Showing 30001 words to 33000 words out of 332834 words
Mikewa yai tsaye ya isa gaban plasma ya kashe sannan ya wuce kitchen domin samu abun da zai sakawa cikinsa, rabonsa da abinci tun da rana, ko lunch din Momy ta hada be ci ba. Tea ya fara hadawa kansa sannan ya bude freezer dake kashe ya dauko cake ya kunna oven ya saka shi a ciki, sannan ya dauki tea ya rike a hannunsa yana ta kallon harabar gidan ta windows kitchen din, ko ina haske ne kamar rana.
Juyowa yai a hankali jin kamar shesshekar kuka a falo, aje cup din dake hannunsa yai ya tako a hankali zuwa bakin kofar kitchen din ya tsaya. Sai ya hango Leila zaune a bakin stairs din sanye da kayan bachi riga da wando sai kuma safar dake kafarta, kanta ba dankwali sai hawaye take tana kallon wani bangare na falon, sam bata lura da shi ba har sai da ta juyo tana cigaba da rera kukan a hankali. Suna hada ido sai tai sauri share hawayenta ta dauke kai sannan ta mike tsaye ta juya a hankali zata hau stairs din.
Har tai rabi ban da kallon mamaki babu abun da Talba yake mata.
“Leila...”
Ya kira sunanta kamar wanda baya son magana, tsayawa tai cak gabanta na mugun faduwa, domin har ga Allah bata dauka yana zaune a falon har lokacin ba, da b zata fito daga dakinta ba, juyowa tai a hankali sai dai bata yarda ta kalleshi, sanin kanta ne ba zai tambaye ta me take yi ma kuka ba, kiran sunanta kawai da yai ya isa ya sanar da ita cewar tambayar damuwarta yake.
“Na yi mafarkin tsoro ne...”
Ta fada tana wasa da yatsun hannunta, bata tsaya jiran abun da zai ce mata ba ta juya da sauri ta haura sama. Da kallo ya bita har ta bace masa sannan ya juyo ya dawo cikin kitchen din, mamaki karara a fuskarsa.
‘Mafarki tsoro?’
Ya maimaita aransa, idan mafarkin tsoro tai me zai saka ta fito a nan ta zauna ita kadai?
“Ko dai saboda ni ne?”
Ya tambayi kansa yana kokarin kai hannunsa ya dauki tea, domin ya san abun da zai tashi hankalin Leila ba karami ba ne, and bayan shi ba ya ji akwai wani abu da zai saka Leila ta yi kuka ko ta shiga damuwa. Kamar wanda baya son bude baki haka ya kai cup din a bakinsa ya soma sha a hankali, dayan hannunsa ya saka a aljihu yana kallon oven din sai dai gaba daya tunaninsa ba a nan yake ba.
Sai da ya sha rabin tea sannan ya kashe oven din ya ciro cake din daya dumama ya aje, ya dauki tissue ya saka a hannunsa sannan ya fara daukar cake din yana ci. Bayan ya gama ya kashe wutar kitchen din ya fito falo ya kashe wutar sannan ya wuce bangarensa. Shirt din jikinsa ya fara cirewa wanda hakan ya bawa kyakkyawar surarsa da murdaden kirjinsa bayyana, a kafadarsa ya dora rigar sannan ya nufi wani madaidaicin daki dake hannunsa na dama, a hankali ya murda kofar ya bude ya shiga, kai tsaye ya nufi teburinsa ya ja kujera ya zauna ya bude system dinsa yana duba sakon da Jahid ya turo masa na adadin kudin da za a kashe wannan watan na gidan marayu.
“Okay”
Ya furta sannan ya rufe system din ya saka hannunsa aljihu ya ciro wayarsa ya kunna data ya shiga WhatsApp.
