Showing 330001 words to 332834 words out of 332834 words
iyayenki ki dawo a nan kin lalata min tawa rayuwar”
Baturiya ta fada cikin kuka tana nuna Ramlee.
“Ai ni na kona, bana jin kauri. Tun farkon fari ya kamata ki san da cutar amman mugum son kudinki ya rufe miki ido, kara ni ai, ban tana aure ba balle na aje yaran da zasu gi bakincikin abun da na aikata nan gaba, kuma ban aikata zina da aurena ba, ke fa duk kin hada, har cikin sunna kika zubar saboda son kudi kuma da cikin kika aikata zina, Allah ya tsare bawan Allah mijinki be da hakkinki shiyasa ya rabu da ke tun kamin ki laka masa cuta”
“Wato kin san mutanen da nake mu'amala da su, suna dauke da cutar amman kika kyale ni saboda kina azzaluma macuciya”
“Ah kudi fa kika so, daman shi Alhajinki na farko a likita daya yake ba mu magani ni da shi, saboda bama shiga asibiti kar a gane mu, ni baki ma fada min yadda akai kika gano kina dauke da cutar ba sai masifa kike ta yi, mutane da yawa zaki same su dauke da cutar nan fa yanzu, ba wani abu bane indai zaki tsare shan magani tun da kowa ya siye rariya ai ya san zata zub da ruwa”
Tsabar bakinciki da takaici Baturiya bata sake ce mata komai ba, ta juya ta fita wasu hawaye masu zafi na sauko mata. Tana isa gidansu ta shige cikin dakinsu ta fashe da kuka tana jin kamar ta kashe kanta ta huta. Kukanta ne ya saka Umma ta shigo dakin da sauri tana tambayar abun da ke faruwa.
“Umma ina son na koma gidan tsohon mijina, ina son na koma gidan Faruk na kula da dana, na yi nadanar duk abun da na yi nasa, Wallahi duk wai abun dana fada karya nake masa Umma, dan Allah Umma ki yi duk yadda zaki yi na koma gidan mijina, ina son Faruk Umma ki taimaka min dan Allah”
Wani irin kuka take na fitar hankali tana riko Umma. Umma kam sai kallonta take tana mamakin ikon Allah, a tunaninta wani asirin ne Faruk yai mata ta haukace tana wannan abun, wata kila ma shiyasa ta fasa auren Al'Qasim. Wani irin zillo Baturiya take tana jin kamar ta dawo da aurenta da karfi ita da Faruk, a yanzu ta san bata da wata mafita kamar ta lallaba ta koma gidansa ko da zai gane Cewar tana dauke da cutar ta riga ta shafa masa dole ta rayu ita da shi a haka. Sai a yanzu take bakinciki da nadamar zubar da cikinsa da tai wata kila da ya dubi yayanta ya dawo da ita.
“Ashe ka tare”
Talba ya kalleshi sai dai be ce masa komai ba. Ali yayi murmushi ya zauna kujerar dake office din.
