Showing 156001 words to 159000 words out of 332834 words
tana kokarin mikar da ita tsaye, Aminatu ta saka dayan hannunta ta rike sabon zanen atamfa da Kaka ta tsaga gida uku ta bata daya ta daura dayan kuma ta yafa sai ta saka shirt a jikinta. Kamar wata igiya haka ta bi Kaka dake janye da hannunta suna tafi, zuciyarta sai zillo take kamar zata fasa kirjinta ta fito, ba zata iya musu zuwa ba kamar yadda ba zata iya fisge hannunta daga rikon da Kaka tai mata ba. Kamar wanda akai wa auren dole haka ta samu kanta tana jin kamar ba ta shirya haduwa da Talba ba. Sai dai bata iya komai har Kaka ta fice da ita harabar gidan ta nufi waje da ita. Kaka da kanta ta isa dakin dake zaure ta kwankwasa kofar sai aka bude daga can ciki.
“To ga Amaryar”
Kaka ta fada tana kaucewa ta yadda zai iya hango Aminatu dake tsaye bayanta kanta a kasa. Murmushi yai yana kallon matarsa.
“Ba ki kishi kenan?”
“Aa ni yau cikin farinciki na ke Alhamdulillah ka yi min abun da nake so”
Kaka ta fada cikin murna da farinciki marar misaltuwa, sannan ta juya ta nufi inda ta fito ta bar Aminatu tsaye a gurin kanta a kasa. Talba ya maida dubansa gurin Kaka har sai da ya tabbatar ta koma cikin gidan sannan ya fito daga cikin dakin ya kalli Aminatu, kamshin turaren da ta ji ne ya tabbatar mata cewar angonta ya matso kusa da ita, sai dai bata iya daga ido ta kalleshi ba har ya kai hannunsa ya riko hannunta, wani kalar yanayi ta samu kanta a cikin, yayinda hannunta yake tsarkafe cikin nasa hannun, janta yai a hankali zuwa cikin dakin yana kallon kafafuwanta kamar mai kirga tafiyarta, takawa take tana jin kamar ba tafiya take ba har suka shiga cikin dakin. Sannan ya saki hannunta ya nufi kofar ya rufe sai ya tako a hankali ya tsaya daga bayanta ya kai hannayensa ya kama zanen da take rike da shi da dayan hannunta.
“Saki”
Ya furta jin yadda ta kara rike zanen da karfi gam, jikinta ya fara rawa.
“Daura miki zan yi, ba wani abun zan miki ba, kin min kankanta sai dai nan gaba idan kin kara girma”
Ya fada a kokarinsa na kawar mata da tsoron dake tare da ita. Sai dai hakan be saka ta yarda ta sakar masa zanen ba, be damu ba ya kama zanen a haka ya saka dayan hannunsa ya cire nata hannun dake jikin zanen a hankali, sannan ya daura ba mata, not like yadda take daurawa but he try domin ya saba daura tawul.
“Yauwa”
Ya furta sannan ya juyo gabanta ya tsaya yana murmushi.
“Amarya”
Da sauri ta dago kai ta kalleshi, sai ta ji kamar ta furta mata kalmar ne saboda ya firgitata, sai dai murmushi da haifar da tai arba da ita a fuskarsa ya hana ta ganin komai. A yau ya fi yi mata kyau fiye da ko yaushe, kimarsa da kwarjininsa sun karu a idonta. Bayan hannunsa ya kai gefen fuskarka yana shafawa a hankali idanuwansan kwancen a cikin nata, yana yi mata haka ne just to make her feel comfortable and saboda yana tausayinta, not because of love, domin ko kadan baya kawo soyayyah a kusa. Ba zai iya cewa ya tsane ba, and haka ma ba zai iya cewa yana kaunarta ba.
A hankali ta sauke kanta kasa hawaye suka kwankwaso mata kofa, kuma ta rasa dalilin zuwan su a yanzu, domin ba farinciki take ba alhalin ma tsoro ne ya cika mata zuciya.
