Showing 219001 words to 222000 words out of 332834 words

Chapter 74 - Bakar wasika Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

65654

ya dagota ya kwanto da ita jikinsa.
 
“Waya taba min Shalele?”
 
Ta yi shiru sai kawai ta fara hawaye, sakata yai a kirjinsa ya rumgume a tunaninsa kewa ce da rashin sabo, ita kuma bata son fada masa ace fa fara kai kara tun yanzu, wata kila zai iya fada da Leila.
 
“Sorry ina gurin aiki amman hankalina yana gurinki, na zo na dawo amman ban samu dama ba, kin ci abincin rana”
 
Ta girgiza masa kai tana kuka.
 
“Okay bari na kawo miki a nan ki ci ko zaki iya fitowa?”
 
Ta girgiza kai masa kai.
 
“Bari na saka a kawo miki a nan, daina kukan ya isa haka”
 
Ya saka hannunsa yana share mata hawayenta, sannan ya sake ta ya mike tsaye ya fice daga dakin, sake komawa tai ta kwanta a saman gadon tana jin kamar bed sheet din na warin jaɓa.
 
 
 
FAHAT POV.
 
“Okay na gode”
 
Ya fada sannan ya sauke wayar cikin rashin jindadi, kansa har sarawa yake saboda maganar da mutumen ya fada masa.
 
“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un”
 
Ya furta sannan ya mike tsaye ya fara zagaya dakin. Mamakin yadda akai Baturiya ta boye masa wannan abu mai muhimmanci yake, sam batai masa kama da wanda tai aure ba har ta haihu, sai dai ya san mutumen da ya saka yai masa abinciken ba zai masa karya ba. Ya tabbatar masa da bata da wata matsala amman ta taba yin aure ta auri wani dan'uwanta har ta haihu daya kuma ta fito da ciki. Zaunawa yai bakin gadonsa gaba daya sai ya rasa abun da ke masa dadi a rayuwa.
 
“Iya wannan ne abun da Momy ta sani ko da wani?”
 
Ya tambayi kansa, kamin ya kai hannu ya matse fuskarsa, sai kuma ya ake mikewa tsaye ya dauki wayarsa ya kira Baturiya few seconds ta dauka kana jin muryarta ka san tana cikin farinciki.
 
“Hello Dear”
 
Sai da yai controlling kansa sannan ya iya yi mata magana.
 
“Kina ina?”
 
“Lafiya?”
 
Ta tambaya domin muryarsa ta karanta da ita ba lafiya ba.
 
“Ba komai, kawai ina son ganinki ne”
 
“Bana gida yanzu, amman idan na dawo zan kira ka”
 
“Okay”
 
Ya amsa, sannan ta sauke wayar da dan mamaki, ta dauke hannun Alhaji dake kirjinta ta mike tsaye.
 
“Ya akai?”
 
“Wanda zai aure ni ne ya kirani, wai ina nake kuma na ji muryarsa kamar akwai matsala”
 
“Babu matsalar komai ki kwantar da hankalinki mu yi komai cikin natsuwa sai ki je ki same shi, wata kila shi ma yana son ya huta da ke ne”
 
“Aa irin wannan mu'amalar bata taba hadamu ba, akwai dai abun da yake faruwa gaskiya”
 
“Oh kina ji da saurayin nan naki, har na fara kishi”
 
“Dan ma baka ganshi ba kyakkyawa ne sosai ga naira”
 
Ta fada tana murmushi
 
 
 
_______________________________
 
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
 
Tana jin Talba zai fito sai tai saurin barin jikin kofar ta koma ta zauna a inda take zaune dazun. Ko da ya fito ya same ta a inda ya barta wannan karon ko inda yake bata kalla ba, har yayi kamar zai je dinning din sai kuma ya nufi kofar fita domin ya fara zuwa ya canja tufafin jikinsa, domin suit ne jikinsa kuma baya sakewa idan yana sanye da shi a gida. Yana fita falon ta tashi da sauri ta nufi upstairs, dakin Momy ta shiga sai ta samu Momy na waya, kusa da ita ta zauna jikinta na rawa.
 