“Har yanzu zuciyarka na raya maka ina son Leila? Idan ta raya maka haka, bata maka karya ba, Tabbas ina kaunar Leila sai dai a irin son da kake mata ba, so na yan'uwanta na aboki da aboki kuma na yaya da kanwa, Talba saboda kai na san Leila da babu kai wata kila ko sunan taba zan taba sani ba, shakuwar dake tsakanina da ita, kai ka sassasata saboda sasanci da nake yawan yi muku, ita kanta ta shaku da ni saboda haka idan har kana ganin na zufafa akan abun da nake, kai ka bada dama Talba, har abada ba zan iya auren Leila ba ko da baka raye, amman tabbas ina tausayinta, kuma ina son farincikinta, ba zan taba lalata alaka da kai saboda mace ba, amman ka bani mamaki ta yadda ka tare da matarka yau kusan wata daya amman baka fada min ba, na so na kyale na bar magana a yadda ka tsarata kuma ka so ta tafi amman sai na ji ba zan iya ba, i wish you success in your marriage Allah ya ba ku zama lafiya”
Har ya gama fadar abun da zai fada ya fice Talbe be ce masa uffan ba. Fitarsa office din da minti arba'in Talba ya gama abun da zai yi, ya fita office din ya nufi gidansa, sai dai be isa ba sai da ya tsaya ya siya mata kayan kwadayi a hanya. Horn daya ya danna mai gadin ya bude masa gate ya shiga cikin gidan. Ya bude motar ya fito ya rike da ledar da yai mata siyayyar sannan ya isa gurin kofar ya kwankwasa. Ba jimawa ta bude masa tana sanye da wando da riga na Turkish kanta ba dankwalin ta daure gashinta gwanin sha'awa. Kamshin turaren wuta ne abun da ya fara yi masa lale marhabun sai kuma sanyi ac da kuma Aminatu da ta rumgume shi tana masa sannu da zuwa.
“Kin yi kyau Shalele na”
Ya fada yana kare mata kallo sai tai murmushi ta mika hannu ta rika ledar hannunsa, shi kuma ya miko hannunsa ya dafata yana shafa bayanta zuwa mazaunanta.
“Me kike dafawa?”
“Doya”
“Wow kamar kin san ina kwadayin doya yau kuwa”
“Da gaske”
Ta fada bayan ta aje ledar hannunta kan kujera ta juyo ta saka hannayenta duka biyu ta rumgumo wuyansa.
“Uhmmm”
Ya fada yana sumbantar kirjinta, sai ta sake shi tana kokarin juyawa ya rike ta yana shafa shape dinta yana sumbatar wuyanta kamin ya juyo da ita ya hade bakinsa da nata. Rayuwa ta zame musu mai sauki idan yana cikin gidansa har mantawa yake yana da da wata damuwa kamar yadda ita ma yake matar da ita duk wata damuwa tata yana faranta mata rai, idan yana gida tana jikinsa idan baya gida suna tare da juna waya. Sai da ta wata biyar a gidan sannan ta samo wanda zata rika koya mata karatun bokon, a lokacin tana da karamin cikinta dan wata uku da Talba ke ta tattali kamar zai cinye.
*Nine months later*
Dan dan zon mutane ne suka cika bakin kotun cikin har da yan jarida, yan'uwan Baaba da wasu daga cikin dangin Daddy da Momy wasu a cikin kotu wasu a waje. Suna sauraren hukuncin da yankewa Leila da Madina tare da mutanen da ta aikata mummunar ta'asar tare da su hukunci a zaman kotu na karshe. Shari'ar Leila ce ta farko da aka fara yi sai da Alkalin ya bawa duka lauyoyin damar magana idan da mai karin bayani kowa yayi maganar. Lawyer Leila ya roki alfamar kotu ta yi ma Leila sassauci ta hanyar biyar diyar Baaba, duba da akan kuskure ta aikata abun da ta aikata kuma ta amsa laifinta ba tare da ta wahalar da kotu ba. Alkalin ya karanta dokoki da kuma hukuncin da dokar kasa ta criminal code ta tanadarwa wanda ya aikata kisan kai.
“Akan wannan hukuncin koru ta yankewa Leila Mu'azu Shimkafi hukuncin kisa ta hanyar rayata....”
Wani irin ihu Leila tai ta zube kasa tana hargagi da kuka marar misaltuwa, Daddy yai saurin yin masa da kansa hawaye suka zubo masa, Momy kuma ta fashe da kuka ta dora hannu a kai.
