Showing 276001 words to 279000 words out of 332834 words

Chapter 93 - Bakar wasika Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

65616

ta juyo da zimmar duba ko waye, sai dai kamin ta karasa juyowa Fahat ya karaso inda take tsaye rike da takardu a hannunsa yana kallonta, kamin ya kalli mahaifinsa da fuskarsa take a hade ya karasa gurin tebur din ya aje masa takardun.
 
“Fee'at mi kike a nan?”
 
Ta dan yi murmushin karfin haka dake hade da mamaki tana sauke hannunta daga nuna Alhaji da take.
 
“Am... Ha.... Eh... Na.. Na.. Nazooo.. Gurin... Abokin Babana ne...”
 
Da mamaki Fahat yake kallonta yana karantar yadda ta rasa matsuwarta da kuma ya tararda ita tare da mahaifinsa.
 
“Daman ka santa ne Abbah?”
 
Ya tambaya yana kallon mahaifinsa, Alhaji Idris ya hade yawu da karfi yana kokarin daidaita kansa.
 
“Eh... Yar abokina ce... Na ce ta zo ta karbi abu ne...”
 
“Ita ce wanda zan aura ai”
 
“Wannan...?”
 
Alhaji Idris ya nuna Baturiya da sauri yana zaro kamar wanda ya ga wani abun tsoro.
 
“Yes”
 
Wani uban gumi ne ya karyo ma Baturiya, wata muguwar mutuwar tsaye tai da mamaki.
 
“Fahat... Alhaji Idris Ali ne mahaifinka?”
 
“Yes, and it seems like you know each other...”
 
Ya fada with confused, domin bata taba nuna masa ta san mahaifinsa ba, duk da yake ba taba zaunar da ita ya fada mata waye takamaiman mahaifinsa nasa ba, kuma ba zama lalle ace mahaifinsa ya san ita zai aura ba saboda ya ce a gurinsa kuma da mahaifinta yake alaka ba da ita ba.
 
“Allah sarki...yarinya mai kirki.... Allah sarki tana da tarbiya sosai.... Ai ban san ita ba ce, mahaifinta yana da kirki sosai abokina ne yanzu ma shi ya aiko ta ta karba masa sako...”
 
Alhaji Idris ya fada yana dariyar data zame masa dole. Fahat ya kalleshi cike da zargi.
 
“Mahaifinta ya rasu Abbah”
 
Sai Alhaji Idris ya kara fada da dariyarsa....
 
“Aha... Aha... Aha.. Haka ne.. Wallahi... Wallahi... Ya rasu... Ka san sabo... Na ga kamar yana raye.... Haka...ne.. Allah ya masa Rahama... Ke. Baturiya kike ko India sai ki tashi ya kai ki gida ai, ba yanzu zan tashi aiki ba ni da sai na sauke ke ki...”
 
Ya karasa yana saka babbar rigarsa ya share gumi dake sauko masa duk kuwa da irin sanyin ac dake office din.
Baturiya da hawaye ya gama wanke mata fuska ta share hawayenta ta maida kanta masa.
 
“Zan hau Napep”
 
“Muje na sauke ki mana”
 
Fahat ya fada, yana jin wani irin abu a zuciyarsa narar misaltuwa, domin a yanzu ya soma yardar da wani abu da zuciyarsa ta taba raya masa akan Baturiya a lokacin da ya ga mai kama da ita a gidan hutawar mahaifinsa yaki yarda da zuciyar tasa.
Wucewa yai gaba ta bi bayansa tana tafiya kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki, bata taba jin kunyar data hana ta numfashi yadda ya kamata ba irin wannan, a yau ba jin take kamar kasa ta bude ta shige ba, ji take kamar ta mutu gaba daya ta huta. Sai da Fahat ya isa gurin motarsa da kusan minti goma sannan ta iso ta bude motar jikinta na rawa ta shiga ta zauna ta rufe motar ta kasa kallon inda yake. Shi ma be kalleta ba har yayi ma motar key ya suka bar harabar ma'aikatar.
Uffan bata ce masa ba shi ma be ce mata ba har suka isa kofar gidansu, ya faka a inda ya saba fakawa, sai ta kasa bude motar ta fita kuma ta kasa kalle inda yake balle tai attempting din yi masa magana.
 
