Showing 231001 words to 234000 words out of 332834 words

Chapter 78 - Bakar wasika Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

65599

da ni ba, daman ta dade tana min wannan maganar, sai dai bata taba min fada sosai kamar dana fada mata cewar iyayenki sun ce na turo ba”
 
Baturiya ta ji gabanta ya fadi.
 
“Akwai wani abu ne daya saka ta tsane ni ko kuma bata son aurena da kai?”
 
“Bana tunaninka, akwai dai saboda tana kawo min yan'uwa da yayan abokanta ni kuma ban yi na'am da ko daya ba, yanzu kuma na gabatar mata da wanda ba zabinta na ce ita nake son aure”
 
“Amman kana jin zata amince?”
 
“Zata amince, saboda tana son abun da nake so, kuma idan har ta yi bincike bata ga wata matsala a tare da ke ba ba zai hana ta amince ba, Abbah zai tsaya min”
 
Ta sake jin faduwar gaba.
 
“Shiyasa a daren nan kace min idan ka koma zaka bata mu gaisa, ina ta jira baka kira ba, tun lokacin zuciyata ta raya min akwai matsala”
 
Idonta ya cika da hawaye.
 
“Ki daina kuka komai zai wuce, ki yi ta addu'a kuma ki sani cewar ina kaunarki, no matter Fee'at”
 
Har cikin zuciyarsa yake wannan maganar da ita, domin yana sonta sosai kuma yana jin cewar abun da aka fada masa ba zai saka ya ki aurenta ba sai idan Mahaifansa ba su amince ba. Dagowa tai ta kalleshi.
 
“Kamin wani alkawari Fahat”
 
Yayi shiru yana kallonta. Sai ta kama hannunsa ta rike hana hawaye.
 
“So nake ka min alkawari ba zaka taba rabuwa da ni ba, ina son ka yi min wannan alkawarin Fahat”
 
Ya kurawa hannunta ido yana kallo, ya kasa cewa uffan har na tsawon lokaci, hawaye sai sauko mata suke tana kallonsa tana son ya amsa mata.
 
“Fahat...”
 
Sai ya janye hannunsa daga rikon da tai masa, ya kawar da fuskarsa.
 
“Fahat...”
 
Ta kira sunansa da mugun mamaki.
 
“Idan har mahaifiyata ta dage akan cewa ba zan aureki ba, to bani da wani zabi daya wuce na barki, amman bayan haka bana ji akwai wani dalili da zai saka na guje miki, kuma ina son ki san cewa ina kaunarki sosai”
 
Ta share hawayenta ta bude motar ta fita, da kallo ya bita har ta shige ciki gidan sannan ya dora kansa saman sitiyarin motar. Fata kawai yake abun da abokinsa ya fada masa ya zama ba gaske ba, duk kuwa da ya san abokinsa ba zai masa karya ba, amman miyasa zata boye masa abu mai muhimmanci irin wannan? Why? Ko tana ganin kamar idan ya sani ba zai aureta ba ne? Wata kila tana jin tsoron rasa shi ne, kamar yadda shi ma yake jin tsoron rasata a yanzu domin abu ne mai wahala iyeyensa da yan'uwansa su amince masa ya auri bazawara a halin yanzu. Ya dade a kofar gidan sannan ya buga motarsa yai reverse ya fita daga unguwar, rasa abun da ke masa dadi, domin tun da yake a rayuwarsa be taba jin son mace ba kamar yadda yake son Baturiya, duk macen da aka kawo masa bata masa sai Baturiya, yanzu kuma wannan matsalar ta bullo bayan ita da shi duk sun kamu da son junansu, da ace ta tun farkon haduwasu ta fada masa komai da zai gina soyayarsu ne akan haka, kuma zai gabatarwa iyayensa da ita a matsayinta na bazawara, amman a yanzu iyayenta da shi kansa duk suna mata kallon budurwa ne, har sai da binciken da binciken daya saka abokinsa ya tabbatar masa da haka, a yanzu ya gane da wannan Mommy take masa shagube, wata kila ita ma tayi nata binciken ta gano haka. Sai dai shi ya kasa nunawa Baturiya cewar ya sani, ita kuma ta ki ta fada masa komai.
Misalin tara da rabi ya faka motarsa harabar gidan, sannan ya bude ya fito kamar marar lafiya haka yake tafiya, har ya iso kofar falon dake bude ya shiga ciki, saman sofa ya fara zama sannan ya tashi ya nufi dakin mahaifiyarsa. Da sallama ya shiga ta amsa masa ta kalleshi tana aje plate din hannunsa, sai ya zauna kusa da ita cikin yanayin damuwa.
 
