Showing 327001 words to 330000 words out of 332834 words

Chapter 110 - Bakar wasika Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

65633

ji ba, ba dan ba shi da muhallin da zai aje mata Ramla ba, sai dan karamcin da mahaifinta yai masa na bashi ita kuma ya kara masa gida, mace mai kyau yar daya tilo a gurin hamshakin dan kasuwa Alhaji Isma'el Zabarma.
 
 
 
A lokacin da Labarin auren Faruk ya samu Baturiya ba karamin tashin hankali ta shiga ba, ganin zai yi aure ya barta kuma yar babban gida zai aura wanda ta fita komai a duniyar nan. Daman a duk lokacin da tsohon miji ko tsohuwar mata suka ji daya zai yi aure hankali daya tashi yake balle kuma ita, da ta san abun da ta aikata. Gashi Yayanta ya matsa mata da maganar fitar da miji tun daga lokacin da ya gane sana'arta hankalinsa ya tashi balle kuma yanzu da suka san halin da Faruk yake ciki na rufin asirin daya samu, sai yake dora mata laifi yana kara tabbatarwa cewar Faruk ne mai gaskiya, domin gashi tun a nan sallah ya masa sakamakon. Umma na ta fara damunta da maganar aure ganin kanwarta ta tsayar da nata mijin, ita kuma har yanzu shiru sai yawan zuwa da ake mata sallama ko da yaushe. Ga kuma Faruk da ta ji zai yi aure bata son ya riga Baturiya.
Sai dai har yanzu bata samu wani wanda yake son kamar Faruk da Fahat ba, mostly ma wadanda suke zuwa gurinta duk ba zancen aure ke kawo su ba,wasu ma ta hanyar Ramlee take saninsu domin ita take hada ta da su, duk kuwa da kasancewar ta nuna mata bata son wannan bakar sana'ar amman ta ki yarda ta kyaleta saboda tana samun kudi da ita sosai.
 Yau ma tana fitowa wanka Umma ta hau ta da fadan ta fitar da daya a cikin masu zuwa gurinta.
 
“Kin fi son Faruk yayi aure ya bar nan makiya da yan gulma suna miki dariya”
 
“Umma zan fitar akwai wanda na yi ma magana, ya ce na dan bashi lokaci zai yi magana da iyayensa ne”
 
Ta fada sannan ta nufi dakinsu ta shige, kasancewar a bandakin falo tai wanka. Ko da ta shigo wayarta na ringing sai ta karasa da sauri ta dauka ganin number Al'Qasim ya saka tai saurin picking. Sai da suka gaisa sannan ya jata da hira daga bisani suka yi sallama, a laifi tana sakin jiki da shi kasancewar shi din ba a hanyar banza suka hadu ba, kuma ya fada masa matarsa da rasa da dansa tun a wacan yammacin da suka hadu a lokacin data fito gidan Faruk.
 The following day da ya zo zance gurinta take gabatar masa da kudinta na aure, ganin sun riga sun fahimci junansu a yanzu, ya san wacece ita ita ta san waye shi. Domin babu abun da ta boye masa na rayuwarta sai bakar sana'arta. Yadda ya amsa mata kadai ya isa ya bayyana irin kaunar da yake mata, jiki na rawa ya turo magabansa aka biya sadaki.
 
Ranar Assabar aka daura auren Faruk da Ramla, daure aurene da ya samu halarta manyan mutane daga gari gari wasu ma har daga waje, kasancewar mahaifinta babban mutum kuma dan kasuwar zinari dake leka Dubai da india gurin sana'o'insa.
 Duk wani abu na al'adar an gabatar kabanin dauren auren, wato event, sannan aka yi dinner a dare da aka daura auren. Washe gari bayan Amaryar ta gaishe da danginta an gabatar da ita ta sauran yan'uwansu aka kaita gidan mijinta da aka kawata kamar ba za a mutu ba. Kana ganin gidan da irin dukiyar da aka bata a gidan zaka san Ramla yar gata ce, domin an yi wasa da nera kamar ba a san zafin nemanta ba. A sabuwar mota aka kai amarya wanda Mahaifinyarta tai mata kyauta, duk uban lefen da Faruk yai mata baka saka kala ko daya a cikin kayansa ba kasancewar mahaifinta yayi mata kayan cin ciki masu mugun tsada zinarin dake wuyanta kadai abun kallo ne. Sai da suka cika sati biyu da tarewa mahaifinta ya biya musu kudin jirgi ya bawa yarsa enough kudi da zai ishesu Honey moon.
 
