masa ya shirya sati na gaba zamu kai masa matarsa”
 
Wanda Kaka ta kira da Uwa ta ta so da saurinta tana dariya.
 
“Kuma dai Hajiya, ba kin ce sai kin ga dama ba, har kin sauko?”
 
“To ya na iya, ita ma Wannan Yar Haj Laraba dana fada mata cewa tai an gama komai sati mai zuwa za a kai masa amaryarsa”
 
Uwani ta nemo number Talba da Kska ta saka aka rubuta mata Mu'azu a ta kira shi, sai da ta fara ringing sannan ta mika mata.
 
“Gashi ta shiga”
 
Kaka ta karba da sauri ta kara wayar a kunnenta ta nufi dakinta. Talba dake zaune a katon falon Momy ya dago kansa kadan yana kallon wayar dake hannun kujera tana ringing, ganin number Kaka yasa ya dauke kai kamar ba zai dauka ba, domin a tunaninsa zata sake masa maganar kudin dazun ne, ko kuma wata maganar ta dabam ba maganar Aminatu ba. Can kuma ya kai hannu ya dauka ya amsa kiran yana kara kishingidawa jikin kujerar.
 
“Assalamu Alaikum Mu'azu”
 
“Na'am Kaka”
 
“Daman na kira na fada maka cewar Innakar Hajiya Laraba tace sati mai zuwa za a kawo maka matarka, sai ka shirya ka aiko da mota”
 
Ya dan saci kallon Leila dake zaune ita da Amal a kujera daya sannan ya ce.
 
“A ina za a dauke ta?”
 
“Gidan yayar mahaifiyarka mana, Hajiya Laraba, amman fa ban siya mata komai ba, babu kayan dafa abinci babu komai”
 
“Na ji zan ji da komai, amman yanzu Fisabilillahi an san yarinyar nan tana gidan nan aka ki nuna min ita? Kin san zuwa na nawa a gidan nan?”
 
“Ai ni na fada maka kar ta bari ka ganta, to mi zaka tsinana mata? Ai kara dai sai an gama yi mata gyaran jikin”
 
“Ku dai kuka sani, dacan ba a san da zacen ba sai yanxu, dan kawai a wahalar da ni”
 
“To yanzu ba fada maka nake ba”
 
“Wace rana?”
 
“Assabar”
 
“Na ji”
 
Ya kashe wayar ya aje, ya kalli Amal dake kallonsa, sai kuma ta sakar masa murmushi. Shi ma dan murmushin yai mata kadan ya mike tsaye ya nufi upstairs, kamin ya karasa shiga dakin Momy har Amal ta cin masa ta bude masa kofar, murmushi kawai yai ya dauke kai ya shiga dakin, domin ya san gulma ta kawo ta. A saman kujera ya zauna Amal kuma ta karasa inda Momy take zaune ta zauna.
 
“Momy ga Yaya nan”
 
Momy ta dago ta kalleta sannan ta kalli Talba.
 
“Akwai wata matsalar ne?”
 
“Aa, akan maganar yarinyar nan ne”
 
Sai kuma yayi shiru.
 
“Ehm miya faru?”
 
“Akan maganar da na taba yi ne, na dawowar ta gidan nan”
 
“Ba kace Kakarta da ita yarinyar sun fi son zamanta a can ba?”
 
“Eh, amman ina ganin zamanta a nan kamar zai fi, saboda a can bata karatu, bata  komai, a nan kuma ina son na saka ta a makaranta”
 
“Talba, kana tafiya kauyen nan ne ba tare da mun sani ba?”
 
Momy ta tambaya da mamakin yadda a yanzu ya dawo da zancen dawowar yarinyar bayan a can baya ya fada mata cewar bata son zama a nan ita da kakarsa, shi kuma ya fadi haka ne saboda Kaka ta dauke masa Aminatu idan be musu wannan karyar ba be san me zai fada musu ba.
 