“Kin yi magana da Abbah?”
 
“Muhammad Fahat, daga shigowarka babu gaisuwa babu komai sai tambayar na yi magana da mahaifinka?”
 
“Na ga yau kwana kusan uku da yi miki maganar nan”
 
“Amman na ce maka kaje na kara bincikar yarinyar nan ko? Kamin ka gabatar da ita gurin mahaifinka ya kamata ka san wacece ita”
 
“Na san wacece ita Mommy, kawai dai baki son ta ne saboda bata daya daga cikin yan matan da kike zaba min”
 
“Ba ko daya, kawai dai yarinyar bata dace da kai ba ne, saboda ta taba aure idan ma baka sani ba bari na fada naka, ni na saka ayi min bincike akanta”
 
Yayi murmushin karfin hali.
 
“Daman abun da kike nufi kenan da ta taba aure? Ai na san bazawara ce”
 
“A can kam baka sani ba, ai baka taba nuna min cewar bazawara ba ce, sai yanzu da kai naka bincike aka tabbatar maka da haka ko? Ko kuma ta gaji ta fada maka, kuma duk da haka ka dage kana son aurenta, to bari na ji na fada maka, in dai ni na haifeka ba zaka auri yarinyar nan ba, sai kace wanda akai wa baki, kana saurayinka matashi ka auri bazawara mata har da danta, ance ma da ciki ta fito gidan wacan mijin”
 
“Mommy duk be dame ni ba, ina son ta tana so na, ba ni da matsala da wannan”
 
“To na fada maka ba zaka aureta ba, kara ma ka rabu da ita tun wuri”
 
Mahaifiyarsa ta fada cikin tsawa, sai ya mike tsaye yana kallonta cikin damuwa.
 
“Idan kin dage na rabu da ita zan rabu da ita Mommy, amman Wallahi ba zan taba son wata ba”
 
Ta juya ya fice daga dakin cikin bacin rai.
 
 
 
_______________________________
 
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
 
FARUK POV.
 
Washe garin ranar aka kai Sultan asibiti tare da Mama. Sai dai kowa bangarensa dabam, kanwarsa da wata yar'uwar Mama suka rakata, shi kuma ya kai dansa bangaren yare a Yariman Bakura. Sultan magani kawai aka rubuta masa da allurar ya dawo da shi. Mama kuma suka bata gado saboda yanayin jikinta. A wajen asibitin ya siye magani suka rubuta masa yadda ake amfani da shi, sannan ya wuce tare da Sultan asibiti da akai Mama domin ita private hospital aka kaita. A wajen asibitin ya tsaya sai da ya kira Maman Safiyya ta fada masa inda suke sannan ya karaso yana dauke da Sultan. A harabar asibitin ya sami Maman Safiyya zaune tana hira da wasu mutane dake kusa da ita. Karasa yai da sallama ya gaishe da mutanen sannan ya zauna a gurin.
 
“Ya jikin Mama”
 
“Da sauki amman sun bata gado tana can ciki”
 
“Okay bari na duba ta”
 
Ta mike tsaye sai ta mika hannu ta karbi Sultan din dake kafarsa, a take Sultan ya juya baya.
 
“Zo nan Sultan, ya jikin naka”
 
“Na ji sauki, ba zan sauko ba”
 
Daga mahaifinsa har mutanen dake gurin sai da suka yi dariya, Sultan akan a bakin gaskiyarsa ba zai sauko ba, domin ganin yake idan ya sauko Faruk zai sake yin tafiya ne ya bar shi, a dole Faruk ya shiga ciki tare da shi. Katon daki ne da aka jera gadajen marasa lafiya a ciki, sai dai ko wane tsab kuma an saka curtains an zagaye kowane gado sai idan kana ra'ayi zaka bude, sai dai kasan cewar rana da dan daga kowane gado an bude shi ga likitoci sun shigo suna duba mutane, yana tafe yana duba dama da hagu har ya ha hango mahaifiyarsa ya kwance ana saka mata ruwa. Rukaiya na zaune daga gefe tana rumtse ido, sallama yai murya kasa kasa ya karasa Nurse din da amsa masa da murmushi a fuskarta, sannan ta aje hannun Mama a hankali bayan ta gama.
 