“Momy ki kashe wayar ki ji”
 
Momy ta yi holding call din ta kalleta.
 
“Lafiyarki?”
 
“Momy yanzu tace masa zata ci abinci”
 
Da sauri Momy ta katse kiran gaba daya.
 
“Bude jakata ki dauki maganin, but make sure babu kowa a falon nan kamin ki saka, ki tabbatar babu mai ganinki”
 
“Ko dai na dauko miyar na kawo nan?”
 
“Zai fi je ki dauko”
 
Ta tashi da sauri ta fice daga dakin, Momy ma tashi tai ta nufi inda ta aje jakarta ta bude ta dauko kullin maganin dake cikin kyalle ta zauna bakin gadonta tana jiran shigowar Leila. Leila kamar wanda tai sata haka ta shigo dakin dauke da miyar ta aje gaban Momy sannan taje ta rufe kofar dakin. Momy ta kwance kyalle ta zuba kadan sannan ta saka yatsanta ta motsa miyar.
 
“Dauki ki kai, kar kuma ki sha, yana zuba mata sai ki dauka ki zubar”
 
Da kai ta amsa mata sannan ta dauka ta nufi kofar ta bude ta fice, Momy ta tashi ta shiga bandaki ta wanke hannunta sannan ta fito ta dauki wayarta ta kira kanwarta Hajiya Sadiya, sai da ta kusa yankewa sannan Hajiya Sadiya ta dauka tana sallama. Momy ta amsa sallamar tana dariya.
 
“Hajaju Sadiya ya gidan ya yara”
 
“Wallahi lafiya kalau, ya su Leila kuma ya aikin ana nan ana ta yi ko?”
 
“To me za a fasa me nema a duhu kuma balle an haska masa? Amman fa na tsallakawan nan har da mu mun tsallaka, Allah yasa dai babu wata matsala”
 
“Aa babu yace ai ko da kun tsalla ba matsala ba ne domin shi da sunanta da sunansa aka hada akai so su kadai abun zai kama, wanda yake da matsala na a abincin nan dai kar ki bari Leila ta ci”
 
“Ai ba zan bari ba, yanzu haka am an zuba mata”
 
“Yauwa haka ake so, so ake ta ci, sauran wanda za ayi kuma yace sai an zo da Leila”
 
Momy ta dan yi shiru.
 
“Zuwan ne aiki ai, kin ga irin mu ba yawan fita muke ba, musamman ma irin kauyen nan ba son shiga nake ba, kar wani ya ganka yace ga wace can ina dadi?”
 
“Haba dai, ai ba shiga zaki yi yadda za a gano ki ba, cikin sirrin zaki shiga kuma ba dole sai kin je ba, Leila kawai ta wadatar”
 
“Ba zai yiyu shi ya zo ba? Ko kuma ya aiko mata da sakon?”
 
“Ai kin san da zai yiyu da haka zan yi, wannan ma dana karbo ai ba zuwa tai ba, amman wanda za a mata na tsakaninta da Talba yace sai ta zo fa”
 
“To a lallaba mana shi idan zai yiyu a dauko mana shi mana”
 
“To bari zan masa magana naji, sai dai kauyen ne na su ba samun network ake sosai ba wani lokacin sai kai ta kira bata shiga sai sa'a amman dai zan yi magana da shi”
 
“Okay duk yadda kuka yi sai ki sanar min”
 
“Toh shi kenan”
 
Daga haka suka yi sallama, Momy ta sauke wayar tana murmushi.
 
 
***     ***      ***
 
Da farko ya shiga dakin ne kawai saboda ya canja tufafinsa, sai dai abu ne mai wahala ya cire wasu tufafin ya saka wasu ba tare da yayi sabon wanka ba, hakan yasa ya daura tawul ya shiga yai wanka a gaggauce ya fito ya saka short jean da jallabiya ya fesa turare ya nufo bangaren Momy, garin sauri har ya manta wayarsa. Danna door bell din Leila ta bude masa tana murmushi, kallonta kawai yai ya shiga cikin falon domin a yanzu mamaki take ba shi, gaba da ta soma canjawa. Dinning ya nufa kai tsaye ya dauki plate ya zuba abincin ya dauki cup ya saka spoon ya nufi dakin da Aminatu take, dadi kamar ya kashe Leila daga inda take zaune ta bishi da kallo har ya shige dakin. A kasa ya aje plate din sai ya dan kwanto da kanta tana kallon abincin, shimkafa da miya ne da coslow daya ji hadi, bata ce masa komai ba har ya fita ya dauko mata lemun kwali da ruwa ya aje mata.
 