“Idan ma na je Momy ai ban yi laifi ba, garin mahaifiyata ne, tana da dangi da iyaye a can, be kuma kamata na watsar da su ba”
 
Momy ta cire gilashin idonta tana murmushi.
 
“Gaskiya ne, amman ai ba su san da zamanka sai da ka girma. Any way ba zan hana ka kawo ta ba, saboda Daddynka ya dade da baka wannan damar ni kuma ba mahaifiyarka bace balle na maka magana ka ji, amman ina son na yi maka magana a matsayina na mahaifiyar matar da zaka aura”
 
Talba ya kalleta, sometimes yana mamakin yadda Momy take sakar masa magana kamar ba ita ba.
 
“Ka san dai mahaifinku ya saka lokacin aurenku, 24 march nan da wata biyu za ayi aurenku, so ya kamata komai zaka yi ka rika shawararta matarka, kuma ka kuje duk wani abu da zai bata ranta, ba wai ka dauko wannan ballagazar yarinyar yar kauye ka kawo ba, kuma ka fara nuna irin halin daka nuna wacan karon akan Leila, so ka yi taka tsantsan, kuma ban yarda ta zauna a nan tare da mu ba, sai dai ka aje ta BQ”
 
A take bugun zuciyar Talba ya kara gudu, wanda hakan yai sanadiyar tunzura jininsa fushinsa da bacin rai suka hau a take.
 
“Ko ba komai Momy, na cancanci idan na kawo wani a gidan nan ki karramashi musamman ace mutumen daga bangaren mahaifiyata yake, babu abun da yake so a yanzu kuma nake kaunar kusanci da su kamar dangin mahaifiyata, na san da tana raye ba zata wulakanta yan'uwanta ba, dan haka a yanzu ma da bata raye ba zan wulakanta jininta ba, na tashi ban san dangin mahaifiyata ba sai kadan daga ciki, a yanzu ne nake neman saninsu su kuma suke sani na”
 
Ya mike tsaye yana gyara rigarsa.
 
“Zata zauna a BQ, ba dan tana ballagaza ba, sai dan tana jinina”
 
Yana kawai nan ya fice daga dakin fuuu cikin bacin rai. Momy ta bishi da ido Amal kuma ta zaro ido tana kallon Momy.
 
“Na rantse da Allah bana son yarinyar nan i hate her so much”
 
“Wata kila akwai abun da dangin mahaifiyarsa suka karanta masa, kallin yadda yake min rashin kunya, akan wata lalatacciyar yarinyar, yar kauye”
 
“Kuma nan zai dawo da ita, zata zo ta takura mana”
 
“Sai idan kun so zata takura muku, akwai wanda ya isa ya takura da a gidan ubansa? Ku dai ya kamata ku takura mata har sai ta ji zaman gidan ya isheta”
 
Momy ta fada tana kallo Amal dake turo baki gaba tana jin haushin dawowar da zata yi a gidan.
 
“Je ki kira Leila”
 
Ta mike tsaye ta fice daga dakin tana sanye da gown din shadda kanta ba dankwali, ko da ta sauko kasa Leila ta saka air piece a kunnenta ta kure Volume tana kallon wata waka a YouTube.
 
“Leila Momy na kiranki”
 
Bata ji balle ta dago kai ma, sai da Amal ta maimaita haka sau hudu Leila bata dago kanta ba, hakan yasa Amal ta karasa kusa da ita ta kai hannu ta cire air piece din, Leila na dagowa bata tsaya komai ba ta mike tsaye ta dauke ta da mari mai kyau. Wani irin ihu Amal ta saka ta zuba da gudu upstairs, Leila ta saka hannunta ta cire baren daya sannan ta bi bayan Amal. Tana shiga bedroom din Momy ta jingina da kofar sai wani yauki take kamar kubewa, bayan ta shiga ciki tana sauraren yadda Amal ta fada ma Momy mari da tai mata, Momy ta kalleta a fusace.
 
