Showing 105001 words to 108000 words out of 332834 words

Chapter 36 - Bakar wasika Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

65647

irin ihu take babu kakakautawa irin na fita hayyaci, Leila na ganin haka tai saurin sakinta ta fice daga dakin, sai kuma ta dawo ta cire key din ta rufe kofar ta waje ta cire key din, sannan ta nufi kofar fita daga corridor da saurinta, bata karasa ba Kabir da Amal suka shigo.
 
“Lafiya?”
 
“Ban sani ba, ihu take ta yi kuma ta rufe kanta daga can ciki”
 
Ta amsa tana kallon Kabir, sai suka nufi kofar shi da Amal, hakan ya bata damar ficewa daga corridor. Sai da Kabir ya fara murda kofar ya ji ta a rufe sai ya shiga kwankwasawa.
 
“Bude kofar”
 
Ko saurarensa ba ta yi gaba daya ta fita daga hayyacinta sai ihu take. Duk yadda Kabir ya so ya bude kofar sai abun ya ci tura saboda an saka key.
 
“Je ki tambayi Momy idan akwai extra key”
 
Amal ta ja tsaki.
 
“Shiyasa bana son baki, gashi nan Ya dauko mana mahaukaciya”
 
Ta fito tana ta mita, domin Amina bata kwanta mata ba, musmman da taji cewar Momy bata sonta, ko bayan haka ma Amal bata son baki ko yan'uwa ne suka zo da sunan kwana biyu sai sun ga canji a gurinta balle kuma wannan da bata san inda ta fito ba, kuma bata san ranar barinta gidan ba. Upstairs ta nufa, sai da ta fara shiga dakinta ta canja tufafinta ta saka uniform din islamiya sannan ta fito ta nufi dakin Momy, daga bakin kofa ta tsaya.
 
“Momy wai ya Kabir yace kina da key din dakin corridor”
 
“Akwai key a jikin ko wane kofa”
 
“Eh yarinyar ta rufe kanta ne, daga ciki kuma tana ta ihu”
 
“Karki dame ni da maganar yarinya, ta kashe kanta”
 
“Momy miyasa Ya ya kawo mana ita wai?”
 
“Oho masa, neman suna mana”
 
Ta saki kofar dakin ta nufo downstairs, kamin ta karasa saukowa ta hango Talba ya shigo yana jin ihun Aminatu ya nufi corridor da sauri, gulmarta ya sakata saukowa da gudu ta bi bayansa.
 
“Miya faru?”
 
Shine abun da ya fara tambaya.
 
“I don't know, muna falo muka ji tana ihu, Leila tace rufe kanta tai daga ciki”
 
Talba ya murda kofar sannan ya kwankwasa.
 
“Auta... Bude kofar”
 
Bata saurarinsa kuma bata fasa ihun da take ba. Baya yai da karfi ya daki kofar da kafarsa ya ji ta gam domin ba irin kofofin nan ba ne masara karfi, ganin kofar ba zata bude ba yasa ya fito daga gurin ya nufi inda suke ajiyar abubuwan a gidan ya dauko wani karfi mai karfi ya dawo ya fara bugawa, karar yadda yake buga kofar ne ya saka Momy da Leila saukowa su nufi corridor tare da Zulai da Mairo.
 
“Talba me ye haka? fasa kofar zaka yi?”
 
Be ko saurari Momy ba sai bugun kofar yake, Kabir ne ya amsa mata.
 
“Idan ba a buge kofar ba babu yadda za'ayi a fito da ita”
 
“Waya aiketa rufe kofar tun farko? Gaskiya yarinyar ba zata zauna Tana gidan nan tana mana hauka ba, wannan ai iskanci ne”
 
Talba be saurara har sai da yai nasarar balla kofar sannan ya saki karfin ya shiga dakin da sauri, a kife suka same ta tana ta ihu, dago ta yai yana kokarin zaunar da ita sai ta fado masa a jikin jikinta nata rawa alamar tsoro still tana ta ihun. Girgiza ta yai kamin ya kai hannayensa ya rika fuskarta, ta yadda zata yi facing dinsa ta gane shi ne, amman ko kallonshi bata yi sai ihun take ta yi.
 
