Showing 255001 words to 258000 words out of 332834 words

Chapter 86 - Bakar wasika Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

65620

paper ya mikawa Talba yana kallon Aminatu dake ta kuka shagwaba, sai dai ganin Ali yasa ta rage sautin kukan.
 
“Me akai mata?”
 
“Ka san ita da Momy basa shan inuwa daya”
 
Talba ya amsa masa.
 
“Make sure ka ci wani abu kamin na dawo, sai ka sha magani akwai allurar da za a maka”
 
Kai Talba ya daga masa, shi kuma ya juya ya fice. Talba ya dago kanta cikin rashin karfi jiki yana kallon fuskarta.
 
“Duk wannan kuka na fadan Momy”
 
“Ba na Momy kadai ba har da na wannan matar da ta dake ni a kafada”
 
Yayi murmushi yana ayyana yadda kuka baya mata wuya, abu kadan sai hawaye, ko da yake daman masu yawan shiga damuwa kukansu a kusa yake, kana taba su za su fara maka kuka kamar jarirai. Tissue din ya zara ya fara goge mata fuskarta.
 
“Yi hakuri, ba su sake ba ai kin ji Daddy ya musu magana ko?”
 
Ta turo baki gaba wasu hawayen na sauko mata.
 
“Miyasa Momynka bata so na wai?”
 
“Momy tana sonki mana, kawai dai ranta ne ya bace saboda abun da ya faru”
 
Ta kai hannu ta murza idonta.
 
“Ka kira min Mama”
 
Ta fada tana kara kwantawa jikinsa kamar kyanwa, sai ya rumgumeta ya dora wuyansa gurin kanta. Ko bata ce masa Hajiya Laraba ba ya san ita take nufi domin ita take kira da Mama kamar yadda yayanta suke kiranta. Da karfi Leila ta turo kofar dakin ta shigo cikin da annashuwar kiran da Momy tai mata ta fada mata cewar Talba ya farka, hakan ya sa ta dawo asibitin da sauri. Sai dai a yadda ta tararda Aminatu da Talba ya saka hankalimta ya tashi kuma ranta ya bace sosai, sai ta nemi farincikin farkawarsa ta rasa. dan dagowa yai daga jikin Aminatu saboda ya san zata ji ba dadi, shi kuma be shirya batawa kowa rai ba a yanzu.
 
“Talba miye haka?”
 
Ta tambaya muryarta na rawa, sai Aminatu ta juyo ta kalleta.
 
“Taya zaka maida kanka wani iri kana hada jiki da wannan yarinyar? Kalleta ba Wallahi ba ajinka ba ce, gaba daya an bi an magance ka baka ganin komai sai ita, dubi halin daka jefa kanka all because of this stupid girl, yarinya karama ta canja ka Talba jikinka mai tsada kake bari wannan kazamar yar kauyen tana tabawa, gaba daya an canja ka Talba, yarinyar nan ta mallakeka”
 
Aminatu ta daga jikinta daga jikin Talba, tana kallon Leila, daman tana bata gama huce haushin abun da Momy da Hajiya Sadiya sukai mata ba, ita kuma ta zo zata kara mata da nata.
 
“Idan asiri gaskiya ne ai sai ki je yi, baki san ma na mallake shi ba sai na hana shi aurenki, kuma kauye ai kowa salinsa kauye ne”
 
Boom! Wannan karon Leila ce ke mamakin jin furucin Aminatu ba Talba ne, he was shocked ace kalaman nan daga bakin Aminatu suka fito, how? Yaushe tai baki haka? Bata ma jin tsoron. Ya kalli Leila da tai shiru tana wani irin cika kamar zakanya, sannan ya kalli Aminatu still yana mamaki.
 
“So you can talk”
 
Leila ta kalleshi da mugun takaici.
 
“What do you mean she can talk? Are you supporting her? Taya kana kallon karamar yarinya kamar wannan tana fada min magana without doing anything?”
 
Hawaye ya sauko a idonta.
 
“I'm not supporting her, ke kika fara fada mata magana marar dadi and ta rama, na ce na goyi bayanta?”
 
