Showing 180001 words to 183000 words out of 332834 words
jikin kujerar da yake zaune yana dan daga gira.
“Na yi fushi, tun dazun nake jiran wayar nan a kashe”
“Ayyah dear kai hakuri, ni ma sai yanzu na lura tana kashe, dazun na zauna a kanta shine ta kashe kanta ban ma lura ba sai yanzu”
“To na hakura, ya kike?”
“Lafiya Kalau, kai fa”
“To gani dai, na dadi ba bakinciki, kin fita yau”
Ta dan yi jimm sannan ta amsa.
“Aa ban je ko'ina ba yau, ya akai yi?”
“Ba komai, kawai na tambaya ne, ya mama?”
“Lafiya kalau take”
“Bari na barki ki huta sai anjima zan kira”
“Okay i love you”
“I love you too”
Ya sauke wayar bayan ta aika masa da sumbata. Da mamaki take kallon wayar, domin be taba tambayarta ta fita ba, why yau ya tambaye ta? Ko dai ya ganta ne. No idan ya ganta zai mata magana ba zai kyaleta ba. Ta dan tabe baki sannan ta kira Ramlee.
“Ramlee da yaushe zamu je?”
“Idan an gama sallah isha'i kin san yafi sirri”
“To wai babu yadda za ayi mu hadu a wani gurin dole sai hotel? Bana son a gan ni ne”
“Babu wanda zai gan ki, idan zaki shiga ki saka mask kuma ai kin ga ba wani dade zaki yi ba, kuma gamawa zan dawo dake gida ko kuma shi ya kawo ki”
“Sai dai ke din, kai Umma ta fara sa ido fa, yanzu ma ta gama min magana, ko yanzu zuwan da zaki yi ki tsaya nesa da gidanmu yadda ba za a ganki ba, domin na fada mata wani zai zo zancen yau, kin ga idan mun fita sai na ce mata daukata yai muka fita yai min siye siye”
“Lalle kanki na kawo wuta Baturiya”
“Yau da gobe ai dole mu saba, yanzu ma yadda zan bullowa tafiyar nan da Alhaji nake domin ya nace sai ya tafi da ni”
“Wallahi Baturiya kina da farin jini sosai, yanzu kin ga wannan mutumen be san ki ba, labarinki kawai na bashi amman karki so ganin yadda ya haukace ya damu yana son ya ganki, duk ya matsu ku hadu”
“Ai dai yau za ayi ta ta kare, kuma haduwa daya zan yi da shi gaskiya, domin ina son na watsar da komai na maida hankali kan aure”
“Toooo amman kin fada masa kina da da?”
“Aa ba zan fada masa ba, kuma ba ganewa zai yi ba dan kin san masu kudin nan ba wani tsayawa suke bincike ba”
“To na mu dai addu'a ne kawai Allah ya tabbatar da Alheri”
“Amin idan na shirya zan kira ki”
Ta kashe wayar tana tunawa da Sultan saboda maganar da da Ramlee tai mata, sai yau kadai ta ji tana kewarsa, ta san yana can gurin danjin ubansa, kuma Faruk ba barinta zai yi ta ganshi ba.
“Allah sarki Faruk, ina son ka Wallahi amman talaucin nan ne matsala, duk mazan nan da nake mu'alama da su babu wanda ya kaika, ko yana ina ma yanzu Oho”
Ta fada sannan ta mike tsaye tana jin kewar tsohon mijin nata da gasken gaske, domin tana sonsa sai dai ba irin son da zai tana ta guje masa ba. Misalin takwas da rabi ta shirya tai kwalliya cikin wata shadda mai kyau sosai da aka mata kwaliya da stones. Amaimakon gyale sai ta saka hijab ta dauko jakarta ta saka facemask a ciki ta da wayarta ta fito daga dakin tana tafiya a natse.
“Umma zan fita ya zo”
Umma ta kalleta daga sama har kasa sannan ta daga mata kai, abun ka da mai nema sai ta fice da kuzarinta tana jindadi. Nesa da gidan Ramlee ta faka motarta kamar yadda Baturiya ta fada mata, da kafa Baturiya ta taka har ta isa gurin motar ta bude ta shiga.
“Kin yi kyau iya kyau, amman da Hijab”
“To ya na iya iyayen ne sai da haka”
Suka saka dariya har Ramlee zata ja motar Baturiya tai saurin dakatarda ita.
