Showing 213001 words to 216000 words out of 332834 words
dinning inda Mahaifiyarsa take zaune tana cin abinci, kallo daya tai ma fuskarsa ta fahimci yana cikin farinciki.
“Mommy yau ina da labari mai dadi da zan baki”
“Ai naga haka a fuskarka ai, minene fada min”
“Sai kin ba ni goro babba”
Ta yi murmushi.
“To fada na ji idan ya kai na baka goron ai zan baka”
“Yarinyar da nake fada miki, yau dai ita da kanta tace na turo iyeyena”
Mommy ta tsayar da cin abincin da take ta kalleshi.
“Shi ne wani abun farinciki?”
Ya dan bata fuska.
“Haba mana Mom kin san fa ina son yarinyar nan”
“Toh Allah yasa alheri, zan sanar da daddynka idan ya dawo, but kamin nan ya kamata ka same ta kai magana da ita”
“Magana kuma?”
Ta tambaya with confused.
“Yes ka yi magana da ita ko kuma ka saka a bincika mana ita kamin a tura manya, domin na yi nawa bincike ina ganin kamar akwai abun da yarinyar nan take boye maka”
Yayi shiru yana nazari.
“Mommy akwai wata matsala ne a tare da ita?”
“Aa ba zaka ji a bakina ba, idan na fada ai laifina zaka gani, wata kila ma ka karyata, amman idan ka bincika da kanka ko kuma kai magana da ita zaka fi gamsuwa”
“Mommy dan Allah kin fada min”
“Babu abun da zan fada maka, lokacin da zaka ganta ka ce kana so ni na fada maka inda take ne? To haka zaka yi naka bincike ka gano komai da kanka”
Tana fadar hakan ta mike tsaye ta zari tissue tana goge bakinta. Jan kujera yai ya zauna da tunani, sannan ya saka hannunsa aljihu ya dauko wayarsa sai yanzu yake ganin ya dace ua bincika friend dinsa daya saka yai masa bincike akan Baturiya, wata kila by now ya samu wani labari da zai fada masa, domin kwana biyu da suka wuce ya kira shi ya tambaye yace har yanzu be binciken yadda ya kamata ba.
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
FARUK POV.
Tafiyar Kwana uku sukai a hanya sannan suka iso Ilela. A sokoto ya kwana washe gari motar data tashi faga sokoto karfe 7am zuwa Zamfara ya shiga, kamin su isa mahaifarsa har ya zaku yana ta marmarin ganin Mama da kanensa da kuma dansa, ga kuma tafiyar da yai ya samu rabo mai yawa wadanda yake jin cewar ya wadatar da shi ya fara sana'a mai karfi da zai rike kansa ko da be samu aiki ba. Ana shiga garin Gusau sai ya ji yanayi da kamshin garin daya baro da inda yake a yanzu ya banbanta. Tasha suka sauke duk fasinjojinsu. Faruk ya fito motar kamar wani buzo saboda sumar daya tara, domin a dajin da suke ko magani babu balle shagon aski wani sai yayi wata daya ma be yi wanka ba, saboda tsoron kar ya tube kaya yaje wanka a sace masa sinari domin sata ake a gurin sosai kana yin wasa da zinarinka za a sace maka shi. Tsaye yai yana kallon cikin tashar kamar wani bako, bangerensa an hagu na rataye da jaka irin ta goyo wanda matafiya suke saka tufafi ko littafai a ciki. Gurin wani mai shago ya nufa ya zaro naira goma dake aljihunsa ya siye pure water ya sha sannan ya nufi kofar fita gate din, kamin ya karasa titi ya tare wani mai achaba ya hau yana fada masa unguwar da zai kai shi.
Yana shigowa cikin unguwar mutanen da suka sanshi suka fara daga masa hannu wasu kuma na kai masa gaisuwa. Sai ya amsa yana daga musu hannu har ya isa kofar gidan ya sallami mai achaba ya shiga da sallama. Kanwarsa na jin muryarsa ta fito waje da gudu ta rumgume shi.
