Showing 9001 words to 12000 words out of 332834 words
zo neman wata alfarma ne a gurinka”
“Allah yasa zan iya Faruq”
Faruq ya busar da iskar bakinsa.
“Wallahi ina cikin matsaloli ba ma daya ba, kasan matsalar kasar nan, mutum zai yi karatu amman aiki shiru, ga dan shagon da na kama sabuwar unguwa ce ba mutane sosai”
“Wallahi kasar ce har ka rasa yadda zaka misalta ta, abubuwan sai a hankali, idan baka yi karatu ba abun ya dame ka idan kuma ka yi aikin ya gagara”
“Shine nake son na fara koyon irin sana'arku, duk da ba iyawa nai ba amman dai idan nayi tare zan iya da yarda Allah”
Shamsu ya masa wani kallo na mamaki, a tunaninsa zai ranci kudi ne a hannunsa, sai ya ji yana masa maganar sana'arsu, ba Shamsu kadai ba kusan duk wanda ya ji mutum mai degree zai yi sana'ar gini zai yi mamaki, domin muna a zamanin da masu degree da kuma mutane suke ganin ba ko wane irin aiki ne ya dace da su ba, wani abun ana ganinsa kamar kaskanci ne, ace kana da degree kuma kai yi shi.
“Faruq zaka iya sana'ar gini kuwa? Kai da kai karatu? Kuma jikinka be saba da aikin wahala ba”
“Shamsu kenan, wanda ya tashi a area kamar wannan kuma dan talaka zai ce be saba da aikin wahala ba? Ya kake magana kamar ba san gidan da na fito ba?”
“To abun ne da mamaki Faruq naga kai ka yi karatu ka ni ban yi karatun ba”
“Ka aje komai a gefe ka duba bukatata idan zai yiyu”
“Inshallahu, sai dai ka san aikin mu tasowa yake ba wai kullum ba ne sai idan ta samu, inshallahu da mun samu zan kiraka a waya tun da ina da number ka”
“To na gode sosai sai na jika”
Ya mika masa hannu sukai musabaha, Shamsu ya koma cikin gidansa cike da mamaki, Faruq kuma ya nufi titi cike da damuwa.
FEE'AH POV.
“Gaskiya kina da kyau sosai”
“Thanks”
Shine reply din da tai ma mutumen da facebook bayan ta tura masa hotunanta masu kyau, kamar yadda ya bukata.
“A ina kike da zama a Gusau?”
Wannan karon tashi tai zaune tana tunanin irin karyar da zata masa, domin bata fada masa cewar tana da aure ba, duk kuwa da kasancewar bata dora hotonta a profile picture ba, sai hoton sunan Allah data saka as her profile picture dinta.
“Gida dari”
Ta bashi amsa.
“Na san gurin idan na shigo zamfara inshallahu zan neme ki mu gaisa”
“To Allah ya nuna mana”
Ta bashi amsa tana murmushi, kamin ta sake shiga profile dinsa ta duba komai nasa, ciki har da gurin da yake aiki da kuma hotunansa, kana ganinsa ka ga wani hamshakin mai kudi mai connection da yan siyasa, domin yadda ake masa fadanci a profile ma ya isa ya sanar da hakan. Murmushi ta sake yi sannan ta dawo inbox din ta duba tambayar da yai mata ta biyu.
“Are you on whatsapp?”
“Yeah”
Ta bashi amsa da sauri tare da rubuta masa number wayarta ta tura masa.
“Okay Thank You so much Baturiya”
Ta sake fadada fuskarta da murmushi tana jin sunan har cikin ranta. Sannan ta fita facebook din ta shiga whatsapp, few massage ta samu ciki har da reply din da MD Saleh yai mata, shi ta fara budewa da sauri jikinta har rawa yake kamin ta gama karantawa.
“Subhanallahi, Allah ya wadata, turo account number dinki”
Mikewa tai tsaye ta daka wani uban tsalle ta dire tsabar murna da jindadi sannan ta tura masa account din tana masa godiya.
“Alhamdulillah”
Ta furta sannan ta shiga group chat dinsu na makaranta, ta fita ta leka na matan aure ta fita ta shiga na novels nan ma bata dade ba ta fita ta bude chat din Ramlee.
