Showing 264001 words to 267000 words out of 332834 words

Chapter 89 - Bakar wasika Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

65565

zo?”
 
“Wannan ai na tsakaninta da Talba ne, yace sai ta zo wannan kuma na Aminatun da Talba ba kin ce shi ne yace zai yi da Ja6a ba”
 
“Eh shi ne, zan koma gobe na yi masa bayani, wata kila an samu matsala ne”
 
Momy ta daga mata kai ba dan hankalinta na gurin ba, tunaninta ya tafi gurin abun da Leila take yi ma ihu, domin ta lura da envelop din hannunta lokacin da zata wuce.
 
“To wai Hajiya na ce ita wannan yarinyar a nan zata kwana tare dashi?”
 
“Aa yanzu nan zan aikata gida, na bar mata dakin ne saboda bana son na yi wata abun da zai saka Engr magana, amman daga yau ma ba zan sake bari ta zo asibitin ba”
 
“Yauwa haka ya kamata, ko da magani sai da aikatawa fa sai ana yaki da baki magani ya fi ci, kuma idan ta koma gidan nan Leila ta saka ido ayi mata miyar ta dabam a saka wannan maganin a samu ta ci, ya ce ta taci fa shikenan bukata ta biya”
 
“Ko ba Leila ba, ni da kaina ma zan saka ta cin abincin ai”
 
“Ya ma fi, tun da ita ba maida hankali take ba, kuma idan ke ce zata iya ce amman Leila zata iya mata rashin kunya ma ko kafiya saboda Talba ya bata fuska ta riga ta raina ta”
 
Momy ta daga mata kai, tana wani tunanin na dabam.
 
‘Wato Madina sake aiko mata tai da sakon nan ko kuma me?’
 
Ta tambaya kanta tana jin kamar ta daga waya ta kira Leila ta tambaye ta, amman ba dama saboda kanwarta na gurin, ita kuma Momy bata yarda kowa ya ji wannan abun da suka aikata ba, Madina ma saboda rashin jin Leila ne rike sirrinta ya saka ta sani.
 
AMINATU POV.
 
Ko da ya fito ya samu Aminatu ta zuba masa komai ta zauna tana jiran ya fito. Ido ta kura masa tana kallon yadda yake cira kafarsa yana takawa a hankali ya karantar da yanayin da yake ciki, duk kuwa da irin kokarin da yake ya boye mata, da ido ta bishi har ya zauna.
 
“Kirjin yana ciwo har yanzu?”
 
“Aa ba sosai ba”
 
“Likita yace ka ci abincin zai zo ya baka magani”
 
Ta fada tana kallonsa cike da tausayinsa. Ya gyada mata kai yana murmushi, sai ta fara mika masa tea har ya mika hannu ya karba sai ta zarce da shi ta kai masa a baki, kallonta yai sannan ya bude bakin zai sha.
 
“Bari dai na ji zafinsa kar ya kone ka”
 
Ta maida kofin bakinta ta fara kurbawa kadan.
 
“Akwai zafi”
 
Ta soma hura masa, ta sake kurbawa sannan ta kai masa a baki.
 
“Bude bakin”
 
Ya bude ta zuba masa kadan.
 
“To hade”
 
Ya hade kamar yadda ta bukata sannan ya sake budewa ta kara masa, ya hade ta sak kara masa.
Wato yau ita ce babba shi ne karami kenan, dariya ce sosai ta zo masa, sai dai ciwon kirjin da yake ji ba zai bashi damar yin dariyar ba, kadan kadan take ba shi har ya sha ya koshi, sannan ta aje ta dauko plate din abincin ta fara bashi a hankali yana taunawa.
 
“Zauna nan”
 
Ya fada yana riko kwankwasonta ya zaunar da ita saman jikinsa. Ba musu ta zauna saman jikinsa tana bashi abinci a hankali yana ci.
 
“Na koshi”
 
Ya fasa yana kawarda kansa, sannan ya mika hannu ya karbi plate din.
 
“Kawo na baki”
 
“Aa bana ci”
 
“Why? Kin ci abinci”
 
“Eh”
 
Ta fada ba dan ta ci din ba. Sannan ta sauka saman jikin ta dauko ruwa ta zuba masa a cup ta kai masa a baki ya sha.
 