‘Zan rubuta maka cheque gobe, after that, ka bincika abun da yan gudun hijira suka fi bukata ka kirga ko nawa za akashe na mutun 300’
Bayan ya gama rubuta masaya kashe data ba tare da ya duba sako ko daya da yake shigo masa ba, balle har ya amsa. Fitowa yai daga dakin ya nufi Bedroom dinsa yana shiga ya aje rigar dake kafardarsa a muhallinta ya cire jean din jikinsa ya nufi bathroom ya jika jikinsa da ruwa ba tare da ya saka sabulu ba yai alwala ya fito, sai da ya tsane jikinsa sannan ya nufi closet din ya dauko kayansa na bachi.
Wando kawai ya saka domin abu ne mai wahala ya kwana da riga komai tsananin sanyi, sai dai ya rufa da bargo, riga na cikin abun da ke takura shi ta hana shi sakewa idan zai yi bachin dare.
BATURIYA POV.
“Wallahi tun da nake a rayuwata ban taba zuwa Kano ba, ni fa ban taba barin Zamfara ba”
Ta fada tana fyace hancinta daya cika da majina tsabar kukan data sha.
“To ya akai kika zo nan?”
“Agwagwa da buje na shiga nace ya kai ni tsohuwar kasuwa sai na ga kansa yan rawa kamar dan tsuntsu, bayansa kuma da gashi shine nace ya sauke ni yana sauke ni na fito da sauri, sai wannan mahaukacin ya biyo ni”
“Minene kuma Agwagwa da buje?”
Ta kalli wanda tai tambayar da idanuwanta da sukai ja abun ka da farar mace.
“Keke Napep”
“Oh Allah na wata kila aljanine ya dauke ki, kin san fa ance suma suna yin Napep din”
“Ga zahiri na gani, wata kila da bance ya tsaya ba da yanzu na tsinci kaina a Russia ko Iraq”
“Lallai kuwa abun na su ba wuya, to yanzu kina da waya a tare da ke?”
Sai a lokacin ma ta tuna da jakarta, domin wayarta da kudinta har da makullin gidanta suna cikin jakar.
“Na shiga uku Wallahi jakata na cikin napep din aljani nan kuma ya tafi da ita”
A take ta fashe da sabon kuka, domin ta san samun wata wayar ma agareta yanzu abu ne mai wahala.
“Subhanallahi, to kina da number wani akai ko mijinki ko Baba?”
“Babana ya mutu sai dai mijina kuma shi ma ya siyar da wayarsa, yau ina cikin ukuba”
Ta kara fashewa da kuka.
“Baki da number kowa akanki”
“Akwai ta yayata da Mamana”
Sai da ta share hawayenta sannan ta karbi wayar ta saka number Mama tana shiga aka dauka.
“Hello Sallamu Alaikum”
“Mama ina cikin matsala Mama gani a Kano”
“Kano kuma Rafi'a? Gurin me?”
A nan ta labarta mata abun da ya faru, cikin labarin tafi nanatawa Mama cewar wayarta na cikin jakarta kuma ya tafi jakar, da alama ma batan wayarta yafi mata zafi fiye da ganin kanta da tai a Kanon cikin kankanen lokaci, yan kudinta ma duk suna ciki. Kamar wata sabuwar mahaukaciya haka Baturiya ta zama har wani yamutsar kai take.
“Wallahi Takauci be yi ba, daman ance idan mutum ya kwana arba'in be ci nama ba idan yai maka baki zai ya kama ka, gashi nan ai laifin Faruq ne”
“Wanene kuma haka?”
Sai tai shiru bata fada ba, domin bata son tace mijinta ace bata jin magana tun da har ya hanata fita kuma ta fita duk kuwa da kasancewar ba wannan ne karo na farko da ya hanata kuma ta fita ba.
Account din mai POS din unguwar aka karba aka turawa Mama ta turo mata kudin mota, aka ciro mata sai dai tafiyar ba zata yi a yau ba domin yamma ta yi gashi kuma hanyoyin nigeria babu kyau a dole ta hakura sai gobe da safe ta kama hanyar dawowa Zamfara.
