Showing 198001 words to 201000 words out of 332834 words

Chapter 67 - Bakar wasika Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

65637

Saratu take ba, sai kawai ya cigaba da magana da Leila.
 
“Kina bukatar wani abu?”
 
Nan ma banza ta bawa ajiyarsa. Sai ya juya ya kalli Momy.
 
“Momy zan wuce, Allah ya sauwake, idan likita ya sallame ku ki fada zan zo na maida ku gida”
 
Uffan Momy bata ce masa ba, har ya nufi kofar fita ya fice sannan ta bishi da harara tare da jan tsaki. Leila kuma ta kara juyar da fuska tana hawaye, abun da Talba yai mata abu ne mai matukar ciwo da azabtarwa, ta ya zai auri wata? Bayan ita bata shirya yin sharing dinsa da kowa ba? Not him ko da wani ma ta aura bata da niyar zama da kishiya, kuma kishiyarma sai irin Aminatu?
 
“Ban san abun da ya gani a jikin yarinyar nan ba”
 
Ta furta tana Juyowa ta kalli Momy har lokacin hawaye na sauko mota.
 
“Talba ya cutar da ni”
 
Ta lumshe ido. Momy ta kyabe baki.
 
“Uhm yayi duk wannan abun ne saboda yana ganin kamar zaki iya mutuwa idan kika rabu da shi, ni Wallahi sai yanzu nake nadamar rainon yaron nan da na yi, ko dan ganin idona ya kamata ace wani abun be aikata shi ba amman sam baya gudun bachin raina”
 
“Haka nake ji Momy, ina jin kamar idan na rabu da Talba zan iya mutuwa, a yanzu na yarda Talba yana so na, domin mai son ka yana gudun bachin ranka, kuma yana son farincikinka, amman Talba baya son farincikina, kuma ba shi da buri sai na saka ni a bakinciki, daman Kabir yana ta fada min ban yarda ba...”
 
Ta fashe da kuka sosai, daga Momy har Hajiya Saratu tausayinta ne ya kamasu.
 
“Allah zai kawo miki wani, zaki samu mai sonki kamar zai mutu”
 
Momy ta fada cike da tausayinta sannan ta tashi ta fara cire kayan dake cikin gwandon.
 
“Wai kina nufin yanzu duk wahalar da kika yi da yaron nan ta tashi a banza kenan? Haka zaki zuba ido yana yadda yake so, ya bar miki ta ki yar a bakinciki bayan kuma ya gama bata mata lokaci, idan ya san baya sonta tun farko miyasa ya amsa cewar yana son ta din?”
 
“To Saratu ya zan masa? Ai idan na bari Leila ta auri ma na zama wata marar zuciya, kuma ita kanta Leila ta zama wata dabam ba ita ba”
 
Momy ta zuba soyayen dankali da kwai ta mikawa Leila.
 
“Ci ko kadan”
 
“To ai ita kam tana sonsa, kamar ki ce zaki rabasu domin yarki ce zata sha wahala shi kuma yaje ya cigaba da rayuwarsa daman haka yake so, kuma bayan kowa ya san an saka musu rana sai ace an fasa aure? Ai kin bawa dangin mahaifiyarsa abun da suke. So kenan”
 
Hajiya Saratu ta fada, ajiyar zuciya Leila ta sauke sannan ta girgiza ma Momy kai.
 
“Ba zan iya ci ba”
 
Ta sauke kafafuwanta kasa ta sauko saman gadon ta share hawayenta ta nufi kofar fita.
 
“Ina zaki?”
 
“Iska zan sha”
 
Ta amsawa Momy ba tare da ta juyo ba, Momy ta bita da kallo cikin tausayawa.
 
“Allah sai isar miki ga Talba, yaron nan ya ci amanarmu kuma ba kowa ya daure masa ba irin Engr shi ya daure masa gindi yana yadda yake so, da an taba shi yace dan dan'uwansa kamar shi yafi kowa dan'uwa a duniya, wannan abun ma ai ba mu kadai yai ma ba har da shi amman baya gani, sai kokarin karesa ma yake”
 
Hajiya Saratu ta bude baki.
 
