Showing 234001 words to 237000 words out of 332834 words
ba ce a gareki, daman kin ki fada gaskiya tun farko kamin tafiya ta yi nisa idan yaji zai iya ya auri a haka yau ala saba saurayi ya auri bazawara balle ki da idan ba an sani ba ba ma za ace kim haihu ba, kuma idan ma yace ba zai aureki ba miye na kuka kina haka da ke tsaye da kyau zaune da kyau”
“Umma ina son shi sosai, kuma kin ga yana da kudi ga shi saurayi kuma yaro, kuma yana so na, kara na auri wanda makiya da magulmata za su ji haushi, kin san halin dana fito fa, idan na auri wanda zan sha wahala ai ko Faruk sai ya min dariya”
“Masu kudin ai da yawa Rafi'a, nima bana miki fatan auren talaka a yanzu, ka fito gidan wahala kuma ka koma kana shan wata wahalar? Idan kika auri talaka ai Faruk da mahaifiyarsa ma dadi za su ji, aa Wallahi kara dai inda zaki huta”
“Ni ma haka nake so Umma shiyasa nake son na auri Fahat”
“Idan ma be auri ba, ai ba zaki rasa mai so ba, amman kya zauna ki yi ta kuka ki saka kanki a wahala saboda namiji? Kika haihu da Faruk ma kika rabu da shi balle wannan”
“Momy Wallahi ina masifar sonshi, idan ya rabu da ni zan shiga damuwa ”
“Ya fada miki ba zai aure ki ba ne?”
“Aa amman alamu ya nuna haka saboda mahaifiyarsa bata son auren, kuma yace idan ta dage ya rabu da ni zai rabu a ni”
“To tun wuri ki ki fada masa gaskiya, ba sai ya gano da kansa ba, ni daman tun da kika saka Aisha tai min maganar nan hankali be kwanta ba, domin ni ban ga abun boye boye ba, kara komai za ayi a fadi gaskiya a huta, amman na kyale ki ne saboda kin nuna kin fi son ki boye masa din, amman ni na san ko gurin Yayanki suka je ai dole zai fada musu gaskiya, ko da nace kar ya fada ba zai yarda ba”
“Amman Umma idan na fada masa yanzu zai iya kara zama silar rabuwa ta da shi saboda ban fada masa ba tun farko na boye masa gaskiya”
“Amman fa dole zasu yi bincika, musamman da kika ce mahaifiyarsa bata sonki, idan kika ba ayi binciken auren ba to auren yar Alhaji wane ne da Alhaji wane, isu isu masu kudi, amman idan mai kudi da talaka ne sai an yi bincike kuma kin ga ita neman aibinki take saboda bata son danta ya aureki”
Ta share hawayenta.
“Idan na fada masa ya ce ba zai aure ni ba fa?”
“Shikenan kin huta babu wani abun boye boye tsakaninku, kuma kina zaune wani zai ce yana so, gari da yawa ai maye baya cin kansa”
Ta sauke ajiyar zuciya da karfi.
“Ki daina wahalar da kanki a kan namiji, haka kika yi ta zaman nan a gidan Faruk kina cutar kanki, yanzu kuma kim fito zaki karawa kanki wani ciwon namiji? Ina dalili”
Umma ta fada tana jin haushin yadda Baturiya take ta hawaye. Share hawayenta tai.
“Zan fada masa, amman idan ta tabbata ba zai aureni ba zan shiga damuwa sosai Umma, saboda ina son Fahat”
Ta karasa cikin kuka.
“Yanzu dai tashi ki wanke fuskarki ki fito ki karya”
“Toh”
Ta amsa cikin kuka, sannan ta tashi ta nufi bandakin tana tafiya kamar zata fadi, Umma ta girgiza kai.
“Allaha ya dauke miki wannan jarabawa da kike sha akan maza, kin samu kin rabu da kaya yanzu kuma zaki daukowa kan ki wani sabon kuka, sai kace shi kadai ne autan mazan duniya”
Cewar Umma sannan ta tashi ta fice daga dakin.