“Thank You”
 
Ta furta tana murmushin daya fi kuka ciwo sannan ta juya zata fice, sai ya kirata da sauri.
 
“Leila...”
 
Bata amsa ba balle ta juyo ta kalleshi ma, ta fice dakin cikin bakinciki da bacin rai. Talba ya kalli Aminatu cikin rashin jindadin yadda Leila ta fita dakin.
 
“You shouldn't talk to her this way Babe, be kamata ki fada mata haka ba”
 
Kamar mai jira nan da nan nata idon ya cika da hawaye.
 
“Ni me na mata da take fada min magana? Ita da mahaifiyarta me na tare musu? Kana jin tana ce min yar kauye kazama”
 
Ya daga kansa sama yana sauke numfashi.
 
‘Oh ya Allah’
 
Ya furta a ransa sannan ya mika mata hannunsa, sai ta nade hannayenta ta matsa baya tana turo baki, hawayen har ya fara sauko mata, wani zafi ma take jin zuciyarta na mata saboda ya shigarwa Leila.
 
“Ni ka kira min Mama, ta zo ta tafi da ni”
 
Sai ya sauko a hankali saman gadon ya mike tsaye, ya karasa inda take cike da karfin hali ya rumgumeta.
 
“Yi hakuri. Kin ga babu waya tare da ni, bari Ali ya shigo ko Kabir na tambaya waya dauki wayata sai na kira miki ita, amman kamin nan yanzu ina son ki hada min tea na sha, sai ki zuba min abinci gashi nan a cooler. Zan wanke bakina”
 
“Toh”
 
Ta amsa cike da shagwaba, murmushi yai ya sake ta, ba karamin burge shi take ba idan tana masa shagwabar, ko ba komai hakan da take tana nuna masa shi ne gatanta, kuma shi ne wanda zai iya share mata hawaye, kuma ya fahimci damuwarta, daman mace da shagwaba aka santa, ba kamar namiji ba. Ya fara takawa cike da karfin yana jin kirjinsa kamar zai rabe gida biyu, sai dai baya son nunawa kar ta gani hankalinta ya tashi. Sai ya shiga bandaki ya rufe sannan ya ya dafe kansa ya durkushe a kasa ya cige bakinsa, alamar yana jin azaba sosai. Sai da ya lumshe ido ya bude a hankali sannan ya yunkurin ya tashi yana ambaton Allah a zuciyarsa ya karasa gurin da tub din yake.
 
 
*** **  ***  **  ***
Leila ta nufi inda su Momy suke zaune tana hawaye ta zauna tana jin kuka na son kwace mata, bata taba sanin haka take kishin Talba ba sai yau, ji tai kamar ace tana da wuka a hannunta ta yanka naman Aminatu.
 
“Ke Lafiya”
 
Hajiya Saratu ta tambaya.
 
“Mama ina shiga dakin nan na same ta rumgume da shi, na yi magana har tana cewa wai ta yi asirin sai ma ta hana shi aurena, imagine yar kauye kamar wannan zata fada min magana”
 
Momy ta saki baki da mamaki.
 
“Ashe yar iska ce? Ita Aminatun ta fada miki haka? Shi Talba yana nan, ita wannan yarinyar har ta samu baki?”
 
“He take her side”
 
Ta amsa tana share hawayenta. Hajiya Saratu ta tabe baki.
 
“Hmmm ai raba kanki da yan kauyen nan, ai idan suka shiga birni sun fi yan birnin iskanci, da nuna isa, ko kishi kike da yar kauye sai a fi sonta da ke, ai yan kauyen nan kwace miji suke yi,duk wata kirsa da kisisinar shiga zuciyar miji sun sani, kuma basa barin zama banza ai”
 
“Tab di jam, Leila ba karamin aiki ke gabanmu, tun yanzu kenan? Me kike tsammani a gaba?”
 
Momy ta fada, sai Hajiya Saratu tai kwafa.
 
“Ki bar komai a hannuna, Wallahi wannan bokan ya iya aiki, shiyasa ma nake son Leila ta tafi ko miye zai mata yayi mata abubuwa su fara tafiya yadda muke so, ya fada min da bakinsa cewar da Ja6a ma zai yi aikin, kin san ko yadda Ja6a take da wari dole ma zai rabu da ita”
 
“Yauwa haka muke so”
 
Cewar Momy, sai Leila ta sake share hawayenta tana kallon Hajiya Saratu.
 