“Akwai abun da za a mata ta daina ihun nan ne?”
 
Ya tambaya yana kallon Kabir.
 
“Allura”
 
“Please”
 
Talba ya fada sai Kabir ya fice dakin da sauri, Momy taja saki ta juya ta fice tare da Amal yayinda aka bar Leila a tsaye tana kallon Talba, zuciyarta na bugawa da karfi saboda rikon da yai ma Aminatu.
 
“Shiiiiiiiiiii ya isa saurare ni, kina a cikin mutane ne ba daji kike ba”
 
Kamin Kabir ya dauko allurar har Talba ya matsu saboda ihun da take bana wasa ba ne, sai da ya saka audiga ya goge mata hannun sannan ya soka mata allurar. Tana jin karfin allurar a hannunta sai ta fashe da kuka ta kamkame Talba, ko minti daya ba ayi ba bachi yai gaba da ita, sai dai hannayenta duka biyu rike suke da rigar Talba, kanta kuma kwance a kirjinsa. Kabir ya mike tsaye yana kallon Leila da hawaye ya cika idonta sai ta juya da sauri ta fice daga dakin, shi ma kallon Amina yai sannan ya fice aka bar Talba rike da Aminatu tana ta bachi wahala a kirjinsa.
Ido ya kurawa fuskarta sai tausayinta ya kara kama shi, idonta rufe yake amman hakan be hana kumburinsu fitowa ba, ga hawaye a fuskarta shabe shabe, ta turo baki gaba lokaci lokaci sai ta sauke ajiyar zuciya.
Yanayi ya so ji na dabam sakamakon rikon da tai masa gashi rabin jikinta yana kirjinsa, domin ta kwanto masa ne. Wata kila saboda be saba rumgumar mata ba ne, wata kila kuma saboda lafiya ta masa yawa ne. Kokarin daga yai daga jikinsa ya dauke ta ya kwnatar da ita saman gadon, ya gyara mata mata kwanciyarta sannan ya kai hannunsa ya taba kafarta a hankali sai ta motsa alamar ta ji ciwon taba kafar da yai.
 
“Baba... ”
 
Ta furta tana turo baki gaba kamar zai fado, samun kansa yai da murmushi, yana ganinta ya san shagwababiya ce. Sai da ya karewa dakin kallo sannan ya juya ya fice zuwa bangarensa.
 
Kusan awa uku tai tana bachi bata farka ba sai tara na dare, kamin ta farka shogowar Talba biyu yana dubata, a na ukun ne ya same ta zaune tana hawaye. Shigowa yai ya zauna bakin gadon yana kallonta.
 
“Mamana baki gajiya da kuka?”
 
Sai ta dago ta kalleshi.
 
“Taya zan rabu da abun da ya zame min azimun? Miyasa kake tunanin rabuwa da iyaye da yan'uwa abu ne mai sauki, taya zan manta komai a take? Saboda ta mutanen da basa maraba da kai abu ne mai wahala! Har yanzu na kasa yarda cewar na rasa komai, ina ta marmari kauyena, da mutanen kirki masu karamci dake cikinsa, na yi kewar mahaifiyata da Babana, har abada ba ni da mai maye min gurbinsu”
 
Ta share hawayenta sannan ta soma wasa da yatsun hannunta wasu hawayen na sauko mata.
 
“A da, ina rayuwa ne cikin wani karamin gari, mai cike da albarkar manoma, duk da kasancewar ban samu ilmin boko ba, na samu na addini daidai gwargwado, kuma ina zaune da yayyuna cikin jindadi da farincikin rayuwarmu ta yau da kullum, ni kadai ce mace bayan mazaje bakwai da mahaifiyata ta haifa, hakan ya saka na zama yar gata, ina jin kamar babu wanda ya fini more rayuwa, abun da ban sani ba, ashe kaddara tana nan tana min wani tsari, a lokacin da mahaifiyata take cikin rashin lafiya na bakinciki abun da akai ma yayanta kasan me ta fada min?”
 
Ta kalleshi sai ya girgiza mata kai alamar be sani ba.
 