 
***   ***   ***
 
Maganar auren Baturiya da Al'Qasim ta fara nisa domin iyaye sun shiga ciki, duk dai ba wani sonsa sake sosai ba kusan yanzu a kullum zuciyarta da tunaninta yana gurin Faruk, rayuwar da suka yi a baya yana ta dawo mata sabo, daman can tana kaunar Faruk sosai kawai dai talaucinsa ne bata so, yanzu kuma ya samu rufin asiri, duk yadda take jin son Fahat na Faruk ya dara a yanzu saboda shi ta rayu da shi ta san yadda yake da hakuri da iya mu'alama kuma ga da a tsakaninsu, sai duk wannan abun da take ji bata yardar da nunawa kowa ba musamman ma mahaifiyarta da tasan zata iya yi mata fada sosai idan ta san da zancen.
Ranar da tasan an daura auren Faruk da Ramla mutuwa ne kawai batai ba amman ta ci kuka har ta gode Allah ga wani uban kishi da bakinciki daya tsaya mata a zuciya, tana ganin ta wahala da shi shekara da shekaru sai yanzu da arzikin ya zo wata zata zo ta cinye ta jidadin mijinta ita tana gefe kamar yajin kosai.
A gashi a cikin mutanen da suka hallarci daurin auren har da yayanta domin har gobe akwai mutunci a tsakaninsa da Faruk, bayan alaka ta zumunci. A week later da auren Faruk ta fara canjawa Al'Qasim idan ya kirata a waya ba zata daga ba sai ta ga dama, idan ya zo zance bata son amsa masa kamar ba ita ta gabatar da shi a idansu da sunan wanda take son auren ba, gaba daya sai ta canja masa daman can ba wani sonsa take ba kawai dai ta fitar da shi ne saboda Umma da Yayanta sun matsa mata, ba wani babban aiki ne da shi kamar yadda take so ba, ko ma yana da shi ita yanzu zuciyarta Faruk yake hange ba kowa ba.
 Ana sauran sati biyu aurensu ya fara ja da baya, shi ma yana dan janye jikinsa kamar yadda take bukata saboda kananan maganganun da yake ji ana kawo masa na suka a cikin kuwa har da Ramlee sai dai be san akwai wata alaka tsakaninta da Baturiya ba, domin bata nuna masa haka ba, sai dai ta fada masa Baturiya bata tsaya ga kanta ba, wai mace ce mai kwadayi shiyasa ta fito gidan mijinta, kuma wanda ta fasa aure kamin shi ya fasa aurenta ne saboda ya gano alakar dake tsakaninta da babansa. Daina zuwan da yai na kwana biyu har yana maganar daga auren zuwa gaba ba karamin dadi yai ma Baturiya ba, domin ita a yanzu burinta ya auren ya fasu ta komawa tsohon mijinta Faruk.
 
“Gaskiya idan har zaka daga auren nan zuwa gaba sai dai a fasa shi gaba daya, taya sai da aka tsayar da magana zaka maida mu mutanen banza yanzu ka zo da wani zance wai a daga aure har gaba? Gaba yaushe? Zaunawa zan yi na yi ta jiranka har gaba? Ga dana yana da bukatata ina son dana a kusa da ni”
 
Ya mata kallon rashin fahimta.
 
“Ban gane kina son danki a kusa da ke ba! Ba kin ce yana hannun mahaifinsa ba?”
 
“Eh amman idan na yi aure ai dole karbo abuna zan yi, za ban barshi a can matar uba tana azabtar da shi”
 
“Amman ba mu da ke cewar zaki karbo dakin ki tafi da shi ba?”
 
Ta masa kallon rainon wayo.
 
“Okay so kake na je kawai nai ta renon wadancan yayan naka da matarka ta mutu ta bari ko? Wato ga yar aiki ka dauko? Amman ni dan yaro daya da zan tafi da shi zaka yi complain, to Wallahi karka dauka zan iya rika maka yaranka kai ma”
 
