Showing 207001 words to 210000 words out of 332834 words

Chapter 70 - Bakar wasika Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

65634

da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
 
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
 
 
 
“Na ji tsoro sosai”
 
Ta fada hawaye na sauko mata fuskarta na tsakiyar hannayensa, yawo kawai yake da idonsa a fuskarta.
 
“I know, dole zaki ji tsoro, amman na miki alkawari daga yau ba zaki sake jin tsoro ba, i will always hold your hand and walk right beside you, you will never be alone”
 
Ya maida ta a kirjinsa.
 
“Me kike so ki ci?”
 
Ya sake dago da ita daga kirjinta yana jiran amsarta, sai ta kura masa ido bakinsa a bushe.
 
“Talk to me Baby”
 
Ya fada yana kallon lips dinta, sai ta marairaice masa tana shirin yin kuka, ganin haka yasa ya maida ita kirjinsa ya rumgume.
 
“Okay, zan kawo miki tea ko wani abu mai nauyi ki sha okay?”
 
Ta gyada masa kai a jikinsa tana kara lafewa kamar kyanwa. Saman kanta ya sumbanta sannan ya dago da ita.
 
“Zaki iya zaunawa na zo?”
 
Ta lake bafada tana turo baki gaba kamar zata yi kuka.
 
“Tsoro nake ji”
 
Ya kai hannunsa ya shafa gefen fuskarta.
 
“Babu abun da zai same ki, okay”
 
Ta mike tsaye a hankali yana dauke hannunsa daga fuskarta Kabir ya turo kofar dakin ya shigo. Sai Talba ya juyo yana kallonsa Kabir ma kallonsa yake daman saka a ransa Talba zai zarge shi.
 
“Look, ni ban dauki yarinyar nan ba, kuma ban san wanda ya dauke ta, kawai sako ya shigo a waya ne cewar naje na dauketa a inda na daukowa da boyayyar number, and a daren da kake magana ban bibiye ka ba, ban san ka aureta ba ma, ko da na sani babu abun da zai... ”
 
Kabir be karasa ba Talba ya isa inda yake tsaye ya rumgume shi da sauri. Tsaye Kabir yai a gurin kamar hoto domin be tsammaci haka daga gurin Talba ba, kallon Aminatu dake zaune tana kallonsu.
 
“Thank you so much”
 
Ya furta sannan ya sake shi ya nufi kofa.
 
“Zanje na samo mata wani abu ta ci”
 
Kabir ya juya ya bishi da kallo da mugun mamaki har ya fice sannan ya juyo ya kalli Aminatu.
 
“Did he...”
 
Sai kuma yai shiru ya daga kafadunsa ya karaso inda take zaune.
 
“Idan kin ci wani abu ki sha wannan maganin ko wane biyu”
 
Ta daga masa sai ya juya ya nufi kofar fita, yana daf da ficewa ta ce
 
“Na gode”
 
Sai ya juyo ya kalleta.
 
“Aikinmu ne ceton rayukan mutane”
 
Ya furta sannan ya fice tare da ja mata kofar. Talba ya shiga motarsa ya dauki wayarsa daya bari a cikin motar ya kira Daddy ya sanar masa, har yayi dialing number Momy sai kuma yai shiru yana nazari, ya san ba dadin labarin zata ji ba, hakan yasa ya fasa kiranta sai ya kira Hajiya Laraba ya fada mata, sannan ta kira Ali. Ring daya ya dauka.
 
“Ka gama fushin ne ko kuma ka kira ka yi min wani fadan ne?”
 
Talba yayi shiru kamar ba zai ce komai ba, sai kuma yai murmushi.
 
“An ga Aminatu”
 
“Wow What? I mean how”
 
“Labarine mai tsayi, yanzu zan je na siyo mata abun da zata ci ne, we will talk later”
 
“Okay kuna ina ne?”
 
“Asibiti Kabir ne ya daukota”
 
“Kabir kuma? How?”
 