“Yaya Faruk oyoyoyoyoyo”
Dariya ya saka sannan ya sake ta nufi dakin data fito wato dakin mahaifiyarsa, domin yana cike da zumudin ganinta yana shiga dakin sai yai tsaye bakin kofa ganinta kwance ta rame sosai kamar ba ita, gaba daya kassanta sun fito idonta yayi wani zurfi tsufan wahala ya taso mata.
“Maa Shaa Allah sannu da zuwa Umaru”
Ya karasa kusa da ita jiki a sanyeye domin be jidadin ganin mahaifiyarsa a haka ba, ya san ya barta a yunwa da rashin lafiya irin ta yau da gobe, amman be dauka abun yayi tsanani haka na.
“Mama baki da lafiya ne?”
Ta yi murmushi.
“Bari ka hutu labari ai zai zo daga baya ko? Kai da ka kwaso hanya, kasa wa kasa bama gari wa gari ba!”
Ya zauna kusa da ita cikin rashin walwala.
“Gashi babu waya, inda nake ba a waya Wallahi sai an fito gari kuma fitowar ne aiki, kullum ina son na kira ko na yi muku aike amman ba dama”
“Babu komai ai yanzu gashi ka dawo, ya hanya”
“Alhamdulillah Mama, tun yaushe ne baki da lafiya”
“Tun tafiyar, daman kasan lafiyar ba wai ta wadace ni ba ne, sannu sannu abun ya fara har ya kai ni kwance”
“Hawan jinin ne ko Mama?”
“Shine kam domin ba ni da wani ciwo sai shi”
“Tunani kika saka a ranki Mama”
“Tunani ai ya zama dole abu ga talaka, kullum kana tunanin abun da zaka ci, abu ga talaka, kuma tafiyar nan da kai babu kira babu sako, dole ai hankalina ya tashi”
“Zaki iya shiryawa mu tafi asibiti ko sai Rukaiya ta rikaki”
“Haba dai Ka bari ka natsu mana, ka ci abinci ka yi wanka kalli gashin kanka ma, kuma ba ni kadai ce mai ciwon ba ai har da danka”
“Miya samu Sultan”
“Kyanda, tun da yai shi be sake lafiya ba, kullum ciwo yake”
“Ina yake?”
“Gashi can gindin icce”
Mama ta fada tana masa zunde da baki tana nuna masa inda Sultan yake. Juyawa yai ya kalli Sultan dake tsakar gidan kwance gindin ice yana sharar bachi, mikewa yai tsaye ya nufi inda yake tun kamin ya karasa kusa da shi ya lura da yadda ya rame sosai yai baki, domin har yanzu akwai dambunan kyandar Jikinsa. Risinaws yai yana kallon dansa cikin rashin jindadi.
“An kai shi asibiti?”
Ya tambaya yana kallon Rukaiya dake bayansa tsaye.
“Aa Yaya ka san yadda muke fama, ta abinci muke yi bata magani ba, Mama da ace da kudi ai ba nan zaka tarar da ita ba sai asibiti”
Hannu ya kai ya taba sai ya ji jikinsa da dan zafi ba sosai ba. Sake dawowa yai dakin ya aje jakarsa gefen daya sannan ya ciro 2k ya mikawa Rukaiya.
“Je ki siyo wani abun ku ci, zan je na yi wanka na shirya sai mu tafi asibitin”
“Toh Yaya”
“Da dai ka hakura sai gobe idan ka huta sai mu tafi”
Mama ta fada murya kasa kasa, baya son musa mata ne, hakan yasa ya amsa mata da toh sannan ya fita daga dakin zuwa asalin dakin da yake bachi. Tufafin jikinsa ya tube ya saka short ya fito ya cika farin bokitin fenti ya shiga bandaki yai wanka ya fito fes da shi, ya saka wasu tufafin sannan ya fita waje. Tun da ya fito yake gaisawa da mutane suna masa sannu da zuwa har ya isa titi, shagon wani mai askin zamani ya shiga shi ma sai da suka gaisa sannan ya zauna mai askin ya kunna injin ya soma gyara masa kansa. Duk tulin gashin dake kansa sai da aka zubar da shi aka gyara masa fuska, sannan ya sallame shi ya dawo gidan.