“Tace kuka na yana nan gaba, sai na tambaye tana take ganin zan iya rayu idan bata raye? Tace min zaki rayu amman akwai kuka a gaba, a yanzu na gane abun da take nufi, tabbas zan rayu amman wace irin rayuwa zan yi? Ban sani ba, kuka da take fada min cewar zan yi na tabbatar shi ne na fara tun a yanzu, yanzu na fahimta wanda ya rasa uwa ya rasa ta har abada, wand ya rasa yan'uwa ya rasa su har abada, abu ne mai wahala farinciki ko murmushi ya sake kusantar fuskata...”
 
Ta fashe da kuka sosai, Talba ya ja dogon numfashi a hankali ya sauke.
 
“Baki taba tunani miyasa Allah ya hada ni da ke ba? Wata kila a yadda nake da rufin asiri idan na tare ki a hanya, ba zaki tsaya ba zaki ji tsoro, wata kila ni kuma ba zan taba jin a kamata na tsayar da ke na tambayi damuwarki ba, amman sai Allah ya kawo silar da zata saka na hadu dake cikin sauki kuma har na dawo dake da zama kusa da ni, idan Allah ya karbe wani abun sai ya maka hanyar wani, ki dauka duka wannan yana cikin jarabawarki, Annabi Muhammad Sallalahu Alaihi Wassalam yafi kowa gata a gurin Allah kuma Allah yafi kaunarsa da kowa, amman a haka Annabi ya girma babu mahaifiya babu mahaifi, ni da ke banbancin kaddararmu kadan ne, ni ma na tashi babu uwa ba uba, sai dai na zamu gata, irin gatan da nake kokarin baki a yanzu, ki dauke ni a matsayin yayanki, saboda ina ganinki kamar yar'uwata ne, duk abun da zan yi ma kanwata Amal ko Leila zan miki, ki sake jikinki, zan maida ke yar gata believe me zaki zama Shalele ta ko'ina”
 
Kanta na kasa tana hawaye har ya gama magana, sannan ta dago ta kalleshi, be yi mata kama da mai karya ba, kamaninsa da cikar kamalarsa be nuna akwai gazawa a tare da shi ba.
 
Sai dai me? Matar daya ambata da sunan cewar matar da zai aura ce zata yarda? Anya ma zata jure zama a gidan tare da ita?
 
“Ina da tabbacin ba duka aka akashe yan'uwanki ba, Inshallah idan hankali ya kwanta kin samu lafiya zan muje mu nemi inda yan'uwanki suke, yanzu taso muje ki ci abinci”
 
“Ina son na yi sallah, ban yi sallah ba ana biyana salaloli da yawa, dazun ma na fara tura keken naje na yi sallah sai.... ”
 
Daga haka ta labarta masa abun da ya faru ciki har da wanda Madina tace idan ya dawo ta fada masa. Be jidadin abun da Leila tai mata ba, sai dai be nuna mata ba.
 
“Okay amman yanzu bari ki fara cin abinci ki samu kuzari, sannan muje ki yi sallah okay?”
 
Ta daga masa kai.
 
“Zulai zata zo ta tura ki bathroom ki wanke bakinki sai ta fito da ke ki ci abincin ki yanzu”
 
“Aa bana so yanzu wannan zata zo ta fara min masifa, kuma zata hana su yi min komai”
 
Ta fada kamar zata fasa kuka.
 
“Kina son na tura ki?”
 
Ta daga masa kai, sai ya mike tsaye ya dauketa ya dora a wheelchair din. Ya turata da kansa har bathroom din ta wanke bakinta.
 
“Zaki yi fitsari?”
 
Ta girgiza masa kai alamar aa. Sai ya turo ta ya fito da ita sai da suka kawo gurin kofar sannan ta kula da kofar a balle take, sai dai bata ce komai ba tana ta kallon hanyar har ya fito da ita falon. Iyakar abun da ta sani Leila ta rika kanta tana ja da karfin tsiya, bayan baka bata san me ya faru ba, sai ganinta tai ta farka daga bachi.
 
“Waya kwantar da ni kan gado dazun?”
 