“Later”
 
Talba ya kashe wayar, domin a yanzu bata mamaki ko tunanin abun da yadda akai komai ya faru yake ba, ta lafiyar Aminatu yake daga baya komai zai zo. Wani restaurant dake kusa da asibitin ya nufa ya siyo farfesu da snacks da drinks, sai kuma wani tea da yaga suna hadawa mai kamshi, ya hado da bread din na kwakwa, sannan ya fito waje ya siye fruits aka hada masa komai da komai dake gurin. Kamin ya dawo asibitin har ya tsawalla tafiyar tai masa nisa sosai. Da taimakon masu mopping din asibitin ya samu ya shigo da duka abun da ya siyo. Sai da suka jera komai sannan ya ciro wani abu daga aljihunsa ya mika musu. Dagowa Aminatu tai tana kallonshi.
 
“Oh na manta ban siyo brush ba, amman ai zan iya wanke miki baki da wannan”
 
Ya nuna yatsansa, sannan ya karasa kusa da ita ya kama hannunta yana wasa da siraran yatsunta.
 
“My cute girl”
 
Ya sumbacin yatsun hannunta, ta kalleshi ido narai narai kwalla kwance a ciki.
 
“Yunwa nake ji”
 
“Okay”
 
Ya sauka saman gadon da saurinsa ya sauko da kafafuwanta da zimmar daukarta sai ra marairaice masa fuska.
 
“Zan iya tafiya fa”
 
Baya musa mata hakan yasa ya kama hannunta ta mike tsaye, sai dai tafiyarce da rawar jiki, yana ganin haka ya saka gefenta a gefen jikinsa ya rumgume yana kallon yadda take takawa kamar mai kirga steps dinta. Sai da ya fara shiga bathroom din sannan ya shigo da ita har lokacin tana makkale a barensa, tap din ya kunna ya tara hannunsa ruwa suka taru sai ya kai mata a baki ya zuka ya kurkure bakin ta zubar.
 
“Good, to yanzu bude baki”
 
Ta bude kamar yadda ya bukata, manununsa na yatsa ya saka ya a cikin bakinta yana gogawa, sannan ya cire yatsan ya sake cika hannunsa da ruwa ya kai mata ta zuka ta sake kurkire bakin ta zubar. Sannan ya sake saka mata yatsan wannan karon da dan karfi ya goga mata saboda ya samu ya wanke mata bakin yadda ya kamata, sai ta bata fuska tana son yi masa kuka.
 
“Da zafi”
 
“Okay”
 
Ya rage gogar da karfi, har ya gama wanke mata ya wanke mata fuska sannan ya rumgumota suka fito daga bandakin. Da zata zauna saman gadon ma be yarda ya kyaleta ta yi da kanta ba sai ya cirata ya dora saman gadon sannan ya fara bude ledodin.
 
“Me kike son ki ci, snacks akwai fruits kuma ga tea shiya kamata ki fara sha”
 
“Ruwa”
 
Ta fada domin ruwan ne abun da tafi bukata a yanzu.
 
“Ki fara shan tea saboda ruwa zai takure miki hanji ne a yanzu”
 
Sai ta lake kafada, kallonta yai cike da burgewa.
 
“Da alama zamu yi ta drama da ke”
 
Ya dauki gorar ruwan ya bude ya mike tsaye ya kai mata a baki, tana shan kadan yai hanzarin cirewa, ya dauko tea dake cikin wani kofin roba ya bude ya kai mata a baki.
 
“Tun da kin sha ruwan yanzu ki sha tea”
 
Ba musu ta bude bakin a hankali tana shan tea har sai da ta sha rabin cup sannan ya rufe ya aje, ya bare ayaba ya kai mata a baki. Sai da ya tabbatar ta koshi sannan hankalinsa ya kwanta ya samu natsuwa, ya bata ruwan ta kara sha.
 
“Wannan likitan yace idan na ci abinci na sha magana”
 
Magana take masa kamar zata yi kuka, domin ko kadan bata son magani balle kuma allura. Ya nufi inda ledar maganin take ya bude duba sannan ya juyo ya kalleta.
 
“Nawa ake sha?”
 
“Wai biyu biyu”
 
Ya ballo ko wane biyu ya dawo kusa da ita ya zauna rike da magani.
 
“Shalele na, magani ne kawai zaki sha saboda ki kara samun lafiya da kuzari”
 
Ta kara bata fuska kamar ta fasa masa kuka, sai ya kai dayan hannunsa ya kwanto da ita jikinsa sayan hannun kuma dake rike da magani ya mika ya dauko gorar ruwan ya kai mata maganin a baki.
 
