Showing 210001 words to 213000 words out of 332834 words

Chapter 71 - Bakar wasika Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

65572

ai kin warke domin zai kula da ke, ki rike abun ki hannu biyu da kyau, ko ba komai ai dan'uwanki ne”
 
Aminatu ta yi kasa da idonta, Haulat ta yi murmushi tana kallonta.
 
“Su Momy sun zo dubaki?”
 
“Eh ta zo, har da Leila”
 
Haulat ta dan tabe baki, sai dai bata ce komai ba, ta bar gulmar a zuciyarta, because this is not the right time da zata yi maganar da wasu da Aminatu no matter how little it's.
 
 
 
***   ***    ***
 
“Ya akai Matarka ta san na auri Aminatu”
 
Talba ya tambaya fuska a hade sam ba zaka ganshi kace shi ne a dazun yake ta washewa Aminatu hakoraba yana rumgumarta.
 
“I told her saboda ta tambaye taga ka saka kudi da duk wanda ya gano inda take, amman ban fada mata abunbuwan da suka faru da Aminatun ba, kawai dai na fada maga gar gudun hijira ce kuma an kashe mata kowa nata, at the end kuma yar'uwarka ce Kaka ta saka ka aureta to abun da ya faru”
 
Talba ya bude motarsa ya dauko jacket din dake ciki ya saka, baya bukatar abokinsa ya rantse masa domin ya yarda da shi 100% akan sirrinsa.
 
“Don't tell me ka zo dubata ne, you're always on Leila side”
 
Cewar Talba yana jan zip din rigar data kara masa kyau. Ali ya sauke ajiyar zuciya.
 
“Look Man I'm sorry, na san na yi abun da be dace ba a ranar, ni ma raina ya bace ne sosai shiya saka abun da kai wa Leila baka kyau ta, taya zaka zargeta da batan Aminatu?”
 
“Idona ne ya rufe ta yadda bana iya ganin komai kuma bana saurarawa kowa a akan Aminatu, kamar yadda naka idon ya rufe ka ci zarafin matata a gabana, kuma kamar yadda idonka yake rufewa a duk lokacin da muka samu matsala da Leila”
 
Mutuwar tsaye Ali yai a gurin sam be tsammaci haka daga bakin Talba ba. Talba ya bude motarsa.
 
“Zan tafi wani gurin, you can take your wife mun gode da ziyara”
 
Yayi shigewarsa motar yai mata key ya bar Ali tsaye a gurin da mugun mamaki, sai da ya daina hango Motar Talba sannan ya ciro wayarsa dake aljihu ya kira matarsa ya ce ta same shi a mota.
 
 
 
_______________________________
 
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
 
 
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
 
 
 
Sai da dare Hajiya Laraba ta zo dubata, domin ta kira mijinta ya ce ta jira har sai ya dawo su taho tare. Haka kuwa akai sai da ya dawo sannan suka zo tare shi ya riko mata kulolin abincin da tai mata, ita kuma ta riko jakar kala biyu data riko mata. Ko da suka shiga dakin Amimatu na zaune kan sallaya tana sallah, Talba kuma na zaune kan kujera rike da wayarsa. Tashi yai ya koma zaman gadon ya bawa mijin kanwar mahaifiyarsa gurin zama.
 
“Maa Shaa Allah, Allah mun gode maka tun dazun na zo na zo ban samu na zo ba, ina fatar dai babu abun da ya same ta?”
 
Ta tambaya tana kallon Talba. Sai ya girgiza mata kai.
 
“Babu abun da ya same ta, kuma dazun  da maraice ma an gwada jininta, hoto ma na can da safe za a karbo”
 
Aminatu na sallamewa ta juyo da sauri ta kalli Hajiya Laraba.
 
“Mama sannu da zuwa”
 
Sai Hajiya Laraba ta tashi da sauri taje ta rumgume Aminatu idonta na cika da kwalla.
 
“Alhamdulillah Auta, kin dawo mana”
 
Talba yayi murmushi domin ya lura da yadda ita ma Aminatun ta kankame Hajiya da alama ta shaku da ita.
 
