Showing 165001 words to 168000 words out of 332834 words

Chapter 56 - Bakar wasika Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

65643

irina. Kamin na manta ki sanar da kawarki ta samu aiki zata iya shigowa Monday”
 
Yana fadar hakan ya karasa gurin kofar ya danna door bell yaja ya tsaya, ita ma a tsaye take a gurin zuciyarta na mugun tafasa, tana kallonsa har aka bude masa kofar ya shige ciki. Kallonsa Momy take har ya karaso kusa da ita ya zauna tare da ciro wayarsa yana kokarin tabawa.
 
“Akwai wata matsala ne?”
 
Momy ta tambaya tana kallon yanayinsa dake nuna ransa a bace yake. Kamar mai jira sai ya dago ya kalleta.
 
“Momy a gaban idonki Leila za tai wannan dress din ta fita?”
 
“What wrong with it?”
 
Ya gyara zamansa yana mamakin Momy.
 
“Kayan fa ya kama jikinta sosai, and even dan Veil din nan da wasu suke sakawa da Leila bata sakawa”
 
Momy ta sauke ajiyar zuciya tare da cire gilashin idonta.
 
“Look Talba, karka bari sheidan yai tasiri a zuciyarka, ba yau Leila ta saba irin wannan shigar tana fita ba, miyasa yanzu kake son maida shi wata matsalar ne kawai”
 
Maida dubansa yai wani bangare na falon, yana jin sabon bachin rai na ta so masa wanda ya fi na Leila.
 
“Idan kana da matsala da Leila, ko kuma kana ganin ta yi wani abun da baka so, zaka iya samunta ku yi magana ku fahimci juna, amman ba ka kawo min kararta ba, aure fa zaku yi ku yi iyali idan ba ka iya fuskarta ta da magana taya kake tunanin zaku gina rayuwa”
 
“Momy kin fi kowa sanin cewar Leila bata jin magana ta”
 
“Ko kuma baka fahimtarta ba, irin rayuwar da kake son ka tafi da ita ba zai yiyu ba Talba, kai da ita dukanku kun yi karatu kun san rayuwa, miyasa ba zaka aje wannan girman kan ba ka bata kulawa yadda ya dace? Ba zai yiyu Leila ta zauna a karkashinka kamar baiwa ba, ta yi kokari na sani, babu irin juyin wainar da baka mata ba, wani gurin ma ita take da gaskiya amman sai na tirsasata yi maka biyayya saboda a samu zaman lafiya, sai dai na fahimci kai din ba canjawa za ka yi ba, na rasa abun da yake damunka, Leila tana iya kokarinta amman baka gani kuma duk abun da kake yi da gangan kake yi, ai lokacin da yarinyar ta zo ina kallon yadda kake kwantar da kai, yanzu kuma har nema mata sauki kai a gidan nan”
 
Uffan be sake cewa ba, har Momy ta gama zazzaga masa ta mike tsaye ta bar masa falon. Sai ya kai hannunsa saitin bakinsa yana wasa da lips dinsa. Abun da Momy tai masa a yanzu ya fi yi mata zafi fiye da wanda Leila tai masa, ko ba komai idan Leila ta fada masa goma zai iya fada mata ashiri, amman Momy be isa yayi mata wata maganar banza ba, a da can idan wani abu ya faru tsakaninsu Momy tana daukar bangarensa ne ta goya masa baya, duk da ya san bata son ganin Leila.
 
 
 
AMINATU POV.
 
A hankali take cin abincin tana sauraren wayar da Kaka take da Talba, bata ji ta fadi sunansa ba sai dai a yanayin yadda suke wayar ya tabbatar mata da Talba Kaka take waya, sai dai bata yarda ta dago ba sai da Kaka ta gama wayar tana kokarin zama kusa da ita.
 
“Ka ji mutum wai yana son magana da ke”
 
Aminatu ta sauke kanta kasa.
 
“Ai na fada masa sai nan da wata uku zai sake ganinki ko yayi magana da ke, har da wani maganar tarewa yake, sai kace yar roba aka aura masa, wai zai zo ya dauke ki ku tare, sai kace dai auren karuwai”
 
Nan ma Aminatu bata ce komai ba.
 