Tabarma ya dauko ya shimfida a waje ya koma dakin ya dauko Mama ya dawo ta ita a wajen ya zaunar da ita, sannan shi ma ya zauna ya tisata a gaba yana ta kallo.
“Na yi kewarki sosai Mama kullum sai na yi mafarkinki”
Mama ra yu murmushi.
“Ai shiyasa na ce ko sa ka kira kar a fada maka bani da lafiya ko danka, saboda za a tada maka hankali ne kawai”
“Amman Mama da na kira din aka fada min ai sai na aiko da na magani”
“Mama bata son tashin hankalinka ne shiyasa”
Cewar Rukaiya dake aikin jajagen kayan miyar da zata yi miya. Faruk yayi murmushi. Yana kallon dansa daya fara motsawa kana ya bude ido. Tsayawa yai kallon Faruk da mamaki yana ganin kamar mafarki ne.
“Daddy”
Ya kirashi sannan ya tashi zaune yana kallonsa.
“Na'am”
Faruk ya amsa ya mika hannu ya dauko shi ya zaunar saman jikinsa har lokacin jikinsa da dan zafi.
“Sultan ya jikin”
Ya taba jikinsa.
“Akwai zafi kuma cikina na ciwo”
“Sannu zaka sha bobo ko madara”
“Aa”
Ya fada yana jin cewar baya son komai domin bakinsa babu dadi. Faruk ya taba jikin nasa yana kara tabbatarda dansa ba shi da lafiya, saboda ya san dansa da kwadayi ko da ya koshi da abu idan akai masa maganar bobo ko madara ko nama jiki na rawa yake cewa eh.
“Dady karka sake tafiya ka bar ni kaga ina ciwo idan baka nan”
“Ba zan sake ba, babu inda zan sake zuwa”
“Dady tare da Momy kuka dawo”
Faruk ya kalli Mama, Mama ta kalleshi.
“Haka yake kullum maganarsa Dady Momy”
“Rafi'a ta zo dubashi?”
Mama ta girgiza kai.
“Wallahi har yau bata zo ba, kuma kullum sai yayi maganarta”
Faruk ya shafa dansa cike da tausayin rashin samun uwa ta gari. A saninsa da ace yayi dacen mahaifiya ba za a dauki sati ba zata zo ta duba shi amman ace har yanzu bata waiwayi inda danta yake ba.
“Shiyasa ma da bashi da lafiyar nan ban fada mata ba”
Mama ta fada. Sai Rukaiya ta kyabe baki.
“Ita fa gani take ta rabu da talauci ta huta, bata da wata damuwa”
“Allah ya sauwake”
Faruk ya fada cike da tausayin dansa, sai duk suka amsa da Ameen har shi Sultan din.
TALBA POV.
A hankali Leila ta sauko downstairs din tana kallon Talba dake zaune dinning area rike da wayarsa yana chat. Sai dai har ta sauko ta karaso inda yake taja kujera ta zauna be dago ya kalleta ba.
“Good morning Babe...”
At first saurare ya tsaya yi da shi take? Sannan ya dago ya kalleta with surprise, murmushi ya gani s fuskarta tana kallonsa.
“Ya mai jiki?”
“Ta ji sauki”
Ya amsa a takaice sannan ya mike tsaye ya nufi kitchen.
“Mairo ba a gama ba”
“An gama ranka ya dade ina hada kayan guri daya ne”
“Zan jiraki a mota”
Ya juyo ya nufi kofar falon.
“A gaisheta da jiki zan shigo anjima da dare”
Be kulata ba balle har ya amsa abun da take fada ya sa kai ya fice. Cikin motarsa ya zauna ya kunna motar yana jiran fitowar Mairo, sai ya hango Leila ta fito rike da kwandon abincin ta nufo motarsa. Da kanta ta bude back seat ta saka masa sannan ta rufe.
