Showing 171001 words to 174000 words out of 332834 words
furta tana jin kamar ace Inna na tsaye a bayanta a yau, ta ga irin kyau da tai. Ji take kamar ta waiga tai arba da Yayanta Saminu mai yawan zolayarta, a yau ta ji tana marmarin fadan da Ya Amadu da Iro suke mata.
“Allah ya miki albarka ya nuna min aurenki Auta”
Maganar Baba ta dawo mata, daman hawayen ba bakin idanuwanta ba ne, a take ta ji tsayuwar wani mashi a kahon zuciyarta wanda ya saba zuwa ya tsaya mata a duk lokacin da irin wannan tunanin ya zo mata. Hannu ta kai ta dafe kirjinta ta runtse ido sosai tana sauraren yadda zuciyarta take raba jinin dake jikinta da sauri. Kwantawa tai a hankali saman gadon tana maida numfashi cikin natsuwa still idonta a rufe.
____________
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
MADINA POV.
Tun da ta dawo daga gurin aiki take zaune harabar gidan ta inda ba kowa zai ganta ba tana sharbar kuka, tun tana yi tana danne sautin muryarta har ta kai bata iya controlling kanta, faduwa tai daga kan kujerar zuwa kasa sai ta kai hannayenta ta kama kitson kanta ta matse sosai tana jin kamar ta kashe kanta ta huta, zuciyarta na mata mugun zafi kamar zata fasa kirjinta ta fito. Bata taba jin nadamar aikata wani abu ba kamar yadda take jin nadamar furucin da tai ma Talba a yau, ta san be dace ta furta haka ba, ga mijin da kawarta zata aura, idan Leila ta ji ya zata yi? Anya ma zata iya sake hada ido da Talba a yanzu? Anya zata iya komawa gurin aikin nan? Wane irin kallo zai mata?Zai fadawa Leila kalman da tai masa? Ta kasa raba dayan biyu tsakanin rashin dacewa da furucinta a gareshi da kuma irin son da take masa, domin ta wani bangaren bata ganin laifin kanta, kusan awa hudu tai a gurin bata aikin komai sai na kuka, tun tana tana yi hawaye na sauko mata har ta kai tana kukan babu hawaye, idonta ya kumbura kamar an hura shi, yawun bakinta suka kafe, kanta sai sarawa yake ya mata wani uban nauyi. Daker ta iya mikewa tsaye ta fara takawa tana jin kafafuwanta da jikinta kamar ba nata ba, takawa take a hankali tana jin kamar kafafuwanta basa iya daukarta. Tana kaifa cikin shiga falon wani irin jiri ya debeta da karfi ta fadi kasa dafe da kanta a take duk wani abu dake motsi a jikinta ya tsaya cak cikin har da bugun zuciyarta da fita da shigar numfashinta. Da sauri Tima ta yo kanta tana girgiza ta.
“Yaya Madina yaya Madina yaya Madina...”
Ganin babu alamar numfashi a tare da ita yasa ta kwalawa Hajiya kira tana ihu da kuka a take.
“Hajiya ki fito Yaya Madina ta suma”
Sau uku tana kiran Hajiya, kamin tai hudu Hajiya ta fito da gudunta daure da tawul jikinta kuma a jike da sanyin ruwa da alama wanka da fito.
“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, Madina. Miya same ta?.”
“Ban sani ba kawai tana shigowa ta fadi a nan”
Hajiya ta kai hannu tana tabata..
“Madina, dauko ruwa Tima”
Hajiya ta fada tana fashewa da kuka, sai faman girgiza Madina take tana kiran sunanta. Tima ta tashi ta shiga kitchen da sauri ta dauki katuwar roba ta kunna tap ta cikar robar ta fito a guje ta nufo Hajiya ta mika mata, Hajiya ta karbi ruwan da sauri ta zubawa Madina gaba daya, kamar wanda aka kwato haka Madina ta farko da karfi tana haki.