“Ba zan bari ku tare ba sai na kankaro miki mutunci, na yi waya da Hajiya Laraba tun jiya tace min zata zo ta tafi dake”
 
Sai a lokacin Aminatu ta bude baki.
 
“Wacece Hajiya Laraba?”
 
“Yata ce, ni na haifi abuta da kaina, amman acan Gusau take zaune a unguwar locos a can take aure har da yaranta, mai kudi take aure gidan ma mai kyau ne har da ac, tace wata uku zaki yi a can sai a shirya ki ayi miki komai, kuma ba zan yarda ya dauke ki ba sai ya miki lefe mai kyau tun da ba yar roba bace ke”
 
Aminatu dai bata ce komai ba, ta dauki ruwa ta sha ta aje kofin.
 
“Zata koya miki komai, ki sake jikinki karki rike wannan noke noken nan, shi wannan mijin na ki da kike gani dan duniya ne, kunya ma bata isheshe ba, kin san yan boko, ke kuma gani yar daji, dole ne ta koya miki wani abun da yadda ake zaman aure”
 
“Zan kai kwanon waje”
 
“Aa aje ni zan kai, ai tace a daina saka ki aiki saboda jikinki ya samu hutu yai kyau, a kai amarya abu haka a bushe kamar wanda ta taso a rame, wannan bakin ma ai yayi yawa ko dai baki murja jikin ne idan kin shiga wanka”
 
“Ina murzawa, fatar ce a haka”
 
“Ikon Allah shi kuma gashi fari kamar larabe sai ku haifi yaya fari da baki”
 
Ta karasa tana daukar kwanon da Aminatu ta ci abinci ta fice. Aminatu kuma ta hau gado ta kwanta tana ta tunanin rayuwarta.
 
Sai da yamma Kaka ta kira yarta Hajiya Labara tana tambayar ranar da zata zo.
 
“Dazun ma ai har kirana yai wai zai zo ya dauki amarya, na ce masa sai nan da wata uku”
 
“Kai kai kai Hajiya wane irin wata uku kuma dan Allah? Waye zai yi aure yai ta jiran Amarya har wata uku?”
 
“Yo ba ke kika ce idan son samu ne ta samu wata uku ana gyarata ba”
 
“Eh gaskiya haka ya kamata, saboda a gyara jikinta da dan abubuwan da zai saka kima a idon mijinta”
 
“Yauwa, kin gani ai dole ya hakura har lokacin, kuma idan yana sonta da gaske zan gane ai, tun da na san ya aureta ne kawai saboda na matsa masa, ga shi kuma wadannan tsinannin sun zubar da yar kimar tata ta mata”
 
“Karki damu da wannan Hajiya, ai gyaran da za a mata yanzu, Wallahi ko budurwa sai haka, tuwon girma ai miyarsa nama, amman sai an kashe kudi gaskiya, kawata ke yi dana fada mata sai tace na dawo da Aminatu gidana zata rika zuwa tana mata komai ko kuma ita a kaita”
 
“To ai sai ki taimaka na fada miki marainiya ce ba uwa ba uba”
 
“Zan yi iya yawa, amman ba zan iya duka ba, dole a samu wani abu daga gurinki”
 
“Aa ni ba za a samu komai a gurina ba, kara dai angon”
 
“Wane irin ango kuma Hajiya? Sai a karbo kudin gyaran amarya a gurinsa? Ban taba ji ba”
 
“Aa na san hikimar da zan masa ai, ai ba zan yi yadda zai gane ba kar ya mata gori wata rana”
 
“To sai dai haka”
 
Kaka ta gyara zama.
 
“Idan kika tafi da ita a wanke fatar nan tai kyau tai dan haske yarinya ga kyau amman fata ta mutu, jiki a bushe kamar kara”
 
Hajiya Laraba ta yi dariya.
 
“Kai Hajiya karki damu, Wallahi har jikinta zaki ga yadda zai canja, har jikin za a bata ai kuma a gyara fatar sai kin ga yadda zata yi heki, indai gyara ne ai yar gidan Mai Fata ba daga baya ba”
 
“To haka nake so, 10k zai isa?”
 
A dayan bangaren Hajiya Laraba ta zaro ido.
 