“Ga abinci ma kawo miki, kuma abun da kika fi so na dafa miki shimkafa da wake”
 
‘Her favorite food’
 
Talba ya fada a ransa.
 
“Ga kuma lemun kwakwa na san shi ma kina son shi sosai”
 
Hajiya Laraba ta fada tana dire katon kofin dake dauke da lemun kwakwa.
 
‘Her Favorite drink’
 
Ya sake fada a ransa yana kara haddacewa.
 
“Na gode Mama, Ina Yusura da Khadija na yi marmarinsu”
 
“Duk za su zo, yau ni zan kwana a nan ne gobe zasu zo su wuni dake”
 
Ta yi murmushi, Talba ma murmushin yake domin yana son farincikin Aminatu.
 
“To ni zan tafi”
 
Hajiya Laraba tana dago tana kallon mijinta daya mike tsaye.
 
“To Allah ya kiyaye, sai da safe”
 
Ya mikawa Talba hannu suka gaisa sannan ya fice. Da kanta ta dauki plate ta subawa Aminatu shimkafa da wanken daya ji vegetables ga egg a gafe sai tiriri yake.
 
“Ya isa”
 
Talba ya fada domin a dan zaman nan na yau da tai asibitin ya lura matarsa ba mai ci bace sosai, gashi daman bata dade da gama cin wani abincin ba. Hajiya ta mika mata, Aminatu ta saka hannu biyu ta karba tana tambayar kaka.
 
“Kaka tana nan lafiya, ban fada mata komai ba, amman nace mata ni da yan'uwa da suke nan da kuma kawaye zamu kai ki gidanki ba sai ta yi wahalar zuwa ba, nace mata idan ta tashi sai ya shirya zan aiko a dauke ta taje ta ga daki”
 
“Kuma ta yarda?”
 
Talba ya tambaya.
 
“Eh ta yarda, amman ta yi da fada daker na shawo kanta, yanzu haka abun da take dauka an kai a jiya”
 
Aminatu ta fara cin abinci a hankali, Talba na ganin haka ya zuba mata ruwa a cup din da Momy ta aiko Mairo ta kawo musu dazun ya mika mata. Sai ta karba ya sha kadan ta rike tana ta cin abinci.
 
Hajiya ta juya ta kalli Talba.
 
“Momynka ta ji abun da ya faru?”
 
“Eh ta sani, dazun ma ta zo ta dubata tare da Leila”
 
“Leila ita ce wanda zaka aura ko?”
 
A nan kam Aminatu dagowa tai tana kallonsa, shi ma kallonta yai kamin ya amsawa Hajiya.
 
“Eh.. Ita ce”
 
Sai Aminatu ta sauke kanta kasa tana tauna abincin a hankali ta kasa hadewa.
 
“Ta ce idan ta ji sauki za mu koma gida a tare, wata kila ma gobe a sallame mu”
 
“Gidan ka ko can family house dinku?”
 
“Family House”
 
“To miyasa ba zaka tare da matarka ba? Kasan dai ba dadin zaman gidan zata ji ba, wata kila ma zata yi ta kallon kamar mun aura maka ita ne saboda mu musguna mata ko yarda daman can ba jituwa tsakaninmu, kuma ga yarta a gidan taya Aminatu zata sake? Ka na ganin dai yarinyar nan marainiya ce kuma amana aka baka”
 
“Bana son na musa mata ne kawai, shiyasa zan zauna da ita a can kamin mu tare din, ke ma ai kin ina da mata ba zai yiyu nai ta zama a gidan ba, kuma for now na san Aminatu tana jin tsoro so zamanmu a can zai taimaka ta manta wani abu kamin mj koma zama mu kadai”
 
Hajiya ta yi shiru tana nazari, kamin ta gamsu.
 
“Toh Allah ya tabbatar da alheri”
 
“Amin”
 
Ya amsa sannan ya duba agogon hannunsa.
 
“Goma ta kusa, bari na tafi gida tun zaki kwana a nan ko?”
 
“Eah Allah ya tsare”
 
“Amin”
 
Ya kalli Aminatu yana jin kamar ya sumbance ta sannan ya tafi amman babu hali saboda Hajiya Laraba na gurin.
 
