Showing 189001 words to 192000 words out of 332834 words
din kofar falon ya fito ya doshi kofar, hannunsa ya saka ya danne door bell din ya rika kara kamar zai tashi gidan sai kuma ya saka kafarsa ya halbi kofar. Cikin tsoro Amal ta bude masa kofar tai baya baya tana kallonsa, kusan a rayuwarta bata taba ganinsa cikin irin wannan bacin rai ba, fuskarsa babu annuri idanuwansa sun rine I kamar ba nasa ba.
“Ya...”
Ya watsa mata harara sai tai shiru, Madina dake zaune ta mike tsaye tana kallonsa, shi ma kallonta yai kamin ya dauke kai ya kalli Leila dake saukowa downstairs.
“Between you and Kabir waya haska ni shekaranjiya da mota? And waya dauke Aminatu yau?”
Tsayawa tai cak tana kallonsa, domin gaba daya bata fahimcin inda kalamansa suka dosa ba.
“I'm talking to you”
A nan ma kallonsa kawai take ba ita kadai ba har da Amal da Madina da gabanta ke mugun faduwa. Door bell din aka sake dannawa sai Amal ta nufi kofar ta bude, Ali ya shigo da saurinsa barin kofar tai a bude ta nufi stairs da gudu, domin fadawa Momy abun da yake faruwa.
“Leila na kira wayarki na fada miki ki fita daga gidan nan for a while, ba ki dauka ba please go back to your room...”
Ali ya fada, sai Talba ya kalleshi.
“Really? How could you do such things Ali? Wait wai me kake so na yi ne? Sitting here watching and not doing anything? What do you expect? Na kyale yarinyar nan ta sha wahala?”
“Wace yarinya?”
Momy ta tambaya, sai ya kalleta.
“Aminatu, someone kidnapped her”
“Kuma ka rasa wanda zaka zarga sai Leila? Tana cikin damuwa zaka kara mata wata?”
Cewar Momy cikin daga murya da fusata.
“Not just Leila ina zargin kowa da kowa, idan wani abu ya samu yarinyar na rantse da Allah ba zan kyale ba, no matter how close I'm to you, alkawarin farko dana fara yi ma yarinyar nan is zan kula da ita, and i won't let anything happen to her. Surely i will fulfill that promise!”
Zaunawa yai a kujerar dake kusa da Madina ya dafe kansa da hannu biyu. Madina kallonsa take da mugun faduwar gaba. Can kuma ya dago cike da damuwa.
“Yarinyar nan bata san location din kowa ba, bata san inda zata ce a kai ta ba, and bata da number kowa a kanta poor girl...”
Yana rufe baki Kabir ya shigo mai gadin gidan na biye da shi.
“Ranka ya dade Jamal ya iso yana waje”
Mai gadin ya fada yana kallon Talba.
“Karbo sakon Hannunsa”
Ali ya fada sai Talba ya ce.
“Je ka ce ya shigo”
“To”
Ya juya da sauri ya fita, sai falon yai tsit kamar babu kowa a ciki. Kamar yadda Talba ya umarta haka Jamal ya shigo yana ganin yadda kowa yai tsaye cirko cirko ya san ba lafiya ba, har inda Talba yake zaune ya karasa ya mika masa wayar da already ya saka sim din a ciki ya kunnata.
“Gata ranka ya dade”
Talba ya karba. Sannan ya mika masa wayar Hajiya Laraba bayan ya cire password din.
“Tura hoton nan a wayarka”
Ya karba da sauri ya shiga ya danna share to Xander, sannan ya ciro wayarsa ya shiga tasa Xander yana connecting.
“Done”
“Aje a buga hoton nan a raba shi ko'ina Wanted, ka bada sanarwarta a gidajen radio, kuma a sanar da cewar duk wanda ya gano inda yarinyar nan take zan ba shi naira miliyan uku”
“An gama ranka ya dade”
Jamal ya fada sannan ya fice da sauri, daga Momy har Ali Madina, Leila da Kabir daya shigo yanzu mamakinsa suke. Gmail din wayar ya shiga ya saka gmail dinsa sannan ya dawo gurin contact ya nemo number Dpo ya kira shi.
“Hello Qasim kana office?”
“No ai na bar garin Gusau yanzu, lafiya dai”
“Zan kira ka”
Talba ya kashe wayar.
“Can someone explain to me abun da yake faruwa?”
Kabir ya tambaya, sai Talba ya kalleshi.
“Har sai an maka bayani? Duk wanda ya dauki yarinyar nan yana a nan tare da mu, and if na gano wanda yai wannan aiki... Wow.... ”
Ya furta yana wani murmushin takaici. Leila ta karasa saukowa tana takawa zuwa inda Talba yake zaune hawaye na sauko mata.