“To bude idon sarkin tsoro, ashe ba zaki iya aikin asibiti ba”
 
Nurse ta fada, sai Rukaiya ta bude idon tana murmushi.
 
“Gaskiya ba zan iya ba, ina da tsoro sosai”
 
“Aiko aikin lafiya yana da kyau mace tai shi, domin ana karuwa da ita, kuma ko ba komai yana mata kyau”
 
Ta fada da yar siririyar muryarta, sai Faruk ya karasa mata yana murmushi.
 
“Musamman irinki”
 
Kallonsa tai tana murmushin daya bayyana dimples dinta.
 
“Na gode, bari na kira Doctor”
 
Ta sadda kai kasa ta nufi hanyar fita daga gurin.
 
“Doc na gama”
 
“Okay”
 
Doc ya fada, ya cigaba da duba file din da yake na wata patient din sai da ya gama sannan ya dawo inda Mama take, Doc ya mika masa suka gaisa.
 
“Ya akai kuka yi sake har hawan jininta ya kai haka? Na tambayi wannan ta ce kun san tana da shi, amman ba ku yi komai ba har ya kai haka?”
 
“Gaskiya mun san tana da shi, amman ni ban san abun ya kai haka ba saboda bana kusa, kuma babu kuwa a kusa da ita sai wannan ita kuma ba wani hali da ita ba, shiyasa abun yai tsamari haka, amman dai ina fatar zata samu lafiya?”
 
“Inshallah, zamu dorata a kan magani, kuma ba ma son ku yi wasa da shi, sannan za a rika yi mata gaji, akwai takardar magani, a je a nemo maganin”
 
Rukaiya ta mike tsaye tana kallon Kabir da dan tsoro da kuma faduwar gaba.
 
“Amman dai likita zata samu lafiya ko?”
 
Doc yayi murmushi.
 
“Zata samu lafiya Inshallah”
 
“Za a nemo maganin yanzu, amman likita akwai dakin da ake kai mutane na zaman mutum daya?”
 
“Eh akwai”
 
“Ina bukatar a kaita a can dan Allah”
 
“Okay”
 
Doc ya fada sannan ya fice daga gurin, Rukaiya ta matsa jikin kujerar Faruk ya zauna Sultan na jikinsa.
 
“Sannu Mama”
 
Ya fada cikin damuwa, sai ta sakar masa murmushi.
 
“Ka dawo? Ya jikin Sultan din”
 
“Da sauki sosai, magani suka rubuta masa, zan bar shi sai na siyo maganin tukuna”
 
“Aa Dady aa”
 
Sultan din ya amsa sa kansa yana kara rike Faruk.
 
“Ba wani garin zanje ba, dawowa zan yi, magani kawai zan yi ma Mama”
 
“To kaje da ni”
 
“Aa zaka zauna gurin Maman Safiya ko Mama Rukaiya sai su baka magani”
 
“Dady karka tafi ka barni Momy ta tafi bata dawo ba, kai ma sai ka dade kake dawowa”
 
Ya fada yana fashewa da kuka, sai Faruk ya rumgume shi yana kallon Nurse din data dawo.
 
“Likita yace za a canja muku daki”
 
“Eh”
 
“Okay, amman fa akwai tsada”
 
Ta fada tana murmushi saboda ganin yanayinsu kamar ba za su iya biyan kudin dakin ba, sai Faruk yai mata murmushi.
 
“Karki damu ko nawa ne a kai, tun da kika ga mun zo asibiti mai zaman kanta ai kin san mun shirya”
 
“Haka ne”
 
Ta fara kokarin cire mata drip din, wata Dattijuwa ce sanye da uniform din masu aikin asibitin ta shiga da Wheelchair, sai Nurse din ta rika Mama ita da Rukaiya suka zaunar da ita saman kujerar, Dattijuwar ta soma turata, sai Faruk ya sauke Sultan kasa ya karbi matar ya soma tura Mama, ita kuma Nurse din ta mikawa Dattijuwar files din Mama da drip din, Rukaiya na kokarin daukar Sultan da ya fara kuka sai ta rigata ta saka hannu biyu ta dauke shi.
 