“Sauko ki ci”
 
Ta dago a hankali ta kalleshi shi, sai kuma ya koma ta yi kwanciyarta kamar ba da ita yake magana ba.
 
“Babyna sauko ki ci abinci mana”
 
Nan ma bata juyo ba.
 
“Ko dan na dade? Na dan tsaya wanka ne, ni ma ban ci abincin ba, yanzu nake shirin ci”
 
Ya juyo ta kalleshi.
 
“Ni bana son wannan abun da aka zuba sama”
 
Ya kalli Coslow din.
 
“Akwai dadi fa?”
 
“Ni dai bana so ba zan ci abincin ba, bana son kamshin wacan abun”
 
Ta nuna cucumber.
 
“Okay na zuba miki wani?”
 
Ta yi shiru kamar ba zata ce komai ba, daman can ita ba wani son shimkafa da miya take ba. Ya zauna bakin gadon yana kallon yadda ta turo baki gaba tana kallon abincin.
 
“Baby waya bata min ke? Da can ba ki wannan abun?”
 
“Ni dai bana so, kuma dazun ma...”
 
Har zata fada masa Leila ta kira yar kauye sai kuma wata zuciyar ta hana ta.
 
“Okay bari na zubo miki da miyar ba da wannan abun ba, zaki ci?”
 
“Aa ni dai bana son abincin”
 
“To mi zaki ci?”
 
“Bana son komai”
 
“Kin ci wani abu ne da rana?”
 
Ta girgiza masa kai tana kallonsa kamar za ta yi kuka.
 
“Okay zan saka Mairo ta dafa miki indomie zaki ci?”
 
“Taliyar yara?”
 
“Eh”
 
Ta danne kafada.
 
“Bana so”
 
“Me zaki ci?”
 
“Ni ma ban sani ba”
 
“Okay”
 
Ya mike tsaye ya dauki abincin ya fice daga dakin, yana aje abincin a dinning Momy na saukowa sanye da wata tsadaddiyar atamfa.
 
“Yayi ango, kai da kanka kake bata abinci baka bari yan aiki da kanenka su yi aikinsu”
 
Ya juyo ya kalleta da dan kunya domin sai yanzu yake jin kunyar abun da yai.
 
“Leila ta fada min bata ci abinci ba, sai na shiga na tambaye ta ko tana son wani abu ne”
 
Momy ya karasa dinning din tana kallon abincin da ba a taba ba.
 
“Bata ci ba?”
 
“Eh wai bata son warin cucumber ne”
 
Momy taja wani numfashi na bakinciki ta aje.
 
“To yanzu yaya kenan?”
 
“Zan fita waje na samo mata shimkafa da wake, na lura tana son shi, ko kuma na bata biscuits da tea ta gwada sha kamin a gama na dare”
 
Bakincikin kin cin abincin da Aminatu tai yasa Momy ta rufe da fada.
 
“Wannan abun da kake rashin kunya ne Talba, kamar kanka farau mata? Yaushe ta zo gidan? Amman har ta fara maka zaben abun da zata ci, ko kunya baka ci ka dauki abu kaje kana kai mata, idan tana bukatar wani abun ka fadawa yan aiki mana ko kuma kanenka ko kuma duk ba su wadatar ba?”
 