“La'ilaha Illalahu Muhammadu Rasullulillahi”
Talba ma sai da hawaye suka zubo masa, Kabir ya mike tsaye yana kallon Alkali cike da tashin hankali, Amal kam bata san lokacin da ta bar inda take zaune ba ta nufi inda Leila take tana wani irin kuka domin ganin take kamar a lokacin za a kasheta. Sai dai kamin ta karasa gandireba suka rike Amal wasu kuma suka tashi Leila ta mike tsaye tana zubewa kasa sai sunan Daddy take kira.
“Daddy.... Daddy.... daddy.... Momy.... Momy.... Talba... Kabir.... Wayyo Allah Allah ya tuba ka yafe min Allah.... Wayyo Allah na.... Kashe ni za'ayi Daddy..... Daddy.....Daddy su kai ni inda ba a dawowa babu wanda zai sake ganina.... Ba zan sake ganin kowa ba..... ”
Wani irin kuka Leila take na tashin hankali da taba zukata, kusan duk wanda yake kotun sai da yayi hawaye, shi kansa Alkalin sai da abun ya taba masa zuciya. Zubewa take kasa gandirobobin dake tare da ita suna rikonta. Ali ma kuka yake sosai yana jin kamar ace akwai wani abu da Ai iya yi.
Can ta samu sa'a ta fisge kanta ta ruga da gudu ta rumgume Daddy sai ya fashe da kuka da kuka ya rumgumeta sosai Momy ta mike tsaye da sauri ya rumgumeta ta baya tana kuka.
“Daddy karka bar ni, Momy ki taimaka min don't leave me”
Da karfi suka bata da Daddy da Momy dake ta uhu cikin kotun, daker aka fito da ita Amal kuka Kabir kuka Talba kuka Daddy kuka Momy kam ana kawowa bakin kofar fita kotun ta yanke jiki ta fadi. Sai da aka dauke ta zuwa asibiti. Leila kuma aka wuce da ita gidan yari. Madina ta aka yanke mata hukuncin shekara goma a gidan yari kamar yadda dokar kasa ta tanadarwar wanda ya aikata kidnapping. Alfa aka yanke masa hukuncin kisa ta yankar harbi da bindiga tare da yaransa.
Daga asibitin Talba ya wuce gida gurin matarsa tun cikin mota yake ta hawaye har ya isa gidan, Aminatu na ganinsa ta san mijinta yana cikin damuwa kamin tace masa komai ya rumgume ta ya fashe da kuka. Ko ace be hada komai da Leila ba ya san an yanke mata wannan hukuncin dole ya tausaya mata balle kuma har sun rayu tare da shi da ita.
“You got lucky kaddararki mai sauki ce Aminatu, idan kika ga kaddarar wasu sai kin gode Allah”
Ya fada yana shafa fuskarta.
“An yankewa Leila hukuncin kisa ta hanyar rayata”
Wani irin sanyi jikinta yayi take hawaye ya kawo a idonta.
“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un yanzu ba kasheta za'ayi?”
Ya daga mata kai, alamar eh
“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un”
Ta furta tausayin Leila ya cika mata zuciya. Ita da Shi sai suka koma kamar marar lafiya. Ta kasa ce masa komai, shi kam yana shiga dakinaa sai bachi yai gaba da shi. Sai da gama komai sannan ta zo gabansa ta zauna ta kai hannunta hannunta tana shafa kansa dayan hannunta kuma a kan cikinta. A hankali ya bude idonsa ya tashi zaune yana kallonta damuwa ce karara a fuskarta idonta yayi ja sosai ya kumbura alamar ta yi kuka sosai.
“Zan tambaye ka wani abu”
Ya kalleta.
“Minene burin Leila na karshe a duniyar nan?”
Talba yayi shiru yana nazari, sannan ya sake kallonta.
“Ban sani ba”
“Aurenka....”
Ya fada wani sabon kuka na zo mata, sai ta mika hannunta ta rika hannunsa ta matsa sosai cikin nata.