“Baki taba fada min ko nuna min kin san mahaifina ba, miyasa kike boye min abubuwa ne? At first na dauka auren da kika taba yi ne kawai abun da zaki boye min”
 
Ta kalleshi da sauri.
 
“Fahat waya fada maka na taba yin auren?”
 
“Bincike, Fee'at ko a cikin masa kai abu ba zai taba boyuwa ba, domin wata rana zai fito kowa ya gani ko ya ji, balle babban abu kamar wannan, a lokacin da na, na yi ta kokarin karyatawa saboda baki fada min ba, amman daga baya na yarda saboda gaskiya ce ko na yarda ki akasin hakan, na ga laifinki sosai a lokacin kuma kin bata min rai, amman na yi ta kokarin danne zuciyata na ganin ban ga laifinki ba, kuma a haka na ayyana a raina cewar zan iya aurenki saboda ina sonki, wannan ya saka na kaurace miki na kwanakin nan saboda na auna son da kike min kuma na nuna miki girman laifin da kika aikata”
 
Be karasa ba ya tsaya saboda bacin dake zuciyarsa dake saka shi jin kamar zai amayar da zuciyar daga kirjinsa, domin muryarsa har rawa take kamae ba tashi ba. Ta kalleshi tana kuka marar sauti irin wannan dake shiga zuciya ya danne numfashi.
 
“Ban boye...maka dan komai ba, sai dan ina tsoron an rasa ka Fahat, ina jin tsoron kar ka san cewar na taba aure har ina da yaro ka fasa aurena... Kuma Wallahi ban san cewar Alhaji Idris mahaifinka ba ne... Ban sani.. Ba Fahat”
 
“A lokacin da na ganki a office din, da farko na yi tunanin ko kin kawo karata ne ko kuma kin zo ki roki mahaifina ya bar ni na aureki ne, sai dai na karanta yanayinki ke da shi sai na fahimci akwai wata alaka mai karfi a tsakaninku, domin na taba ganinki a gidansa amman ban bar zuciyarta ta kulla abun da take son kullawa ba saboda na kyautata miki zato, na rasa gane wace irin macece ke Rafi'ah, taya zaki yi taraiya da mahaifina kuma a haka zuciyarki ta daya miki aurena daidai”
 
“Billahil Azeem ban san Alhaji Idris mahaifinka ba ne Fahat, ban sani ba”
 
Ta fada tana Fashewa da wani irin kuka.
 
“Na ji, fitar min a mota”
 
Ta bude motar ta fita still tana kuka kamar ranta zai fita, wani mugun kallo Fahat ya watsa mata yana jin wani irin tsanarta a zuciyarsa domin kazantarta ta shahara a gurinsa, bayan boye masa asalin aurenta yanzu kuma ya gama fahimtar mu'alamar ta da mahaifinsa, domin da farko ne yayi ne kawai saboda ya bugi cikinta kuma ta bashi damar fahimtar komai.
 
 
 
 
 
LEILA POV.
 
A gidan Hajiya Saratu ta kwana a dakin Momy.  Momy kuma ta kwana a bangaren Abbah, bata dawo bangarenta ba sai da safe shi ma saboda ta zuba masa nasa abun karyarwa ne da yan aikinta suka gama gadawa. Bayan Momy ta gama shiryawa Daddy komai nasa na karyawa sannan ta juya zata fita.
 
“Ina ganin gobe a asibiti zamu yi breakfast da lunch da dinner”
 
Momy ta juyo ta kalli Daddy da mamaki.
 
“Asbiti kuma?”
 