“Haba Hajiya wane irin 10k kuma? Kar fa ki manta Mu'azu babban mutum ne, kuma gyara za a mata wanda shi kansa sai yayi mamaki”
 
“Ai ni tsoro nake kar ya wulakantata Wallahi, tun da ya ga ita bata da kowa, amman na kula yana dan tausayinta”
 
“Hmmm ai Wallahi Hajiya, idan muka gyara ta, be isa ya wulakantata ba, idan kika ga ya juya mata baya to ba yin kansa ba ne sai idan asiri akai masa, kuma idan so yana son yarinya domin da baya son ta da ba zai aureta ba”
 
“Ni ma na yi wannan tunanin, yanzu dai zan karbo dubu ashirin ai zai yi ko?”
 
“Hajiya karamin gyara kike son ayi mata ne? Domin hawa hawa ne, indai na manyan mutane sai kin karbo 100k na fada miki har dilke za a mata kuma za a bata wanda jikinta zai dan murmure fatarta tai kyau tai sheki, shiyasa ake son a fara da wuri ai ba a kuraren lokaci ba”
 
“Ashe Laraba baki da hankali? Har dubu dari za'ayi gyaran jiki kudin fili? Da wani gida? Yo ko gwamna zata aura ai ba zan yi almubazzaranci ba, balle wani Mu'azu”
 
“Hajiya ba laifina ba ne, mai gyara ce tace haka, kuma idan gyara be yi ba ai dole za a biya kudi, idan kana son abun kwarai dole sai an cire kudi mai kima fa, ke ma dan kina a nan ne kike ganin 100k a wani kudi mai yawa, amman ba wani kudi ba ne, idan ma kika ji masu yi na miliyoyi sai kin yi mamaki, kuma kudin nan fa Hajiya ba ke zaki bada ba a jikin wanda za ayi ma gyaran za su fito”
 
“Kin tabbatar idan gyara be yi ana biyan kudin?”
 
“Eh dole ne ma wannan”
 
Hajiya Laraba ta fada tana dariya, ta fadi hakan ne kawai saboda Kaka ta yarda ta bada kudin domin ta san halin kaka.
 
“To yaushe zaki zo?”
 
“Idan ya baki kudin kamar a yau ni kuma zan zo gobe na tafi da ita”
 
“To, zan kira shi da safe, amman ko da ya biki a can karki yarda ya ganta fa ko a waya ban yarda su yi magana ba”
 
“Hmmm ai ba zai ma fara ba, yaushe rabonsa da gidana? Shi a rayuwarsa ai be san kowa ba sai dangin Mahaifinsa da dangin Amina, mu da muke talakawa ai babu ruwansa da mu, yana taka gidana ma sai na mata tass Wallahi”
 
“Ki yi masa kam, ai Amina ce bata koya masa son dangin uwarsa ba sai nata, shiyasa ai na dage sai da akai auren nan in ya sonta hadi zuciya ta mutu daga ita har mijin nata, ya auri yar'uwa dai kuma dole ya rika zuwa gurin danginsa”
 
“Ai Wallahi kin kyau, shiyasa ai nake son ayi mata gyaran kwarai”
 
“To zan karbo kudin, amman rabi zan bada sai idan bukata ta biya sai a cika saura”
 
“Haba Hajiya sai kace mai nema magani, na ji zan cika sauran ni sai ki ba ni”
 
“To haka yayi, zan aje waya ki kashe”
 
Sai da Hajiya Laraba tai dariya sannan ta kashe wayar. Kaka ta sauke wayar tana fadin.
 
“Hauka ake yi da zan dauki har dubu dari na bada”
 
 
 
LEILA POV.
 
Driving take hawaye bakinciki na sauko mata, for the first time yau tana jin tsanar Talba a zuciyarta, ta rasa gane kansa ta rasa yadda za ayi su fahinci juna ita da shi. Taya ma zai fada mata cewar wai ta yi arha samu a gurinsa?
 
“Me yake daukar kansa ne?”
 
Ta tambayi kanta tana goge hawayenta, ba wani kwaliya tai sosai ba sai dai haka be hana fuskarka lalacewa ba. A harabar gidansu Maryam ya faka motarta sannan ta kai kanta jikin sitiyarin motar ta kife wasu hawayen na sauko mata, bata dago ba har sai da wayarta tai kara, sannan ta share hawayen ta kai hannu ta dauki jakarta ta bude ta ciro wayarta.
 