“Ban ja miki kunne akan sakawa Amal hannu ba? Mike damunki ne Leila?”
 
“Momy abu ne nake a wayarta fa shine kawai ta cire min air piece, idan ma zata fada min kina kirana why not ta taba ni, amman abun da tai min wannan ai wulakanci ne”
 
“Hannu ya saba da daukewa a kan Amal, ba zan lamunta ba, next time kika sake yi mata wani abun zan baki mugun mamaki, ke shikenan ba ki iya controlling zuciyarki? Kawai da an bata miki rai sai ki ce zaki yi ma mutun abun da duk ya zo ranki”
 
“Amman Momy ya kamata ita na tana kiyayewa saboda ta san halina, sometimes ai ba da niya nake ba, kawai dai rai na ne yake baci”
 
Momy ta bude drawer gadonta ta dauko ATM dinta ta mikawa Amal.
 
“Shi kenan ki daina kukan, ka atm ki samu direba a cikin direbobin gidan nan ko brothers dinki wani ya kai ki yi shopping gobe da safe tun da yanzu dare yayi”
 
Ta karba da sauri tana mikewa tsaye a take kukam ya koma dariya har tana yi ma Leila gwalo.
 
“To Momy na gode, amman ni yanzu zan je gaskiya”
 
“Allah ya tsare”
 
“Amin”
 
Ta amsa sannan ta fice da sauri, haka take idan aka ce za a mata shopping ko taje tai jikinta har rawa yake, ba dan bata da kudi a nata account din ba, sai dan kudin wani sun fi dadin kashewa a gurinta. Sai da ta fice daga dakin sannan Momy ta kalli Leila.
 
“Talba ya fada miki zai dawo da yarinyar nan gidan nan?”
 
Leila ta ya mutsa fuska.
 
“Wace yarinya? Ba dai wannan ba?”
 
“Ita fa, yanzu yake fada min”
 
Leila ta karasa kusa da Momy ta zauna.
 
“Bayan kuma yace ta fi son zama can? What make him change his mind?”
 
“Oho, yace dai wai a nan zata samu karatu a can bata karatu”
 
“Wai miyasa yake son dawowa da ita nan ne?”
 
“Oho ai kina cikin mutanen da suka yi supporting dinsa ya dawo da ita”
 
“Eh amman saboda Madina ta bani wannan shawarar ne, kuma ina ganin kamar mafita ce a gare ni”
 
“Ai komai Madina ce take kitsa miki, idan Madina tace ni ban ma isa na ce ki dauka ba, komai dai Madina ce ta iya”
 
“Amman ai na share maganar da ya fadi cewar bata son nan din, kuma naga kamar ya fita sabgar yarinyar”
 
Leila ta fada sai Momy ta amsa ta cikin bacin rai.
 
“Beta fita ba, tun da yanzu gashi ya dawo mana da maganar, hakan yana nufin kenan yana zagayawa bayan idanuwanmu yana tafiya gurin dangin mahaifiyarsa, shiyasa ni na lura tun da aka saka date din auren nan baya wani farinciki, babu ma wani shirye shirye da yake yi, kuma babu wani abu daya canja daga halinsa ko irin ya nuna yana son auren sosai ko yana sonki, na san yana da girman kai, amman da can ai har maganar auren ya taba miki, yanzu kuma an saka amman baya wani murna, daman ba sona suke ba, kuma ba son ki za su yi ba, wata kila hure masa kunne suke suna zugashi, shi ne yanzu za su dauko wannan yarinyar su bashi ya dawo da ita gidan nan saboda ta shiga tsakaninku”
 
Leila ta yi shiru tana nazari.
 