“Eh, kin san mun saba yin breakfast da lunch tare every week, so wannan weekend din Mu'az yana asibiti a can ya kamata mu yi tare da shi zai jidadi”
 
Daddy ya fada bayan ya kai soyayyen dankwali bakin. Sai ta amsa masa domin ta san bata isa ta musa masa ba, kuma bata isa ta nuna masa bata so ba, saboda ta san yadda yake jin Talba, abu kadan zai iya munana mata zato.
 
“To Allah ya kaimu, a shirya komai kamin lokacin”
 
Ta fada sannan ta juya ta fice tana tabe baki, bangarenta ta dawo bacin rai da damuwar da take ciki ba zai barta ta tsayawa yin breakfast tare da Daddy ba, shi kuma be damu ba domin ya saba time to time ta kan yi breakfast dinta ita kadai ba tare da shi ba, ko kuma shirya masa abun karyawa ya ci shi kadai kuma tana a zaune kusa da shi ba tare da ta ci ba. Da mamakin maganar da Daddy yai mata ta dawo bangarenta ta shiga dakinta ta samu Hajiya Saratu tana karyawa, kusa da ita ta zauna tana labarta mata abun da Daddy ya fada mata.
 
“Tun ba yau ba ai ina ta nuna miki hanya amman kika rufe ido gam kika toshe kunnuwa ke ba zaki saureare ni ba, yanzu ai ga irinta nan”
 
Momy ta daga kai.
 
“Ai ko jiya sai da na tuna da maganarki, na ce da na bi shawararki da yanzu ba wannan labarin ake ba, shiyasa na ce ki kwana a nan saboda mu san yadda za a bullowa lamarin nan”
 
“Bullowa lamari ya wuce ki tashi tsaye, ki kama mijinki hannu biyu ya zama kamar waina a tanda, yanzu irin wannan kudirin da yai na cewar aje can a ci abinci idan isassun mata ne ya isa ya yanke wannan hukuncin ba tare da ya shawararce ki ba? Ke kina ganin idan wata Hajiyar ce mai amsa sunanta Talba har ya isa ya taka dokarki balle ya fakaici idonki ya aurowa yarki kishiya wata yar kauye jahila?”
 
“Abun da na gama tunani kenan jiya, sai a yanzu nake ganin illar tsallake maganarki da nake ta yi Wallahi”
 
“Yanzu ni abun da nake ganin yafi kawai ayi miki na mallaka tsakaninki da mijinki, a mallake miki kowa har Talban, ai yawancin matan manyan gidaje haka suke yi, sai ki ga ko kallonsu ba a son yi saboda tsoron”
 
“Gaskiya ina son irin wannan ta yadda idan na fadi magana daya ta zauna kenan ba canji. Bayan shi kuma akwai wata matsalar”
 
Hajiya Saratu ta dauki kofin tea ta sha ta aje tana kallon Momy.
 
“Wace matsalar ta Aminatu?”
 
“No”
 
Cewar Momy tana kallon Leila wance da shigo sanye da gown din doguwar rigar atamfa kamar kullum kanta babu mayafi. Kusa da Momy ta zauna cikin yanayi na tausayi da ramar fuska irin na tashin hankali.
 
“Mama Saratu Good morning”
 
“How are you Leila? Baki jin dadi ne?”
 
Momy ya janyota jikinta ta kwanto da ita cike da tausayinta.
 
“Ina lafiya ita kuma kawa ta saka ta gaba”
 
“Ban gane ba, kawa kamar ya?”
 
Momy ta sauke ajiyar zuciya tana tunanin ta inda zata fara bawa kanwarta Saratu labarin abun da ya faru, sai dai ya zama dole ta fada mata komai saboda amsawa kanta mafita.
 
“Kuskure ne ya faru, akwai wata mai aiki da na yi wata tsohuwar da muke kira da Baaba idan zaki tuna”
 
“Na san Baaba kam, ba ta bata ba?”
 
“Ba bata tai ba, mutuwa tai”
 
Cike da mamaki Hajiya Saratu take kallon Momy.
 