“Haba Hajiya dan jira mana, kar ace zuwa yai ya dauke ni kawai, kara dai mu yi kamar mun yi dan zance haka”
Sai da Ramlee tai jiran minti talati sannan ta tashi motar suka kama hanya, suna tafe suna hira har suka isa hotel din. Baturiya ta ciro face mask dinta ta saka sannan ta mika hannu ta karbi number dakin da Ramlee ta mika mata a karamar takardar.
“Yana ciki yana jiranki”
“Okay”
Ta bude motar ta fita, rashin sabo da zuwa hotel yasa ta fara jin wani iri tana ganin kamar idon kowa yana kanta ko kuma wanda ta sani zai iya ganinta ko ta ganshi. Haka dai ta samu ta kusa ciki har ta isa bakin kofar dakin ta kwankwasa aka bude mata sai ta shiga gabanta na dan faduwa. Kai tsaye ta nufi gurin gadon zata zauna ta cire mask dinta, wanda ya bude mata dakin ya maida ya rufe sannan ya juyo suka hada ido. Mikewa tai tsaye da sauri tana kallonsa, shi ma da yake sanye da boxer da vest kallonta yake with shock.
“Rafi'a...”
“Yaya...”
“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un”
Ya furta sai tai saurin kawarda kanta A take gumi ya fara tarar mata. Mamaki yake ya akai be gane ba, tun a lokacin da Ramlee take kwatanta masa ita, kuma ta fada masa sunanta Rafi'a sai dai be kawo ita ce ba saboda be yi zaton yar'uwarsa na irin wannan sana'ar ba, ya kai ma ta san Ramlee? Zaune yai a gurin ya kifa kai da guiwa.
_________________________
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
MADINA POV.
Ta faka tsakar gidan tana kuka, tare da kai kanta ta jingina jikin sitiyarin tana kuka, gaba daya ji take kamar ta kashe kanta ta hutu. Jin ana kokarin bude gambun motar yasa ta dago kai ta kalli Mahaifiyarta.
“Madina ina kika je cikin daren nan? Karfe 11pm fa hankalina ya tashi”
“Kawai na fita na samu sukunin zuciya ne, Hajiya zan iya mutuwa Wallahi ni kadai na san abun da nake ji a raina”
“Sauko motar fito”
Hajiya ta rika hannun yarta cike da tausayawa, sai Madina ta sauko Hajiya ta kashe motar ta cire key din ta rufe motar sannan ta jata suka nufi cikin gidan. Amaimakon ta kaita dakinta sai Hajiya wuce da ita dakinta kai tsaye, har saman gadonta ta zaunar da ita sannan ta zauna.
“Bana fada miki idan kin tashi zamu yi magana ba? Sai kuma ki kama ki fita tun yamma har dare? Madina karki jefa kanki a cikin wata matsalar fa”
“Hajiya ina son Talba sosai, duk yadda zan misalta miki ba zaki gane ba, ni kadai na san abun da nake ji”
Idon Hajiya ya cika da kwalla.
“Ki yi hakuri Madina wannan jarabarwarki ce, haka Allah ya kaddara miki kaunar Talba ke kanki kin san ba zai yiyu ya fasa auren Leila ya aureki ba”
“Amman Hajiya baya son Leila”
“Baya son ta zai aureta? Lafiyarki kuwa Madina? Kar abun nan ya taba ki”
“Zai aureta ne kawai saboda Daddy, amman baya son ta, baya son ta Hajiya baya sonta...”
Ta fada tana kallon wani gurin daban sai kuma ta kalli Hajiya.
“Ko kuma yana yaudarar kansa ne...”
“Madina karki kuskura ki bari Leila ta gane, kina son Talba, karki yarda shi ma ya sani”
“Na riga na masa alama da haka, na fada masa wasu kalamai da ba su dace ba, ban san ni ba ko ya fadawa Leila tana ta kirana na kasa dagawa”
Ta lumshe ido hawaye na sauko mata.
“Hajiya ba zan iya jure Talba ya auri wata ba, ba zan iya ganinsa da wata ba, Hajiya ina sonsa sosai”
Ta fashe da kuka, sai Hajiya ta kara matsawa kusa da ita cike da tsananin tausayinta ta rumgumeta tana hawaye.
AMINATU POV.
Ta mamaki da tunanin abun da Talba yai mata ta kwana, hannunta a kan lips dinta.