“Kawata kin yi ciniki, wani ya ga Hotonki a wayata ya matsa na nemo masa ke”
Tana gama karanta sakon kawarta Ramlee ta zaro ido tare da sakin baki a lokaci daya, domin ta san sana'ar kawarta, tana da connection da manyan masu kudi tana hada su da mata kyakkyawa kuma masu siga kamar yadda ita ma take hulda da su, sai dai duk iskanci Baturiya bata taba aikata alfasha ba, za dai hadu da mutum har su gaisa ko kuma ta yi masa nata wayon ta waya ta samu yan canji, amman bata san tai mu'alama da maza ba, bayan Faruq babu wanda ya taba saninta a ya mace.
“Gaskiya aa Ramlee ni dai ina jin tsoro ba zan iya ba, amman idan kin san irin wanda zan yi ma wayo ne na ci kudinsa ba sai mun hadu ba, ba matsala”
Ta mayar mata da amsa duk da kasancewar Ramlee tana Offline a lokacin, sannan ta kashe datan ta aje wayar ta mike tsaye ta fito waje.
“Sultan zo nan yau zamu ci kaza”
Ta fada tana zaunawa jikin kofar falon tana mikawa danta hannu fuskarta cike da murmushi kamar yadda zuciyarta take fal da farinciki saboda kudin da za a turo mata, Sultan din ya rugo da gudunsa yana murna.
“Abba zai siyo mana ne”
Ta shiga kabe masa riga tana fadin.
“Ba nace ka daina cewa Abba ba? Ka rika cewa Daddy, yayan talakawa ne suke cewa Baba ko Abba, yaran masu kudi kuma su ce Daddy ka ji?”
“To Daddy ne zai siyo mana?”
“Aa adashen zan kwasa yau sai na siyo mana, amman karka fadawa Daddy ka kaji? Har da lemun kwalba zan siyo mana”
Sultan din ya shiga murna yana jindadi yau za su ci kaji, rabon da su ci nama har ya manta.
AMINATU POV.
A bakin kofar shiga gidansu ta hadu da Sanusi tsaye yana latsar karamar wayarsa.
“Ya Sanusi”
Ya kalleta sai kuma yai dariya.
“Igee ai sai ki fada mana cewar kin fara fita zance, mu shirya yi miki aure”
Ta cinno baki gaba.
“Ni dai dan Allah ka daina, Allah yasa ba ka fadawa Inna ba ko Baba”
“Ban fada ba, amman dai zan fada masa, Baba ma baya nan”
“Ina yaje?”
“Gwaggo ta Makka aka aiko bata da lafiya sosai, shi ne suka je tare da Junaidu a babur”
“Yanzu?”
“No tun dazun”
“Allah ya bata lafiya shi kuma ya dawo da ita lafiya”
“Inna tace naje na dubo ki, idan kin shiga ki ce ni na zo da ke”
“Wallahi ba zan fada ba”
Ta fada tana nufar cikin gidan.
“Ni kuma zan fada mata cewar kin yi saurayi”
“To na bari”
Ta yi saurin fada har tana dawowa baya, sai ya saka dariya ya biyo bayan kanwarsa suka shiga cikin gidan tare. Kamar Kullum inna na zaune tsakar gidan tana jiran dawowarta, domin bata bachi sai ta saka yarta a ido.
“Oyoyo Auta yar albarka, an siyar ko?”
Aminatu ta aje kwallon tuwon da bokitin miyar da plates din roba a gaban ina tana sauke gajiya.
“Eh Inna wai Baba ya tafi gurin Gwaggo?”
“Eh an aiko bata da lafiya, aka ce mai rabon ganawa da ita ya zo”
“Allah ya bata lafiya”
Ta fada cike da damuwa, sannan ta ciro kudin cinikin ta mikawa Inna, sai da Inna ta kirga kudi ta ga sun cika sannan ta cire wadanda ta saba bata tana sakawa a asusu ta mika mata.
“Ga na ki”
“Na gode”
Ta fada bayan ta karba tana kallon Sanusi zuciyarta sai raya mata take zai fadawa Inna maganar, sai har sukai yar hira da zasu yi suka gama bata ci ya dauko zance ba, hakan yasa ta ji dadi sosai. Bata bude wasikar da Maniru ya bata, da fitilar da take zuwa talla ta haska wasikar da ya rubuto mata da hausar ajami, tana karantawa sai murmushi take tana jindadin yadda ya jera mata kalaman soyayya da kwantar da hankali.