“Ahhh to laifin waye? Ai laifin duk naki ne, tun farkon da kika fara ganin take takensa sai ki daukar masa mataki, yanzu haka zaki zuba masa ido yaje ya rayu da wacan yarinyar karama dazun nan ma fa kika gama bani labarin abun da ya faru da yarinyar”
 
Momy ta zauna a kan gadon majiyanta tana kallon yar'uwarta.
 
“To ya zanyi? Na isa na yi wani abun Engr ya fara min masifa yace zan kashe masa da? Hmmm ke ma dai kamar baki san yadda yake ji da Talba ba”
 
“Ai ba kirkiri zaki masa ba, ta hanyar da mutanen nan suka bi ta nan zaki bi, ke yanzu ko ance muki Talba a hayyacinsa yake wannan abun zaki yarda? Daman can yan'uwan uwarasa ba kishi suke da ke ba? Allah kadai ya san hanyoyin da suka bi suka ka laka masa son yarinyar nan, amman Talba dake ji da kansa ko ance min ha kula wata wanda bata kao yarinyar nan ba zan yi mamaki balle kuma wannan!”
 
Momy ta kalli kofar dakin dake rufe tana nazarin kalaman Hajiya Sadiya. Ganin haka ya bawa Hajiya Sadiya damar cigaba.
 
“Ke yanzu kina tunanin Talba a karon kasa zai yarda ya auri yarinyar? Har ya fara wannan haukar akanta?”
 
“Ban fa gane me kike nufi ba?”
 
“Tsaye za a tashi mana, a gyara shi ya dawo hayyacinsa, kuma a mallake shi ta yadda zai yadda kika juya shi ke da Leila, ai daman gidan Babban mutum kamar Engr haka ake yi, ba ma shi kadai ba kowa ayi ma ake sai ki ga kowa tsoron matar gida yake sai abun da ta fada ake bi, kuma ba a isa a tsabawa umarninta ba kowa tsoronta yake, amman yanzu duba ki ga halin da Leila ta shiga, har kike ikirarin za a fasa aure, idan ma kin ce haka ai ba lallai ne mahaifinta ya yarda ba, kuma yadda kika ga yana wannan rawar kadan idan ma an yi auren ba dadi Leila zata ji ta matar zai yi ta yi, domin bana jin a banza suka bar shi har ya amince da aurenta ma”
 
Ta kara tana wani kada kai kamar kadangarawa. Momy ta jinjina kai tana kara cika da tsananin mamaki sai a yanzu ita ma tunaninta ya bata haka.
 
“Lallai da maganarki, daman ba so na suke ba, gani suke na tare musu komai, tun ba kai haka ba suke fadar wai bana bari yana shiga gurin dangin mahaifiyarsa kaza kaza, sai dangina nake nuna masa magana dai ba kai, ni kuma gani na yi tun da ba wani abun azo a gani suke masa ba, miye na wani bibiyar dangi talakawan banza da basa tsinana masa komai, a nan tare da mu kuma ba rasa komai ba”
 
Hajiya Saratu ta tabe baki.
 
“Hmmm ni Wallahi ko a mafarki ban dauka Talba zai iya miki haka ba, ko da ma zai iya yi ma Leila ai ke be kamata yai miki ba, ko da yake ba a cikin hayyacinsa yake ba, idan ba haka ba ace har da dan'uwanka ka zarga? Ko shi mahaifin waya sani ko wani abun suka masa yake masa wannan haukar son kamar zai cinye shi, balle mutanen kauye nan da kika gani suna da sirrika kala kala kuma sun fi mu shiga malamai”
 
“Ai ni yanzu na yarda da maganarki, ko da ace Talba yayi haka be dace ace akan wannan karamar yarinyar yake wannan abun ba, saboda yarinyar bata dace da shi ba sam, a matsayinsa na babban mutum dan babban mutum, kuma yarinyar da ta gama tambade da lalacewa a cikin daji tare da barayin nan waya sani ma ko tana da wani ciwon?”
 