“Alhamdulillah”
Hajiya ta furta da sautin kuka tana dafe zuciyarta dake bugawa da karfi Tima ta dafa ta.
“Sannu Ya Madina”
Madina ta kalleta.
“Miya same ni?”
“Suma kika yi baki da Lafiya ne?”
Madina ta kalli Hajiya.
“Ba ni da lafiya, kuma ciwo ne da ba zan tana warke shi ba”
“Wane irin ciwo ne haka? Idonki ma duk ya kumbura dubi fuskarki Madina me yake damunki”
Amaimakon ta amsawa Hajiya sai ta lumshe ido ta fashe da wani sabon kuka, can kuma ta bude idon ta soma yunkurin tashi sai ta kasa saboda jikinta babu kuzari.
“Tima rika ni na shiga daki”
Tima ta kamata da sauri Hajiya kuma ta rika dayan bagaren suka mikar da ita tsaye, a hankali take takawa har suka isa cikin dakinta, saman gadonta suka zaunar da ita.
“Na hada miki tea?”
Sai da ta kalli Tima da idanuwanta da suka kumbura sannan ta amsa mata.
“Aa kawo min ruwa na sha”
“To”
Ta juya ta fita da sauri, sai Hajiya ta zauna kusa da Madina tana kallonta cike da tausayi.
“Saboda Talba ne?”
Madina ta yi jimmm na dan lokaci kamin ta daga mata kai alamar eh.
“Hajiya dan Allah ina son ki nema min izini gurin Abbah ina son na koma Kaduna da zama gurin Baba Shehu”
Hajiya ta mata kallon mamaki da kuma rashin fahimta a lokaci daya, sai dai shigowar Tima rike da kofin ruwa ya hana ta cewa komai har ta mikawa Madina ruwan, Madina na karbar ruwan sai ya zube a jikinta saboda bata da kuzarin rike kofin ruwan ma. A take Tima ta saka kuka, domin bata taba ganin yar'uwarta a irin wannan yanayin ba, kuma bata wasa da su balle tace wasa take musu.
“Na shiga uku Ya Madina miya same ki wai?”
“Ba ni da lafiya gobe zan tafi asibiti”
“To Allah ya baki lafiya”
Ta fada tana share hawayenta tare da kai hannu ta dauki kofin ta fice. Hajiya ta kai hannu ta rika fuskar Madina ta juyo da ita.
“Madina... Miyasa kika bari zuciyarki ta kamu da son wanda soyayyarsa zata azabtar da ke har haka?”
“Hajiya shi nake ta kokarin ganowa, akwai maza da yawa miyasa ban kamu da son kowa ba sai mijin da aminiyata zata aura, ga maza da yawa miyasa sai Talba? Hajiya ina jin kamar na sha wani abu na mutu wani lokacin ina jin kamar na yi hauka”
Ta yi saurin kama hannayen Mahaifiyarta ta rike gam.
“Ina son na yi nisa da nan, ina son na tafi nesa saboda na daina ganinsa ko jin duriyarsa, bana son ayi aurensa da Leila ina raye, bana son na zauna a gari daya da su, zan iya cutuwa kuma zan iya cutar da su”
Ta saki hannu Hajiya tana ta share hawayenta.
“Na san be kamata ba, be dace na yi haka ba, amman miyasa na yi? Kaddarata ce a haka right Hajiya? Right?”
Ta fashe da kuka mai karfi, Hajiya ta runtse ido tana hawaye, ma dake tsaye rike da wasu ruwan da ta debo mata hawayen take.
“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un”
Hajiya ta furta sannan ta bude idon ta share hawayenta.
“Tima kawo mata ruwan ta sha”
Tima ta karaso ta dauki tissue ta share mata fuska sannan ta bata ruwan a baki ta sha mai yawa sosai.
