Showing 321001 words to 324000 words out of 332834 words
da yayi sai dai gaba daya hankalinta baya kansa yana can gurin faruk tana mamakin yadda rayuwa ta sauya shi ita kuma kaddarar ta canja ta duniya tai mata juyin masa, ta rasa Faruk ta rasa Fahat, gashi yanzu Faruk yayi kudin da take da buri amman a tare da ita ba. Kamar marar lafiya haka ta shiga cikin gidan. tana sai ta samu Umma zaune tana gyaran shimkafa suna hada ido Umma ta banko mata wata uwar harara.
“Sai yanzu kika ga damar dawowa? Allah yasa ba tsayawa kika yi magana da Faruk din ba”
Ta zauna a bakin kofar falon ba tace komai ba.
“Wai dan baki da kunya har ki dauki kafa ki shiga cikin gidan Faruk? Miya kai ki bi ta kofar gidan ma?”
“Mun fito gidansu Anty Halira ne, sai muka biyo ta kofar gidan, na aika yaro a kira min Sultan sai Mama ta dage sai na shigo ciki”
“Sai kuma kika shiga saboda baki da zuciya”
“Saboda Sultan na shiga Umma, yanzu ba ni da kamar da na”
“Allah yasa dai ba zawarcin Faruk kike ba, abun da kafi karfi ka koma kana shimshina”
Bata ce komai ba ta tashi ta shiga ciki dakin tana jin ranta ba dadi.
*** *** ***
“Mama saboda me zaki mata izinin shigowa cikin gidan nan?”
Mama ta zauna kusa da shi tana murmushi.
“Faruk idan wani abun ya wuce, a bar shi ya wuce har a bada, ita kanta a yanzu ta san ka mata nisa, kuma babu yadda zaka yi ka yanke alakar uwa da danta, zuwan ta gidan nan baya nuna komai sai nadama wanda ke haifar da dana sani, da can ai bata kula da Sultan din ba, sai yanzu ta zo kofar gida ta aiko a kira mata shi ta ganshi amaimakon na tura mata shi can waje sai na zabi ta shiga saboda ban san abun da zai faru ba idan suka tsaya a wajen, daker ma ta shigo cikin gidan baka ga farincikin da yaron nan yake ba da yai arba da mahaifiyarsa”
“Duk da haka dai, bana son zuwanta gidan nan, da kin san yadda na tsani ganin fuskar Rafi'a Wallahi da ko mai sunanta ba zaki kira ba a kusa da ni”
“Abun da ya wuce ai ya wuce, sai ka gode Allah gashi ta zo ta ganka a yadda ba ta yi zato ba, ta guje ka saboda talauci yanzu gashi Allah ya rufa maka asiri, kuma ya baka mata mai wanda ta fita kyau ta fita asali kuma yar manyan mutane, ya baka aiki ni kaina da nake mahaifiyarka ina zaune a gida mai kyau, kuma baka san me Allah ya tanadar maka gaba ba nan gaba”
Ya sauke ajiyar zuciya.
“Haka ne, amman bana son ganinta kusa da dana sai idan ya zama dole”
“Ai yanzu idan kai aure ya samu wata uwar zai samu kwanciyar hankali fiye da yanzu kuma zai ji sanyi, fatana dai Allah yasa ta rika shi kamar danta, soyayyar da take nuna masa a yanzu Allah yasa ta nuna masa shi idan ta shigo”
“Ameen, na zo da mota waje”
Mama ta wara ido.
“Motar waye?”
“Tawa, motar da kika ta jira ta zo”
Ya fada yana murmushi, Mama ta fito dakin da sauri tana fadawa Rukaiya shi kuma ya rika hannun Sultan suka fito tare. Mama ta riga Rukaiya fita waje gurin ganin motar farincikin da ya lullube zuciyarsu da fuskarsu marar misaltuwa ne. Rukaiyah bata san lokacin san lokacin data rumgume yayanta ba tana murna, Sultan ma da yake karami murna ya rika yi yana ta tsalla, a daren ba su kwana ba sai da Faruk ya saka su mota ya zagaya gari da su cikin motar suka je har gidan kanwarsa wato yayar Rukaiyah. Bayan ya dawo da su gida ya shirya cikin wasu tufafin ya fesa turare sosai sannan ya shiga motar ya dauki hanyar gidansu masoyiyyarsa Ramla.