Bayan ta gama karantawa ta rumgume wasikar a kirjinta, can kuma ta tashi ta saka a cikin littafanta na Islamiya kamar yadda ta saba, sannan ta gyara gurin kwanciyarta ta kwanta. Inna kam bata kwanta ba sai da ta gama komai ta kintsa komai kamar yadda ta saba sannan ta kwanta tare da rage fitilar kwai dake dakin, hasken ya rago sai dai bata kashe gaba daya ba saboda Aminatu na tsoron duhu sosai, bata bachi babu fitila a kusa da ita.
Misalin 12am gidan yayi tsit domin kowa ya nemi gurin kwanciya ciki har da yan awaki da tumakin da ake kiwo, can cikin bachi Inna ta soma jiyo hayaniya, tare da karar babura hakan yasa ta ta tashi zaune tana sauraren jikinta na bata ba lafiya ba, domin kowa ya san matsalar kasar a yanzu, balle kuma su da suke kauye. Aminatu kam sharar bachinta kawai take bata ma san ana yi ba, jin ihu da kuma fadar Innalillahi a makota yasa Inna ta nufi inda Aminatu take ta shiga tashinta.
“Auta Auta”
Ta fada murya can kasa kasa, a hankali Aminatu ta bude ido ganin Inna yasa ta tashi zaune.
“Inna...”
“Shiiiii”
Inna ta mata alama da tai shiru. Wanda hakan yai daidai da banko kofar gidan ta kwano a shigo, ga wata uwar fitila mai shegen haske da suke ta hasken gidan da ita.
“Innalillahi Wa'inna illahirraji'un”
Inna ta furta gabanta na bugawa da mugun karfi, Aminatu ta mike tsaye da sauri kamar wanda ta rude, Inna ta shiga duba dakin tana jin kamar ace akwai wata hanya da zata bi ta fita, a rikice ta nufi gadonta.
“Shiga nan Auta shiga shiga”
Da sauri Aminatu ta nufi karkashin gadon na karfe ta shige, zuciyarta na wani irin zillo kamar zata fito, Inna ta nufi kofa domin duba sauran yayanta sai dai kamin ta isa kofar suka shuri kofar da mugun karfi ta cire suka shigo cikin dakin kamar an aikosu. Baya baya Inna tai tana fadin.
“Innalillahi Wa'inna illahirraji'u”
“Rufe mana baki dan ubanki”
Yanayin yadda yai maganar da karayar halshe kadai ya isa ya sanar da cewar gayu ne suka hauro garin a yau, wato bandits abun da ba a taba ba, domin duk wani hargitsi da ake fama da shi sai dai su ji a makotan kauyukan ko kuma a hanya abun ya rutsa da yan garin, amman ba a taba shigowa cikin garin ba. Ba Inna kadai ba har Aminatu dake karkashin gado sai da ta saka hannayenta ta rufe bakinta. Ta ko'ina jikin Inna rawa yake, ganin manyan makaman da ke hannunsu.
“Ina mijikin yake?”
Kasa magana tai bakinta sai rawa yake kamar jikinta ga wani gumi dake karyo mata.
“Wato ke ce uwar yaran ga yan iska ko?”
Nan ma Inna kasa cewa komai tai sai ambaton Allah take a zuciyarta, hannayenta duka biyu rike da bakinta.
“Innalillahi”
Inna ta jiyo muryar yayanta a tsakar gidan, wani irin abu ne ya ziyarci zuciyarta sai ta ji kamar ace akwai abun da zata iya yi ta ceci yaranta.
Dun dun dun ta ji tashin bindiga kamin ta tantance komai ta ji muryar Sanusi yana kuka.
“Wayyo Allah na, la'ilaha illahu, Innalillahi”
A lokacin ne hawaye ya cika idonta, irin hawayen da kowace uwa take yi idan ta kasa taimakon yayanta.
“Wayyo”
Ta jiyo ihun matar Amadu, bata san da inda kuzari ya zo mata ba har ta iya tambayarsu kamar ta rikice.
“Me muka muku?”
“Tambaya ma kike? Ba kun aje yan sakai a gidanku ba, wai masu yaya ko? To yau sai mun kashe su sai mun muku wulakanci”
Inna ta hade hannayenta biyu tana kuka tana rokonsu.