“To yi shiru kyale Daddy, ya sauke ka?”
 
Sultan ya daga mata kai.
 
“Tafiya zai yi ya bar ni, ba zai dawo ba sai an dade”
 
“Saboda me?”
 
“Ni ma ban sani ba, Momy bata dawo ba, kullum Mama tana cewa zata zo bata zo ba”
 
“Miyasa bata dawo ba”
 
Ta tambaya tana dariya, ta kalli Rukaiyah.
 
“Ina mamansa? Ko ta...”
 
Sai kuma ta kasa karasawa, a tunaninta ta rasu ne kuma ba a son a fada masa ne.
 
“Tana nan”
 
Da mamaki Nurse din ta ce.
 
“Miyasa ba a kai shi gurinta? Ba a gari daya suke ba?”
 
“A gari daya suke”
 
Ta dan rage tafiyar da take saboda Faruk yai nisa da su sosai.
 
“Bata da lafiya ne?”
 
“Kina da son tambaya”
 
Rukaiya ta fada tana murmushi, ita ma murmushin tai ta gyara Sultan.
 
“Rabuwa suka yi ba irin wanda ake so ba, domin ta guje shi saboda ba shi da kudi wai ba zata iya zaman talauci ba, abun bakincikin kuma yar'uwarsa ce ta jini”
 
Nurse din ta tsaya cak tana kallon Rukaiya da mamaki.
 
“Da gaske?”
 
“Wallahi, kuma tun da suka rabu bata sake zuwa ta duba danta ba, shiyasa muma ba mu damu mu kai mata shi ba”
 
Ta kalli Sultan cike da tausayi kamin ta maida duban gurin mahaifinsa dake kokarin shiga corner.
 
“Amman ya kike da shi yaron nan?”
 
“Dan dan yayana ne, ni ce auta a gidan mu, shi ne Babba sai yayata da akai wa aure kwanakin baya”
 
“Allah sarki, ni kuma ni ce ta farko a gidanmu Babana yana so na sosai”
 
Sai duk suka saka dariya, sannan suka cigaba da tafiya. Sai da matar da duba dakin da babu kowa sannan ta shiga ciki Faruk ya bi bayanta, da kansa ya dauki mahaifiyarsa ya dorata a saman gadon, sannan nurse din da shigo tare da Rukaiya, sai a sannan ta sauke Sultan kasa Faruk ya kalleta.
 
“Wai daman daukarshi kika?”
 
“Eh mana so kike yayi ta kuka? Ka aje shi kana dutyn wata, ni ma ai dole na yi naka”
 
Faruk yayi murmushi.
 
“Mahaifiyata ce”
 
“To sannu mai uwa, Mama kina jin shi ko?”
 
Mama ta yi murmushi, Nurse din ta karbi Files din dake hannun Dattijuwar ta aje su a muhallinsu sannan ta shiga dorawa Mama drip.
 
“Ashe kana da karfi, dan dai na san kai ka dora Momy a nan”
 
Ta fada ba tare data kalleshi ba, sai yai murmushi ya kama hannun Sultan.
 
“Ke yanzu kya kalli majiyi karfi irina ki ce ina da karfi”
 
“Ji yadda kake magana kamar wani Jarumi, Ke yanzu kya kalli majiyi karfi irina ki ce ina da karfi”
 
Ta karasa tana kwaikwayar muryarsa har da wani yatsina fuska take. Murmushi yai, Mama ma murmushin take tana kallonsu.
 
“Rukaiya bani takardar maganin”
 
Rukaiya ta mika masa da sauri sai ya karba.
 
“Akwai abun da kuke bukata?”
 
“Eh zan je na fadawa Maman Safiyya an canja mana daki, kuma ta zo ta zauna da Mama zan je gida na dauko kayan shimfada”
 
“Okay zan taho da abinci idan zan dawo”
 
Kamin Rukaiya tace komai, Nurse din data gama daurawa Mama drip ta kalleshi.
 