“Waye kai”
Ya furta ba tare da ta kalleshi ba, hannunsa ya kai ya taba fuskarsa wai ko wani abu ya canja ne daga fuskarsa daya saka bata iya gane shi ba.
“Akwai abun da ya banbanta daga ni ne, da ya saka yau ba ki gane ni ba?”
Ta dago ta kalleshi hawaye na sauko mata.
“Asalin kai nake nufi, har yanzu ban gama sanin waye kai ba”
“Me hakan zai amfanar miki?”
“Ban taba gani ba, ban taba ji ba ko a tarihi cewar wani mutum mai daraja da kima irin ka ya auri mace irina ba, kana da komai na duniyana ki kuma na rasa komai na rasa kowa, ban iya karantawa ba balle na rubuta, ban san wani abu rayuwar birni ba balle na waye, rayuwata ta canja daga daren da Barayin Shanu suka shigo mana a gari, kuma na shiga hannunsu sun wulakanta ni saboda ba su san darajar mace ba, ba su san iya abun bakincikin da mace take ji ba ba idan ta rasa martabarta, kuma likitan daya karbe ni ya bani taimako yai min aikin, abokin ka ne, duk baka duba wannan ba ka amince da aurena saboda ka faranta ran Kaka? Baka tunanin a kokarinka na faranta ranta zaka iya ruguza sauran natsuwar da ta rage min? Zuciyarka bata taba ayyana maka kyamata ba?”
Kallonta kawai yake, yana mamakin irin yadda Allah ya zuba mata baiwa da kaifi basira a kwakwalwa fiye da shekarunta. Sai da kalli kasa sannan ya sake kallonta sai kuma ya kai hannu ya kama hannunta ya kai saitin zuciyarsa.
“Wannan ya kamata ki tambaya miyasa ta amince da kudurin Kaka? Wata kila ba saboda faranta ran Kaka ne kawai ba, har da kokarin faranta na ki ranki, zuciyata tana son farinciki”
Ya aje numfashi a hankali sannan ya cigaba.
“Ba zan boye miki ba, bana jin komai a yanzu, kyamarki ko hange wani abu daya same ki a matsayin abun da zai hana ni aurenki ko kuma yin farinciki da ke, ban sani ba wata kila a gaba zuciyata zata iya sauya sai dai bana fatar hakan, kuma a duk halin da na tsinci kaina na miki alkawarin adalci da farinciki”
Ya karasa yana matse hannunta sosai a cikin nasa.
“Sai dai kamin nan ina rikon alfarmarki, ina son...”
Sai kuma ya ji kamar ba zai iya fada ba, kansa ya daga sama kadan ya sauke yaja hannunta a hankali zuwa inda katifa take ya zaunar da ita. Ya saka duka hannayensa ya rika kafardarta.
“Ina son ki min wani alkawari”
Kallonsa tai ba tare da tace komai ba, hakan ya bashi damar gabatar mata da uzurin nasa.
“Ina son auren nan na mu ya zama na sirri, bana son kowa ya san cewa mun yi aure, musamman Momy, Daddy, da kuma Leila da duk wani da yake gidan, daga lokacin da zan dauke ki mu bar gidan nan bana son ki kalleni a matsayin mijinki, har sai idan lokacin bayyana hakan yayi!”
Wani irin kallon rashin fahimta tai masa, a take zuciyarta ta fara raya nata abubuwa mabanbanta, kunyar nunata yake a gurin yan'uwansa ko kuma ya aureta na dan lokaci ne ya rabu da ita shiyasa har baya son kowa ya san alakar dake tsakaninsu? Kamar ya san abun da ke ranta sai fayyace mata komai ta siffar da zata fahimta.