“I love you so much”
 
Ya fada yana rumgumota, har cikin ransa yake jin kaunarta. Sun dade a haka sannan ya sake ta ta aje cup din tana kokarin hada kayan abincin gefe daya Ali yai knocked dakin, sanin yadda ya tararda su dazun ya saka yanzu ya zabi sanar musu da zuwansa kamin ya shigo.
 
“Yes”
 
Talba ya fada, sai ya turo kofar dakin ya shigo hannunsa rike da ledar magani.
 
“Allah yasa ka ci abinci”
 
“Yeah na ci”
 
“Good”
 
Ya fada yana aje maganin a inda aka tana da domin aje magani, sannan ya bude ledar ya fara hada allura, Aminatu na gani ta rumtse ido. Talba ya saci kallon Ali ya ga hankalinsa ba a gurinsu yake ba, sannan ya saka kafarsa ya goge a kafar  Aminatu kadan, sai ta bude ido ta kalleshi ya sakar mata murmushi sai ta maida idon ta rufe.
 
“Neighbor din mu ya kirani yace shi ne yayan yarinyar nan yana son ganina bla bla bla, zai zo ya same ni, wai yana son ganin yarinyar na ce masa a a, ni ma a karkashin ikona take ba, bari zan yi magana da mijinta tukuna”
 
Aminatu na jin haka ta bude ido da sauri.
 
“Wallahi da gaske ne, yayana ne na ganshi, Ya Bashir ne”
 
Talba ya kalleta sannan ya kalli Ali.
 
“Yaushe ka san makocin ba”
 
“An dade gaskiya, kuma abun da yasa na yarda da shi saboda Matata ta taba fada min cewar an kashe masa duka family da suke kauye Galadi, har gaisuwa na yi masa a lokacin, amman abun da yake ba ni mamaki ya akai ya zama yayanta bayan ta fada mana cewar an kashe mata kowa”
 
Yana kai aya, Aminatu tai karaf jiki na rawa ta ce.
 
“Wallahi ba karya nake ba, a lokacin...”
 
Bata karasa Talba ya riko hannunta ya girgiza mata kai.
 
“Bari na yi magana da shi, idan har da gaske yayanki ne, abin farincikin mu mu duka, kuma babu abun da zai saka na hanaku haduwa da juna, amman sai mun bincike sosai, saboda bana son abun da zai cutar da ke, ki kwantar da hankalinki okay”
 
Ta daga masa kai idonta na cika da kwalla, tana sauraren yadda yana murza yatsun hannunta a hankali. Ya mikawa Ali dayan hannunsa dake da cannula yai masa allura, sannan ya cire safar hannunsa ya balla magani ya mika masa. Talba ya karba da hannunsa na hagu sai Aminatu ta zare hannunta daga nashi ta zubo masa wasu ruwan ta mika masa ya karba ya sha maganin.
 
“Ka bincika mana shi sosai Ali, har DNA test sai anyi, saboda bana son wani abun da zai je ya dawo, kasan dai ba mu gama fita daga wani ramen ba”
 
“I know”
 
“Ina wayata?”
 
“Tana office”
 
Talba yayi shiru be ce komai ba, har Ali ya gama abun da zai yi.
 
“A kawo maka wayar ne?”
 
“Yeah”
 
Ali ya juya ya fice daga dakin. Ba dade ba da fita ba Momy ta turo kofar ta shigo Aminatu na ganinta ta sha jinin jikinta, ta dan matsa can kusa da gadon asibitin ta tsaya, Talba ya kalleta yana jin tausayinsa ganin yadda ta rakube yanayinta ya canja saboda shigowar Momy kawai.
 
“Ke je waje direba yana jiranki zaku tafi gida”
 
Aminatu ta kalli Talba da sauri kamar mai shirin yin kuka.
 
“Ai yayi waya da Mama tace zata zo ta dauke ni yanzu”
 
Momy ta kalli Talba dake kallonta.
 
“Wace ce Mama?”
 
“Hajiya Laraba”
 
“Okay baka yarda da zamanta a gidanku ba ne, shiyasa zaka kira wata ta tafi da ita ko me?”
 