Kamar kullum sai bayan sallah isha'i Faruq ya dawo gida. A bakin kofar gidan ya tsaya ya kwankwasa yana sauraren ta bude masa amman shiru bata bude masa ba, ya sake kwankwasa nan ma ba a bude masa ba, yayi haka kusan sau hudu sai a na biyar ya saka makullin hannunsa ya murda ya bude kofar daman can a tunaninsa ko ta rufe kofar ne daga ciki kamar yadda ta saba, sai dai tun a yanayin yadda ya tararda gidan ya tabbatar masa da matarsa bata nan. Yayi sa'a akwai wutar nepa sai ya kunna gulob din waje dana falo ya shiga daki ma ya kunna, tsaye yai yana karewa dakin kallo komai a watse kamar yadda ya fita ya bar shi, daman yana fita ta shirya ta fita bata tsaya gyaran komai ba. Gashi kuma be tararda ita ba, ajiyar zuciya ya sauke.
“Rafi'a Allah ya shirya ki”
Ya furta cikin yanayin dake nuna alamar be jidadin daya sami gidan a haka ba, babu abun da ya fi bakanta masa rai ma kamar tararda ita da be yi ba a gidan, ko da yake halinta ne ko da ba zuwa unguwa ba takan fita makota tai taje can tana hira ko ta rika musu aiki alhalin ga nata aikin na gidanta ta bari, sai dai shi ya kasa sabawa da wannan halin, domin duk mai mata baya son ya shigo gida ya tarar matarsa bata cikin gidan idan ba da wani dalili ba, babu irin fadan da be mata ba amman bata canja ba, har ya gaji ya saka mata ido.
Gadon ya fara gyarawa sannan ya kwashe kayan data bari ya aje su a guri daya, ya gyara shimfidar Sultan ya dauko tsintsiya ya share dakin har zuwa falo, sannan ya zauna saman kujera ya daga kansa sama yana tunanin halin damuwar daya samu mahaifiyarsa a ciki, kusan kullum uwarsa bata rabuwa da damuwa domin idan babu na abinci akwai na rashin lafiyarta, sai dai a yanzu ta fi shiga damuwar fiye da koyaushe, a da tunanin na yadda zamu samu abun da za su sakawa bakinsu ne ko kuma na maganinta tsabanin yanzu da tunanin aurarda yarta wanda kanwace a gurin Faruq ya hanata sakat, ba Mahaifiyarsa kadai ba, idan aka fasa auren nan shi kansa zai shiga damuwa balle kuma ita kanwar tasa, domin mijin yace ya gaji da daga auren da ake ta yi, su kuma ba su da wani abun aurar da ita a yanzu, sadakin da suka karba da dadewa Mama ta saka shi a cikin kasuwancin da take ta zimmar zata dan juya ko zata samu riba, sai gashi ba wan ba kanen wato ba uwa balle kuma riba, daman sana'ar talaka sai Allah, balle kuma irin nata sana'ar da ake ci ciki.
Bayan matsalar kanwarsa ga matsalar kudin hayan da ke jiransa next week, gashi ba shi da mafitar kudin a halin yanzu, dan aikin da yake ta applying shi ma shiru kamar wanda ya zagi gobnati.
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”
Ya furta yana dafe kansa.
“Allah ka kawo min sauki Allah ka yi min mafita”
Ya fada yana mikewa tsaye ganin har goma ta kusa matarsa bata dawo ba, duk yawunta bata wuce tara na dare sai idan biki ake ko kuma wani abu ke saka ta kai dare, ko da makota ta shiga bata wuce 9pm.
‘Ina tunanin tafiya nijar zai fi min gurin ginar zinari, sai dai shi ma ai dole sai ka samu kudi, samun wanda zai baka rance ma a yanzu ai aiki ne’
Ya nufi kofa yana ta sake-sakensa da tunanin inda zai samu mafita. Babu waya a hannunsa balle ya kira ya tambayi inda take domin ya bada wayar jingina tun shekaran jiya ya karbo musu abinci, hakan yasa ya fara nufar gidansu Maman Amira makociyarsu domin Baturiya tafi zuwa can ta wuni saboda suna da rufin asiri daidai gwargwado, ba shi ma ko mutanen unguwar sun shaidi Baturiya da son shigewa masu kudi, idan ka ga tana shiri sosai da mutum to mai rufi asiri ne.