“Dan Allah ka cika mata wannan burin, ka aureta ko na rana daya ne, ka rumgume ta ka fada mata kana kaunarta ka cika mata wannan burin kamin ta koma ga mahaliccinta dan Allah Talba... Ka yi min wannan saboda ni saboda abun da zamu haifa”
Ta dora hannunsa saman cikinta dan wata shida, sai ya daga mata kai ya kwantar saman cinyarta hawayenta na sauko suna diga gefen fuskarsa.
Washe garin ranar da aka suka yi haka, ya samu Daddy da zancen, kuma Daddy ya goya masa baya aka tara few people aka daura musu aure ba tare da sanin Leila ba. Sannan Daddy ya kira Lauyerta ya zo gida suka tafi tare da shi da Daddy da Alhaji Tukur abokin Daddy. Domin har lokacin Momy tana asibiti. Ba au sha wahalar ganinta ba kasancewar suna tare da Lauwyer ta ne, Talba na tsaye har ta gama gaisawa da da su Daddy da Alhaji Tukur, Leila na zaune kanta a kasa, ta ki yarda ta kalli kowa, har lokacin hawaye take, zuciyarta har wani zafi take saboda bakinciki. Agaban Talba Daddy da Alhaji Tukur suka yi ta bata magana suna kokarin kwantar mata da hankali, har suka yi suka gama sannan ya zauna daga shi sai ita yana kallonta hawaye na sauko masa.
“Na sani wannan ba abu ne mai sauki ba Leila...”
Sai kuma ya kasa karasawa saboda kuka. Ya mika hannunsa ya riko hannunta ya saka a gefen fuskarsa.
“I'm sorry...”
Sai ya mike tsaye ya mikar da ita tsaye ya ya zagaya gafen da take ya rumgumeta.
“Na san burinki na karshe Leila, aurena an daura mana aure da ke yau”
A take ta fashe da kuka mai karfi ya rumgume shi.
“Ina kaunarki sosai, ina son ki Leila”
“Ka yafe min Talba ka yafe min duk abun da na yi maka please forgive me, kudi da yan'uwa ba su amfana min komai ba, mummuman halina ya kai ni ga halaka”
Talba ya rumgume ta sosai.
“Ya isa Leila, kaddararki ce a haka I love you so much”
Ya dagota jikinsa ya hade bakinsa da nata, sannan ya cire ya jingina goshinsa da nata, ita da shi suna maida numfashi, sai gata tana murmushi.
“I'm happy zan tashi da aurenka Lahira, i will be among your wife's”
“I will hold your hand to janna In'Shaa Allah Leila i love you so much”
“Ina Momy tana lafiya?”
“Tana asibiti”
“Please take good care of her, and Amal duk wani abu da kasan ba shi da kyau da kake hana ni na aikata ka cigaba da hana Amal”
Ya girgiza mata kai, sannan ya sumbanci hannayenta.
“Duk wanda kasan na taba mu'amala da shi ka roke shi ya yafe min, ni na yafewa kowa, build a huge Mosque for me, and ask Allah to forgive me”
“I will Leila a will i love you do you know that?”
“Now i know....”
Ya sake hannunta bayan ya sumbanci hannun, saboda security dake fadar lokaci yayi. Sai ta rike masa hannu ya rumgume shi.
“Stay here one more time...I'm so weak...”
Daker ta barshi ya tafi tana kuka shi ma yana kuka suka rabu, a ranar Leila ta raina kanta, tarin dukiya da sutura da dangin da iko ba su kwace a gaban alkalin duniya ba, idan ta tuna cewar zata goge laifinta ne har a gurin Allah sai ranta yayi sanyi.
Ranar da za a zatar mata da hukuncin aka fito da ita duka danginta suna nan, sai da tai magana da kowa ya nemi yafiyar kowa ta rumgume Kabir da Talba da Amal da Momy da Daddy, sannan ta shiga mota aka wuce da ita tana kallon yan'uwanta ta bar nan duniya. Tafiyar da ba a dawo da ita ba kenan sai gawarta, addu'a sosai akai mata kuma ta samu jama sosai saboda mutuwarta ta zama darasi a gurin mutane da dama musamman masu rayuwa irin nata.