“Bude baki sai ki sha ruwa kadan”
 
Fashewa tai da kuka, daman ko a gidan idan tao ciwo. inna da Baba suka ce ta sha magani kuka take.
 
“Sorry”
 
Ta bude bakin ba dan ranta na so ba, daker ya samu ya tura mata maganin, sannan ya dora mata da ruwa, tana hade maganin take ta shan ruwa. Ya kai hannunsa ya shafa kanta.
 
“Ko dankwali babu akanki haka kika fita ko kuma su suka miki haka?”
 
“Da hajab ns fita ko lokacin da zasu min dure abun nan ina da hajab a nan dai ne na farko na ga babu hijab a jikina”
 
Ya gyada mata kai, baya son ya cika ta da tambaya ne abun ya tsaya mata a rai. Mikewa yai tsaye ua fara gyara gurin yana dauke abubuwan da ta ci ya maida su gefe daya, suna haka akai knocking kofar kamin ya bada damar shiga police din suka shigo cikin shigar gida.
 
“Pls ku dan jira a waje ta kintse mana”
 
Da okay suka amsa masa suka juya suka fice, dai ya cire shirt dinsa ya mika mata.
 
“Daure kanki”
 
Ta kalli kirjinsa dake rufe da vest.
 
“Kai fa?”
 
“Ina da veat ai kuma ina da jacket a mota”
 
Ta nada rigar ta daura yadda zata iya sai ta ki tsayawa akanta saboda riga ce ba dankali data saba daurawa ba. Da kansa ya dauki rigar ya nadata kamar naden dankwali ya daura mata kai, ya gyara mata rigar jikinta, sannan ya maida ta gurin kan gadon.
 
“Zauna a nan”
 
Ya nufi kofar fita ya bude ya leka ya kirasu, sannan ya dawo da sauri ya zauna kusa da ita ya kareta ta yadda ba zasu iya ganin jikinta ba, sai fuskarta shi ma idan ya leko. Tambayoyi suka yi mata akan mutanen da kuma inda suka kaita da abun da sukai mata, bata boye komai ba, tun daga daukarta da akai har zuwa yanzu da take kwance a asibitin sannnan suka saka aka kira musu Kabir sukai masa tambayoyi daga karshe suka karbi wayarsa suka tafi da ita saboda bincika wanda ya aiko masa da sakon. Sai da suka fice sannan Talba ya juyo ya kalli Aminatu sai tausayinta ya kara zurfafa a zuciyarsa.
 
“Kin shiga taskun rayuwa kala kala, amman yanzu komai ya wuce, babu abun da zai sake faruwa na miki alkawari, wani ba zai sake taba ki ba, ko a bachi ne”
 
Zancensa na karshe ne ya bata dariya har sai da ta bayyana hakoranta.
 
“Ya zaka san wani ya taba ni a bachi?”
 
Kallonta yake da murmushi a fuskarsa.
 
“That's cute smile i miss it...”
 
Ya kai hannu ya laba lips dinsa, aka turo kofar dakin, wannan karon Momy ce tare da Kabir sai kuma Leila dake tare da ita. Aminatu na ganin Momy da Leila wani irin tsoro ya kamata sai tai saurin kwance rigarsa dake kanta ta mike masa ta matsa baya. Kallonta yai sai ga gaba daya ta rasa natuwarta, ta sauke kai kasa. Juyowa yai ya kalli Leila dake sanye da wata farar rigar yadi saidai ta matse ta sosai tana rataye da jakarta sai bakar hula dake kanta, dauke ido yai ya kalli Momy wacce ta tabe baki tana kallonsu.
 
“Abun farinciki haka ba za a fada mana ba saboda an dauke mu makiya, sai Daddynka ne yake kirana ya sanar min”
 
“Ban san yadda zaki ji ba idan an sanar miki hakan ya saka ban sanar miki ba”
 
“Murna zan yi mana, ko ma komai surukata ta dawo, kuma zargin da kake akan yayana zai wanke, any way mun zo ne dai mu dubata ya jikin nata”
 
“Ta ji sauki”
 
“Bata iya gaisuwa ba ne”
 
Momy ta fada tana kallon yadda tai kyau kamar ba ita ba, duk da kasancewar a yanzu bata cikin kwanciyar hankali. Aminatu ta dago a hankali ta kalli Talba, sai ya gyada mata kai, sannan ta kalli Momy.
 