“Aifa sai ki yi, shi yanzu ba ganin duk ganin wannan yake ba, an riga an rufe masa idon, magani kawai a warware abun sannan a kalle tsakaninsu, ya ji babu wanda yake so a duniya sai Leila sai ki ga ya koma kamar ba shi ba, amman yanzu kika ce ki raba tsakaninsu  ai ita zaki cutar”
 
“Haka zaayi bari dai mu koma gida, kuma na warware wasu matsalolin da suke gabana, da wata fitina data kunno min kai”
 
“Ta me ba?”
 
Hajiya Saratu ta tambaya, sai Momy tai sarin kawar da zance, domin ko kadan bata son kowa ya ji hali da suke ciki ita da yarda a game da Baaba.
 
“Aa tsanina da masu aiki ne, zan yi solving din komai In Shaa Allahu”
 
Momy ta fada tana kashe ido, domin ta matsu su koma gida ta tafi gidan gonarta ta binciki mai gadinta. Leila ta kusan awa a waje sannan ta dawo dakin tana kallonta kasan akwai damuwa tare da ita domin fuskarta da yanayinta ya nuna haka.
 
“Leila ki samu ki ci wani abu, ki kwantar da hankalinki komai zai wuce”
 
Hajiya Saratu ta fada tana daukar jakarta ta rataya, Leila ta kalleta sannan ta nufi gadon ta zauna, sai Hajiya ta matsa kusa da ita tana murmushi.
 
“Ke kwantar da hankalinki indai Talba ne zaki same shi yadda kike so, komai zai wuce”
 
A take idon Leila ya cika da hawaye.
 
“Mama Saratu babu abun da zai sauya, Talba ya riga ya bata komai”
 
“Aa lokaci be kure ba, za a gyara komai, duk wannan abun da yake ba a hayyacinsa yake yinsa ba, za a kare ko minene da yardar Allah”
 
Leila ta yi shiru tana nazari.
 
“Asiri akai masa kenan?”
 
“Kema kina gani ai kin san haka, idan ba asiri ba mi Talba zai yi da yarinya kamar wannan, na yi magana da Yaya Amina idan komai ya laba hankali ya kwanta sai a dukufa da addu'a”
 
“Amman Mama Saratu idan aka kare abun zai rabu da ita?”
 
“Idan ya dawo hayyacinsa kan ai kin san komai zai koma kamar ba yi ba ne, kuma zai dawo miki kamar bawanki”
 
“Da gaske Mama Saratu?”
 
“Ke dai kwantar da hankalinki kawai, na miki wannan alkawari, taya zamu zuba ido ya bata miki lokaci kuma yanzu ya bulo da wannan, ai ba zai yiyu ba”
 
Leila ta kama hannu Hajiya Saratu ta cike da jindadi.
 
“Na gode Mama, na gode”
 
Ta fada hawaye na cika idonta, domin hae ga Allah tana son Talba so mai tsanani, musamman ma a yanzu da take ganin haibarsa da kyausa na kara kwarjini a idonta, fitar da tai a waje ma tunanin yadda zata rayu babu shi a rayuwarta sai ta ji ba zata iya ba, kamar yadda ba zata iya bar ma wata shi ba, haka ma ba zata iya tarayya da shi da wata ba.
 