“Zan tafi akwai abun da kike bukata na zo miki da shi da safe?”
 
Taki daga ido ta kalleshi kuma ta ki amsawa for no reason, har sai da Hajiya Laraba ta maimaita abun da ya fada sannan ta ce.
 
“Aa”
 
Ya juya ya nufi kofa, sai da ya juyo ya kalleta sannan ya fice.
 
 
 
LEILA POV.
 
tana tsaye jikin windows din dakin Momy tana kallon Talba daya faka motarsa ya fita ya nufi part dinsa, sannan ta saki curtains din ta juyo ta kalli Momy zuciyarta na mugun zafi.
 
“Momy anya zan iya jure wannan abun? Kalli fa sai yanzu ya dawo gida yana can gurin wacan yar iskar”
 
“Haka nan zaki daure har ki saba, idan ba haka ba muna nuna mata tsantsar kiyayya, wani abu na faruwa za a fara tuhumarmu, amman idan kika daurewa zuciyarki abun da kike ji babu wanda zai zargi komai, duk kuma kika kuskura kika ce zaki nunawa yarinyar kiyayya karara matsala za ku samu da Talba, wata kila ma yace ba zata zauna a gidan ba ya dauketa su tare can dabam, kin ga tun nan mun fara samun matsala, ni kuwa ba bari zan yi ba ko daki daya ba zan bari su kasance ba balle kuma gida daya”
 
“Amman Momy kina ganin zai yarda ta zauna bangarenmu shi kuma yana can?”
 
“Ai ba a yi kirikiri, na yan siyasa za ayi siye zuciyarsa za'ayi kamin tafiya tai nisa aure ya bare, be da zancen wata mace sai ke”
 
Leila ta sauke ajiyar zuciya.
 
“Amman Momy za a dade kamin abun yayi? Baki ji yadda nake ji ba”
 
“Bana jin zai dade, ke dai bari Hajiya Saratu ta dawo sai mu ji komai, je dakinki ki kwanta da safe kuma ki gaishe shi ko ki tura masa sakon gaisuwa, kuma ki fada masa kina gaishe da yarinyar”
 
“Toh”
 
Ta mike tsaye ta fice daga dakin tana share hawayenta. Sai da Momy ta tabbatar sha daya ta yi sannan ta sauko kasa ta fita daga falon ta nufi harabar gidan. Gurin Mustapha mai gadinta ta nufa yana ganinta ya taso da sauri sai ya koma gefe ya bi bayanta suka tsaya.
 
“Ka bincika?”
 
“Eh Wallahi, su ma garin sun ce be zo ba, rabon Sani da garin nan yanzu wai wata uku”
 
“Subhanallahi, to Allah yasa lafiya yake dai ace a rasa inda mutum ya shiga”
 
“Amin Yanzu haka dana fada musu hankalinsu duk ya tashi”
 
“Magidancin mutum ace ya bata lokaci daya, ko da yake bana jin bata yai tun da har ya iya sakawa gidan padlock wata kila guduwa yai, dalilinsa na guduwa ne ba mu sani ba”
 
“Allah dai yasa yana cikin aminci”
 
“Amin”
 
Ta amsa sannan ta juyo ya dawo cikin falon da tunani kala kala, sai kusan sha biyu ta shirya cikin kayan bachi ta sauko ta nufi bangaren mijinta.
 
 
 
MADINA POV.
 
ta saka hannunta ta dafa goshinta ya sauke ajiyar zuciya sannan ya juyo ta dawo karshen dakin tana sanye da tufafinta na bachi.
 
“Yanzu Abokiyar fadana daya ce, Leila ba Aminatu ba”
 
Ta fada tana cikawa bakinta iska ta busar, tun lokacin da Leila ta fada mata cewar Mama Saratu tace za a tashi tsaye ta kasa samu kwanciyar hankali, tana ji a ranta idan har ta bar Leila ta aikata abun da take kudi ba Aminatu kadai ba har ita kanta ta rasa Talba kenan har abada. Zauna tai bakin gadonta ta dauki wayarta ta kira Leila bugu daya Leila ta dauka.
 