“Why is she so important to you? Miyasa idan wani abu ya sami yarinyar nan kake haukace ka fita daga hayyacinka, and why I'm always the first suspect?”
“Because he love her”
Kabir ya amsa mata. Sai Ali yai saurin shiga tsakani.
“No... Ba..”
Be karasa ba Talba ya tari numfashinsa yana mikewa tsaye.
“Yes you're right, i loved her ni ma a yanzu na san da haka, domin idan bana sonta i won't hold her hands and kiss her i wouldn't hug her har ka gan mu a daren daka haske mu a mota”
Ali ya daki kirjinsa cike da bakincikin furucin da yake da kuma zargin Leila, and the way da Leila take hawaye ya saka shi cikin bakinciki.
“Enough.... Talba ka zura da yawa you lost it.... And ka daina zargin Leila ko Kabir ba su suka dauke ta ba”
“Kai ka dauke ta kenan?”
Talba ya fada yana kallonsa with angry face. Ali ya dauke kai yana murmushi sannan ya sake kallonsa.
“Leila was right, kai ne da matsala Talba, and ka bi ka haukace akan yarinyar nan, the girl you meet on the street of the hospital, the girl that was kidnapped and rape? Why is she so special to you? I'm your best friend, Leila is your fiance, Kabir is your blood, Amal and Momy are also there amman idonka ya rufe saboda yarinyar da she can't read and write?”
Talba ya sake tsayuwa a gabansa da kyau yana masa wani mugun kallo.
“Now i know who my friend is, i will soon know my enemies, and kar bakinka ya sake furta wata mummunar Kalma akan Aminatu! You know it ba zan iya daukar hakan ba, a matsayina na mijinta...!”
Kabir yayi gwalo ido waje.
“Oooooo wooooo wait what do you mean?”
Talba ya watsawa Kabir wata uwar harara, Momy, Leila Amal da Madina mamaki ya kusa kashesu a tsaye, Madina ta dafe zuciyarta.
“Aurenta kai?”
Ta tambaya a zuciyarta ba tare da ta san tambayar zata fasa bakinta ta fito ba har kowa ya ji.
“Yes i marry her, i can't hide this anymore, Aminatu is my wife....”
Talba ya amsa mata da kansa yana kallonta, saurin dafa kujera tai saboda kafafuwanta da suka kasa daukarta, a take hawaye suka kwankwaso mata kofa, bakinciki yai mata sallama. Momy ta kalli Talba da wani irin duba na wulakanci da kaskanci.
“Ka tsaya a gabana, kana zargin Yaya da sace yarinyar da bata kai ta wanke tufafin gidan nan ba, you stand in front of me and my daughter, telling us ka auri wata banza sharar bola, Mu'az ko kadai ka rage namiji Leila ba zata aureka ba! And daga yau na ja jan layi tsakanina da kai babu ni... Babu kai.... A yau ina son ka sani ka rasa tun kana karami kuma rashi na har abada I'm not your mother and i will never be...”
Momy na kaiwa nan ta taka zuwa inda Leila take tsaye tana kallon Talba ta riko hannunta ta fisgota da karfi da zimmar ta jata su nufi upstairs, sai Leila tai baya ta sulale kasa sumammiya, Ali da Amal suka yo kanta da sauri suna kiran sunanta. Momy ta yi baya da sauri tana rufe bakinta tare da fashewa da kuka, Madina ta dauki wayarta ta fice da gudu tana wani irin kuka da bata san ta inda yake zo mata. And now it's between Talba and Kabir kowa na kallon dan'uwansa, kallon kallo akuya kallon kura...
Juyawa Talba yai ya dauki wayarsa da wayar Hajiya Laraba ya fice daga falon. Motarsa ya shiga yai mata key masu gadin na ganin haka suka sake bude gate din daman suna komarin rufewa ne bayan da suka budewa Madina ta fita. Tuki kawai yake not knowing what to do or go, gaba daya duniyar ta rikice masa.
“Where are you Shalelena.... Who do this to you....?”
Ya furta yana lumshe ido, be ankaro da driving yake ba har sai da motar dake gefensa ta danna masa horn da karfi saboda hawa tsakiyar titi da yai, da sauri ya sauko saman titin ya faka gefe ya dafe kansa yana jin zuciyarsa na bugawa da karfi. Can kuma ya sake hawan titin ya dauki hanyar da zata kai shi office din Daddy, be taba samun kansa a cikin tsoro marar misaltuwa ba irin yanzu, be san irin kallon da Daddy zai masa ba, but he most face this, ya kamata ya fadawa Daddy da kansa kamin ya ji a gurinsu Momy. Farkin yai harabar ma'aikatar sannan ya fito ya shiga ciki yana tafiya cike da nauyin kafafuwa. For the first a yau ya ji ba zai iya tunkarar office din Daddy ya shiga kai tsaye ba, har sai da ya bukaci Sakataren Daddy yai masa iso, shi kansa Sakataren sai da yai mamaki ganin Talba yayi abun da be taba ba, ko Daddy baya nan shiga yake ciki sai dai ya zauna zaman jiransa hakan yasa idan Talba ya zo sai dai ya gaishe shi, be taba hana shi shiga.