Wannan karon har da yan jaridu na social media da kuma na newspaper. Daddy ba jidadin hakan ba sai dai babu yadda ya iya domin aikinsu suke yi kuma da Leila bata aikata ba da basu mata haka ba. A wannan ranar kam Leila ta rufe fuskarta da mayafinta ta zauna a inda aka tanadar mata kusa da lawyer dake tare da rakiyar duka lawyers din chamber su. An gabatar da shari'a biyu kamin ayi ta Leila, kasancewar Lauyer kwararen ya gabatar da da kansa a matsayin lauyan da zai tsaya mata. Sannan aka shiga cikin shari'ar. Iyakacin abun da Lauyer yake nunawa Leila ta aikata hakan ne a kan kuskure, wanda hakan ya bawa Lauyan gwanati karyata ta shi da nashi hujojin. Daga karshe Barrister Fatihu ya nemi a bada belin Leila sai dai hakan be samu ba, alkali yayi duba da laifin data aikata ya sake bada umarni tsareta a gidan kaso.
A ranar ma Momy ta dawo gida cikin wani irin yanayi mai wuyar fassara, domin jikinta a kullum sanyi yake tana ganin kamar Leila ba zata samu sassaucin kotun ba, musamman lura da tai da yadda Alkalin yake da zafi.
Yan'uwan Baaba suka tafi gida cikin farinciki kamar wacan karon, domin suna ganin alamun kamar za ayi musu adalci.
Bayan sallah azahar Talba ya shigo dakin Momy domin dubata sai ya same ta zaune kasa tana ta jan carbi. Karaso yai kusa da ita ya zauna al'adarsa a yanzu duba lafiyarta safe rana dare. Kallonsa kawai tai ta sauke kai kasa ba tare da tace komai ba.
“Ina tunanin daina shan maganin nan zaki yi ma Momy kar yaje ya sama miki matsala”
Ta kalleshi sai dai bata ce komai ba har lokacin, fatar idonta har wani baki tai saboda bakinciki da kuka.
“Kina ji lokacin da Kabir ya fada miki cewar shan magani da kike ba zai amfana miki komai ba matukar baki daina tunani ba, haba Momy kalli yadda kika rame abinci ma baki iya ci, kullum sai kuka da tunanin Leila, ba laifi ba ne tunaninta amman zaki iya kamuwa da wani ciwon kin ga an yi ba ayi ba kenan”
“Ina ta kokari amman na kasa, ji nake kamar na mutu na huta Talba, zuciyata har wani zafi take”
Ta fashe da kuka sosai jikinta na rawa.
“Komai zai wuce Momy, ake rasa rai ma a hakura balle ke da Leila take a raye, kuma ina kyautata zaton zata dawo gareki”
“Ban ga alamar hakan ba, tun da gashi ko belinta sun ki bada ba”
“Ba daga nan take ba, Alkali yana bada beli ne idan ya gamsu da hujojin da aka bashi da kuma duba da yanayin shari'ar, Leila tana amsa laifinta a duk inda aka je, kin ga bata wahalar da kotu ba kuma hakan ya nuna ta yi nadama duk kotu zata duba wannan kamin yanke hukunci”
“Allah ya sa hakan ya kasance”
“Ameen, bari na kawo miki wani abu ki ci dan Allah”
Ya mike tsaye sai ta kalleshi tana jinsa kamar dan cikinta, domin kulawar da yake bata da nuna mata damuwarsa ko Kabir da yake danta baya mata shi.
“Ina Aminatu?”
Ta fada a yayinda ya kusa isa gurin kofar dakin, sai ya juyo da sauri ya kalli Momy cikin tsananin mamaki yana kokarin tantancewa ko dai be ji daidai ba ne. Sai dai murmushin daya gani a fuskarta tare da hawaye ya tabbatar masa da muryarta ya ji.
“Tana Lafiya?”
Kallonta kawai yake kamar mai shawarar amsawa.