“Ku dubu girman Allah ku yi hakuri, ku kashe ni kar ku kashe yarana dan Allah...”
Bata gama rokon ba, wani ya karaso kusa da ita ta fisgi rigar jikinta.
“Cire wannan rigar ai har ke da kike uwarsu ba zamu bari ba”
Sai a lokacin Inna ta kara firgicewa, ta fara bin fuskokinsu da kallo tana ganin komai kamar a mafarki.
“Cire cire”
Sai ta rika jin kamar ba hausa suke mata ba, gaba daya ta rasa gane abun da suke nufi, bata fahimci manufarsu ba har sai da suka barge rigar dake jikinta suka kama zanen shi na suka fisge suka jefar da shi can gefe, suka mata tsirara a gabansu. Aminatu dake karkashin gado ta yi saurin kara rufe bakinta wasu irin zafafa hawaye na sauko mata, saurin rumtse ido rai hango mahaifiyarta tsirara a kwance yaron da be wuce sa'ar danta na biyar ba ya fara keta mata haddi!!
Ba mutum daya yai ba, ba biyu ba, ba uku ba, ba hudu ba, haka suka jera su goma sha daya suka yi mata yadda suke so, sannan suka fita suka barta kwance kamar tsumma. Abun ka da uwa suna fita ta yi karfin halin rarafawa ta isa inda zanenta yake da idanuwan da take jin kamar kukanta ya kare a yau. Ta dauki zanen da hannunta amman yadda zata sarrafashi ta daura ta suturta jikinta ne ta manta sakamon jin ihun Sanusi, cikin rashin kuzari zuci da na jiki ta isa jikin kofar tana kallon yadda yan bidigar majiya karfi, suka danne Rilwanu a kasa, dayansu ya kunna babur dinsa ya hau ta kan wuyansa ya tsaya.
“La'ilaha Illahu”
Inna ta fada da wata irin muryar da bata taba sanin tana da ita ba, tana mika musu hannu. Ba su kulata balle su fasa abun da suke, ba su saukar da babur din a wuyansa ba sai da suka tabbatar ransa ya rabu da gangar jikinsa, daman haka suke ma irin su Rilwanu masu aikin sa-kai domin kare rayuwarsu da kuma ta al'ummarsu, idan suka halbeka da bingida suka ga bata tashi ba, sai su gwada adda, idan ita ma ba tai ba sai su saka dutse ko babur. Bayan sun kashe Rilwanu suka fashe rumbun hantsen dake gidan suka saka Iro a ciki suka kunna masa wuta, tare da hatsin. Wani irin ihu yake yana neman ceto amman babu wanda zai iya kawo masa dauki.
“Kaico Kaico kaico”
Inna ta fada tana kallon yadda danta ke ci da wuta, ga kuma wani a kwance, wani irin shiga da fita numfashinta ya rika yi da karfi, tana jin wani abu na mata yawo a ciki, gaba daya sai ta nemi dan sauran kuzarin nata ta rasa, a bakin kofar ta fadi kwance yawu da majina suna zubo mata a lokaci daya, cikin karfin hali ta dan dago kanta ta juyo ta kalli Inna Aminatu take boye, sannan ta juya tana kallon yadda suka dauko katon dutse suka daga sama suka saki a akan Amadu da yake da wasu barayin suka danne a kasa ko motsi baya iya yi, kamar yadda sukai ma Amadu haka wadancan barayin da suka zagaya gidan Musa suka masa, domin duk wanda ya san yayan Mai Damma ya san wuka ko bindiga bata hudasu, ya sha kuma ba bawa yaransa, ba dan komai ba sai dan kariyar irin wannan ranar, sai dai ayau shan be amfana musu komai ba, ba su kadai ba har da sauran mazan gari da bindiga bata fasawa, sukan kashe su da babur ko dutse, balle kuma Rilwanu da Iro da sukai kwarin suna a garin saboda aikin sa-kai da suke.
Sanusi kam sai yai kamar ya mutum ganin nasa mai sauki ne, domin da babur sauka hau kafarsa dan kawai su gana masa azaba, baya ambatar komai sai Allah, ba a gidan Mai Damma kadai ba, a garin gaba daya haka suka ci suka shude babu wanda ya kawo agaji, suka ci karensu babu babbaka yadda ransu ya so sannan suka bar garin bayan su kwashi abinci da mata cikin har da matan Musa da matar Amadu.