“Na san zaki yi ta Sake Sake a ranki, ba wai na yi hakan da wata manufada nufin cutar dake ba. Tun farko na sanar da Daddy da Momy cewar ina son aurenki, sai dai ban samu goyon baya daga gurinsu ba, and ba zan iya cewa Kaka aa ba, and ba zan iya barin ki fadawa wata rayuwar ba, so i decided na yi auren a boye ba tare da saninsu ba, ba wai ina nufin auren zai yi ta zama a boye ba har abada, no na dan lokaci ne, kuma wannan maganar ina son ta tsaya a tsakaninmu bana son Kaka ta san da komai”
Kallonsa take hawayen dake cika mata ido ya hana ta ganinsa da clear, ta wani bangaren tana jin kamar zata iya, sai dai bata san abun da iyawarta zata haifar ba a gaba, za su yarda su karbe ta ko kuma wani sabon babi na cin mutunci da kyama za su nuna mata, bata gama yanke dayan biyun ba ta ji ya saki kafadarta ya kama hannunta
“Zan tafi yau, ba tare da ke zan tafi ba, kuma zan rika zuwa ina dubaki kamin lokacin da zan dauke ki mu tafi can gaba daya, karki ji komai idan akwai abun da kike bukata sai ki fada min ko ki fadawa Kaka”
A nan mata ce komai ba, sai sauraren yadda yake murza yatsunta a cikin nasa take. Cikin natsuwa ya dago ya kai bakinsa goshinta ya sumbanceta sai ya lumshe ido hawaye suka sauko mata.
“Ba zaki ce Allah ya tsare ba?”
Ya rada mata saitin kunnenta, sai ta aje numfashi a hankali ta hade yawu, tana jin lokacin daya mike tsaye sannan ya mikar da ita sai ya rumgume ta a kirjinsa. Lamooo tai kamar kyanwa tana sauraren yadda zuciyarta da tasa suke bugawa da karfi kuma a lokaci daya.
“Tsarabar me zan miki idan zan dawo?”
Nan ma bata ce komai ba, sai ya dagota a hankali ya kalli kyakkyawar fuskarta yana murmushi.
“Sarkin kuka har da yau kukan kike so ne? Yau fa ranar farinciki ce”
Ya fada yana kai rage tsawonsa ya kai hancinsa saitin nata ya goga mata a hankali, har lokacin idanuwanta a rufe suke.
“Zan je na yi sallama da Kaka..”
Shiru tai tana sauraren sautin tafiyarsa har ya fice daga dakin sannan ta bude idonta sai ta durkushe zaune wasu hawayen masu zafin gaske suka sauko mata. Makomarta take hangowa, ta yi aure auren da Baba da Inna suke da addu'a da burin gani yau ta yi, a lokacin da mutuwa tai mata yankan kauna, kuma auren ya zo mata a baibai ta fuskar data kasa fahimtar ina suka dosa, wani irin zama za su yi kamin komai ya zama daidai? Anya ma komai zai zame mata daidai? Bayan rashin iyaye da rayuwa mai kyau, yanzu kuma kaddarar aure ta bude mata sabon shafi.
“Allah ka taimake ni, ba ni da kowa sai kai Allah, ba ni da gata sai naka Allah, rayuwata tana tafiya a yadda alkalamin kaddarata ya tsara komai, Allah ka yaye min bakincikina ka kuranyen min damuwata, Allah karka jarrabe ni da abun da ba zan iya dauka ba, karka jarrabe ni da abun da zai saka na butulce maka”
Ta roka tana daga hannayenta sama sannan ta shafa addu'ar a fuskarta tare da hawayenta. Tana dukushe a gurin har ya gama abun da zai yi a cikin gidan ya fito, daman tun kamin ya saka Kaka ta kira masa Aminatu ya fada mata cewar ba da ita zai tafi ba, sai ya fara zuwa ya dawo tukuna. Tana jin lokacin da suka iso bakin kofar dakin Kaka na masa addu'ar Allah ya tsare yana amsawa da Ameen, sai wani sabon hawaye ya fara sauko mata wannan karon ba na tunanin makomarta ba ne, na nisantarta da Talba zai yi ne, haka take ji a can lokacin da zai tafi a yau ma haka take ji, saboda tana jin sa kamar wani bangare na rayuwarta, ko kadan bata son yayi nesa da ita. Da kansa ya shigo dakin ya tsaya gabanta yana kallon fuskarta.