“Yanzu fa nake son kiranki”
 
“Gashi ni na kira ai, ya kike?”
 
“Lafiya kalau, labari zan baki”
 
Madina ta nade kafafuwan kan gadon tana gyara zama.
 
“Wane irin labari ne?”
 
“An ga Aminatu oh Mai sunan Momy ya kama na ce, ko ma nace kazamar yarinyar nan yar kauye”
 
“An ganta a ina?”
 
Leila ta bata labari, sai Madina ta tabe baki not surprised.
 
“Daman ai na san za a ganta”
 
“Kamar ya kin san za a ganta?”
 
Ta dan yi shiru tana nazarin abun da ta furta.
 
“Yeah saboda an baza hotunan a ko'ina, kuma gashi har da tukicin kudi Talba ya saka, kin ga ba zata yi wahalar gani ba, wata kila ma a cikin mutanen da suka dauketa wani zai iya blackmailing din wanda ya sace ta yaje ya kaita saboda kudin, hakan zai saka mai wanda ya dauke ta jin tsoro ya jefar da ita”
 
“Ai ba jefar da ita sukai aka tsinceta ba, sms aka turawa Kabir yaje ya dauke ta”
 
“Ya kai aka samu number Kabir din?”
 
“Oho muma shi ne abun da yake ta bamu mamaki, Momy tace na kusa da mu yake playing wannan game din”
 
“Gaskiya kam, yanzu tana can asibitin kenan?”
 
“Eh amman Kabir yace za a sallame ta gobe, kuma Momy tace a dawo da ita a nan gidan ta zauna”
 
“Kuma kin yarda?”
 
“To miye a ciki ta zo ta zauna din, indai Talba ne ai kwana biyu zasu bare na san halin mutumena ai”
 
Madina ta sauka daga kan gadon.
 
“Allah yasa dai ba kina nan kam bakarki ba, ta yin asiri”
 
“Kai hana ina! Ai tun da kika bani shawarar nan na watsar da maganar, kawai dai ina son na nuna masa ban damu bane ni zan ma iya bar mata shi gaba daya”
 
Sai a lokacin Madina ta samu salama har ta sauke ajiyar zuciya.
 
“Gaskiya kam, kara dai karki yi ki saka musu ido kawai”
 
“Haka zan yi ai, zan kwanta kawata sai da safe”
 
“Sai da safe mu kwana lafiya”
 
Leila ta sauke wayar tana murmushi, for the first time ta fara yi ma Madina karya tana boye mata sirrinta kamar yadda Momy ta koya mata. Aje wayar tai ta fice daga dakin tana saukowa kasa ta nufi kitchen tana son hadawa kanta tea, domin tun ganin da tai ma Aminatu da Talba a dazun bata sake saka komai a cikinta ba. Tana shiga ta samu Kabir a tsaye yana wanke apple a tap. Gurin da aka jera cup ta nufa ta bude ta dauko cup din.
 
“Ina fatar ba wani abu kuke shiryawa yarinyar nan ba, ba zan sake bari ki aikata wani kisan kai ba bayan wanda kika yi ma Baaba”
 
Juyowa tai ta kalleshi.
 
“Da Momy ya kamata kai wannan maganar ba da ni ba”
 
“Saboda Momy ce ta kashe Baaba?”
 
Ta yi shiru tana kallonsa maganarsa na mugun sukarta.
 
“I warn you, karki cutar da yarinyar nan she's innocent bata ita tace Talba ya aureta ba, idan zaki yi fadanki ki yi da Talba not her”
 
Yana kaiwa nan ya dauki plate din dake dauke da apple hudu ya fice daga kitchen din ya barta tsaye tana kallonsa da mugun bacin rai.
 
 
 
BATURIYA POV.
 
 
Fahat ya wara ido yana kallonta da mugun mamaki, domin ya dade yana jiran zuwan wannan ranar, a duk lokacin da yai mata magana sai ta kawo wani uzuri yau kuma da kanta take gabatar masa da bukatar.
 
“Da gaske ko dai mafarki nake yi?”
 
Ta yi murmushi.
 