“Hello Madina”
 
“Baki shigo ba, ana ta jiranki kuma kin san be kamata ace an yi birthday Maryam babu ke ba”
 
“Na shigo, ina waje ina cikin mota zaune”
 
“Ya na ji muryarki kamar da damuwa?”
 
“Ina cikin damuwar ne Madina”
 
Ta sauke wayar tana kuka marar sauri, cikin yan mintuna Madina ta iso gurin ta bude dayan bangaren ta shiga ta zaune tana kallon Leila cikin tashin hankali duk kuwa da kasancewar tana cikin nata tashin hankalin.
 
“Lafiya?”
 
Leila ta dago tana hawaye ta labartawa kawarta abun da ya faru, a take Madina ta ji nata damuwar ya wartsake.
 
“To be sincere, Talba ya wuce gona da iri, and ina tunanin lokaci yayi da ya kamata ya san cewa kin banbanta da sauran mata kamar yadda kike fada”
 
“Kin ma mi nake ji yanzu? I hate him”
 
“Kina da wannan damar, kuma ki yi hakuri da abun da zan fada miki, tsakani da Allah Talba baya son ki, domin mai son ka zai so abun da kake so, zai guji bacin ranka, kuma zai rika rawar jiki da son kusantarka not like yadda yake miki a yanzu, ki duba yadda yake tarairayar yarinyar nan amman ke ko da rana daya bana jin ya taba miki haka, fadi tashi yake ta yi akanta har sai da ya sama mata yan'uwa, idan ke ce kina tunanin zai miki haka? Amman yaje yana kula yarinyar da ko talkami bata isa ta goge masa ba”
 
“Madina miye abun yi a yanzu?”
 
“Ban sani ba, amman Tabbas Talba baya son ki, ina tunanin ya amince da ke ne saboda kar ya bawa Daddy kunya”
 
Ta lumshe ido tana jin wani kalar zafi da zuciyarta ke mata, hawaye kuma na sauko mata har hancinta ya soma ja.
 
“Yanzu dai ki koma gida ki huta, be kamata ki shiga gurin nan haka ba, zan fadawa Maryam baki jindadi”
 
“Okay”
 
Ta amsa sannan ta share hawayen sannan ta sake kallon Madina.
 
“Yace ma fada miki zaki iya shiga monday a kamfanin”
 
“Okay, yanzu ba lokacin yi wata magana ba ne, kawai ki shiga gida ki huta zan shigo gobe”
 
“Okay”
 
Ta sake amsawa, sannan Madina ta bude motar ta fita tana jin wani irin dadi na lullubeta, Leila kuma taja motarta ta fice daga gidan cikin damuwa da tunanin yadda zata samawa kanta mafita.
 
“Ba zan maka kuka ba Talba, ba kai na zubar da hawayena akan ba, miye namijin ma da har zan bata lokacina ina kuka akanka?”
 
Ta furta tana share hawayenta, sai kuma ta shafe da kuka mai karfi tana jin irin kalar bakinciki, maganar Madina na dawo mata. Can kuma tai yi saurin share hawayenta
 
“No one deserves my tears”
 
Ta furta cikin muryar tana jin kamar hade zuciya ta mutu.
 
 
BATURIYA POV.
 
Wannan karon sai da ta baro gidan gaba daya sannan ya amsa kiran Fahat ko ba komai zata fi sakewa a wajen gidan fiye da ciki.
 
“Har yanzu dai kin ki ba ni damar da yanzu mun shiga next level”
 
Ta yi dariya.
 
“Me kake ci na baka na zuba? Nan da kankanen lokaci zan ce maka ka aiko”
 
“Kankanen lokacin har yanzu be zo ba? Da kin san yadda nake jinki a zuciyata ba zaki rika min wannan jan ajin ba”
 
“Ba jan aji ba ne, kasan komai na rayuwa yana son tsari, na yi ma iyayena magana sai suka ce na dan dakata shiyasa, amman da zarar sun ba ni dama zan sanar da kai”
 
“Allah yasa dai ba wani suke son aura miki ba”
 
“Bana jin iyayena za su aura min wanda bana so, kawai dai akwai wani tsare tsare da suke ne, ni kuma ai ba zan yarda na rasa namiji irinka mai qualities da nake so ba”
 
“To Allah ya tabbatar mana da Alhari”
 
“Amin Dear, ya maganar tafiya?”
 