Be ce komai ba, kuma daman ba zai ce din ba, sai dai abun da ya tabbatar Leila ce yai ma haka ba zata yi fada ba sai dai ta yaba masa. Shi kuma yana yin haka ne saboda ganin Aminatu bakuwa ce a gidan kuma bata sake da kowa ba kamar yadda ta sake da shi. Hannayensa ya saka aljihu ya nufi kujerar da ta Leila ta tashi ya zauna, domin Leila bata falon a lokacin. Momy ta kara masawa tana kallon shinkafar gashi bada ta yawa sosai da zata ci zata iya cinyeta tass amman ta ki ta ci kamr wanda ta san an saka wani abu a ciki. Daukar abincin Momy tai ta nufi kitchen ta zuba abincin a dustbin, sannan ta kalli su Mairo dake ta hada hadar hada abincin dare.
 
“Ina miyar da aka ci abincin rana da ita?”
 
“Leila ta zuba a shara, sai kular ta aje mana tace mu wanke”
 
“Good”
 
Ta fada sannan ta juyo ta fito daga kitchen din, ta nufi upstairs har ta fara takawa sai kuma ta sauko ta nufi bangaren da dakin Aminatu yake ta tura ra bude kofar sai ta hangonta kwace rairaim tana watsa da yatsunta tana ta silawarta a hankali. Momy ta saki kofar ta haye sama cikin bacin rai domin kin cin abincin sa Leila tai be yi mata dadi ba sam. Ta maida kofar dakin ta rufe tana jan tsaki, Leila dake zaune rike sa waya tana chat ta kalleta.
 
“Miya faru?”
 
“Bata ci abincin nan ba, wai wani bata son warin cucumber kiji min iskanci da samun guri”’
 
Leila ta zaro ido.
 
“Bata ci ba kuma? How ya shiga daki da abincin fa”
 
“Hmmm wannan yarinyar idan ta kara gogewa nan gaba sai ta yi ma mutane iskanci”
 
“A yanzu ma baki ga ruwanta ba, dazun fa saboda mu da Amal mun tsargeta sai cewa tai wai saboda ta fito kauye ba shi yake nufin a musguna mata ba, ko tsorona dana Kabir bata ji kuma ta ki cin abincin Wallahi wai ita uwar zuciya”
 
“Ai dole tai ba yayi ta hauka yana abubuwan ba akanta, ko wacan fadan da yai da ke a kanta ai kin san ba mantawa zata yi ba, tun daga lokacin zata fara ganin damarki ai, ”
 
“Kuma ina jin Momy wani gurin ya kaita ta waye sosai sai kamshi take, ta yi kiba ta yi kyau abun har mamaki yake ba ni”
 
“Gurin wannan kanwar mahaifiyarsa ya kaita fa,a garin nan ba shi da wata shakikiya ta bangaren mahaifiyarsa da ta kai Laraba, acan aka koya mata wannan makircin shi kuma sai wani rawar kai yake kamar wata amaryar azo a gani”
 
“Ni Wallahi na matsu komai ya faru, ya sauwake mata ta koma can daji cikin yan'uwanta”
 
“Sai an yi hakuri Leila, ba wai farat daya komai yake faruwa ba da sannu sannu yake fara kamawa har ya wuce inda ake so, dazun ma na yi waya da ita ta ce yace sai kin zo akwai aikin da zai yi, amman gaskiya ina jin tsoron tafiya irin gurin nan saboda yanayin tsoro kuma zaka iya haduwa da wanka ka sani ko ya sanka”
 
“Aa Momy sai na rufe fuskata, indai za a samu biyan bukata ina ruwana da duk wanda zai gan ni!”
 
“Amman dai na yi magana da ita, idan zai yiyu shi ya zo nan din ko nawa ne zamu kashe”
 
“Idan ma be zo ba ni zan iya zuwa, biyan bukata ya fi dogon buri”
 
“Ki daina garaje Leila ki bi komai a hankali, abu na biyu kuma kar na sake ganin Madina a gidan nan, kar wata alaka ta sake hada ku, riga na ja mata kunne idan bata ji to zata janya kanta matsala”
 
Leila ta kalli Momy da sauri.
 