“Da gaske mana, a gida sun min magana sun ce na fito da miji ni kuma na fada musu babu wanda nake so kai sai suka ce na fada maka ka turo”
 
“Alhamdulillah, na dade ina jiran zuwan wannan ranar, Wallahi gani nake kamar ma mafarki ne”
 
“Gaske, daman na ce yau zan maka albishir da abun da kake so”
 
“Aiko goronki mai girma ne a yau, na jidadi sosai kuma na miki alkawari kyauta ta musamman”
 
Ta yi murmushi, wani irin kallonta yake cike da shauki yana jin sonta na karuwa a zuciyarsa.
 
“I can't wait to talk my mom”
 
“Ba ka ce akwai wanda take son ka aura ba?”
 
“Yes amman ai dole zata so wanda danta yake so ko?”
 
“Haka ne, Allah yasa tai maraba da ni”
 
“Zata ma yi i promise you ina zuwa gidan yau zan bata ku gaisa”
 
“Aiko da na jidadi sosai”
 
Rumgume hannayensa yai yana kallonta cike da shauki, domin har cikin zuciyarsa yake jin son Baturiya, domin tana da siffar da yake so a jikin mace gashi kuma naturally Allah ya saka masa sonta sosai. Sun dade suna hira sannan ta bude motar ta fito rike da ledar da yai mata siyayya ta shiga cikin gidan ita ma cike da shauki. A falo ta baje hajar turarukan saya siyo mata tana murmushi.
 
“Lallai mutumen nan na ji dake, duk ya zo sai yayi miki siyayya mai yawa”
 
Cewar Aisha tana sauko daga kan cushion din da take zaune ta duba kayan.
 
“Dan masu kudi ne sosai, idan na aure shi ba ke ba ko kawayenki sun huta balle kuma ke, fatana dai Umma ta bani hadin kai”
 
“Ba ruwan Umma ita daman abun da take so kenan ai, Ya ma da kansa yai magana ya ce ki fito da mijin aure fa”
 
“Na sani, ai yanzu haka na masa maganar, yace min zai je ya samu iyeyensa yai maganar da su, duk yadda sukai zai kirani ya fada min, kuma yace kamin su zo zai so ya gaishe da Umma kuma su gaisa da Yaya”
 
“To miye abun tsoron?”
 
“Aisha be san na taba aure ba, kuma ban taba fada masa ba, a zatonsa ni budurwa ce, shi ne nake son na lalaba Umma ta goya min baya ta yi magana da Yaya”
 
Aisha ta rufe baki.
 
“Amman kin yi kuskure gaskiya, ai gwara dai ki fada masa gaskiyar idan ma ya ji ba zai iya aurenki a haka ba ai kin ga dai kin fada masa gaskiyar, domin idan ya sani zai ji haushi”
 
“Abu ne mai wahala ya sani, domin su masu kudin nan ba wani bincike suke akan aure ba, ko ba su ba ma yanzu an daina wani dogon bincike akan aure ai”
 
“Amman idan ya aureki zai gane ai, sannan ya zaki yi da Sultan idan zai zo ganinki musamman idan yai wayon ya san yaje gurin mahaifiyarsa?”
 
“Sultan saba masa zan yi da zama a gurin mahaifinsa shiyasa ai ban damu naje na duba shi ko sau daya ba, duk da yana rai na amman bana son ya saba da ni ne. Wannan kuma kamin na yi auren zan tafi gurin yar gidan mai fata ta gyara ni zan siye set din back to virgin shikenan an wuce gurin”
 
“Tab amman dai gaskiya kin yi sakaci, da dai kin fada masa gaskiya idan ya ji zai aureki a haka sai ya aureki, idan kuma ya ji ba zai iya ba kin ga baki yaudare shi ba”
 
“Ni dai yanzu abun da nake so dake ki taimaka min, ki lallaba min Umma ta amince kuma ni ma zan yi magana da ita kuma zan saka Anty ma ta yi”
 
“To Allah yasa ta aminta”
 
“Aamin yawwa yar kanwata haka nake son ji”
 
Ta fada tana dauka kusan turare uku ta mika mata kyauta.
 
FAHAT POV.
 
yana shigowa falon ya zarce

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login