“Kuka dai? Ni ko kin ga ban shiri da mai kuka”
Ta yi saurin saka hannayenta ta share hawayen, sai dai hakan be hana su zuba ba, murmushi yai saka nasa hannayen ya rike fuskarta yana share mata sauran hawayen, ganin sun ki tsayawa yai yunkurin rumgumeta, sai dai shigowar Kaka dakin ta dakatar da komai cikin har da saurin dauke hannunsa a fuskarta. Kafafuwanta kawai kake take kallo so take ta gano idan Talba ya taba ba, domin bayan ta kawo ta ta tafi hankalinta be kwanta ba, tana jin kamar zai iya aikata wani abun ya tafi ya bar mata ita daga karshe ma yace ya sake ta.
“Me take yi ma kuka?”
Kallon Kaka yai kamin ya sake kallon Aminatu.
“Bata son na tafi”
“Allah yasa dai ba wani aika aikar kai ba, ka tafi ka barta”
Kaka ta fada tana daga zanenta ta duba kafafuwanta.
“Ku yan birnin nan lamarinku da wahala yake, ni ma ai na yi wauta da na bar maka ita”
“Lokacin da zan aikata ba ki isa ki hana ba, domin matata ce ko a gabanin zan iya komai”
“Allah dai ya tsare yasa babu abun da ya shiga tsakaninku, ke ya miki wani abun?”
Kaka ta tambayi Aminatu, sai ta girgiza mata kai alamar aa. Kaka ta kyale ne kawai ba dan ta gamsu ba, taja hannunta suka nufi kofar fita sai Aminatu ta juyo tana kallon Talba daya biyo bayansu, suna fita daga cikin dakin Kaka ta nufi bangarenta da ita sauran mutanen gidan kuma suka rako Talba har gurin Motarsa suna masa Allah ya tsare, sai a lokacin ma ya tuna da Ali dake zaune cikin tasa motar yana jiransa gaba daya ya manta da shi. Ali na ganin abokinsa ya fito daga tasa motar ya nufo inda Talba yake tsaye.
“Kana can gurin Amarya ka manta da ni”
Talba yayi murmushi.
“To ai dole kai hakuri da ni, ni ma yanzu mai iyali ne”
“Na fika sani, ni da nake da yara ma na rigaka jindadin aure ai, domin ko a yanzu baka da maraba da gwaro, kai da zaka tsere ka bar amarya, kuma wanda ya auri kwaila ai be more aure ba”
“Malam baka san sun fi dadi ba? Kai zaka koya musu komai, amman manyan mata nan idonsu a bude yake sun san komai jikinsu har rawa yake su taba ka”
Ali ya mika masa hannu suka taba suna dariya.
“Talba ashe kai ma A ne”
“To in ba iskanci ba ni zaka fadawa Mace, ni da nake da Leila”
Ali ya bata fuska.
“Matsalarka ke nan, baka da makiyiya Irin Leila, bayan duk cin amanarta da kake a yanzu, gashi har ka yi aure bata sani ba”
“Kai kasan da Leila na aura na fada mata cewa ba zan nuna ta a gurin dangina ba har na wani lokaci da na shiga uku, amman wannan ko magana kasan min ta yi, but i know one thing for sure yarinyar nan tana so na, domin da Kaka taja hannunta za su fita waigena kawai take kamar tace min kar na tafi”
“Daman wace mace ce zata ce bata sonka? Look at you my friend komai ya ji, ai zaka yi tsada sosai shiyasa kake yi ma Leila yadda kake so”
“Take min yadda take so dai, and now komai is over ba zan sake daukar rainon wayonta ba”
Ali ya masa wani kallo.
“What do you mean? Dan ka auri yarinyar ka yi ha'inci Leila kuma yanzu kace zaka bullo da wani abun nooo ba zan bari ba Talba, be kamata ba, ba zan iya saka maka ido ka cutar da Leila ba”
Talba kallonsa yake da wani tunanin na dabam.