Cikin almajiran dake zama bakin kofar gidan ya kira daya ya aike shi cikin gidan ya kira masa Rafi'a, almajirin na shiga ya fito dauke da Sultan dake bachi ya mikawa Faruq.
“Ance wai bata nan, tun dazun da ta shigo bar Sultan tace zata je kasuwa bata dawo ba, kuma ta kira wayarta a kashe”
Cikin fargaba Faruq ya karbi dansa ya juya yana yi ma almajirin godiya ya koma gida, kwantar da shi yai ya fito waje zuwa gurin mai shagon daya bada jinginar wayarsa.
AMINATU POV.
Sai da yamma lis ta farka, ta dade da farkowa daga suman da tai sakamakon ruwan da suka zuba mata ga kuma zafi rana dake dukanta. Kana kallon kwayar idonta zaka karanci gajiya, da wahala dake tattare da ita. Gaba daya jin take kamar babu mararta zuwa kasan cinyoyinta, ko motsasu ta kasa yi, hakoranta kuma sun dantse gam kamar a hade aka haliccesu, a kwance take amman jiri sai dibanta yake tana ganin hadarin dake haduwa yana juyawa. Ba ita kadai ce a cikin wannan halin ba, sai dai wasu sun fita juriya domin suna da aure wasu kuma sun yi har sun fa ra warkewa. Kamar jira suke ta farko sai wani yaja hannunta ayayinda sauran jikinta yake kasa zuwa gurin turken da suke daure matan, a kafa duka daureta kamar sauran matan, sai dai har lokacin a kwance take ta lumshe ido tana sauraren yadda numfashinta ke fita a hankali, babu tunanin komai a kanta tana son tai tunanin amman ta kasa, tana tai kuka ta kasa sai a yanzu ta gane ashe yin kuka ma wani babban gata ne, yin tunani ma wata baiwa ce, yau ta rasa ta ina zata fara tunani balle ya gayyato kukanta.
Sama sama take jin kafarta na mata zogi, saboda tafiyar data sha da kuma Ƙayoyin da suka taka, ba ita kadai ba kusan kowa yana fama da ciwon kafafuwan wasu sun taka kusa wasu kaya, sai dai basa jin zafi a lokacin sai a yanxu, wasu kuma daurin da akai musu ne yake musu ciwo, domin na da wasa suke daure mutum ba.
Kamar dazu da safe haka aka biyo su ana ba su abinci a hannu cibi biyu wasu uku, kowa aka zubawa sai yai sauri ya cinye saboda yunwa ta ci su har ta galabaitar da su, daman idan suka ci cibi biyu ko uku da rana ba za su sake ci ba sai kuma dare, wani lokaci ma ci daya ake a rana.
Komai tsananin zafin rana ko sanyi ko ruwa ba a basu abun rufa ko gurin fakewa, sai dai sanyi ya kare akansu, haka ma idan ruwa ne sai dai ayi ruwa a gama ya jika musu kaya kuma tufafin ya bushe a jikinsu, idan rashin lafiya ta same su sai dai su mutum domin babu zancen basu magani balle kuma akai su asibiti.
“Dan Allah ku kwance mu yi sallah magariba ta yi”
Daya daga cikin mutanen dake daure ya fada, kusan wannan shi ne karo na barkatai da yake rokon su barshi yai sallah. Sai wasu kananan samari suka nufo inda yake suka kwance shi suka ware shi gefe suka saka bulala mai kyau suna dukanshi.
“Wato kai shege ko, baka daddaraba”
Duka suka masa ba na wasa ba, daman jikinsa da sauran bulala da suka masa dazun saboda yace su bar shi yai sallah, a kullum sai yayi magana kuma a kullum sai sun masa duka.