“No ta kira ni ne, saboda ta mun yi da ita cewar yaranta za su zo su duba mai sunaki, sai na fada mata cewar na samu hatsari ina asbiti, shi ne tace zata zo ta duba ni daga nan sai ta tafi ta ita saboda tufafinta suna can idan ta dauko sai akaita can gidan gurinku”
 
“To ka fada mata, ya zo mata da tufafinta, gidanmu zata zauna domin ita a yanzu matarka ce”
 
“Toh Momy”
 
Ta kalli plate din abincin.
 
“Ka ci abinci?”
 
“Yeah na ci har na sha magani”
 
“Okay, ki jira ta zo idan kuka gaisa sai direba ya kaiki gida”
 
Ta karasa tana kallon Aminatu, kamin ta juya ta kalli Talba.
 
“Ka kirata ka fada mata ta zo mata da tufafinta”
 
“Okay”
 
Ta juya ta fice daga dakin, komawa tai gurin Hajiya Saratu ta dauki jakarta.
 
“Saratu zan je gida na dauko kayan kwana na dawo”
 
“Oh ke zaki kwana da shi? Na dauka Kabir zai kwana a nan ai”
 
“To zan yi magana da shi na ji, idan zai kwana nan ne sai mu dawo tare shi ya kwana a dakin mu kuma mu kwana a waje, wai kin jin yaro munafuki hatsarin nan daya faru har ya kira dangin uwarsa ya fada masu”
 
Hajiya Saratu ta kebe baki.
 
“Too shi Talba?”
 
“Eh, wai har yana fadar Hajiya Laraba zata zo ta tafi da Aminatu”
 
“Karki yarda Wallahi”
 
“Ai na ce masa aa, ta zo dai su gaisa a nan din. Ni zan tafi sai na dawo”
 
“To Allah ya tsare”
 
Momy ta nufi kofar fita tana kiran direbanta a cikin motar data saka shi jiranta tun a lokacin daya kawo ta asbitin, ba dan ta dauko tufafi take son tafiya gida ba, sai dan tai magana da Leila kuma ta bincika halin da yarta take ciki.
 
 
***  ***  **
 
Momy na fita Aminatu ta zuba a gurin zata fara kuka, Talba yai saurin mika mata hannunsa.
 
“No no noooo, karki yi kuka na san baki son zuwa can ai, wayo zamu yi ma Momy idan ta zo sai ta tafi dake a boye”
 
Ya fada yana riko hannunta ya matso da ita kusa da shi, sannan ya saka dayan hannunsa mai cannula ya share mata hawayen da suka fara mata zuba. Knocked din da Ali yai ne yasa shi sakinta ya kalli kofar.
 
“Yes”
 
Ali ya turo kofar ya shigo, ya mika masa wayar, ba tare da yace komai ba ya kalli Aminatu sannan ya juya ya fice
 
 

Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
 
Kunna wayar ya yi ya shiga ma'adanar numbobi ya nemo number Hajiya Laraba ya yi dialing din number ya saka a speaker, sannan ya dago kansa yana kallon Aminatu dake tsaye kusa da shi tana kallon wayar. Dayan hannunsa ya saka ya zagaye madaidaicin kunkurunta, fuskar shagwaba tai, sai dai tana jin muryar Hajiya Laraba sai ta fara murmushi.
 
“Assalamu Alaikum”
 
“Amin'Wa'alaikissalam Mama ya gidan?”
 
“Lafiya kalau, na kira wayarka na ji ta a kashe”
 
“Eh na samu hatsari ne, amman dai da sauki, ina asibiti yanzu haka”
 
Daga can cikin wayar Hajiya Laraba ta amsa da
 
“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, Subhanallahi, garin ya?”
 
In brief ya fada mata abun da ya faru sai hankalinta ya tashi sosai.
 
“Allah ya tsare gaba, kana waje asibitin yanzu?”
 
“Huda Special Hospital”
 
“Toh gani nan zuwa yanzu, wani daki”
 
Sai da ya kalli Aminatu take da zumundin a bata wayar sannan ya ce.
 
“Emergency, Mama ga Aminatu tana son magana dake”
 
“Okay tana kusa da kai?”
 
“Eh”
 
Ya mika mata wayar, tana karba sai ta raba jikinsa da nata ta nufi kofar fita, shi dai binta kawai yai da kallo har ta bude kofar dakin ta fice, a zahiri karamace amman tana da basira da wayo irin na manya. Sai da ta janyo kofar dakin ta rufe sannan ta jingina kusa da kofar ta kara wayar a kunnenta.
 