“Lafiyarta kalau Momy”
Ta daga masa kai, sai ya juya ya fita. Downstairs ya sauko ya dauki plate ya zuba mata abinci ya dora a tray ya shiga kitchen ya dauko lemu da cups da ruwa ya dora a tray sannan ya dauka ya nufi upstairs, yana kallom Kabir dake zaune a sofa yana waya da Rukaiya. Sannu sannu yake takowa har ya hauro sama ya shiga cikin dakin ya aje tray gabanta.
“Shimkafa da miya ne, kuma na san kina sonsa”
Ta kalli abincin sannan ta kalleshi.
“Kwanakin baya, Daddynka ya min magana akan matarka yace ya maka maganar tarewa ka nuna masa baka son na shiga damuwa, ka ce ya bari sai gaba”
Ya mika mata plate din abincin yana fadin.
“Ba yanzu ba Momy, muna cikin wannan hali be kamata Daddy yayi wannan maganar da ke ba”
“Amman yana da gaskiya Talba, za a iya daukar lokaci ba a gama shari'ar nan ba, ka ga mun shiga hakkinka da na matarka, karka dubi halin da nake ciki ka hana matarka tarewa a gidan ta, daman ance kana naka Allah na nashi, muna ta zancen aurenka da Leila sai gashi ka auri yarinyar nan, yanzu kuma ana son yin auren sai ga wannan abun ya faru, mu barwa Allah ikonsa mu yarda da kaddara kawai shi ya fi”
Da ya kalleta sai tausayinta ya rufeshi, ya sani da can ba son Aminatu take ba, saboda Leila a yanzu kuma ita da kanta take bashi damar tarewa da ita.
“Shikenan nan Momy zan duba”
“Dan Allah kai yi abun da mahaifinka yake bukata, na san na shiga hakkinku kai da matarka amman duk...”
“Shikenan Momy ki ci abincinki dan Allah, zan yi”
Ya share hawayenta kamar karamar yarinya ta fara kai abincin a baki tana taunawa duk kuwa da kasancewar ta daina jindadin abincin tun daga lokacin da wannan tashin hankalin ya sameta, sai rashin lafiya ga rama da yawan kuka kullum Leila na cikin ranta ga zullum shari'ar da ake bata san yadda karshen zai kasance ba.
FARUK POV.
Sannu Sannu alaka mai karfi ta shiga tsakaninsa da Ramla, har ya fara zuwa Lagos gurin aikinsa yana dawowa gida yayi weekend. Kullum sai ya kirata sun yi hira, idan kuma ya dawo week zai yi mata tsaraba duk kuwa da kasancewar ta nuna masa bata so.
A wani kamfanin siyar da motoci da koyar da tuki ya koyi yadda ake tukin motar, bayan ya kamalla suka ba shi certificate, ta waya ya dauki hoton ya turawa Ramla ta rika masa dariya wai ta ya sani ya bari ta koya masa ai ta iya.
“Ai ko yanzu dare be mana ba, kuma ba a kure lokaci ba”
“Aa yanzu ai ka rika ka je wani gurin ka koya, dan haka ni zan koya maka ba tun da an rigani”
“Ki ce duk abun da ya kwana baki cin dumame kenan?”
“Wani abun ba...”
Ta fada, sai yai dariya ya dauki chocolate ya kai bakinsa.
“Me kake ci?”
“Dan gidanki”
“Let me guess i chocolate”
“Yes kin koya min shansa yanzu, na zama kamar wani karamin yaro kullum sai na sha”
“Aa ni fa ba kai na koyawa ba, da na Sultan”
“Ke kika koya min mana, na lura yana cikin favorite dinki, shiyasa ni ma na ko yi ci, kar wata rana ki zo kina ci kina min kori”
Ta yi dariya mai sauti.
“Saboda Chocolate din?”
“Yes, Mama ta fada min duk wani abu da kike so na koyi sonsa, wanda kuma nake so na koya miki sonsa, idan kuma tsanarsa na yi to na koya miki yadda zaki kiyaye aikata abun so that mu samu zaman lafiya”
Ta yi murmushi mai sauti tana ta saurarensa. Sai kusan goma dare suka yi sallama, ba dan ya gaji ba sai dan baya son shiga hakkinta domin ya lura ta fara jin bachi.