“Kwanta ki yi bachi idan kin tashi zamu yi magana”
Hajiya ta fada, sai Madina ta daga mata kai ta kwanta rairan saman gadon ta lumshe ido. Ganin haka yasa Hajiya da Tima suka fita tare da ja mata kofar dakin a hankali, bude idon tai ta janyo filon dake saman gadon ta rumgume shi a kirjinta tana hade yawu.
BATURIYA POV.
cikin natsuwa ta maida tufafin jikinta sannan ta juyo ta kalli Alhaji dake wani shegen murmushi.
“I hope idan mun je ba dadewa zamu yi ba”
“Aa idan mun je ba zai wuce mu yi sati biyu ba, sai idan kina son Kasar sai mu kara”
“Aa satin biyu dai ya isa, saboda akwai planning din da nake, badan ma ka matsa ba da ba zan je ba gaskiya”
Ya gyara bed sheet din yadda zai rufe masa jikinsa da kyau tana kallonta
“Baki son fita wata kasar ne? Irin Dubai London da sauran kashashen duniya?”
“Ina so kam sosai, sai dai kasan irin mu da mike zaune da iyaye dole sai da dabara muke fita, saboda idan mutane suka gane zai iya taba kimarmu, balle ni da nake da niyar aure”
“Aure kuma? Yaushe ska fara abun da har zaki gaji? Duka duka yaushe kika shigo wannan kasuwancin”
“Na samu iya abun da zan samu, kuma na samu wanda nake so, me kuma zan jira”
Yayi dariya.
“Yaro man kaza, ke yanzu har kina ganin kin tara abun da zai isheki? Ni kaina da nake tsoho ai ban ki na kara ba balle kuma ke da yanzu kurciyarki take cinki, yanzu kike cikin lokacinki”
“Ba ni da dogon buri kuma mijin da zan aura shi ma yana da rufin asiri, beside son sa ba zai bari na dade a haka ba domin shi ma kansa ya matsa min sosai”
“Eyee wani mai sa'ar ne haka? Zai dauke min sweet Baturiyar mata”
Ta yi dariya sannan ta dauki mayafinta ta yafa.
“Wani ne kyakkyawa sosai, mai kudi dan gidan mutunci”
“Gaskiya yayi sa'a samun mace irin ki ai sa'a ne, ina fatar dai alakarmu ba zata yanke ba, duk dai bana son mu'alama da matan aure, amman ina jin kamar ba abu ne mai sauki rabuwa da ke ba”
“Aa gaskiya, ba zan yarda mijina ya gane ba, bana son mu samu matsala da shi duk wani abu da zamu yi zan zubar da shi ne a nan waje”
“Ni dai roko nake, kin san dai dole ne na aje sirrinki ko dan kaina”
“Kadai mu bar shi a nan kawai”
Ta fada bayan ta dauki jakarta ta rataya, sai da ta karaso kusa da shi ta sumbanci goshinsa ta shafa kirjinsa dake sake sannan ta daga ta nufi kofa.
“Na tafi sai mun yi waya”
“Okay Baby”
Juyowa tai ta kalleshi tana murmushi sannan ta bude kofar ta fita. A falon ta tsaya ta saka face mask da katon bakin gilashi sannan ta fito harabar gidan ta fara takawa, kamin ta karasa gate din mai gadin gate din ya bude gate din sai ga wata farar mota ta kunno kai da sauri Baturiya tai kasa da kanta domin bata son tai ido biyu da wanda ke cikin motar duk kuwa da kasancewar tana sanye da mask ba lallai ne a gane ta ba, kamar yadda be zama lallai ace ta san shi ba ko ya san ta, wata kila ma direbansa ne. Ta karamar kofar gate din ta bi ta fice da sauri ta fara tafiya kamar da gudu gudu sauri sauri ko kadan bata yarda ta waiwayo ba sai nitsawa take babban titi unguwar tana nufar inda zata samu Napep..