“Ni”
 
Ya amsa mata a takaice sannan ya tura kujerar har gurin dinning, babu kowa a falon daga shi sai ita sai katon Plasma. Da kansa ya shiga zuba mata abincin, sannan ya mika mata. Sawun takun talkami da taji ne ya saka ta waiga ta kalli Upstairs din sai ta hango Madina da Leila suna saukowa a tare, suna hada ido da Leila tai saurin maida kanta kasa cike da tsoro. Kallo daya Talba yai musu ya dauke idonsa, kusan a tare suka kalli juna, ba Leila kadai ba har Madina ta ji zafin ganin Talba na zubawa Aminatu abincin da kansa, sai dai ta dannewa zuciyarta bata yarda ta nuna ba, duk da kasancewar Leila ta fada mata komai daya faru dazun.
 
“Amman wannan wulakancin ne, haba Talba? Taya zaka zuba mata abinci a irin plate din da muke cin abinci? Kuma ka kaita har gurin dinning?”
 
Madina ta yi saurin rike ta.
 
“Haba Leila miye haka?”
 
“Ai dole na yi magana, dazu fa har rumgumar ta yai...”
 
Tana kokarin kai hannu ta taba Aminatu data make guri daya Madina ta yi saurin rike ta da karfi.
 
“Leila miye haka wai?”
 
“Wallahi sai ta bar gidan nan, na rantse da Allah ba zata zauna a nan ba”
 
Ta fada da karfi kamin ta kwalawa Momy kira tana ihu. Uffan Talba be ce mata ba, ko kallonta be yi ba sai aikin zubawa Amina ruwa yake a cup. Kamar da gangan Madina ta saki Leila ta karasa gurin dinning.
 
“Karki taba yarinyar nan”
 
Furucin da yai mata ne yasa saka ta tsaya cak, domin bata ji wasa a muryarsa ba kamar yadda fuskarsa ma bata nuna wasan ba. Aminatu ta yi saurin sakin plate din abincin dake hannunta idonta cike da hawaye. Hango Momy na saukowa tare da Amal da Kabir yasa Leila ta dauki ruwan da Talba ya zuba a cup ta watsawa Amina.
 
“Haba Leila miye haka?”
 
Madina ta fada tana zaro ido tare da saka hannayenta ta rufe baki.
 
“You should apologize ki bata hakuri yanzu nan”
 
Talba ya fada yana nuna mata Aminatu.
 
“No Leila ta yi kuskure, amman ba zata bata hakuri ba, you're just hurting her”
 
Kabir ya fada, Momy na karasa kusa da ita ta maida Leila.
 
“Ya isa haka Talba, ba zan yarda ka wulakanta Leila akan wata banza ba”
 
“Momy kin san abun da ta yi”
 
“Be dame ni, amman ta duka ta bawa wannan musakar hakuri ne ba zata tayi ba!”
 
 
Nan da nan jikin Aminatu ya fara rawa, Talba ya kalli Momy.
 
“Wannan ba daidai ba ne Momy”
 
“Miye daidai tana yar riga kace ta bawa wata banza hakuri? Wai gata ka fi leila ne ko kuma miye?”
 
“Kuma na rantse da Allah ba zata zauna a gidan nan ba, Wallahi Momy sai dai ku zaba ni ko ita...!”
 
Leila ta fada tana buga kafa a kasa. Leila ta ji wani irin dadi, komai ya faru kamar yadda take so, duk da kasancewar bata yi zaton da wuri haka komai zai faru ba, daman ta zo gidan nan kawai saboda Leila ta kirata tana kukan rumgumar da yai ma Amina, sai dai a yanzu komai ya yafi kamar yadda take son ya tafi. Da sauri ta nufi Aminatu dake kuka taja kujerarta.
 
“Madina ki kyale yarinyar nan a gurin nan?”
 
Sai ta girgiza ma Momy kai.
 
“Dan Allah Momy ki gafarce ni, be dace ku yi wannan fada a gaban yarinyar nan ba”
 
Bata jira abun da Momy zata sake cewa ba, ta tura Aminatu zuwa corridor, a azaton Momy Madina ta yi hakan ne saboda bata son su yi fadan a gabanta kasancewar su yan'uwa.
 