“Amman aka ce mana fa bata”
 
“Mun yi hakan ne saboda a rufe komai, abun da ya faru muna zaune Falo tare da Amal, sai Leila ta shigo cikin fushi ta nufi dakinta, to a lokacin Baaba na tsaye stairs tana mopping, a maimakon Leila tai mata magana tace mata ta bata waje ta wuce sai ta fisgota ta hannu ta jefar, kin jikin tsufa, sai matar nan ta gangaro ta fado kasa, tun da ta fado bata motsa ba har muka dauke ta zuwa asibiti, kamin mu isa asibitin ta farfado tai kalmar shahada tana fadin kafarta kanta sai kuma yai shiru, na faka mota na taba ba ban ji alamar numfashi ba, sai na yi zaton ta mutu kuma kin san idan muka ce zamu je asibiti dole kowa zai yi, ga Leila sai kuka take min, na rasa yadda zan yi da ita sai na yi tunanin binneta”
 
Hajiya Saratu ta gwalo ido tana kallon Momy da mugun mamaki da kuma tsoro, Leila kuma ta fashe da kuka tana shigar da kanta jikin Momy tana boye fuskarta.
 
 
 
 
_______________________________
 
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
 
“To kika yi yaya da gawar?”
 
Hajiya Saratu ta tambaya baki sake tana mamaki yadda Momy ta iya aikata wannan abun. Cike da nadama da damuwa Momy ta ce.
 
“Mai gadin tsohon gidan gonata na kira, na fada masa ina son ya haka min rame saboda na zuba wasu kudade da gwalgwalai, gudun kar yayi wani tunani ya saka na ce yayi ramen a tsaye kuma na fada masa a cikin dare nan nake son yayi min shi, a take a fasa bangaren da muke aje tankin ruwa ya yi dogon rame, sai na isa gidan ya tsaya a gaba ya marasa ramen, sannan nace ya fita waje ya tsaya daga waje ko da zai ga wani mai zuwa, ni da Leila muka dauko gawar muka saka a zaune cikin ramen saboda ba zai isa mu kwantar da ita ba, haka dai muka saka a takure muka rufe, sannan ya kira shi ya dawo na fada masa cewar na aje dukiya mai yawa a gurin, kuma saboda na yardar da shi ne yasa na yi haka, bam yarda ya fadawa kowa na yi ajiya a gurin ba ko da kuwa matarsa saboda za a iya budewa idan kuma aka bude shi zan zarga, sai na saka ya dauko takin ruwa ya mulmulo shi zuwa gurin kasar na ce ya sika shi da ruwa, ban bar gurin ba sai na tabbatar ya cika tankin da ruwa”
 
“To yanzu ina mai gadin yake?”
 
“Wallahi ban sani ba, lokacin da Madina ta fara yi mana abubuwan nan, naje duba shi aka ce wai ya tashi daga gurin tare da matansa da yayansa, kuma babu wanda ya san inda suka koma, har garinsu na saka an bincika min ance baya can, ban san inda yaje ba, gidan ma an rufe shi da padlock da na so a bude amman ina tsoro ban san ko gawarsa ce a cikin gidan ba ko kuma wani abun, kar na shiga ciki na jefa kaina a matsala kuma kar na kira mutane a tararda wani abun asirinmu ya tonu”
 
“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, kai Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, Allah ya tsare mu da mummunar kaddara, domin wannan ita ake cewa mummanar kaddara”
 
“Shi ne sai...”
 
Momy ta zayyana ma Hajiya Saratu komai from A to Z, na abun da Madina take mata har zuwa jiya da ta aiko mata da wannan wakon. Hajiya Saratu ya jinjina kai tana kallon yar'uwarta.
 
“To ai ni har na fasa wanne ya fi bani mamakin tsakanin abun da kika aikata da kuma wanda Madina take yi, yanzu Fisabilillahi duk kin san da wannan abun amman kika rufe baki fadawa kowa ba?”
 