AMINATU POV.
Tana gama wankan ta dauki tufafin data cire zata maida sai ta ji yana mata magana kamar ya san abun da take.
“Karki maida wannan tufafin”
Ta kallin tufafin dake hannunta.
“To akwai wani? Ai babu wani”
“Akwai mana”
“To ba ni”
“Kin rufe bandakin ya za'ayi na baki?”
Ta aje kayan hannunta ta matsa kusa da kofar ta kara gyara daurin zanenta ta bude kofar a hankali ta mika masa hannunta.
“To ba ni”
Tana jiran ta ji ya miko mata tufafin sai taji ya rike hannunta yayi sama da shi yana shafawa a fuskarsa, a dayan bangaren kuma yana kokarin tura kofar ya bude, tana dannowa da karfi sai ta danne hannunta a dole ta saki kofar ya bude yana murmushi.
“Wai ke sarkin wayo ko?”
Ta bata fuska ta ki kallonsa.
“Na rantse kin ma fi kyau da kika yi fushin nan”
Ya fada yana janyota ya fito da ita daga cikin dandakin, sai ta saka dayan hannunta ta rike tawul din kirjinta.
“Sake min hannu”
Ta fada a shagwabe, a maimakon ya sake ta sai ya mika dayan hannunsa ya kama dayan hannun ya rike yana kallon black skin dinki data jika da ruwa tana ta shining.
“Idan anki fa”
“Ba zaka kai ni asibitin ba?”
Ta fada idonta na cika da kwalla, a take ya saki hannayen nata ya rika kanta cike da kulawa.
“Zan kai ki mana, kan yana miki ciwo har yanzu”
Ta daga masa kai.
“Okay saka tufafin sai muje yanzu”
“Ba kace akwai sabo ba?”
“Babu wasa nake miki”
Ya juya ta koma bandaki sai ya sauke idonsa a kasa yana kallon bayanta.
“Fine girl...”
Ya fada da muryar da shi kadai zai iya ji yana murmushi, sannan ya koma sannan gadon ya zauna yana kallon kofar bandakin a idonsa yana auna yadda take saka tufafin, yana gama observation dinsa tana bude kofar ta fito, sai ya dauke kai yana murmushi ya mike tsaye, ya mika mata hannunsa.
“Zo ki saka Hijab dinki”
Ta matso kusa da shi, amman bata rika hannun nasa ba, sai ta hau saman gadon zata dauki hijab din, sai jin tai an kwanto ta baya ta, ya dora kansa saman bayanta ya rumtse ido, yana shafata da duka hannayensa.
“I Love So much”
Ya fada cikin wata kalar murya yana kokarin jan rigarta yai sama da ita, sai wayarsa tai ringing.
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
A dole ya sauka saman jikinta ya mulmula gefe ya kai hannu ya dauki wayar.
“Leila”
Ya furta kamin yai picking. Ya kara a kunne ba tare da yace mata komai ba.
“Hello Baby”
“Ya akai?”
“Haba sai ka ce mai waya da makiyinsa? Ko da yake na san na maka laifi amman kai hakuri dan Allah, daman na kira ne na baka hakuri, kuma na ji idan mai sunan Momy na kusa na bata hakuri ita ma”
Talba ta kalli Aminatu dake kokarin saka Hijab dinta ya ce.
“Bata kusa”
“Okay idan ka dawo gida ina son ganinka, ko kuma ka fada min inda kake zan kawo muku abinci dan Allah”
“Bana tare da ita, na kai ta gidan Hajiya Laraba”
Ta yi wannan karyar ne saboda ya samu sallama, domin ya san anjima kadan Momy zata iya kiransa ta ce ya dawo da Aminatu gidan, ya kuma san Amintun zata iya cewa ba zata koma ba.