(As I'm writing this mutumen da yake cewa su bar shi yai sallah is no more, Wallahi sun kashe shi neighbor din mu ne, and they sent his friend wanda aka kamasu tare ya fadawa iyalinsa bayan an biya kudin fansar karbo shi)
Bayan sun gama dukansa suka maida shi gurin da yake suka sake daure shi yana ta kuka, ga wahalar yunwa ga na dukan dazu dana jiya ga shi yanzu kuma sun kara masa da wani.
Ana gama sallah magariba ruwa ya fara sauko, ta yanayin garin suke iya gane magariba ko azahar da la'asar domin babu masallaci balle su ji kiran sallah balle kuma agogo. Yan bindigar ne suke ta gudu suna neman gurin fakewa, mutanen da aka ma kuma suna daure aka fara ruwan kama da bakin kwarya yana sauka a kansu, iyakar abun da suke shi ne su dukar da fuskarsa saboda kar ruwan ya taba fuskarsu, wasu kuma su saka hannu su kare fuskar tasu, sai dai hakan be hana ruwa ya jika su.
A cikin mutanen da ruwan saman ya jika har da Aminatu, dake kwance galabaice kamar sauran matan da basa da kuzarin yin komai, abincin da aka bata ma bata karba ba, komai ganinsa take kamar ba shi ba, har yanzu bata yarda mutanen da suka kashe mata uwaye da yan'uwa suka kawota daji suka keta haddinta yan'adam ne masu zuciya da jini a jikinsu ba. Ta kasa yarda a duniyar da ta sani take, gani take kamar daukarta akai aka jefata a wata duniyar ta dabam mai cike da azzalumai, kuma marasa tausayi da tsoro Allah.
Haka suka kwana a cikin sanyi cikin kwabon ruwa har safe, sam ita ko yunwar bata ji, sauran da suka dade nan kuma suna fama da yunwa domin sun sabu da gurin ya zame musu kamar gida, wasu sun yi wata uku wasu biyu wasu hudu har biyar ma.
*** *** ***
MONDAY MORNING 9:21am.
“I wonder what wrong with our country? Kashe mutane ya zama kamar abinci?”
Cewar Kabir yana kallon hotunan da aka turo na harin da aka kai a garinsu Aminatu, abun ya kazanta kuma yayi muni sosai, musamman harin nan na biyu yafi na farkon ma, domin a yanzu an bar garin ba kowa, tun a lokacin da abun ya faru suka kashe na kashewa suka tafi da wasu, sauran da sukai rai suka gudu zuwa wasu garuran gudun Hijira!
Talba ya kalleshi yana kokarin gyara agogon hannunsa. Ba al'adarsa ba ce yin breakfast a bangaren a week days sai dai weekend, idan har zai karya to sai dai ya karya bangaresa ya sha tea ko kuma ya tafi office dinsa ya karya, sai dai ya zame masa al'ada shigowa ya gaisa da Momy kamin ya tafi aikin, sanadin hakan yasa suka sabu da Baaba idan ya shigo tana masa kirari ko da ba zai amsa mata ba zai mata murmushi ya gaishe ta sannan ya fita.
Yau sai ya ji dabam domin ya saba idan ya shigo zai tarar ita take shirya abun karyawa sai idan weekend ne Momy take tayata su hada komai a tare.
“Wai ya ake son talaka yayi ne? Su fa suke noma, yanzu an hana su noma wadanda sukai kuma a kone kuma a ashe su a dauke matansu kai jama'a wannan abun yayi yawa, nan gaba abinci ma sai yayi wahala”
Momy ta kalle tana kokarin aje flakes din ruwan zafi a dinning.
“Shiyasa ga su nan sun bi sun cika mana gari da bara kamar za su kwata da karfi”
“Haba ai dole Momy, ki duba yadda mutumem kauye yake alfahari da noma amman su bar komai nasu su dawo inda babu kowa suna bara, abun tausayi ne Wallahi”
“Su ma ai sun so, tun da su suka fara kashe Fulanin”
“No wannan