“To idan haka ne, Momy ki hana shi kawo ta a gidan nan mana kawai”
 
“Ni na isa? Yanzu yaje ya fadawa Daddynku ya kara min wani sakin? Yace ban isa na hana dansa abun da yake so ba a gidansa? Hmmmm ke dai Allah ya sauwake kawai”
 
Leila ta lula wata duniyar tana wani tunanin na dabam, sai kuma ta mike tsaye da sauri ta fice. Dakinta ta shiga ta fara safa da marwa wayarta a kunnenta tana ala ala Madina ta amsa kiranta, domin tun da rana take kiranta ba tai picking ba.
 
 
 
 
TALBA POV.
 
A mota ya labartawa Ali abun da ya faru, da kuma yadda sukai da Kaka.
 
“Amman Talba ina ganin kamar zamanta a gidan nan zai iya haifar muku da matsala, tsakanin kai da Momy da kuma Leila, da zaka dauki shawarata da ka sakata a wani gidan dabam ta zauna”
 
“Taya zan aje ta dabam? Bayan a gidan zan rika kwana ba? Kana ganin ita zata iya zama a gidan ita kadai?”
 
“Aa zaka iya sama mata wata wanda za su zauna tare”
 
“No ba zan yi haka ba, ni fa ba dan Daddy ba, da babu abun da zai hana ni bayyana aurena da ita, saboda abun da Momy take min”
 
“No karka ce zaka ga laifin Momy a nan ma, matar nan ita ta rene ka tun kana karami har ka girma, dole a yanzu da ka girma suke controlling dinka ta rika ganin kamar suna mata fin karfi ne”
 
“Suna controlling dina kamar ya? Please stop saying that, ni dai yanzu i just call to telling you yadda muka yi da Kaka so that ka fara nema mana gida da wuri”
 
“Okay ba matsala, amman please kar wannan ya zama wata matsala a tsakaninmu, na san yadda ka damu da yarinyar”
 
“Yes yanzu haka ma ina hanyar zuwa gidan Hajiya Laraba, ganinta kawai nake son yi, just to make sure tana lafiya”
 
“Oh boy ko kaje ba barinka zata yi ka ganta ba, ka hakura kawai har a kawo maka matarka”
 
“Ba zanje mata kamar yadda na saba ba, a yau kam da na san inda yarinyar nan take ba, ba zan iya kwana ba sai na saka ta a idona”
 
Ali yayi dariya
 
“Idan aka yi magana kace ba son ta kake ba....”
 
Be karasa ba, Talba ya tsinke kiran ya aje wayar, ya maida hankali gurin tukinsa, sai da ya shiga unguwar sannan ya rage gudun motarsa ya shiga slowly har ya isa bakin gate din gidan Hajiya Laraba har zai danna horn sai kuma fasa yaja motar ya faka ta gefe ya fito ya taka da kafa, at first daya kai hannunsa a karamar kofar gate din knocked zai yi sai ya ji kofar a bude, da alama a bude suke barin kofar ba kamar su ba da sai mutum ya kwankwasa za a bude masa. Turawa yai a hankali ya shiga, kai ya dagawa mai gadin yana sama gaisuwar da yake masa. Sannan ya nufi main door din, ita ma a bude ya same ta domin yana turawa ta bude kamar wacan karon da ya zo same ta a bude. Shiga yai ciki ba tare da sallama ba, not because of be iya sallama ba, but because of baya son sallama in a place like this da akwai mutane da yawa, saboda baya son daga muryarsa. Yaran Hajiya Laraba na ganinsa suka gane shi sai gaisuwa ta biyo, a nan kam dole ya bude baki ya amsa musu sannan ya bisu da kallo ko zai yi arba da Aminatu.
 
“Je ki kira Mamanki”
 
Ya ce da yar karamar yarta, sannan ya maida kansa kan wayarsa sai dai gaba daya hankalinsa baya kan wayar. Be dago ba har sai da Hajiya Laraba ta fito ta zauna a kujerar dake fuskarta tasa.
 
“Ikon Allah wai ashe dai Talba ka san gidan nan, Yanzu zuwanka na hudu kenan, dacan kam baka san ka takonka gaishe ni

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login