“Mama”
 
“Na'am Aminatu kina lafiya”
 
Hajiya Laraba ta fada cike da tausayin Aminatu.
 
“Lafiya Kalau, Mama ki zo yanzu ki tafi da ni dan Allah, Momy tace zan kwana a gidanta ni kuma bana son kwana a gidanta, kin san ita da Leila wulakanci suke min, ko yanzu da ta zo sai da ta fada min magana marar dadi, kuma ni dai na fi son gidanki”
 
“Toh gani nan zuwa yanzu Auta”
 
“Toh kuma Mama na ga Yaya Bashir yau”
 
Hajiya Laraba ta dan yi shiru tana nazari.
 
“Wane Yaya Bashir?”
 
“Yayana ne uwa daya uba daya, wanda yake zaune a nan garin”
 
Hajiya Laraba ta saki kirji.
 
“A ina kika ganshi Aminatu? Yana raye kuma?”
 
“Eh gidan abokin Ya Talba wannan likita nan Doc Ali makotansu ne, amman matar bata bar ni na yi magana da shi ba, kuma Ya Talba yace sai sun bincike shi”
 
“Toh Alhamdulillah, gani nan dai zuwa yanzu”
 
“Toh Mama ki zo da sauri”
 
Ta fada sannan ta sauke wayar tana kallon kiran screen din da kiran ke reading har lokacin, ba iya kashewa tai hakan yasa ta juya ta tura kofar ta shiga ciki ta mika masa wayar.
 
“Gashi nan ka kashe”
 
Ido ya sakar mata yana ta kallonta kamin ya kalli wayar sannan ya saka hannu ya karba, kamin ya kashe wayar Hajiya Laraba ta katse daga dayan bangarenta.
 
“Come here”
 
Ya rika hannun Aminatu ya zaunar da ita saman cinyarsa, ya mika mata wayar.
 
“Hold this”
 
Ta rike kamar yadda ya nuna mata, sannan ya karanta mata password din wayarsa yana nuna mata kowane harafi, har ya bude wayar da pin number, sannan ya umarce ta data saka so that ya tabbatar ita ma ta iya, ta saka da farko sai tai mistake sai ya sake nuna mata ta saka da kanta, sai wayar ta bude, da sauri ta kalleshi tana murmushin jindadi.
 
“Idan kina son ki kira wannan wajen zaki shiga”
 
Yana fada yana nuna mata har da yadda zata katse kira idan ta kira, sannan ya shiga can cikin wayar ya dauki shatin yatsanta as his finger print, ya nuna mata yadda zata yi ta bude wayar da yadda zata rufe.
 
“Amman ai ba wayana ba ce”
 
“Zan siya miki ta kii nan gaba, idan kin kara wayo”
 
Ta wara ido jin abun da ya fito daga bakinsa.
 
“Kai ina da wayo fa”
 
“Na sani ai, tun da kika iya rufe ni a cikin daki ki fita waje ki yi waya da Mamanki”
 
Cikin siririyar muryarta ta kyalkyale da dariyar da be taba jin ta yi irinta ba, ta rufe fuskarta da hannayenta alamar kunya ya shigar da fuskarta kirjinsa ta boye kanta. Samun kansa yai da murmushi yana jin kaunarta na kara neman muhalin a zuciyarsa ta zauna, hannu ya saka yana shafa bayanta.
 
“I love you”
 
Ya furta mata murya kasa kasa, sannan ya dagota daga kirjin nasa dake masa zafi har lokacin.
 
“Fada min me kika ce?”
 
Ta sauke kai kasa tana watsa da yatsunta.
 
“Ba komai”
 
Ta amsa sannan ta dauko carpet ta shimfida zata zauna.
 
“Me zaki yi?”
 
“Zama”
 
“No karki zauna a nan, zo ki zauna a gado mana”
 
“Gado ai naka ne, idan na zauna Momy ta gani zata iya yi min fada ma”
 
“Ba zata miki ba, zan fada mata cewar ni na ce ki zauna”
 
Ta mike tsaye ba dan ta gamsu Momy ba zata mata fadan ba, sai dan bata son yi masa gardama. Sai da ta nade carpet din sannan ta hau saman hadon ta zauna. Kallonta kawai Talba yake kamar ya cinye ta, the way da yake kallonta sai na ka rantse da Allah his life depend on her.
 