“Ina wuni?”
 
“Lafiya kalau ya jikin”
 
Momy ya amsa bayan ta bata kusan minti biyar tana kallon yadda bakar fatarta ke shining. A nan ma Aminatu kallon Talba tai yi sai da ya daga mata kai sannan ta amsa.
 
“Alhamdulillah”
 
“Sosai ko sai an fitar da ita waje?”
 
Kamin Talba yai magana Kabir ya tari numfashinsa.
 
“No daman sun bugar da ita ne,wata kila saboda kar ta ji ko ta gane inda take, amman ba wata matsala da na gani gaskiya, zama a iya sallamarta yau”
 
Momy ta juya ta kalleshi.
 
“No, ka bincika jininta in and out, kuma ayi mata hoto, ina son na tabbatar tana lafiya kalau so that mu samu salamar zuciya kamin mu zauna da ita”
 
“Tace ba a mata komai ba.”
 
Talba ya fada, sai Leila ta kalleshi tana dan daga gira zuciyarta na mugun soyuwa na ganinsu zaune a muhalli daya, daman dazun da ta tararda rigarsa a kan Aminatu shi yana sanye da Vest mutuwa ne kawai ba tai ba, I domin zuciyarta ta buga matuka.
 
“Really...? And you believe her?”
 
Talba ta juya ya kalli Aminatu dake cike da tsoro idonta har ya cika da kwalla, sai kuma ya juyo yana murmushi ya kalli Leila.
 
“Me zai hana? I trust her”
 
Ta yi murmushin takaici.
 
“That's good”
 
Ya sakar mata murmushi as respond, sannan ya kalli Momy dake fadin.
 
“Idan an gama bincikar komai aka tabbata tana lafiya, sai ya dawo da ita gida”
 
Kabir ya kalleta da mamaki.
 
“Gida...?”
 
“Yes.. Tana da gurin daya fi inda mijinta yake zaune ne?”
 
Talba ma kallon Momy yake kamin ya kalli Kabir su hada ido.
 
“Anjima Mairo zata kawo muku abinci da abubuwan bukata, idan kuma akwai abun da kuke so zaka iya kirana, and zan iya turo Zulai ta kwana da ita ko Hajiya Saratu”
 
Momy ta fada sai Talba ya girgiza mata kai.
 
“Za ta iya kwana ita kadai”
 
Leila ya kalleshi kamin ta sake Kallon Aminatu da har lokacin kanta yake kasa, ji take kamar tai kukan kura tai cikinta ta makureta.
 
“Allah ya bata lafiya, ya tsare gaba”
 
Momy ta fada sannan ta juya, Leila ce ta fara fita sannan Momy Kabir ya zama daga karshe. Suna ficewa Talba ya kai hannu ta dago fuskar Aminatu dake hawaye, sai kawai ta fashe masa da kuka sosai har wani shessheka take alamar kukan ya tarar mata.
 
“Ohhhh”
 
Ya rumgume kirjinsa da sauri.
 
“Miye na kuka yanzu?”
 
“Baka fada min cewar Momy ta san ka aureni ba? Kuma ka san zata iya yi min komai, gashi Leila ta gan mu tare... ”
 
Yayi murmushi ya sumbanci saman kanta.
 
“Na yi laifi, amman ai kin ga yanzu kika dawo ko? Yaushe ma muka zauna Hira balle na baki labarin? Amman zan fada miki komai idan hankali ya kwanta”
 
Kamar yace mata na fada din haka ta ji, sai ta karawa kukanta mai har tana dan daga murya. Kara rumgumeta yai ya hura mata iska a saman idon sannan ya fara shafa kanta.
 
“Yi hakuri, ba zan sake ba ki daina yawan kuka yana damuna kuma kina takurawa kanki”
 
Ta dade tana ta kukan sannan ta tsagaita ba dan ta gama ba, sai dan ta gaji da kukan for now. Dagota yai daga kirjinsa
 
“Hey Black beauty.... So kike ni ma nai kuka?”
 
Ta kai hannu ta share hawayen daya makalle a idonta, sai ya yi murmushi ya kai hannu ya ja lips dinta ta turo gaba. Wayarsa ce tai ring sai ya mike tsaye ya dauki wayar ganin number Ali yai picking
 
“Hello?”
 