“Idan ma kana tare da ita, ni ba wani abun zan yi ba, domin na rumtse ido ban ga kyau a makanta ba, kana wani abu kamar kai ne mutum na farko da zaka fara saninta a ya mace, miye abun burgewa a auren macen da maza fiye da biyar suka kwanta da ita a lokaci daya? Har kake ganin kamar ka yi wani abun arziki?”
Ya tashi zaune ransa a bace.
“Leila ke baki san kaddara ba ne? Ba ki san kowa be isa ya wuce kaddararsa ba? Idan za a bata zabi kina tunanin zata zabi abun da ya same ta ne? Ko kuma ke zaben rayuwa kika yi aka baki?”
“Na san kaddara mana Talba, ai na san kaddara ce ta saka ka auren bazawara a matsayin budurwa, kuma kaddara ce ta saka ka auren da wasu mazan wulakantatu kaskantattu suka gama amfani da ita, mazan da ba su kai ma su wanke maka mota ba, kana ji da kanka kana dan Babban mutum amman ka auri mai kamar akuya wanda bunsura suka gama bibiya, shiyasa ai ka boye auren saboda ka san ba abun kwarai ka aura ba, kuma ka kasa yin bikin tarewa sai boyun amarya kake, ko garkuwar da akai da ita waya san iya abun da suka mata...?”
“Look at you da farko kina magana kamar mai hankali kamar da gaske kin yi nadama, amman sai kishi da hassada yasa kika kasa rike kanki, hakan yana nufi ba zaki taba iya controlling kan ki da zuciyarki ba Leila, duka abubuwan da kika zano na riga ki saninsu, kuma a haka na ji zan iya zama da ita, kuma kin san minene, ko da rana daya ban tana jin ma tsane ta saboda wannan ba, and this should be the last time da zaki sake bude baki ki fadi wata mummunar kalma akan matata, kuma ya zama na karshe da zaki sake saka hannunki ki daki Aminatu, na rantse miki da Allah Leila kika sake yin daya daga ciki, sai mun samu matsala da ke matsala ta har abada, idon wanda baki taba mafarkin samu zamu ba”
Yana kaiwa nan ya yanke kiran yana jin wani irin tsanar Leila da be taba ji ba a rayuwarsa, domin duk tsabanin da suke samu ya kan ji ransa ya bace amman baya jin tsanar, sai dai a yau tsanarta yake ji a ransa fiye da kima. Ya saka wayar aljihu ya dauki keys dinsa sannan ya kalli Aminatu dake kallonsa hawaye na sauko mata tana murmushin da ya fi kuka ciwo. Takawa yai ya karasa kusa da ita ya rika fuskarta ransa a bace, ko be fada mata ba ta san abun da suka tattauna akai, domin ta fahimcin wani bangare na hirarsu.
“Tana nanata maka abun da ta fada min ne a dazun? Ba a taba jefata da wata kalma da nake jin kamar na kashe kaina na sake sabunta rayuwata ba irin kalmar da Leila take jefata da ita, ka fada mata ba da son raina komai ya faru ba, shim ita ba mace ba ce? Bata san zafin da mace take ji ba idan wani namijin ya keta haddinta ba tare da son ranta ba? Na sha wahalar rayuwa na samu yanzu na yantu amaimakon a tausaya sai kuma ya zama abun gori a gareni? Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un”
Ta fashe da kuka mai karfi, sai ya kurawa fuskarta ido yana jin wani sabon tausayinta na kara kama shi.
“Rayuwa tana cike da kalubale Aminatu, ba zaka taba zama 100% babu damuwa babu jarabawa ba, kamar yadda ba zaka taba zama 100% cikin farinciki da jin dadi ba, no dole ne sai an surka maka, kowa ye kai kuwa a rayuwa, sai da kaddararce kowa tasa daban. Ina son ki saka a ranki a duk lokacin da wani ko wata zai fada miki wata magana saboda ya muzantaki ko ya muzanta rayuwarki, ki saka a ranki, Talba yana nan kusa da ke, kuma ba zai taba gudunki ba, ba zai taba kyamarki ba”
Ya rumgumeta a kirjinsa, sai ta ji wata rahama da natsuwa da bata taba ji ba sun lullubeta, sai ta samu sa'ida a zuciyarta tana jin kamar damuwarta ta warke.