Washe gari kamin tun da asuba suka tashi kamar yadda suka saba, sai dai bata shiga bandakin ba sai da kowa ya gama alwala, sannan ta shiga ta rufe kofar, kamin tai alwala sai da ta kai hannu ta taba lisp din tana kallon kanta a madubin daki. Sai yanzu take jin kamar ba gaske ba ne, kamar mafarki ne ta yi. Sai dai ta ji abun har cikin jikinta sakon da yake son isar mata ya isa har cikin kwakwalwar kanta, kuma ya samu muhali a zuciyarta ya zauna, ta kuma kasa daina jin soft lips dinsa a jikin nata, har yanzu tana jin motsin halshensa a bakinta, and his perfume is wow ta kasa daina jin kamshinsa. Alwala tai ta fito ta yi sallah, for no reason ta ji kyiyar yin azkar yau, gaba daya tunanin abun da Talba yai mata ya dauke mata Hankali, sai ta nade carpet din ta aje.
Haka ta wuni ciki tunanin abun da Talba yai mata, minti daya biyu sai ta kai hannu ta taba lisp dinta, can kuma sai tai murmushi. Ta soma jin kunyar kanta da mutanen gidan kamar an fada mata sun san abun da akai mata.
Misalin tara daidai na dare mai gadin gidan ya kwankwaso kofar falon, Hajiya Laraba tai masa iznin shigowa sai ya shigo ya risina yana fadin.
“Hajiya wai Talba yana sallama da Aminatu a waje yace ta zo da sauri sako zai bata”
Aminatu da hannunta yake cikin plate din tuwo ta sauke kai kasa gabanta na faduwa, abun da ya faru tsakaninta da Talba a jiya sai ya dawo mata.
“To gata nan zuwa, yau ba zai shigo ba kenan”
Hajiya Laraba ta amsa, sannan ta kalli Aminatu.
“Tashi kije idan kin dawo sai ki karasa cin abinci, amman karki dade kina karbar sakon ki juyo”
Aminatu ta mike tsaye ta nufi dakin da suke kwana, ta shiga bathroom din ta wanke hannunta sannan ta fito ta dauki Hijab dinta ta saka ta fito a natse ta ratsa falon ta fice. Bata ganshi harabar gidan ba kamar yadda ta ganshi a jiya, sai kawai ta doshi gate a tunaninta ya tsaya a can ne kamar jiya da ya aje motarsa. Da tunanin abun da zai mata a yau ta isa gate ta bude ta fito, sai tai arba da wata farar mota daidai inda Talba ya faka farar motarsa a jiya, tsayawa tai kallon motar sannan ta karasa gurin motar ta tsaya, banbancin wacan motar da wannan kadan ne, wacan ta Talba ta dan fi tsayi kuma tana da farin gilashi tsabanin wannan dake da bakin gilashi. Bude mata front seat akai ba tare da ta ga wanda ya bude mata ba sai ta leka ciki wata fuskar ta gani mai dauke da mask daya rufe ilahirin mamalakin fuskar, irin mask din da yan fashi suke sakawa, sai ta dago da sauri kamin tai wani yunkuri ta ji an rike ta gam ta bayanta tare da kai katon hannu a rufe mata baki, sannan aka bude bayan motar da karfi aka saka ta a ciki, a nan tai arba sa wani mai mask din hannunsa rike da zungireriyar wuka yana nunata da ita tare da yi mata alama da tai shiru, slowly suka ja motar sukai baya baya sai da suka yi nisa da gidan sannan suka juya suka hau babban titi, mutumen dake rike da ita ya ciro wani bakin kyale ya daure mata idanuwa. Kamar wanda akai wa iyaka da magana haka ta kasa furta komai ko da kuwa roko ne, sai dai bugun zuciyarta ya fara aiki fiye da kima.
LEILA POV.
10am tana zaune tana karyawa wayarta tai kara alamar kira, dubawa tai tana ganin Number Madina sai tai saurin picking.
“Lafiya na yi ta kiranki jiya baki daga ba? Har ina cewa yanzu idan na gama karyawa zan je na dubaki ko lafiya”
Madina ta yi murmushi.
“Lafiya Kalau maganin mura na sha, sai bachi ya dauke ni tun da rana nake bachi har dare, sallah kawai nake iya tashi na yi”
“No wonder, amman dai yanzu kin samu lafiya ko?”
“Gani ma na shigo office amman ban ga angonki ya shigo ba”
“Yanzu ya gama karyawa ya koma bangarensa, maybe zai sake shiri ne kamin ya fito”
“To yayi kyau, amman Leila da ni ce na kira wayarki baki daga ba, ba zan iya kwana ba sai na ji lafiyarki”
“Ni ma fa yau nake son zuwa na duba, ke akwai ma labari fa, wai Talba zai dawo da yarinyar a nan?”