“Minene Ja6a Mama Sadiya?”
 
“Wata abu ce mai shegen warin tsiya, zaki ganta kamar 6era amman ita wari ne da ita sosai, ba a son tana ra6ar mutane ne ma saboda warinta”
 
Leila ta dan shinshina jikinta.
 
“Amman fa ni ina jin wani wari, marar dadi ni ban ma taba jin irinsa ba, ko dazun sai da na yi wanka sannan na daina jinsa, sunan Aminatu kika bada ko nawa?”
 
Daga Momy har Hajiya Saratu kallon Leila suke da mamaki.
 
“Tun kwanan baya na fara jinsa, ina jin yau kwana biyu ko uku kenan warin har hawan kaina yake...”
 
Leila na kai aya kiran Madina ya shigo wayarta dake hannunta, sunan Madina na appearing gaban Leila yai mugun faduwa.
 
 
 
 
 
_______________________________
 
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
 
Mikewa tai tsaye ta nufi wani bangare na asibitin dake nesa da su Momy ta yadda ba za su iya jin wayarta da Madina ba..
 
“Now what?”
 
Madina ta yi murmushi tana gyara kwanciyarsa saman gado.
 
“Kawata kenan, kawai na kira ne na gargade ki, karki kuskura kowa ya ji maganar da muka yi”
 
“Kina magana kamar kin manta wacece ni Madina, kina tunanin zaki iya juya ni yadda kike so ne?”
 
“Na san wacece ke mana, Leila Mu'azu Shimkafi, kin yi wasa da damarki ne, shiyasa na ke taya ki jefa kwallo a raga, your destiny is in my hand now”
 
“Abun mamaki, wai Madina ce yau take min maganar, kina wasa da wuta a hannunki ba tare da kin sani ba”
 
“Ke ce dai kike wasa da wutar, kin san babu yadda za'ayi rayuwata ta lalace na cire rai daga samun abun da nake so, kuma ke da kika haddasa komai na saka miki ido, at least we're friends ai, ya kamata ace idan na fadi ke ma ki fadi”
 
“Duniya tana bani tsoro wani lokacin ace abokiyar da kuka ta so tare tun kuna yara, rana daya ta koma makiyiyarka”
 
“Duniya tana cike da abubuwan mamaki kala kala Leila, a cikin akwai aure Talba da Aminatu tai, ga kuma butulce min da kika, a tunanina, a yadda muke da ke, idan kika fahimci ina son Talba zaki iya yafe min shi, ko da a munafurce ne, sai gashi kin bani mamaki, a lokacin ne na kara fahimtar cewar abotar da nake da ke, akwai yaudara a ciki”
 
“Yaudara ta wuce wanda kika min? Wata kila da auren Talba nake still zski kulla soyayya da shi a waje?”
 
“Ban kira saboda mu yi irin wannan maganar ba, na kira ne kawai na gargadeki”
 
“Miyasa kike jin tsoro? Ashe ma ke karamar yar iska ce”
 
“Ina jin tsoron yadda duniya da yan'uwanki zasu kalleki idan na fallasa wannan sirrin naki”
 
“Ba ni kadai duniya zata kalla ba, har da ke”
 
“Iyakar abun da duniya zata ji akaina, shine na ci amanar kawance mun, ke kuma fa? Yar aikin gidanku kin binne gawarta tare da Mahaifiyarki ba tare da sanin kowa ba”
 
Leila ta yi murmushi.
 
“Madina kenan, idan kina son asirinki ya rufu ba sai kin tona nawa ba, zaki iya fadawa Mutanenki su nisanta daga inda Aminatu zata gansu, ko kuma ma su kasheta, ke da su hankalinku ya kwanta, kin ga babu wanda ya san kin aikata haka sai ni,  ni kuma ba fada zan yi ba”
 
Madina ta yi shiru tana nazari, kamin ta tashi zaune ta girgiza mata kai kamar tana gabanta.
 