“Ko babu komai Allah ya hada ni da wanda ke damuwa da kukana”
Ta fada cikin kuka tana rumgume shi abun da bata saba ba. Sai yai murmushi ya sumbancin saman kanta.
“Kuma yake son ganin murmushinki”
Ya sake ta, ya rika hannunta suka fice daga dakin, sai da suka isa gaban motar ya bude mata ta shiga sannan cikinsa ya soma kuka.
“Kin ga kin hanani cin abinci ko? Kuma dan abun da na ke ta kwadayi ban samu ba”
Ya fada yayinda ya shiga cikin motar yai mata key, sai ta kalleshi ta soma masa magana cike da kulawa da muryar kuka.
“Me kake kwadayi kwai? Zan iya sake soya maka yanzu”
Yayi murmushi domin ya san bata fahimcin inda zancen nasa ya nufa ba.
“No zan siye abinci a hanya”
Ya mika mata bakinsa.
“Kiss me zan je na bude gate”
Ya sakarwa bakin nasa ido kamin ta sauke kai kasa.
“Ke fa nake jira”
“Ban iya ba”
“To kawo ni na miki”
Ta mika masa hannunsa.
“Baki na ce”
Ya fada cikin yanayin dake nuna har yanzu be gama hucewa daga kalaman da Leila ta fada masa ba. Ta kalleshi sai ta sauke kanta kasa, ganin zata bata masa lokaci yasa ya fita motar ya zagaya side dinta ya bude motar ya sumbanci bakinta sannan ya nufi gate din ya bude ya dawo cikin motar yaja ta suka fita waje, ya sake dawowa ya rufe gate din, sai kuma ya sake komawa cikin motar. Wannan karon be jira cewar ba ya kai hannunsa ya riko fuskarta ta sumbanci kumatunta sannan ya fara driving da hannu daya, dayan hannun kuma ya mika mata sai ta saka hannunsa cikin nasa, yatsunsa da nata sukai taraiya a gurin daya.
“Saka hannunki ki ciro min waya a aljihuna”
Ta mika hannunta inda aljihun yake ta saka ta ciro wayar, sai ya janyo hannunta ta dora sitiyarin motar.
“Rike haka nan karki saki kuka karki murda”
“Ban fa iya ba”
Ta fada a tsorace domin ganin take kamar hadari za su yi. Sai ya sumbanci gefen fuskarta dake kusa da shi.
“Na sani”
Ya saka dayan hannunsa ya cire password din wayar ya kira Ali ya saka wayar a speaker ya dora a cinyar sannan ya rike sitiyarin, ita kuma ta dauke hannunta da sauri tana jin tsoro.
“Ali kana gida har yanzu?”
“Haba sai ka ce dai kai? Ina asibiti ka. Shigo ne?”
“Gani a hanya dai”
“Okay sai kun iso”
Ya kashe wayar sannan ya kalli Aminatu dake kallonsa.
“Sarkin tsoro”
“To idan muka yi hatsari fa?”
“Shikenan sai na mutu sai ki auri wani”
Ya fada yana dariya, sai ta bata fuska ta sauke kai kasa tana jin kamar tai kuka. Murmushi yai ya cigaba da tukin ba tare da sake ce mata komai ba, lokaci lokaci take dagowa ta kalleshi sai ta kara matse hannunta a cikin nasa, murmushi yai ba tare da ya kalleta ba ya cigaba da tukin. Sai ya ya fara harabar asibitin sannan ya saki hannunta ya kalleta.