 
 
***    ****   ****
 
Daga asibitin gidansu Hajiya Laraba ya wuce, yana fatar samun wani labari daga gurinta. A waje ya faka sannan ya fito ya nufi gate din yana tabawa ya ji shi a rufe, be yi mamaki ba wata kila saboda abun da ya faru ne yasa mai gadin yake rufe gate din a yanzu. Kwankwasawa yai mai gadin ya fara lekowa ganin Talba ne sai ya bude karamar kofar yana masa sannu da zuwa. Talba be kula shi ba domin s
haushinsa yake ji sosai saboda abun da ya faru, gani yake kamar ma shi yai causing din komai. Kai tsaye ya nufi main door din yana tuna yadda ta fito ranar ganinsa da ita na karshe. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali sannan ya kwankwasa kofar falon, yau ma Hajiya Laraba ce ta bude masa kofar.
 
“Talba...”
 
“Ina kwana?”
 
“Lafiya Kalau, ya hakuri akwai wani labari ne?”
 
Ta tambaya tana kallonsa cike da tausayawa domin ta ga sauyi sosai a fuskarsa, ya yi rama kadan ga damuwa karar da idanuwansa da suka nuna be samu yin bachi ba a daren jiya.
 
“Babu, na zo na ji ko an samu wani abu ne”
 
“Shigo ciki mana”
 
Ta kara wangale masa kofar, har yayi kamar yace aa ba zai shigo ba, sai kuma ya kasa musa mata ya nasa kafarsa daya a cikin falon ya shiga. Falon tsif kasancewar yaranta duka sun tafi makaranta, da kanta ta nufi fridge ta dauko masa ruwa da cup ta kawo masa, sai ya saka hannu ya dauki ledar pure water din ya fasa ya kai bakinsa, be aje ba sai da ya shanye, ya sake daukar wasu ya shanye sannan ya aje ledar yana kallon wani bangaren na falon.
 
“Kaka ta kira ka?”
 
“Aa”
 
“Ta kirani akan maganar tarewawarta tana tambayar abun da ya dace mu yi, na fada mata ta bar komai a hannuna har kawo amaryar ba sai ta zo ba zan kaita, bana son na fada mata abun da ya faru ne hankalinta ya tashi”
 
Talba ya hade yawu ba tare da yace komai ba. Can kuma ya mike tsaye.
 
“Akwai wanda kike zargi da aikata wannan abun ne?”
 
“Babu Wallahi, tun da Aminatu bata da abokin fada, ni kuma ban san wani wanda zai iya yin haka ba, da akwai ai da na fada tun a lokacin da police din suke min tambaya”
 
Ya sake hade yawun bakinsa a karo na biyu.
 
“idan an samu wani labari dan Allah ki kirani”
 
“Inshallah, amman mutanen da suka dauke ta bana tunanin yan satar mutane ne, domin da su ne da yanzu sun kira”
 
“Aminatu bara gama sanin unguwanni ba, kuma bana jin tana da nunber kowa a kanta, balle ta ba su su kira ko kuma ita ta kira”
 
Ya fada yana kara jin ba dadi.
 
“Kai Allah dai ya bayyanata cikin aminci, kuma ya tsareta”
 
“Ameen”
 
Ya amsa sannan ya nufi kofar fita Hajiya Laraba ta rako shi har kofar falon, zuciyarta cike da tausayinnsa, tsaye tai yana kallonsa har ya fice sannan ta koma cikin falon. Da kansa ya bude kofar gate din ya fito ya nufi motarsa, zama yai a cikin motar ya rasa abun da ke masa dadi.
 
“Duk wanda ya aikata wannan abun idan ma saboda ya nisanta ni da ke ne, ko ya saka na gujeki yayi kuskure, idan kuma saboda ya saka ki a damuwa a ba zan taba yafe mishi ba, kowaye ne”
 
Ya fada yana hade duka lisp dinsa ya ciza da karfi yana mai jin ina ma ace zai ga wanda ya aikata wannan abun. Slowly yake driving har ya isa office, kamar wani marar lafiya haka ya fito daga motarsa yana tafiya kamar mai tausayin kasa ya shiga cikin kamfanin. Bata kallon masu gaisheshi balle ya amsa, daman can ba al'adarsa ba ce amsa gaisuwar ma'aikatansa balle kuma yanzu da ba gaisuwar ce a gabansa ba. Zaune a kujerarsa ta office ya saka hannunsa daya yana murza goshinsa dake masa mugun zafi kamar zai cire. Tsakanin shigowarsa office da kwankwansa kofar da Madina tai be fi minti biyar ba zuwa bakwai.
 