“Allah ga yata nan ta dawo gareka, Allah ka yafe mata, ka karbi bakuncinta ka saka mutuwa ta zama hutu a gareta, kuma ya karbi tubanta, Annabi ya san da zuwanta”
Shine abun da Daddy yake ta fada har aka kaita gidanta ma gaskiya bayan ayi mata sutura an mata sallah. Kusam wata biyu Momy tai asibiti bayan rasuwar Leila sannan aka sallamota bayan ta fawwallawa Allah komai.
BATURIYA POV.
Sai da Umma ta saka ta gaba da fada ta tambaya sannan ta fadawa Umma gaskiyar komai, da kuma turba da Ramlee ta dorata, da irin cin amanar da tai ma Faruk. A lokacin ana ta shirye shiryen auren Fahat da Amal d kuma na Kabir da Rukaiya da za'a hade ayi lokaci daya. Faruk kuma matarsa Ramla na daf da haihuwa, karamin bakinciki da kunya Umma ta ji na jin cewar yarta ce marar Gaskiya, domin ita ma ta yi ma Faruk rashin mutumci da kyautawa. Hankalinta be kara tashi ba sai da fahimci yarta na dauke da cutar nan mai karya garkuwar jiki, ita kanta Baturiya a lokacin ne ta gane rayuwarta ta kare domin Faruk Fulani din da ta so komawa ya mata nisa har bada, duk hanyar da zata bi ya kula ta ta bi amman ba ta yi nasara ba, har Sultan dake gurin Mama kasancewar ya bar mata shi ne a gurinta ya zauna. Ta bi ta bi ta hanyar Mama amman ba wani alamun nasara.
BAYAN WANDASU SHEKARU....
A hankali aka yaye kyallen da aka rufe wani dan karamin asusun tallafawa yan gudun Hijira da marayu da Aminatu da kaddarar tare da Yayanta Bashir. Sai kowa ya ware hannun yana taba musu yan jarida na dauka. Babban dakin taro ne mai dauke da mutunen kusan dari biyar. Faruk da Ramla suna zaune a teburinsu Faruk na rike da Nimra, Ramla kuma na rike da Namra second set of twins dinsu da suka haifa. Rukaiya da Kabir a tebur daya, rike da dansu Abul-khairi. Yayinda Amal da Fahat suke zaune a guri daya yaronta Affan a kujera daya, sai tsohon cikin dake jikinta. Mommy da Daddy kuma na zaune da gaba rumgume da Little Leila wato yar Aminatu ta farko sai yaron cikin dake jikinta a yanzu. Sai da Talba ya gabatar da yawajin godiya na masu halarta taron sannan Aminatu ta kaddamar da asusun tallafi da naira miliyan goma. Kana ta kora da wajabin dalilin na som tallafawa yan gudun hijira da marayu a cikin halshen turanci. Kusam duk manyan bakin da Talba da Daddy suka gayyato sai da suka bada na su tallafin har Daddy da Momy. Sannan aka tashi taron bayan anci ansha kowa yana hamdala.
Ni ma na ce Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!
Fatar Allah ya datarda mu ya tsare mu da aikim dana sani, kuma ya tsare mu da sherin yan bindiga.
For wadanda suka karanta ba su biya ba, ku sani wannan shari'ar sai gaban Alkalin da babu Lawyer ba mai kariya, shi zai mana hukunci.
For those who patronized me, na gode Allah ya bar kauna ya rufa muku asiri duniya da lahira. I love you All 😍 Zan yi missing dinki sosai more especially yan Comments Group💔😪
Subhanaka Allahumma wa bihamdika, ashhadu an la ilaha illa Anta, astaghfiruka wa atubu ilaika🥰