“Gani na yi ba wani abun dadi ba ne da zaka yi ta yadawa duniya, kuma kin san halin mahaifiyarmu tana jin maganar nan zata fitine ni”
 
“Ai ba dole sai ta jiya ba, a tsakaninmu ma sai mu samawa kanmu mafita, yanzu da kin fada min wannan abun tun wuri ai duk be kai ga haka ba, balle har ita Madina ta samu wata dama ta yi ma Leila zagon kasa”
 
“Yanzu dai aikin gama ya gama, mafita muke nema shiyasa ma nace ki zo nan ki kwana, domin abun ya daure min kai, duk tunanin da na yi sai ga kamar ba mafita ba ne”
 
“Yanzu ita Madina ko d ace Leila ta barta sak ta yarda ta auri Talba saboda bata da kunya ko?”
 
“Ai da ta san kunya da bata aikata abun da take aikatawa a yanzu ba, duk kuwa da ta san da cewar an gano ita ce, shiyasa ai jiya na aika mata da sako”
 
“Kika ce mata me?”
 
Hajiya Saratu ta tambaya, Leila kuma ta dago tana kallon Momy domin bata san Momy ta aika mata da sakon ba. Hajiya Saratu ta girgiza kai bayan Momy ta fada mata sakon data tura mata.
 
“Wani lokacin kina ba ni mamaki yaya, kina babba amman tunaninki kamar na autar mu, ke da kike neman mafita kuma zaki yarda ki tura mata wani sako irin wannan?”
 
“To ya zan yi Saratu? Ta saka Leila a gaba, ga tashin hankalin da muke fama da shi na Aminatu ita kuma wannan ta kunno kai tana son kara mana wani”
 
“Ai ba zaki nuna mata komai ba, so that tai ta zaton kuna jin tsoronta, daga nan zamu samu sa'a ku cafke kafarta ku jefa rame”
 
“Taya, a yadda na fahimta ba zata daina abun da take ba saboda bata samu cikar burinta, kuma kin ga tana tsoron asirinta ya tonu na sace Aminatu da tai ya zama ita kadai ce a kan case din, so take ta jefa Leila ciki ayi mutuwar kasko”
 
“To ai wannan kadai ya isa ya saka bi bita sannu sau da kafa har ki samu sa'arta”
 
“Yanzu me kike ganin za'ayi?”
 
“Me kuwa za'ayi da ya wuce a binneta”
 
“A binne ta kuma?”
 
Wannan karon Leila ce tai tambayar cike da mamaki.
 
“Eh mana, mai neman mutuwa ba kamata yai ka tura shi a rame ya mutu ba, ke yanzu ban da shashanci irin na ki irin wannan sirrin ai ba abari ya fita, mutane da yawa suna aikata irin wannan abun wasu ma dagangan suke amman basa barin kowa ya san abun da suka aikata”
 
“Ni ma abun da na yi ta nuna mata kenan”
 
Momy ta fada tana kallon Leila. Hajiya Saratu ta ce.
 
“Ko da saboda irin wannan abun, ya saka mutane suka daina binne gawa sai dai a jefar, saki ki ance an tsinci gawar wane ko wance a guri kaza ba a san wanda ya akashe ta ba, wannan ko Madina bata yi ba wai mai gadin zai iya yi muku idan ya san me muka aje a gurin kuma akai sa'a dan duniya ne, gaskiya kin yi sake Yaya ai jefarwar ake, sai ku samu wani rame ko bakin ruwa ko rijiya ki jefata”
 
“To kuma idan aka gano gawarta fa na ce mi? Lokacin da abun ya faru dare ne ba safiya ba ko rana, domin tana mopping din dare ne, a lokacin mopping biyu take mana saboda ta san bana son kazanta tsantsin gurin ne ma da be gama bushewa ba ya kara janta ta fadi”
 
“Sai ki ce kin aiketa ta siyo miki wani abu, amman irin wannan abun ba dan kuna yan babban gida ba ai da police ma madai za su iya gono karya ne domin za su iya fadada bincike su gano gaskiya, ai ko Amal da Kabir be kamata su sani

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login