“Abun da kake ba kyautawa ba ne, Talba, be kamata ba, ko a dazun ka rumgume yarinyar nan a gaban Leila kuma kasan dole zata ji ba dadi ba, and now kana kokarim feeding dinta for what”
 
Talba ya nuna Kabir da yatsa.
 
“Don't you dare tell me what is right and wrong, don't you dare judge me, this is my life waye kai da zaka kalubalanci abun da na yi?”
 
“So baka isa ka kawo wata a gidan nan just to hurt my sister in front of us? And now ba zamu zabi wata akan Leila ba, take her away”
 
Wani irin kallon kallo suke tsakanin shi da Kabir ko wane zuciyarsa ta kawo kamar ya rufe dan'uwansa da duka yake ji. Daker Talba ya samu hade numfashinsa ya kalli Leila dake tsaye sannan ya nufi corridor da zai sada shi da dakin da Aminatu take ciki. Bakin kofar dakin ya tsaya yana kallon Madina dake rumgume Aminatu tana share mata hawayenta da dankwalinta, ita ma tana kuka.
 
“Dan Allah ki yi hakuri ki daina kukan nan, ban taba rasa kowa ba, amman na fahimci yadda kike ji, akwai ciwo sosai ki kwantar da hankalinki Inshallah Talba ba zai bari ayi miki komai ba, ni kuma zan kula da ke kamar kanwata Inshallah”
 
Yadda take hawaye sai ka rantse da Allah kukan gaske take, zaka yi zaton da gasken gaske take tausayin Aminatu. A badini kuma tana yin hakan ne saboda ta ji kamshin turaren Talba ta san yana tsaye bakin kofar dakin ko ma cikin daki.
Aminatu na hada ido da Talba ta saki Amadina tana kuka.
 
“Dan Allah ka kai ni inda yan gudun hijira, ko wani gurin, bana son fada bana son fada dan Allah karka yi fada da su dan Allah...”
 
Karasowa yai cikin dakin ya risina gabanta yana kallon fuskarta, magana yake son yi mata amman ya rasa ta ina zai fara.
 
“Idan zamanta a nan zai kawo matsala, zan iya tafi da ita gidamu, Mamana bata da matsala kuma zan iya kula da ita, kamin Momy da Leila su sauko”
 
Madina ta fada muryar na rawa, a ranta tana ala ala ya amince, a hankali Talba ya juyo ya kalleta.
 
“You can trust me. Wallahi ba zan mata komai ba, tare na da Leila ba zai saka na cutar da wani ba, yarinyar nan ta cancanci rayuwa mai kyau...”
 
A nan ma Talba be ce mata komai, ya juya yana kallon Aminatu.
 
“Excuse us Madina”
 
Murmushi ne ya cika fuskarta, saboda ya kiran sunanta, kusan tun da take da Leila ba zata  iya tuna rana daya ta taji sunanta a bakinsa ba.
 

Shin kin san Kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud
Sandal flakes
Sandal wood
Signature
Kajiji
Damboun kajiji
Halud ball
Wardrobe ball
Coconut sandal
exclusive gowe
Black humra
Body milk
Kulaccam
Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin da kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya, domin siye ko sari ku tuntubi Ramla incense ta wannan number 07038392576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa
 
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
 
“Kar abun da Leila tai ya dame ki, tana da zafi ne, amman a sannu zata fahimta ta daina”
 
Aminatu ta saka hannu ta share hawayenta, wasu a sauko mata.
 
“Komai be da sauki a rayuwar duniya, komai ka sara yana da wahala ka samu abun da zai maye maka gurbinsa, rayuwarmu da ta ku akwai banbanci, kuma tana da gaskiya, ni yar kauye ce marar gata wanda bata waye a komai ba, ba kamar ni ba talaka kuma yar kauye, be kamata na zauna a mazauninsu ba, ko kuma na ci abincin a inda suke so, muna da banbanci mai nisa a tsakaninmu”
 
“Ban taba ganin wannan banbanci ba, ban taba jin cewar Leila ko ni mun fiki ba saboda dukiya, ita ma kuma kurciya ce ke janta”
 
“Idan ita kurciya ce, Momy fa?”
 
Yayi shiru kamar mai tunanin abun da zai ce

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login