“Kuna Room nawa ne? Gani tare da Madam zamu dubata”
 
Talba ya fada masa sannan ya aje wayar ya kalleta.
 
“Ya kamata na sama miki tufafi mai kyau da zaki saka, bana son na ga jikin mace a awaje ko kuka mutane suna kallonta anyhow, bana son na ga mace tana barin jikinta a waje even though most of ladies sun dauki hakan a matsayin wayewa, amman ni bana so, kwaliyar mace da sakin jikinta is only for her husband, not for society”
 
Hausar kawai take oya ganewa idan yai, duk kalarmar daya hadata da turanci bata fahimtar komai idan ba Okay ba, shi ma saboda ya zama ruwan dare ne. Ta daga masa kai alamar to, sannan ta dauki rigarsa ta dora akanta ta kalleshi sai yai dariya har fararen hakoransa suka bayyana domin yadda ta dora rigar ne abun dariya.  After like five minutes Ali ya turo kofar ya shigo, irin zaman da Talba yai a dazun da polisawan nan suka zo shi ya sake yi ya tare matarsa, fuskarsa ba yabo ba fallasa Ali na ganinsa ya san be gama saukowa daga fushin da yai ba. Haulat ta matsa kusa da Aminatu ta aje kular abinci tana kallon Talba.
 
“Maa Shaa Allah, wannan ce Amaryar ta mu?”
 
Amimatu ta kalleta da idanuwanta da sukai ja, sannan ta kalli Talba ya gyada mata kai sannan ta gaishe da Haulat matar Ali. Haulat ta amsa tana murmushi sannan tai ma. Talba barka da arziki.
 
“Can we talk”
 
Ali ya fada sai Talba ya mike tsaye daman yana jin kumyar ganinsa da vest da Haulat tai yi, a ganinsa hakan be dace ba, ko ba komai ita ai matar wani ce kamar yadda yake jin ba zai iya kyale matarsa ta kalli wani a haka ba. Ali ne ya fara fita sannan Talba ya bi bayansa, Haulat na ganin haka ta dawo kusa da Aminatu ta zauna.
 
“Ashe Amaryar ta mu kyakkyawa ce shiyasa Talba ya haukace mana”
 
Aminatu ta yi masa da kanta, sai Haulat tai murmushi.
 
“Da ma kin sake jikinki domin ni ba bakunta nake ba, na dade ina jiran na fa matar da Talba zai aura, muna ta saka ran Leila ce ashe kina nan daga gefe kina fadin ni ce”
 
Ta fada da fuskar zolaya tana lekan fuskar Aminatu, domin har ga Allah Aminatu ta burge ta, ga ta yarinyar kuma da alama bata da hayani da ji da kai ba kamar Leila ba da sau daya suka taba gaisawa da ita duk kuwa da irin shirin da Talba yake da Ali. Har Haulat ta bude baki ta sake zolayarta sai kuma ta fasa.
 
“Bari dai na kyale ki da ganin wannan ruwa ruwan kuka ce, kar Talba ya zo yace na saka masa mata kuka, amman dai ai zamu yi hira ko?”
 
Nan ma Amimatu bata ce komai ba, sai watsa take da yatsunta.
 
“Doc yace min galadi kike ina da yan'uwa a can wane gefen kuka a galadi? Ni ina ta kan wurin sarki ne”
 
Ko da jin an ambaci garinsu sai ta dago kai ta kalleta.
 
“A marnawa muke mu”
 
“Okay na san marnawa, akwai ma wani makocin mu dan can ne yana yawan zuwa, sai dai yanzu hare haren nan da ake kaiwa yasa ya daina zuwa dan yace an kashe masa yan'uwa gaba daya, yace yanzu ba shi da kowa sai dangi na nesa, matarsa ma ta dade rabon da taje garin balle kuma ni da yan'uwan nesa ne a garin rabona da garin yanzu kusan shekara goma kenan”
 
“Kai kin dade”
 
“Eh gaskiya na dade, tun Kakata na da rai, Yanzu rashin tsaron nan ma ai ya hana zumunci sai dole”
 
“Muma barayin suka koremu sun kashe min kowa”
 
“Haka Doc ya fada min, ai Wallahi na tausaya miki, Allah ya musu rahama amman yanzu komai zai wuce ai, kuma yadda Allah ya hada ki da Talba

Join Our Groups

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login