“Haba dai”
A nan ta tsakura mata yadda sukai da Momy.
“Allah yasa dai kar ta kawo muku matsala”
“Hmm tama isa, sai dai ta kawowa kanta, domin zaman kaya zata yi, and ina da wani babban labari da zan baki, kuma akwai abun da na shirya amman maganar ba zata yi a waya ba, and maganar tafiya na gyaran jiki ina son mu yi shawara kamin Momy ta fara kawo min nata”
“Okay zan shigo idan mun ta so aiki”
Daga hala suka yanke wayar. Talba be shiga office ba ai kusan goma, ba Madina kadai ba kowa dake kamfanin idan ya kalleshi zai lura da yana cikin nishadi ba kamar kullum da yake shigowa fuska babu annuri ba. Ita kanta Madina ta yi mamakin yadda ya sake mata fuska yana ta yawan murmushi tana shigowa ya ambaci sunanta kuma ya karbi files din data kawo masa da kansa, tsabanin baya da sai dai ta aje kan tebur. Kamar an mata kyauta wata rayuwa haka ta ji, saboda ganin masoyinta cikin farinciki sai ya saka ita ma ta samu kanta cikin farincikin, a take ta ji duk damuwarta ta wanke, domin bata yi zaton haka ba, ta yi tunanin ko zai koreta ne ko kuma ya tsawalla mata saboda kalaman da tai masa, sai dai ta lura kamar hakan be dame shi ba.
Ana sallame sallah Magariba, Leila ta sauko falon ta zauna tana taunar chewing gum, hankalinta kuma yana kan Zulai da Mairo dake aikin jera abincin dare, dan tabe baki tai ta dauke kai a rayuwarta ta tsani ganinsu a gidan ba tare da sun tare mata komai ba. Sau biyu ana taba door bell din kofar sannan Zulai aje aikin da take ta nufi kofar, wani uban tsaki Leila ta ja.
“Oh na dauka ai jiran kuke sai na je na bude kofar, kamar ba aikin da aka dauke ku kui ba kenan”
Mairo ta kalleta kawai ta dauke kai, Zulai kam ko Juyowa ba tai ba har ta isa gurin kofar ta bude ta sai mai gadin ya miko mata envelop.
“Ga sako in ji wani wai a bawa Hajiya Leila”
Zulai ta karba sannan ta maida kofar ta rufe ta nufo inda Leila take zaune ta mika mata.
“Ga sako ance a baki”
Leila ta kalli envelop din ta yatsina fuska.
“In ji waye?”
“Yusufa ne ya kawo ban san ko waye ya bada ba”
“Dora ta a nan”
Ta fada tana dauke kai, Zulai ta aje a inda ta nuna mata sannan ta nufi dinning dan karasa abun da suke yi. Leila ta cigaba da lasa wayarta na kusan minti ashirin sannan ta aje wayar ta dauki envelop din ta cire salatip din tana duba abun da ke ciki, can kuma ta saka hannu ta ciro dankwali da aka linke yayi datti sosai ga kasa a jiki. Jefar da shi tai da sauri ta mike tsaye with shock har haki take, wani irin ihu ta saka wanda ya saka Mairo da Zulai kallonta, sai kuma tai sauri ta rufe bakinta ta nufi upstairs da gudu tana kiran Momy.
____________________
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
LEILA POV.
Kamin ta karasa hawa sama har da zamewa tai ta fadi, ta tashi da gudu ta banki kofar dakin Momy ta shiga da gudu. Momy dake tsaye jikin wardrobe ta juyo da sauri tana kallonta, Leila ta karasa kusa da ita ta kama hannayenta ta rike jikinta na mugun rawa.
“Ke Lafiya?”
Sai ta nunawa Momy kofa ta kasa cewar komai, kafafuwanta kuma suka kasa daukarta sai ta zube a gurin rike da hannayen Momy.
“Talk to me miya faru?”
“Momy.... Momy... Envelop aka.... Aka... Kawo... Da na.... Bude... Sai... Na... Ga dankwali.... Da....kasa a jiki..... Kamar kamar kamar na Baaba...”
A rarrabe take maganar saboda tsoro, daga karshe kuma sai ta fashe da kuka. Wani irin faduwa gaban Momy yai sai ta zare hannayenta daga rikon da Leila tai mata, tai baya baya ta zauna kan gado with so much shock tana kallon wani bangare na daki, can kuma ta kalli Leila.
“Waya kawo sakon?”
“I don't know, i don't know, Zulai ce ta karbo”
Momy ta mike tsaye da sauri ta fice