Haka suke kullum sai yayi waya da ita da dare, idan kuma yana Gusau Saturday da Sunday yana gidansu sai goma na dare zai dawo. Wani lokacin zata shirya masa abun da ta san yana so ta tarbe shi da shi. Every weekend idan ya zo sai ya bawa Mama kudi ta siya masa wani abu ta aje tana ta tara masa kayan lefa masu kyau da tsada, idan kuma ba shi a gari aka kawo kudin shagon daya bude ya saka wani yaro yana siyar da kayan electric sai ta fada masa a waya ta shiga kasuwa ta siya masa tufafi masu tsada. Ita kanta a yanzu bata daura karamar atamfa sam ba zaki ganta a gidan ita da Rukaiya ba ki ce ita ce, sai ka dauka daman can masu rufi asirin ne. Wannan weekend din ta fi sauran da yake zuwa yi masa dadi domin zai zo ya nunawa Mama da Ramla motar daya siya ne, ba ta iso ba sai yanzu, sai dai be fada musu cewar motar ta iso ba, duk kuwa da irin tambayarsa da Mama take kullum har tana cewa Allah yasa mutumen be gudu masa da kudi ba. Karfe biyar na yamma ya sauka Gusau bayan ya baro Zaria garin daya yada zango ya huta bayan fitowarsa daga Lagos.
A bakin gate din gidan ya faka motar sannan ya bude ya fito da tsararba sa yai musu ya nufo cikin gidan rike da makullin motar da farinciki ya shigo, sai dai yana shiga falon na su da aka kawata da kayan alatu sai fuskarsa ta canja ya nemo farinciki ya rasa, sakamakon arba da yai da Baturiya tana zaune saman kujerar falon da aka kawata da kayan alatu tare da kanwarta, Sultan na zaune saman jikinsa ta rike hannunta kanta a kasa. Tana jin sallamarsa gabanta yayi mugun faduwa wata kalar kunya ta lullubeta sai ta ji da ma ace bata shigo ba.
“Yaya sannu da zuwa”
Rukaiya ta fada sai ya amsa, mata ya kalli mahaifiyarsa dake masa murmushi.
“Faruk ya hanya?”
“Alhamdulillah”
Da gangan ya share Sultan dake masa ayoyo yana saukowa jikin Baturiya ya nufo shi da gudu. Kanwarta gaishe shi sai ya amsa ya dauke kai ya nufi dakin Mama, sai da yai daf da shiga sai kuma ya juyo ya kalli Baturiya da har ta mike tsaye jikinta na rawa, domin bata san zai dawo ba a yanzu ba, domin ta san ba anan yake aiki ba, bayan Fahat ya fada mata ta fara bibiyar rayuwarsa har Ramla da yake da nufin aure ta sani a yanzu.
“Me kika zo yi nan Rafi'ah”
Kamin ta amsa masa Mama ta ce.
“Aa waje ta tsaya ta ce a kira mata Sultan ta ganshi ni na aika na ce ta shigo cikin gidan”
Faruk ya kalleta cike da rashin jindadi abun da Mama tai ya ce.
“Saboda me Mama?”