“Kai abokin Leila ne kenan not me”
“Ni abokin ka ne? But i won't let anything or anyone hurt her ko da kai ne so karka ce zaka yi mata wani abun just because of ka auri yarinyar nan, bayan kuma kasan idan ta sani zai iya jefata a damuwa, Allah ya tsare hanya”
Ali ya fada da iyakar gaskiyarsa sannan ya juya a fusace ya nufi motarsa, Talba binsa yai da kallo yana mamakin yadda abokin nasa yake zakewa da yawa akan Leila. Yana tsaye a gurin har Ali ya shiga motarsa yai mata key ya kama hanya, Talba yayi murmushin da dan mamaki sannan ya bude tasa motar ya shiga.
MADINA POV.
A firgice ta farka har haki take kamar wanda ta kwato numfashinta da karfi, ta hada wani uban gumi kamar babu ac a falon. Hajiya dake rike da wayarta ta kalleta
“Lafiya?”
“Hajiya Mafarki na yi, mafarki na yi Talba yayi aure ya auri yarinyar nan da na kawo gidan nan”
Ta fada kai tsaye idonta na cika da kwalla kamar ta manta a gabanan mahaifiyarta take.
“To sai me? Ko mata hudu ya aura ma ina ruwanki?”
Ta kalli Hajiya a hankali hawaye na cika idonta.
“Ba saboda ni ba saboda Leila”
“Ba saboda Leila ba ne, daman na lura da take takenki, kuma ina kara jan kunnenki akan lamarin nan ki fita daga hanyar Talba! Ba zaki iya gasa da Leila ba, ba kuma zan bari ki lalata alakata da Mahaifiyarta ba”
Ta yi kasa da kanta hawaye ya sauko mata.
“Hajiya saboda Leila ne”
“Ai na sani, shiyasa daga gama sallah kika kwanta sai mafarkinsa”
Bata sake cewa komai ba, ta mike tsaye ta dauki Hijab din da tai sallah da shi ta nufi hanyar dakinta zuciyarta na wani irin zafi marar masaltuwa, ji take kamar ba mafarki tai ba, kamar gaske ne saboda yadda yanayin ya zo mata. Tana shiga dakinta ta maida kofar dakin ta rufe ta jingina da kofar ta fashe da kuka, mafarkin sai dawo mata yake tana ganin yadda Talba ya angwance cikin farar shadda mai kyau gaske sai far'a yake ana ta shagalin biki, a dayan bangaren kuma Leila tana ta masifa amman ya dage sai yayi auren. Gaba daya sai ta ji tsana bachin rana ma saboda ta yi mugun kafarkin kuka tai sosai ta saka hijab dinta ta share hawayen sannan ta tashi ta isa gurin gadonta inda wayarta take ta dauka ta shiga Instagram ta nemi account dinsa ta makalle a ciki tana kallon hotunansa.
Sai a lokacin ta ji ta dan samu natsuwa, domin ta san yadda yake da kyau nan kuma yake ji da kansa abu ne mai wahala ya auri mace kamar Aminatu.
“Sherin mafarki ne kawai”
Ta fada tana jin zafin zuciyarta na karuwa, kamar wanda za'ayi ma kishiya. Ta fito daga instagram din ta dannawa number Leila kira, ring daya a dauka.
“Hello Madina”
“Na'am Leila ya kike?”
“Lafiya kalau”
“Leila kin yi magana da Momy akan dawowar yarinyar nan gidan nan? Ina ji miki tsiron abun da zai iya zuwa ya dawo domin zata iya dauke masa hankali ya fara zuwa can yana barinki ki daina ganin kamar bata da wani aji wani lokacin maza ba su da tabbas”
“Na yi magana da Momy na san kuma zata masa magana, dole zai dawo da ita gidan ko ba komai zan jidadin wulakantata a gabansa, kuma zan shiga tsakaninsu”
“Yayi kyau, yana gida ne?”
“No ya fita, wai ke baki san me?”
Leila ta kwashe komai ta fada mata. Madina ta mike tsaye da sauri ta nufi gurin windows din dakinta da mugun mamaki.
“Shiyasa ta wani bangaren ina jin tsoron kar a dawo da ita gidan nan ta goge yace zai aureta, na san be isa ya fasa aurena ba, amman zai iya cewa zai hada mu, ni kuwa ba zan taba tarayya da wata ba akan Talba,