“Tana nan gobe tun da safe zan wuce yanzu haka na shigo Office din Abbah ne zan dauki wasu takardu ne”
 
“Allah ya tsare min kai ya dawo da kai lafiya”
 
“Ameen i love you”
 
“I love you More”
 
Ta sumbaci wayar har sai da ya ji karar kiss din sannan suka yi sallama. Saman tebur din Abbah ya aje wayar ya janyo wasu takardun yana dubawa. After like 20 minutes aka turo kofar office din wani mutum da ba zai wuce sa'ar babban yayansu ba ya shigo rike da wata leda a hannunsa dayan hannunsa kuma rike da takardu.
 
“Dr Adamu”
 
“Ranka ya dade yau kai ne a kujerar Alhaji?”
 
Fahat yayi murmushi
 
“Ni ne”
 
“Allah yasa dai lafiya”
 
Ya tambaya bayan ya zauna.
 
“Lafiya kalau, ni ma wasu takardun ne na shigo dauka, saboda zan yi tafiya gobe”
 
“Okay, ke nan yau gaba daya Alhaji be shigo ba?”
 
“Ya shigo da safe, amman yanzu ya tashi gaba daya lafiya dai?”
 
“Daman maganinsa ne na zo masa da shi, tun da bana nan zan koma sai gobe ko jiki sai na shigo”
 
“Maganinsa kuma? Abbah yana shan wani magani ne?”
 
“No na ciwon jiki ne kawai”
 
Fahat ya kalli katuwar ledar da ke dauke da magani ba daya ba.
 
“Zan iya wuce masa da shi gida ai”
 
“No gaskiya wannan a tsakaninmu ne, zan dai ba shi da hannuna kamar yadda na saba”
Fahat yayi shiru yana kallon Dr Adamu dake kokarin mikewa tsaye, a iya saninsa Abbah baya shan maganin komai, domin be san shi da wani ciwo ba bayan hawan jini shi ma kuma sai idan abun ya taso masa yake sha.
 
“Haba mana, Dr zauna dan Allah”
 
Dr Adamu ya koma ya zauna yana kallon Fahat daya soma masa magana a natse.
 
“Idan akwai wani abu ka sanar da ni, dan sa ne ni, karka ci tsoro ko fargabar komai, dan Allah ka fada min akwai wata cuta ne da take damun mahaifina?”
 
Dr Adamu yayi saurin amsawa.
 
“No, idan ma akwai shi ya kamata ya sanar da ku ba ni ba, saboda abun da ya shafe shi ne, idan har be sanar da ku ba ni kuma be kamata na yi katsalandan ba, domin rayuwarsa ce, mu wuni lafiya”
 
Ya mike tsaye da sauri ya nufi kofa, Fahat kuma ya bi shi da kallon da mamaki da kuma tunani kala kala a zuciyarsa.
 
“Ko dai akwai cutar da take damun Abbah ne, be fada mana ba?”
 
Ya tambayi kansa, sai kuma ya sauke ajiyar zuciya, yana tunanin ko dai diabetes ne, amman idan har shi ai be kamata ya boye ba, saboda yanayin abinci da yake ci da kuma wasu abubuwan. Haka dai yai ta sake sakensa kamin ya hada takardun da zai dauka ya fice tare da rufe office din.

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
 
 
OCTOBER 3RD...
 
Ya jingina jikin motar Ali ransa a bace kansa har wani sarawa yake.
 
“To wai ina ta kai yarinyar ne?”
 
“Oho mata, da alama ma yarinyar bata cikin gidan nan fa, domin da tana ciki yadda na yi mata tijara yau da sai ta nuna min ita”
 
“Oh No Talba don't tell me ka yi rigima da tsohuwar nan?”
 
Talba ya dago ya kalleshi.
 
“To mi zan yi? Ban san inda ta kai yarinyar mutane ba, kuma ta ki fada min komai, tun tana cewa wata biyu zata yi gashi har mun shiga wata na hudu”
 
Ali yayi dariya.
 
“Yar mutane kuma? To ai tafi kusanci da Kaka fiye da kai, kuma kasan ita ma tana

Join Our Groups

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login