“To sannu acici mala'ikun tauna, ita dai maganar kayan shimfida tai ba na abinci ba”
 
Da kamar mamaki Faruk yake kallonta, wata kila fuskar yara ta gani a nasa fuskarsa shiyasa take masa zolaya any how. Girgiza kai yai ya fice ba tare da ya sace cewa komai ba, sai ta bishi da kallo tana murmushi, bayan ya fice ta saka hannunta aljihu ta ciro karamar wayarta kalli Rukaiyah.
 
“Saka min number mu rika gaisawa ko?”
 
“Ai ba ni da waya”
 
“Kamar ke za a ce baki da waya?”
 
“Allah da gaske nake”
 
“To ki saka min number Mama ko wani wanda zan iya kiranki mu gaisa mana”
 
“Mama bata da waya yanzu, sai dai Ya Faruk”
 
“To saka min, idan na kira sai nace masa ya bani ke mu gaisa, Rukaiyah ko?”
 
“Eh”
 
“Ni kuma Sunana Ramla Isma'el”
 
“Allah sarki”
 
Ta karbi wayar ta saka mata number, sannan ta mika mata.
 
“Ni zan tafi gida na gama aikina na yau, sai kuma gobe”
 
“Okay to Allah ya kai mu”
 
Ramla ta kalli Mama
 
“Mama zan tafi Allah ya sauwake”
 
“Amin Ramlatu mun gode”
 
Ta juyo ta kalli Mama tana wara ido.
 
“Laa haka Mamana take kirana Ramlatu”
 
Mama ta yi murmushi, ta bita da kallo cike da burgewa har ta fice.
 
“Tana da far'a da son mutane”
 
Rukaiya ta fada, sai Mama tai murmushi.
 
“Ni ma na lura da haka, tana da saukin kai”
 
“Mama bari na tafi gida na dauko kayan kar rana da kara yi, gashi ko abun sallah ba mu da shi”
 
“To sai kin dawo”
 
Ta fice daga dakin, Mama ta gyara kwanciyar ta lumshe tana murmushi.
 
 
 
BATURIYA POV.
 
tun da ta shigo dakin take ta kuka taki ta fadawa kowa abun da yake faruwa, kamin safe idonta ya kumbura har bata gani sosai da shi. Tana yin sallah asuba ta koma ta kwanta wai ko zata samu tai bachin da bata yi ba jiya, amman ina damuwar abun da ya faru jiya ya hana ta rumtsawa ta rufe idon kawai amman babu alamar bachi ma a kusa da idon nata. Sai da ta gaji da kwanciyar sannan ta tashi zaune wasu sabbin hawayen na sauko mata, har kusan sha daya na safe bata fito daga dakin ba, kanwarta har ta shirya ta tafi makaranta. Ganin haka yasan Umma ta leka dakin tana kiran sunanta.
 
“Rafi'a Lafiya kike yau kuwa? Har rana baki fito ba?”
 
Baturiya ta daga ido daker ta kalli Umma, a lokacin ne hankalin Umma ya tashi domin fuskarta ta kumbura sosai idanuwanta ma sun ciko kamar an busa su. Zuwa tai ta zauna kusa da ita tana kallonta.
 
“Subhanallahi me ya same ki?”
 
Kamar tace bude baki ki fara kuka sai kawai ta fashe da kuka ta kwanto jikin Umma.
 
“Ba kuka zaki yi ba, bude baki ki fada min abun da yake damunki mana”
 
Sai da tai kuka ta gaji sannan ta share hawayenta ta soma magana cikin kuka.
 
“Umma Fahat din da nake fada miki na tsayar har na fada masa ya turo iyayensa ba zai aure ni ba?”
 
“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, saboda me?”
 
“Mahaifiyarsa bata so na...”
 
“Ko dai ta gano kin tana haihuwa ko? Abun da kike ganin kamar ba za su gane ba yanzu sun gano ko?”
 
“Ba su gano ba ai da ya min maganar, kawai dai daman can ya taba fada min tana kawo masa yan mata yace baya so sai da ya hadu da ni”
 
“To Allah ya sauwake, auren da uwar miji bata so ko anyi shi ba dadi yake ba, kuma duk yadda kike gani da tunanin zaki iya boye cewar baki tana haihuwa ba, ba zai boyu ba, saboda a garin nan kike kuma agarin nan kika haihu, mutane da tsegumi, ni sam bana ganin haka a matsayin wata dabara, ba mafita

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login