“Ya ce ka shigo”
Sakataren ya fada bayan ya shiga ya sanarwa Daddy. Talba dake zaune ya shafa fuskarsa sannan ya mike tsaye ya nufi office din cikin damuwa da faduwar gaba.
“Yau kai ne da neman izinin shiga office dina da kanka?”
Daddy ya tambaya yana kallon Talba with serious look. Talba ya kasa cewa komai kuma ya kasa daga kai ya kalli Daddy har ya isa gaban teburin ya zauna.
“Akwai abun da yake damunka?”
Daddy ya sake tambaya cike da kulawa, domin ya ga dansa ba a yanayin da ya saba ganinsa ba.
“Daddy magana nake son yi da kai, ina son na fada maka wani abu, amman ban san yadda zaka kalleshi ba, ban san yadda zaka ji ba, amman ina son kasan cewar na aikata abun da na aikata ne saboda gyara ba barna ba...”
“Ina saurarenka...”
Jimmm Talba yai ya dade kansa a kasa kamin ya soma bawa Daddy labarin auren Aminatu da yai a boye da kuma yadda komai ya wakana. Murmushi Daddy yai.
“Come on my friend... Control your tongue young Man”
Sai a lokacin Talba ya dago ya kalle Daddy idonsa cike da kwalla.
“Da gaske nake Daddy, na san zaka kalle a wani mutum dabam kuma zaka ji ba dadi dan Allah kai hakuri ka yafe min”
“Miyasa ka zabi ka fada min a yanzu then?”
“Saboda an sace ta”
Daddy ya sauke ajiyar zuciya ya kai hannunsa kan bakinsa.
“Garin ya?”
“Ban sani ba, ban san manufar wanda ya dauke ta ba, and now i exposed every thing, Momy ta yi fushi da ni”
Ya karasa cikin wata murya mai ban tausayi tare da yin kasa da kansa.
“Hakan yasa kake tunanin ni ma zan iya fushi da kai? Kuskurenka kawai na yi min karya ne ka ce baka sonta, ni kuma ka san ba zan taba shiri da abun da baka so ba”
“A lokacin ban san ina sonta ba Daddy”
“Yanzu kuma ka sani?”
Yayi shiru kansa a kasa.
“Ban san wane hali take ciki ba, ko ta ci abinci ko bata ci ba, ko dukanta suke Allah kadai ya sani... Daddy karka yi fushi da ni dan Allah abun zai min yawa”
“In shaa Allahu tana ciki koshin lafiya, babu abun da zai same ta, a can lokacin da kana karami, idan kai ma Momy ka laifi ko wani bayana kake guduwa ka boya, sai a yanzu da ka girma kake ganin ba zaka iya gudowa bayana ka boya ba? Young Man you're wrong very very wrong, Ba ni da farincikin daya wuce naka, damuwarka damuwata ce, Daddy is always on your side, zan yi magana da CP, za a gano ta In Shaa Allah, ina tunanin wanda ya sace ta yayi ne kawai dan ya gwadaka, so be a Man”
Talba ya mike tsaye da sauri ya zagaya ya nufi Daddy, Daddy na ganin haka ya mike tsaye Talba ya rumgume shi.
“Ba uba kawai ka zame min ba Daddy, ka zamar min har da uwa, ranar da baka nan Daddy zan shiga wani hali”
Ya fada cikin kuka kamar ba shi ba, har cikin zuciyarsa yake jin kaunar mahaifinsa fiye da kima. Daddy yayi murmushi.
“I'm proud of you Talba, and now i know how my son is, ashe kana da raunin zuciya haka?”
Talba ya dago ya share hawayensa ya kalli Daddy.
“Daddy your Son is in Love i don't know what is wrong and right for now, gaba daya bana da kwanciyar hankali”
Daddy yayi murmushi irin na su na manya, sannan ya kai hannu ya dafa kafardarta.
“Karka damu, i was in your shoes before, it's hard right?”
Ya gyadawa Daddy kai.
“Yeah it's”
Daddy yayi murmushi ya kai hannunsa ya danna telephone.
“A fadawa Direba ya shirya zamu je gurin CP yanzu”
Shine kawai abun da ya fada, sannan ya kalli Talba.
“Go home and rest zan kula da komai”
Talba baya son musawa Daddy hakan yasa ya gyada masa kai, ya nufi kofar fita ba dan yana jin zai ma iya zuwa gidan ba, balle kuma wani zancen hutawa ya biyo baya, ba taba samun kansa a cikin tashin hankali irin wannan ba.