________
Na zo muku da albishir guess what? A have alot of kayan mata masu kyau gaske, akwai na infection, akwai maida tsohuwa yarinya, akwai set din da ake hadawa for matan da basa gane kan mazajensu, akwai na mallaka kala kala, muna kaza mai magani, tantabaru, akwai kaza mai Yasin, akwai na mallaka sirrine mai karfin gaske. Ina masu son zama madubi a gurin mazanje su? Ina matan dake cewa na gwada ban dace ba? Muna da gumba da garin magani kala kala da na tsarki ga Humra da turarunka kala kala amman fa na kayan mata. Akwai dan wata bakwai.
Ga masu bukata za su iya tuntubar number nan 08036126660 zan saka miki a mota na aika miki har inda kike da yarda Allah.
Serious Buyers Please idan ba ki shirya ba kar mu batawa juna lokaci.
I just published "04" of my story "BAKAR WASIKA". https://www.wattpad.com/1188003519?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=KhadeejaCandy&wp_originator=gvBvvJY%2Brh7%2BfdxLjDxcLbTx9rDGdNBA0sMHgr3XMPr%2FqwZ4sIWJ88oZCr4nOa%2BILP0eBQ%2FKRLIQm73M62araHO6%2BoJXjoYprLv7YGhRYyguc1ysae3vRDycS1qvuqiM
*💔 BAKAR WASIKA 💔*
By Khadeeja Candy
Page -4️⃣
“So yanzu ka yarda zaka bata hakuri kenan”
Talba ta girgiza kai.
“Kai no never ni fa ba zan taba ba wanda yake kasa da ni hakuri ba”
Ali ya kalleshi.
“Amman ka ce Daddy yace laifinka ne, kuma kaje ka bata hakuri”
Yayi shiru kamar ba zai ce komai ba, sai kuma ya shafa kansa ya sauke numfashi a hankali.
“Yeah ba wai yana nufin na ce tai hakuri ba, ni yanzu so nake ka kirata ka bata hakuri kuma ka dauke ta ku je yawo ta wayance Shikenan komai ya wuce, amman karka ce ni na ce ka bata hakuri fa”
Ali ya rausayar da kai yana kallon abokin nasa cike da mamaki.
“Miye a ciki dan kace tai hakuri? Ko kuma ka dauke ta kuje yawo, faduwa kai?”
Sai Talba ya amsa masa kai tsaye.
“Yes, taya zaka bawa mace hakuri macen ma wanda take kasa da kai, ni me fa Ali”
“To wai idan kuka yi aure kuka samu matsala, kuma kai kake da laifi...”
Kamin Ali ya karasa Talba ya tari numfashinsa.
“Sai ta ba ni hakuri”
Ta fada da iyakancin gaskiyarta, domin har ga Allah be ga dalilin da zai saka shi bawa wanda ke kasa da shi hakuri ba, kuma mace sai dai shi a ba shi. Ali yayi murmushi.
“Yanzu dai for the sake of Daddy zaka yi”
“For the sake of him na zo har ina rokonka da kai, idan ba haka ba babu abun da zai saka na roke ka ma”
“Look Talba I'm not her boyfriend, ban san kalaman da zan mata ba, kuma ba ni nai mata laifin nan ba”
Talba ya mike, ganin hakan yasa Ali ma ya mike tsaye.
“Fine, amman tare za mu je, kana driving ina baya”
Talba be ce masa uffan ba ya nufi kofar fita, wanda hakan ya tabbatarwa Ali cewar ya yarda kenan. Sai da Ali ya shiga yai sallama da Samira sannan ya fito ya samu Talba a cikin motarsa. A hankali Talba yake tukin har suka fita daga cikin gidan suka hau titi.
“Kirata ka tambaye ta tana ina”
Ali ya masa wani kallo.
“Kiran ma? Talba wai kai zaka bata hakuri ko ni? Just ka kirata ka tambayi tana ina ma you can't?”
Ko kallon gefen Ali Talba be yi ba balle ya tanka masa.
“Fine”
Ali ya fada sannan ya zaro wayarsa ya shiga contact dinsa ya nemo number Amal, domin baya son batawa kansa lokaci tambayar Talba number ta