“Saboda mahaifiyarsa”
Mama ta amsa masa tana mikewa tsaye, be sake cewa komai ba ya shige dakin nata ta bi bayansa. Baturiya ta fito da sauri ko sallama bata tsaya yi ma Mama ba, Rukaiya da bita da harara tana tabe baki, daman bata so shigowarta cikin gidan ba saboda kawai Mama ta ce ta kira ta ta shiga ciki ne wai kar ta a fitar mata da Sultan din a waje ta dauke shi ta tafi da shi. Sauri kawai take zubawa gumi na tarar mata a hijab har ta fito gate din, tsaye tai cak tana kallon sabuwar motar Faruk, ko ba a fada mata ba ta san motarsa ce domin ya faka ta daf da gate din gidan wanda ke nuna alamar cikin gidan yake da niyar shiga da ita, wani abu ta hade da karfi sannan ta bi bayan kanwarta wanda tai nesa tana tafiya saboda haushin shiga gidan da sukai daman ita bata so suka shiga ba. Tafiya Baturiya take tana waigen motar kamar wanda bata son tafiya, bata hankaro ba ta ji sanyin hawaye a kumatunta. Hannu ta saka ta share hawayen da sauri ta cira kafa tana tafiyar sauri sai dai duk da haka bata cin ma kanwarta tuni ta tari abun hawa ta hau ta yi gaba ta bar Baturiya a nan. A kafa ta rika takawa har ta isa wata unguwa dake kusa da unguwar wani dan guri ta samu ta zauna tana hawaye. Wani irin bakinciki take ji wanda bata taba jinsa a rayuwarta, ta dade zaune a gurin tana ta aikin kuka kamar wanda akai ma mutuwa. Sai dai abun da bata sani ba tun a lokacin da take tafiya a kafa wani mutumen yana biye da ita da motar har ta iso gurin ta zauna tana aikin kuka. Matashi ne da ba zai rasa mata daya da yara biyu ko uku ba, yana zaune cikin motarsa nesa da ita sai dai ba sosai. Ganin kukan nata ba mai karewa ba ne ya bude motar ya fito ya zari tissue ya nufo inda take zaune. Zuwa yai gefenta ya tsaya yana kallon harabar da take kallo.
“Hey pretty kina kukan rashi ne?”
Ta dago ta kalleshi a hankali still hawaye na sauko mata.
“Ka san zafin rashin wani ne?”
Sai a lokacin ya kalleta.
“Yeah zafi na rashi i lost my son zafi rabuwa i lost my wife”
Wani sabon kuka ya zo mata
“Kuma abun nan akwai bakinciki sosai”
“Sosai ma”
Ya furta da muryar dake nuna tsantsar bakincikinsa, yana kallon wani gurin dabam tsabanin ita da take kallonsa, sai kuma yai murmushi mai kyau ya kalleta.
“Fada min wa kika rasa?”
Ta yi kasa da kanta hawaye na sauko mata.
“Wani ne, mai kyakkyawar zuciya, mai kyakkyawar makoma, mai kyakkyawar fuska amman na rasa shi...!”
Ya mika mata tissue dake boye a hannunsa, sai da ta kalli tissue din sannan ta karba.
“Ya mutu ne?”
Ta share hawayenta.
“A idanuwana ya mutu domin na rasa shi har abada, amman a zuciyata rayayye ne har abada”
Ya zauna kusa da ita yana kallon kyakkyawar fuskarta wanda taja shi zuwa gareta.
“Did you he break ur heart?”
Ta girgiza kai.
“No i break his heart, yana so na nima ina sonsa, amman kaddara ta raba mu”
“Mijinki ne?”
Ta kalleshi kamar zata amsa masa, sai kuma ta ga babu dalilin yin haka ga mutumen da bata sani ba be santa ba. Mikewa tai tsaye.
“Zan tafi gida”
Sai shi ma ya mike tsaye.
“Da zaki ba ni dama da na saukeki gidan”
Ta girgiza masa kai ta fara takawa tana tafiya.
“Please, akwai abun da nake son fada miki”
Ta tsaya sai kuma ta juyo ta kalleshi sai yai mata alama da motarsa, sannan ya jera da ita suka nufi motar da kansa ya bude mata ta shiga sannan shi ma ya shiga driver seat yai ma motar key. Suna tafe yana mata hira yana kokarin kwantar mata da hankali, ciki har da gabatar masa da kanshi da yayi sai dai gaba daya hankalinta baya kansa yana can gurin faruk tana mamakin yadda rayuwa ta sauya shi ita kuma kaddarar ta canja ta duniya tai mata juyin masa, ta rasa Faruk ta rasa Fahat, gashi yanzu Faruk yayi kudin da take da buri amman a tare da ita ba. Kamar marar lafiya haka ta shiga cikin gidan. tana sai ta samu Umma zaune tana gyaran shimkafa suna hada ido Umma ta banko mata wata uwar harara.
“Sai yanzu kika ga damar dawowa? Allah yasa