“Safe drive”
Kallonta yai sannan yai reverse ya nufi gate din gidan, har ya isa asibitin tunanin abun da Leila tai masa a yau yake, da zuciya daya tai ko kuwa dai tana da wata manufa? Ganin Aminatu ne yasa ta zubar da duk wani hali nata da girmankan da take ji da shi ko kuma me? Yana yin parking kiran Ali ya shigo wayarsa, picking yai ya kara a kunne ba tare daya ce komai ba.
“I just call to ask...”
“Uhmm...”
“Ya jikinki Aminatu?”
“Ta ji sauki, za a sallame ta yau”
“Allah kara sauki, ina son magana da kai serious talk”
“Okay zan kira ka idan na fito”
“Okay”
Ya sauke wayar ya saka aljihun jean dinsa sannan ya bude motar ya fito ya bude back seat din ya dauki abincin ya nufi ward dinsu Aminatu.
AMINATU POV.
“Mama ina kwana”
Hajiya Laraba ta yi murmushi tana kallon Aminatu.
“Lafiya Kalau Auta ya jikin?”
“Na ji sauki”
“Me kike son ki ci?”
“Ba komai”
Ta fada tana yin kasa da kai. Hajiya Laraba ta daka mata tsawa har sai da ta zabura.
“Ke... Sake jikinki idan kina son wani abu ki rika fada, birni ba irin kauye ba ne, musamman ma inda zaki zauna yanzu, ban san irin tarbar da zasu miki ba, amman ba sonki suke ba, duk abun da akai miki ki bude baki ki fadawa mijinki, idan kuma ya kasa komai ki fada min ko kuma idan shi din ma ya taba ki ki fada min, idan akai miki abun da baki gamsu ba ko baki so ki rika magana, idan ba haka ba rainaki zasu yi, kuma ban da kazanta kin ga irin turbar da muka doraki to ki bita ta zame miki jiki, karki kuskura ki bari su raina ki wannan sukukun da kike ba zai amfana miki komai ba a can, kina ganin da gogangin yan duniya ne kuma wayayyi, amman saboda son da mijinki yake miki ya saka dole su zauna dake, kuma karki sake masa yai ta zama dake a gidan, kara ku tare a naku gidan kinji ko?”
“Toh Mama”
Ta amsa sannan ta dago ita da Hajiya Laraba suka kalli kofa, Talba ne ya shigo rike da abinci fuskarsa da murmushi sai da ya gaisa da Hajiya Laraba sannan ya karaso ya aje abinci sannan ya kalli Aminatu.
“Ina kwana...”
Ita da shi suka hada baki gurin mikawa juna gaisuwa, sai Hajiya Laraba tai murmushi.
“Ai ita ya kamata ta gaishe ka”
Shi ma murmushin yai ya kalli Aminatu.
“Ya jikin?”
“Na ji sauki”
“Ashe manya na tashi da wuri, 6:30 fa”
Cewar Hajiya Laraba, sai ya kalli agogon hannunsa.
“Tun 4am na tashi Mairo na ce ta shirya mata breakfast”
“Baka son matar taka ta ji yunwa kenan”
Yayi murmushi ya sauke kai kasa, sai ta mike tsaye.
“Bari na kira oga mu gaisa”
Ta dauki wayarta sannan ta fice, tana fita Talba ya janye daga jinginen da yake jikim gadon ya koma kusa da Aminatu ya zauna.
“Pretty na”
Ta ki dago kai ta kalleshi, sai ya kai bakinsa gefen bakinta ya sumbance ta.
“Good Morning Babe i miss you so much”
“Minene i miss you din?”
Ta tambaya tana kallonsa domin ta san good morning. Murmushi yai ya rumgumeta yana kara kissing dinta
“Ina nufin na yi kewarki”
“Sake ni kar ta dawo taga ka rika ni”
Ta fada tana kokarin kwace kanta daga rikon da yai mata.
“Okay ki sumbance ni sai na sake ki”
Ta zaro ido da mugun mamaki da tsoro domin bata tsammaci jin haka daga bakinsa ba.
“Kai....”
“Yes”
“Dan Allah sake ni”
“Wallahi ba zan sake ki ba, kin sumbance ni kin ji kuma na rantse, sai dai ta tararda mu a haka”
“Dan Allah dai...”