Fahat na yi parking ya fito da sauri ta tako kasa zuwa gurin gate din yana kallon matar data fita daga cikin gidan. Mamaki yake yi wacece kuma mi ta zo yi a gida? A yanayin rashin jiki da farin fata ta masa yanayi da Baturiya, sai dai ko kadan be kawo cewar ita din ce ba, saboda ya san Fee'at bata daga cikin irin matan da za su aikata wani abu makamancin wannan, from first place be ma kamata ya munanawa mahaifinsa zato ba, what if wani abun ya kawo ta? Sai da ya daina hangota sannan ya juyowa ya dawo cikin gidan jikinsa a sanyeye, ko kadan baya son ya zargi mahaifinsa da abun da zuciyarsa take ayyana masa, amman idan har haka ne ba mi yarinyar mace kamar wannan zata zo yi a guest house dinsa? Har ya iso bakin kofar shiga falon be samu natsuwar da yake son ya samu a gurin mahaifinsa ba. Kasancewar kofar falon tana unlock ne sai kawai ya tura ya shiga, a falon ya samu mahaifinsa zaune yana latsa waya, fuskarsa a hade kamar an masa mutuwa.
“Abbah...”
Ya dago ya kalleshi yana kara hade girar sama da kasa.
“Ya akai? Ban fada muku kar wanda ya shigo min a nan ba tare da ni na kira shi ba?”
“Kai yi hakuri Abbah, daman kudin nr da na ciro na je gida sai Momy tace ta fita, kuma na san ka baro office shiyasa na yi tunanin naka nan ne”
“Amman ai ya kamata ka kira ni kamin ka zo, ba wai ka zo min haka nan kawai ba, kudin tashi zan yi da su da ba za a iya jirana da su a gida ba?”
“Na yi ta kiran number ka a kashe, ka yi hakuri ba za a kara ba, kudin yana cikin mota”
“Ka koma da su can gida”
Ya fada yana mikewa tsaye ya nufi bedroom dinsa sai kabe rigar shaddarsa yake, kana ganinsa ka san ransa a bace yake, ba komai kuma ya bata masa rai ba kamar zuwan Fahat ba tare da saninsa ba, da ace be ji motsin tsayawar motarsa ba yai hanzari saka tufafinsa da Allah kadai ya san a wane hali zai same shi, kuma da Baturiya ba tai hanzarin tafiya ba da yanzu wani labarin ake ba wannan ba, duk da dai yasan ba zai fada masa daki ba tare da ya bude masa ba, domin a lokacin da suka shiga dakin rufe shi yai da key fitar da Baturiya tai ne ta bude kofar bata rufe ba. Fahat ya mike tsaye jiki a sanyeye ya fito daga falon ya nufi motarsa, ya bude ya shiga yai reverse ya aka bude masa gate ya fice yana driving kamar wanda baya son tukin. Ko kadan be ji dadin abun da ya gani ba, domin yanayin yadda Abbah yake masa masifa ya tabbatarsa da zargin da yake, be taba tunanin dattijin mutum kamar mahaifinsa zai iya maida zuciyarsa ta yara ba, yaran ma marasa tsoron Allah da basa jin kunyarsa. Da tunani kala kala ya isa gida, nesa da kofar falon ya faka motarsa ya fito ya nufi kofar yana jin tausayinsa mahaifiyarsa da kuma su kansu da suke yayansa, ya dade a tsaye jikin kofar kamin yai knocking a bude masa, kamar wanda yai wani aikin wahala ya gaji haka ya shiga cikin falon, be tsaya komai ba ya nufi upstairs da zimmar shiga dakin mahaifiyarsa, sai ya ji tana kiransa.
“Muhammad Fahat”
Juyowa yai sai a lokacin ya lura da inda take zaune tana gyaran fruits, takawa yai ya karasa inda take ya zauna kasan carpet din ya aje makullin motar a gabanta.