“Bude ki fita”
Sai ta leke fada, alamar ba zata rufe ba tana kallonsa da fararen idanuwanta da suka kara haska bakar fatar fuskarta. Murmushi yai ya bude side dinsa ya fita ya zagaya ya bude mata, sannan ta fito sai kallonsa take kamar yai ta fara ganinsa, matsawa yai da ita daga jikin motar sannan ya samu ya rufe kofar ya danna key din hannunsa sai ya kama hannunta suka shiga ciki. Kai tsaye office din Ali suka nufa, shi kuma ya rubuta musu takardar ya turasu gurin hoto tare da wata mata. A nan Talba yake labarta masa abun da ya faru tsakanin Aminatu da Leila. Ba laifi akan kan ya dan bawa Leila laifi amman kadan ta dayan bangaren yana ganin zafin kishi ne ya saka ta yin abun da tai, a office din Ali Talba ya hada tea ya sha da biscuits domin baya iya cin bread idan rana tai, shayin ma iyakarsa ta sha na safe wani lokacin ya kan da dare sai dai ba sosai ba. Bayan an dawo da hoton Ali ya duba komai sannan ya kalli Talba yana murmushi.
“Kanta ya samu matsala gaskiya, zata iya mantawa da kai”
Talba ya kalli Aminatu dake zaune a kujerar dake facing dinsa yana murmushi.
“Idan ta mutu ko? Domin ko mutuwa na yi bana jin Shalele zata manta da ni, sai dai idan ita ta mutu shi ma saboda ance ana manta komai”
Ali yayi murmushi.
“Toh yayi sarkin soyayyah, babu abun da ya samu kanta buguwa ce kawai kuma zata samu sauki soon”
Aminatu ta yi masa da kanta, sai Talba ya mike tsaye ya rika hannunta.
“Ta so muje”
“Gida zaka mai da ita?”
“Tace bata son can, kuma ka san Daddy ma ya kore ni yace ba mu sati daya mu tare a gidanmu”
Ali yayi murmushi.
“Ka ce Daddy ya maka abun da kake so kawai”
“Wallahi kuwa, amman duk da haka ba zan koma ba sai da amincewar Momy, domin ita ma uwata ce”
“Hakan na da kyau Allah ya bada sa'a”
“Ameen”
Aminatu ta zare hannunta daga rikon da Talba yai mata a hankali saboda ganin Ali ya taso zai rakosu.
“Ka ga ta ma fika kunya”
“To ni kunyarka zanji? Haba Malam”
Ali yayi dariya, ya rakosu har inda Talba ya aje motarsa, suna tafe suna hira har suka iso. Talba ya bude motar Aminatu ta shiga ta zauna ya rufe ta ya juyo yana magana da Ali.
“Ka yi magana da Madina?”
“No sai ranar Monday, zan kirata office dina na yi magana da ita”
“Okay, for Leila karka dauki abun nan da zafi sosai Talba kai ma kowane bangaren adalci, ita ma tana sonka kuma ta jin kishi dole tai abun da tai”
“Na sani, ba dan adalcin ba Wallahi ba zan aureta ba, a rayuwata ba ni da burin auren mace fiye da daya, kuma bana son fitinar mata kasan kuma Leila zata yi da kirkiro abubuwa kala kala”
“Haka ne, amman hakuri ake, mata sai hakuri”
Talba ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya dauko masa zancen abun da Leila tai masa dazun data kira shi. Kalle kalle Aminatu ta fara yi sai ta hango farin mutumen nan da ya taba sace ta, shi ma ita yake kallo kasancewar farin gilashi ne, sai dai shi zare mata ido yake yana tsortata har ya shiga motar dake kusa da ita yai mata alama da tai shiru ta hanyar dora dan yatsansa saman bakinsa, sai gum kamar yadda ya umarce ta tana masa kallon tsoro har ya tashi motarsa yai reverse ya kama hanya, sai yai