“Momy Allah yasa ba maganar envelop kika mata ba? Momy na fara canja mata fa duk dai saboda na gano idan ita din ce, amman yanzu haka da kika yi idan ba ita ba ce kin lalata alakarmu kenan fa haba Momy”
 
“Karki dame ni da wata magana, tashi ki fita”
 
Momy ta fada tana nuna mata kofa fuska babu alamar wasa. Leila ta mike tsaye kamar zata yi kuka ta fice daga dakin, downstairs ta sauko ta nufi inda ta bar wayarta ta dauka ta kira Madina. Sai ta samu Talba zaune a gurin yana kallon stairs din da alama jiran saukowarta yake. Bata ce masa komai ba ta kai hannu ta dauki wayarta.
 
“Miye a cikin Envelop din dazun?”
 
Ta mike tsaye a hankali gabanta na faduwa tana tunanin irin amsar da zata ba shi.
 
“Invitation card ne na birth wani friend dina he wanted to surprise me, that's why ya baka yace ka bani”
 
Ya dauke kai ba tare daya ce mata komai ba kuma ba dan ya yarsa ba. Juyawa tai da sauri ta fice daga falon zuwa harabar gida. Mikewa Talba yai tsaye ya nufi kitchen, Mairo da Zulai na ganinsa suka gaishe shi ya amsa musu da kai, sannan ya dauki karamin cup ya nufi flask din ruwan zafi ya bude ya zuba ya saka lipton da cube sugar uku sannan ya bude inda ake aje musu biscuit ya dauko leda biyu ya dora a plate ya fito daga kitchen din ya nufi dakin da Aminatu take. A hankali ya bude da dayan hannunsa yayinda dayan yake rike plate mai dauke da cup din tea da biscuits manya biyu. Murmushi yai yana sauraren yadda muryarta take da dadin sautin a yayinda take karanta Suratul Yasin.
 
“Maa Shaa Allah, to sauko ki ci wannan kamin akai ga na dare”
 
Tsoroce ta juyo domin bata ji motsin Shigowar ba, sai ta tashi zaune da sauri tana kallonsa har ya aje plate din a saman gadon.
 
“Tea ne da biscuits zaki ci?”
 
Ta daga masa mai, domin tana jin yunwa. Sauke plate din yai kasa ya sai ta sauko ta nade kafafuwanta ta zauna. Kallonta yake for no reason bakar fatar jikinta tana burgeshi, gashi kyauta sai karuwa yake a fuskarsa, shi ma saukowa yai kasa ya zauna ya rika hannunta na dama da take cin biscuit din da shi yai kissing sannan ya matsa kusa da ita yai hugging dinta.
 
“I love you”
 
Ya saka hannunsa ya dago fuskarta tare da kwanto da tashi.
 
“Mu ji biscuit din yana da zaki”
 
Ta kai hannu zata dauki daya ta mika masa sai ya kai bakinsa daman ba rikon wasa yai na ma fuskarta ba, tana kokarin kwacewa amman ta kasa, a light kiss yai mata but very romantic one. Sannan ya cire bakinsa ya mike tsaye sai kuma ya kai hannunsa ya shafa kanta zuwa fuskarta yana murmushi ya fice. A hankali yaja kofar dakin ya rufe ta yadda ba zata yi kara ba, sannan ya nufi kitchen din ya hada na kansa tea da biscuits ya fito falo ya zauna yana sha.
Misalin 6pm Amal ta dawo daga islamiya, tana ganin Talba a falon gabanta ya fadi, ta yi zaton ko zai mata maganar abun da tai ma Aminatu ne a yanzu, da tsoro tsoro ta gaishe shi, sai ya kalleta yana murmushi.
 
“Little Sis kin dawo?”
 
“Eh kai kadai kake zauna a nan?”
 
Ya daga mata kai, cikin tsoro ta nufi stairs tana ta jiran ta ji ya kirata ya mata wata maganar amman shiru ba ce mata komai ba har ta haye sama. Ba shi ya tashi gurin ba sai da akai Magariba, sannan shiga bangarensa yai alwala sai a lokacin ya tuna da ya bar wayarsa a gurin, hannu ya kai ya dauka sai ya tararda  eight miss calls from Ali, dan tabe baki yai ya saka wayar aljihu yana tuna kiran da Ali yai masa cewar yana son

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login