“Idan Abbah ya dawo ki basa kudin suna cikin motarsa, yace a dawo da kudin gida”
“Miya faru ya fasa siyen filin ne? Ai daman na fada maka zai iya cewa ya fasa, domin filin miliyan arba'in ya masa kadan, tun da ba zama zai yi ba ajiya ce kawai”
“Ba fasawa yai ba, kawai dai yace a dawo da kudin gida”
Ta mike tsaye cikin yanayin damuwa, har ya juya Momy ta kira shi.
“Muhammad Fahat?”
Ya juyo ya kalleta.
“Kamar kana cikin damuwa miya faru?”
Yayi shiru yana tunanin yadda zai fada mata cewar wata matashiyar yarinya ya gani a gidan mahaifinsa, ya zata ji? Ya zata kalle abun zuciyarta zata iya dauka?
“Ba komai”
Ya amsa sannan ya juya ya fara tafiya.
“Ko dai mahaifinka ya maka fada ne akan yarinyar nan?”
Ya sake juyowa ya kalleta.
“Abbah ba shi da matsala da ita, ke ce kike hana ni aurenta saboda kina ganin kin zaba min wata, amman ba Abbah ba, dan haka babu wani dalili da zai saka Abbah yai min fada akanta, kaina ne yake dan ciwo zan jr na kwanta”
“Allah ya sauwake, ka sha magani please”
Ya gyada mata kai sannan ya dauke kai ya nufi kofar fita. Bangarensu ya nufa domin an ware bangaren yan mazan gidan dabam matan ma bangarensu dabam, kanensa da kuma wadanda ake riko a gidan. Yana shiga Dakinsa ya zauna saman kujera ya ciro wayarsa ya shiga muhallin kira, number Baruriya ya aikawa kira, sai aka sanar masa har lokacin wayarta na a kashe. Dauke wayar yai daga kunnensa ya shiga gallery ya kamo hotunanta yana kallo. Samun kansa yai da murmushi yana kallon kyakkyawar fuskarta sai ya ji son ta ya karu a zuciyarsa. Baturiya na da kyau tana da siffar da kowane kalar namiji zai so ta, amman tana da kyaun zuciya? Tana da tarbiya? Ta fito a gidan kima? Ya tambaye kansa yana kara kallon hotunanta, a yanayin yadda take nuna masa da yadda ya fahimci mu'amalar ta tana da tarbiya, kuma ta fito a gidan mutuncin domin ta dade tana boye masa gidansu da ikirarin ba a barinta zance, sai dai daga baya nan ta kan tsaya da shi a kofar gidan da take ikirarin na su ne. Mikewa yai tsaye ya nufi gurin plasma ya kunna sannan ya dawo ya zauna tare da aje wayar gefe, can kuma ya dauki wayar ma'adanar lambobi ya shiga ya zakulo number Isma'el ya danna kira.
“Hello Isma'el”
“Oga Fahat ya gida?”
“Lafiya Kalau ba zaka daina ce min oga ba ko?”
“Ya za'ayi na daina, ai ka yarda kawai kai oga ne”
Fahat ya dan yi murmushi.
“Ya aikin ya kwana biyu?”
“Alhamdulillah ya na ku?”
“Mun gode Allah, wani aiki ne zan baka kuma sirrina ya zama tsakanina da kai please”
“Okay ina saurarenka”
“Zan turo maka hoton wata yarinya da number wayarta da kuma sunanta da unguwarsu, dan Allah ina son a bincika min komai a kanta, bana son ka boye min komai”
“Yayi Alhaji ka ce lokaci yayi”
Fahat yayi murmushi.
“Amman bana mutuwa ba, ina son yarinyar sosai gaskiya, sai dai kasan halin Momy, to ina son na fara bincike da kaina ne ne kamin su yi na su, dan nasan zasu yi, ina son idan akwai wata matsala na fara sani kamin su, domin ina ta kokarim shawo kansu ne a yanzu”
“Karka damu Insha Allah zan bincika yadda ya dace, Allah ya tabbatar da alheri”
“Aamin ya Rabbi, na san dai ka fini sanin garin nan sosai a yi min