“Fada min, kuna kama da yayanki?”
 
He just ask dan ya dauke mata hankali daga tunanin da yake ganin ta fara, sai ta kalleshi ta dan yi murmushi kadan.
 
“Ba sosai ba, saboda mutane suna cewa ni na fi kama da Baba, shi kuma yana kama da Innata, amman shi yana da dan haske ba kamar ni ba”
 
“Natural beauty... Bakinki mai kyau ne mai daukar hankali i love it”
 
Ta dan yi murmushi.
 
“Haka Inna take cewa, tace duka na fi yan'uwana kyau kuma ba gaskiya ba ne, wasu sun fi ni kyau”
 
“Bata ganin wasu sun fiki kyau ne, balle har ta ga muninki, kamar yadda a yanzu nake ganin kamar kin fi duka matan duniya kyau”
 
Dariya tai mai sauti kamar ba ita ba, domin ta san yana yi ne kawai saboda ya wasata.
 
“Baki karyata?”
 
Ya tambaya yana kallon yadda dariyarta ta kawata fuskarta ta kara mata kyau da annashuwa.
 
“Ka fada dai kawai”
 
“Bana fadar karya ai”
 
Ta sauke kai kasa tana kallon yatsun hannunta, sannan ta kwanta saman gadon a hankali.
 
“Ba bachi zan yi ba”
 
“Ni ma bance bachi zaki yi ba”
 
Ya amsa mata yana maida hankalinsa gurin wayarsa, ganin haka ya bata damar rufe ido daman barawon jira kawai yake sai yai gaba da ita. Dagowa yai ya kalleta sai yai murmushi ya mike tsaye ya isa gurin gadon ya risina ya sumbanci kumatunta sai ta bude idonta da bachi ya shiga ciki yai kwance kamar ruwa. Hannunsa ya saka yana buga bayanta irin yadda ake yi ma yara idan ana son su koma bachi take ta sake rufe idon ta bawa gadon amanar kanta. Blanket din dake gurin ya dauke ya lullba mata sannan ya dawo ya zauna saman kujerar yana kallon fuskarta, bachi take hankalinta kwance numfashin ma fita yake a hankali yana shiga cikin sukuni. Ta kusan minti ashirin tana bachin sannan aka turo kofar dakin aka shigo, Talba da idonsa ke kan wayarsa ya dago yana kallon Hajiya Laraba wacce ta shigo tare da yayanta mata uku, biyu ba za su wuce sa'ar Aminatu ba sai babbarsu. Dukansu da sallama suka shigo, sai dai shi kanwar mahaifiyarsa kawai ya amsawa. Cike da tausayin da kulawa ta karaso kusa da shi tana kallon jikinsa,  a zatonta zata ga an sake gurare da yawa sai dai bata ga komai ba bayan cannula dake hannunsa, gashi zaune a kan kujera Aminatu kuma na kan gado kwancenta da blanket din daya lulluba mata.
 
“Kai ne baka da lafiya ko ita?”
 
Hajiya Laraba ta tambaya tana yi masa kallon mamaki, sai yai murmushi ya kalli Aminatu.
 
“Ni ne, tana jin bachi ne shi ne ta kwanta kamin ki zo”
 
Hajiya Laraba ta yi murmushi.
 
“Ya jikin na ka?”
 
“Alhamdulillah, daman a kirji ne kawai na bugu kuma nan yake min ciwo, shi ma kuma da sauki”
 
“Allah ya tsare gaba ya kara lafiya”
 
Ya amsa da Ameen sai yaranta suka masa ya jiki ya amsa, sannan Hajiya ta dora.
 
“Gaskiya Talba baka da uwar kwarai, yanzu da baka kira ka fada mana ba, shikenan babu wanda zai san abun da ya faru cikinmu? Muna yan'uwan mahaifiyarka uwa daya uba daya?”
 
“No ba haka ba ne, ita ma hankalinta ya tashi ne sosai, shiyasa ba tai tunanin kiran kowa ba”
 
“Ba wani tashin hankali tun kamin wannan ma ai bata taba kira tace

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login