“Kina ta kokarin kakaba min abun da ban aikata ba, saboda ni da ke mu zama masu laifi daya ko? Ni ban dauke Aminatu ba, ban kuma san wanda ya dauke ta ba, babu wasu mutane da nake aiki da su da zasu dauketa”
 
“Madina kar mu yi haka mana, a dare da abun ya faru ina gida, Momy kuma bata san da maganar auren ba, balle a zarge ta, haka ni ma. Sannan a daren Talba yace mota ta haska su, shiyasa saka ya zo gida yana zargina da Kabir, ni kuma ban fita ba a ranar, babu kuma dalilin da zai saka Kabir yai masa haka, saboda Kabir ba son Aminatu yake ba, balle ya dauke Aminatu dan kar ta auri Talba, haka kuma, ba kyamar aurenta yake da Talba balle ya dauke ta gudun kar Talba ya aureta. Sannan da kika sace ta kika rasa yadda zaki da ita gudun kar asirinki ya tonu sai kika yi amfani da Mutanenki kika saka suka turawa Kabir sako, saboda Talba ya zarge shi kin ga ke kin fita kenan, saboda kin san yana zargina da Kabir. Kin iya game Leila kuma na jinjina miki, sai dai kuskuren da zaki yi a yanzu shi ne na wasa da damarki ki tonawa kanki asiri”
 
Madina ta ji gabanta yayi mugun faduwa, sai dai bata yarda ta nuna ba.
 
“Abun da kika tsara a ranki kenan? What if akwai wani mai son ganin bayan Aminatu ko Talba? Waya sani ma ko ke da kanki mai maganar akwai hannunki a ciki? Na kira ne kawai na gargade ki karki yarda ki fadawa kowa maganar da muka yi, kuma idon yana kanki daga yanzu, and don't forget the rules idan baki son asirinki ya tunu”
 
“Rules?”
 
“Yeah, ko har kin manta? Ban fada miki ki janye zancen aurenki da Talba ba?”
 
Leila ta buga wani uban tsaki ta kashe wayar. Sai Madina ta mike tsaye tana kwafa.
 
“Okay kashe min waya kika yi”
 
Tana fadar haka ta dago da sauri ta kalli kofa jin an turo kofar an shigo. Hajiya ta tsaya jikin kofar tana kallon Madina cike da zargi, ita kanta ta san kalar kallon da Hajiya take mata a yau ba irin na kullum ba ne.
 
“Da wa kike waya?”
 
Ta sauke numfashi a hankali ta yadda Hajiya ba zata ji ba sannan ta ce.
 
“Wani abokin aikina ne”
 
“Abokin aikinki? Madina me kike kokarin aikatawa? Ko kuma na ce me kika aikata?”
 
“Babu komai Hajiya, kin ji wani abun ne na dabam?”
 
Hajiya ta maida kofar ta rufe ta nufo inda take ciki tsawa.
 
“Karki maida ni karamar yarinya mana Madina, ina tsaye jikin kofar nan ina sauraren duk abun da kike fada”
 
“Wata kila ba ki ji da kyau ba ne Hajiya, amman ni babu wanda na yi ma komai, kawai dai ina waya da abokin aikina ne?”
 
“Leila ita ce abokin aikin? To yayi kyau”
 
Hajiya na fadar hakan ta juya ta fice daga dakin, sai Madina ta dora hannu a goshinta tana jin wani gumi na taso mata.
 
“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un”
 
Ta fara safa da marwa a dakin tana tunanin abun da zata fadawa Hajiya ta wanke kanta.
 
“Gaba daya ta ji abun da ta fada ko kuma wani ta ji?”
 
Ta dora duka hannayen saman kanta, jefar da wayar tai saman gado ta nufi kofar fita da sauri ta bude kofar ta fita, falon ta fara dubawa bata ga Hajiya ta nufi kitchen nan ma bata ciki, sai ta juyo ta nufi dakinta, sai ta isa gurin kofar dakin gabanta ya tsananta faduwa. Juyawa tai zata koma sai kuma ta juyo ta mika hannu ta bude kofar, can kuma ta dauke hannu tunanin yadda zata wanke kanta take, ta san idan bata fada ma Hajiya gaskiya ba, zata kara jefa kanta cikin wani ramen ne. Cike da karfin hali ta tura kofar ta shiga gabanta na faduwa, ko sallama kasa yi tai not just her heart ilahirin jikinta ma rawa yake. Ta karasa kusa da Hajiya ta zauna tana kallonta. Hajiya ta hade rai ko da wasa bata dago ta kalli inda Madina take zaune ba.
 