Ta marairaice masa tana shirin yin kuka har ta turo baki gaba. Hannu ya kai ya taba bakinta cike da burgewa.
“Na fa rantse ba zan saki ba, sai kin sumbance ni”
Ya kalli kofar gabanta sai faduwa yake, sannan ta kai hannunta ta daba bakinta ta shafa masa a gefen fuska.
“Nop ba haka ba, bakinki zaki saka ki sumbance ni”
Ya fada har da lumshe ido yana jiran ta sumbance shi, hawaye ne ya sauko mata shi kuma sai kara janta yake jikinsa. a dole ta mike beautiful lips dinta ta sumbance shi ta dauke bakinta da sauri.
“To na yi”
Ta fada tana kallon kofar kirjinta sai bugawa yake gani take kamar Hajiya zata shigo ta tararda su a haka. Murmushi yai ya bude idon ya sumbanci saman hancinta sannan ya saketa ya mike tsaye ya koma inda yake tsaye ya rumgume hannayensa yana sotsar lips dinsa kamar ya samu sweet sai kallonta yake, suna hada ido ya kanne mata ido daya, sai tai saurin kawar da fuskarta tana turo baki ta sa hannu ta share hawayenta.
Hajiya Laraba na dawowa dakin ta zuba ma Aminatu abinci, soyayyar doya da kwai sai tea da aka hada yana ta kamshi, da farfesun naman rago. Bayan ta zuba mata ta zuba ma kanta.
“Talba a zuba maka?”
Kamar zai ce eh sai kuma ya kalli abincin Aminatu.
“Aa zan ci anjima”
“Okay”
Kadan kadan take cin abinci Hajiya kam tuni ta gama ta sha ruwa mai sanyi. Da ido yake ta gadinta har ta gama cin abincin Hajiya ta mika mata ruwa ta karba ta sha sannan ta aje.
“Kin koshi?”
Talba ya tambaya, sai ta girgiza masa kai alamar aa tana turo baki, saboda ganin Hajiya kanta na wani gafen bata ganinta, wai so take ta rama kissing din da ya saka ta tai bata so ba.
“Hajiya a kara mata”
Hajiya ta juyo ta kalleta.
“A kara miki?”
“Na ce na koshi”
Ta furta tana kallon Talba, sai ya dan fiddo ido, can kuma yai murmushi, ita ma murmushin tai ta sauke kanta kasa tana kallon siraran yatsunta.
“Jiya da dare likita ya shigo bayan tafiyarka, amman ba wacan likitan ba ne, ya dai ce jikinta ba shi da matsalar komai wai idan likitan safe ya shigo zai sallame ta”
“Eh idan Kabir ya shigo anjima zai sallame ta”
“Can din zata zauna kenan?”
“Eh amman ba wai zama ta dade ba, kawai dai zata zauna ne kamin komai ya koma daidai”
Hajiya ta sauke numfashi.
“Ke dai Auta na fada miki ko?”
“Tau”
Hajiya ta mike tsaye.
“Ni zan tafi na yi wanka na shirya, idan likitan ya sallame ta sai ka fada min da wuri saboda yarana suna son zuwa a nan, idan kuma ta kuma can kuma duk daya zasu je su dubata”
“Okay In shaa Allah”
Ta hada kayan data kawo abincin da su jiya ta dauka.
“Bari na sauke ki”
“Aa ita kadai za a bari a nan? Kasan dai abun da ya faru ba mu gama fita daga zullumi ba, zau hau Napep”
“Okay Allah ya tsare”
“Aamin”
Ta nufi kofa, Aminatu ta bita da ido ido narai narai kamar zata yi kuka, ji take kamar ta bita. Sai da ta fice sannan Talba ya tashi ya koma can kan carpet din da Aminatu take zaune ya zauna ya dauki plate din data ci abinci ya zuba farfesun ya saka spoon ya fara ci.
“Babe na”
“Ni ka daina ce min Babe”
“Saboda me?”
“Yarinya ce ni da zaka ce min Babe”
Dariya ya saka irin wanda