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
MADINA POV.
daker ta iya kai kanta gida saboda kukan da take, tana jin zuciyarta da mugun nauyi kamar zata fashe. A galabaice tai farkin ta bude motar ta fito ba tare data kashe ba, jikinta har rawa yake kamin ta isa gurin kofar falon ta kai hannu ta kwankwasa, sai kuma ta jingina jikin ginin saboda bata iya tsayuwa da kafafuwanta. Ana bude mata kofar ta shiga da sauri ta tana kuka kamar ranta zai fita. A tsakar falon ta fadi tana kuka kamar wanda akai wa mutuwa har da dora hannu a kai. Hajiya ta fito dakinta da sauri ta doso inda take.
“Ke lafiya?”
“Hajiya Talba yayi aure...”
Ta fada da karfi tana kuka.
“To shi ne me? Daman ai kin san auren za'ayi tun da aka saka musu rana”
“Ba da Leila ba Hajiya, ai na fada miki baya son Leila, da wata da yake so ne wata dabam, yarinyar da ya kawo gidan nan...”
Hajiya ta cika da tsananin mamaki domin bata taba zaton haka ba.
“To ke miye na ki a ciki? Wai Madina ba zaki raba kanki da wahala ba? Da ace kina gabansa ai da yanzu ya fara kula dake, amman ya tsallakeki ya auri wata, kuma Leila da Mahaifiyarta suna gani ba su iya yin komai ba? Har kike tunanin za ki iya yin wani abu da za ki burge shi yace yana sonki? Kina cutar da kanki ne kawai, kuma kina mafarkin da ba zaki taba farkawa ba har a bada”
Dagowa tai ta kalli Hajiya, tsakanin abun da Talba yai a yau da kuma kalaman da Hajiya take fada mata sai ta rasa wanne ya fi yi mata ciwo.
“Ko wace uwa, tana kokari ta ba yarta abun da take so, a yau Momy ta ci mutunci Talba, saboda ya auri wata wanda ba yarta ba, bayan kuma ya san yarta tana sonsa. Amman ni kalleni na rasa wanda nake so, kuma mahaifiyata tana kara min da wani bakincikin”
“Gaskiya nake fada miki Madina, kuma ba ki rasa masoya ba, kawai kin bawa kowa dama ne, saboda tunaninki da hankalinki ya karkarta ya koma gurin Talba, tausayinki nake karki jefa rayuwarki cikin matsala”
Ta daga kai, sannan ta saka hannayenta ta share hawayenta ta mike tsaye, ba tare da tace komai ba. Ta nufi kofar fita ta fita daga falon, Hajiya ta bita da kallo har ta fice sannan ta nufi kujera ta zauna cikin damuwa, domin har ga Allah tana tausayin yarta. Gurin motar Madina ta koma ta kashe motar ta kwashe takardunta da jakarta ta dauki wayarta sannan ta rufe motar, sannan ta dawo ciki daman a bude ta bar kofar. Kallo daya tai ma Hajiya ta dauke kai ta nufi hanyar dakinta.
“Ki yi ta addu'a, sonsa ya fita zuciyarki”
Tsayawa tai cak sannan ta juyo ta kalli Hajiya.
“Lokacin da sonsa zai shiga zuciyata ban ma sani ba, ba addu'a na yi ya shiga ba, kawai na samu kaina ne cikin kaunarsa, irin kaunar da bana jin Daddy ma yana masa irinta, wata kila akwai abun da Allah yake nufi da hakan, mu barwa Allah komai Hajiya”
Tana gama fadar haka ta juya ta shige dakinta. Saman gadonta ta sauke komai sannan ta zauna kanta na mugun ciwo, ta kasa daina jin muryar Talba a lokacin daya amsa mata cewar ya auri Aminatu.
“Talba ka kasa gane cewar ina sonka, ka kasa ganin hakan a cikin idona da mu'amala ta, miyasa idonka ya rufe haka? Baka jin tausayina? Baka ganin ya dace na samu farinciki a tare da kai?”
Ta mike tsaye ta nufi madubinta tana kallon kanta.
“Miyasa jarabawa ta zata zo min ayanyin da ba zan iya dauka ba? Dole ne ka fahimta Talba? Dole ne ka karancin kaunarka a idanuwana kuma ka san da ita a zuciyata”
Ta lumshe ido tana sauraren yadda zuciyarta take mata zafi sosai.
*If na gano wanda yai wannan aikin... Wow...*
Kalamar ta tsaya mata a rai, iyakar kokarin da take na ganin ta kwantar da hankalinta ne ta manta da komai cikin har da furucin Talba na cewa ya auri Aminatu. Ta dade a haka sannan ta bar gaban madubin ta nufi bandaki sai da ta shiga sannan ta cire tufafinta ta