“Hajiya...”
 
“Idan kin san kin zo nan ne saboda ki min karya ki tashi tun yanzu ki bani guri”
 
Hajiya ta fada ba tare da ta kalleshi ba, sai da Madina ta kalli wayar da Hajiya take tabawa sannan ta ce.
 
“Gaskiya zan fada miki Hajiya, ba abun da kike zargi ba ne, da gaske da abokin aikina nake waya”
 
Hajiya ta kalleta
 
“Idan ma wani abun ne, ki fada tun da wuri, saboda mu yi tifkar hanci. Kurciya na damunki kina neman jefa kanki a halaka, naja miki kunne akan Talba ba ki ba, me kika aikata Madina?”
 
Madina ta hade yawu da karfi idonta na cika da hawaye.
 
“Hajiya...”
 
Sai kuma ta kasa magana, ta mike tsaye zata fice daga dakin.
 
“Idan wata matsalar ta doso ki, karki yi tunanin kina da wata uwa da zata share miki hawayenki, matukar baki fada min damuwarki a yanzu ba”
 
Juyowa tai ta kalli Hajiya hawaye na sauko mata.
 
“Fada miki damuwata a yanzu, kamar kara jefa kaina ne a cikin wata damuwar, saboda zaki tsane ni ki fara min fada”
 
Kallonta Hajiya take da kyau tana karantar hawayen dake sauko mata.
 
“Zo ki zauna”
 
Ta tako a hankali ta zauna a inda ta zauna dazun still hawaye na sauko mata.
 
“Me kika aikata”
 
Ta yi shiru sai kuka take.
 
“Ki fada min damuwarki, wata kila zan iya taimaka miki tun a yanzu, zamu iya samun mafita a yanzu ba sai gaba ba lokacin da komai zai chabe mana”
 
Nan ma kasa magana tai sai hawaye take.
 
“Ni mahaifiyarki ce Madina, baki da wata kawa a duniyar nan da ta wuce ni, bayan Allah baki da wanda zai miki maganin damuwarki kamar ni, ki fada min abun da yake faruwa so that mu samu mafita tun yanzu”
 
“Hajiya.... Na aikata kuskure, a lokacin da zan aikata ido ya rufe ban ga komai ba, har sai bayan na aikata”
 
Hajiya ta dafata cikin sanyin jiki.
 
“Me kika aikata?”
 
“Hajiya kin san yadda na ke son Talba, ina sonsa sosai Hajiya, ina masa irin son da ko Leila da wanda yake aure a yanzu basa masa irinsa”
 
Sai tai shiru. Sai Hajiya ta ce
 
“Na sani”
 
Madina ta yi saurin kama hannanyen Hajiya ta rike.
 
“Dan Allah Hajiya karki min fada, karki tsane ni, na san kin yi ta ja min kunne akan Talba, amman Hajiya abun da kake so rabuwa da shi ba zai yiyu ba a cikin sauki”
 
“Har yanzu ba ki fada min abun da kika aikata ba”
 
“Hajiya, kin san irin kawance dake tsakanina da Leila bata iya boye min komai”
 
“Na sani”
 
“Hajiya Leila ta gaba kashe wata mata mai aikinsu, sunanta Baaba”
 
Hajiya ta dora hannnu a kirji tana zaro ido, iya abun da ta ji ko ta sani shi ne Baaba ta tafi ganin gida garinsu ba a san inda take ba, domin Madina bata taba fada mata komai akan haka ba.
 
“Ta kashe ta?”
 
“Eh, amman ba da gangan ta aikata ba, a yadda ta fada min kuma na san ba zata min karya ba, sai suka dauke ta suka saka ta a mota ita da

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login