“Yes...”
 
Ta fada ba tare da ya dago kai ba, ai ta tura kofar ta shiga rike da karamar kula, sai da ta kusa isa inda yake sannan tai masa sallama. Dagowa yai ya kalleta with surprise.
 
“Na san baka samu ka ci komai ba, saboda damuwa shiyasa na hada maa wannan cake din, kuma zan hada maka tea idan kana so”
 
Shirun da yai yana kallonta ne ya bata damar cigaba.
 
“And we can talk if you want...”
 
“Madina abokin wasarki ne ni?”
 
“Aa nima ba wasa na zo na maka ba, amman ina ganin kamar babu laifi ka nunawa mutum kulawa, ko ba komai Talba kai ne wanda Leila zata aura”
 
“This should be the last time da zaki sake shigo min office ba tare da ni na baki umarni ba, idan hakan ya sake faruwa a bakin aikinki, and ni ba irin mutanen da zaki rika tsayin game da su ba ne, get out”
 
A yadda ta ga temper dinsa ta hau ta san taba cewa tak zai iya marinta ko ma ya sallame ta gaba daya daga kamfanin. Da sauri ta juya rike da kular daman bata aje ba ta fice tana jin kamar ta fashe da kuka. Office dinsu ta dawo ta zauna bangarenta ta aje cake din a kasa tana boye fuskarta saboda idanuwanta dake cika da hawaye. Ta rasa taya zata samu kusanci da Talba, bata san abun da zata masa ba ya sake mata, a yanzu take gasgata zancen Leila da take fada mata cewar Talba mutum ne mai wuyar sha'ani.
 
‘Ko yaya yarinyar nan tai ta shiga ransa? Gashi nan duk ya be ya haukace akanta, yarinyar da bata kai ma ta wanke min talkami ba balle kuma shi’
 
Ta fada a ranta tana jin ina ma ace ita ce yake so haka ba Aminatu ba. Bayan fitar Madina ya kira Sakatarensa ya fada masa cewar baya son kowa ya dame shi, be ma'ana kar ya bari kowa ya shigo masa office, yana gama bada umarnin wayarsa tai ringing alamar kira da sauri ya ciro wayar daga aljihu ya duba, ganin Ali ne mai kiran yasa ya aje wayar kan tebur ya kwanta jikin kujerarsa yana lilo. Kiran na yankewa Ali ya sake yi masa wani, sai ya dauki wayar ya kasheta gaba daya ya aje.
 
 
 
 
_______________________________
 
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
 
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
 
Ali ya girgiza kai tare da maida wayar aljihu.
 
“Bana jin mun taba samun matsala da Talba da ta kai na jera masa kira fiye da hudu ya ki dagawa, ko da be daga kirana ba daga baya zai iya kirana sai dai yace min ina damunsa, ko kuma idan na sake kiran ya amsa, amman tun jiya da abun nan ya faru nake ta kiransa ya ki ya daga kuma be kira ni ba, Talba ya dauki zafi da yawa wannan karon”
 
Leila ta daga kai ta kalleshi.
 
“Saboda yana sonta ne right?”
 
Ali ya kalleta sai ya ji tausayinta ya kara kama shi, shekara nawa tana rainon soyayyar Talba a zuciyarta, ta shanye duk wulakancin da yake mata girman kansa da ji da kai duk ta dauka, amman ace a yanzu ya saka mata da wannan, shi kam yana ji Leila bata cancanci ma yai mata kishiya ba ko da tana gidansa balle kuma a yanzu da be aureta ba ya auri wanda bata kai tai tarayya da ita akan Talba ba, kuma ba

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login