Da mugun mamaki yake kallonta domin can da bata fada masa haka ba, shi kuma irin mazan nan ne da basa kaunar yaron wani a gidansu, kuma basa bari a fita da nasu. Da gangan Baturiya ta kirkiro wannan abun saboda ta lalata alakar dake tsakaninta da shi so that ta samu yacw ya fasa ko ba zai iya ba. Sai faduwa ta zo daidai da zama domin shi ma abun da yake da buri kenan a yanzu. Musamman da yaji cewar da danta zata tafi ga kuma abun da Ramlee ta fada masa har tana nuna masa hotonta a wayarta.
Kamin ya bar kofar gidan sai da Baturiya ta fusata shi suka yi rabuwar rashin dadi sannan ta shigo cikin gidan tana jindadin abun da tai. Shigowa ta dauki buta ta shiga toilet din tsakar gida tai zawo ta fito, kwana biyu haka take fama da yawan ba haya kuma idan ta shiga bata komai sai tsawo sai yawan ciwon kai da ciwon kashi bone pain duk inda kashin jikinki yake ciwo yake, sai dai bata dauki abun so serious ba ganin dan kanoma yana saka haka, sai tai ta shan maganin hausa na dan kanoma amman na canji. A ranar da sukai fadan be kwana ba sai da ya samu Yayanta wanda yake a matsayin ubanta ya fada masa yadda sukai, yayanta ya bashi hakuri ya ce zai same ta yayi mata magana, amman Al'Qasim ya nuna masa shi dai ya hakuri da ita gaba daya. Haka kuwa akai auren ya fasu kamar yadda take so, sai dai ta sha fada a gurin Yayanta da Umma sosai musamman ma Yayanta da yace ya bata sati daya ta kawo wani wanda take so.
 
“Ni ba ni da kowa yanzu”
 
“Ban gane baki da kowa ba? Baki da kowa kuma kika ci wa wannan yaron mutunci?”
 
“Wai Rafi'a mi yake damunki? Ko dan wannan yaron Fahat daya fasa aurenki be kamata ki auri wani ba saboda ki bashi kunya? Ga kuma Faruk din nan shi na har yayi aurensa”
 
Yayanta ya kalli Umma.
 
“Wannan yarinyar da kike gani, bata da mutumci, kuma a zaman su ita take cutarsa shiyasa yanzu amanarsa take fita shi kuma yana ta yi gaban”
 
Umma ta tabe baki.
 
“Kai dai har gobe ba zaka daina ganin laifin Faruk ba, a kullum shi ne mai gaskiya ne a gurinka”
 
Ya girgiza kai yana murmushin takaici.
 
“Umma baki san halin wannan yarinyar ba, Wallahi makira ce kina ganinta kamar ta kwarai babu alheri a zuciyarta, ni kadai na san ko wacece ita”
 
Baturiya dai kansa na kasa domin tasan abun da yayanta yake magana akai.
 
“Kar na sake ganin wani a kofar gidan nan idan ba aurenki zai yi ba, na fada miki ko?”
 
Ta daga masa kai alamar gamsuwa.
 
“Babu wanda zai sake zuwa Yaya ba zan sake sauraren kowa ba”
 
Umma ta kalleta baki sake.
 
“Ban gane ba zaki sake sauraren kowa ba”
 
Sai kawai ta fashe da kukan munafurci.
 
“Duk wanda ya zo ya ji cewar kana da da sai yace ba zai aureka ba, ko kuma ba zaka tafi da shi ba”
 
“To ina ruwanki, yaron dake hannun ubansa?”
 
“Ni ba zan bar shi a can ba, ban san iya azabar da matar uban zata masa, ina yin aure zan dauke ďana, idan har na bar shi ya zauna a gidan nan sai idan ni ce a tare da shi”
 
Yayanta yayi murmushi domin ya fahimci manufarta. Umma ma haka.
 
“Kar dai ki ce min so kike ki koma a gidan mutumen da ya gama wulakantaki?”
 
Ta yi shiru bata ce eh ba balle aa.
 
“Aa Faruk be mata komai ba, ai da ya ci amanarta da yanzu shi ne Alhaki zai bibiya ba ita ba”
 
Cewar Yayanta sannan ya kara da cewa.
 
“Kar ma ki kuskura ki ce zaki tunkari wani da wannan maganar, ta ya zaki bude ido yanzu ki ce kina son komawa a gidansa saboda yayi kudi ko? Bayan can da ki murje ido kin ce ba ki bukatar zama da shi sabida taja talaka”
 
Tashi tai tana turo baki gaba alamar maganar bata mata dadi ba ta nufi dakinsu, daga Umma har yayan nata kallo suka bita da shi. Takaici ya hana Umma cewa komai, da tunani kala kala ta kwana a ranta, na yadda Faruk zai yi mu'amalar zamantakewar aure da amarya ita tana nan gidansu, ta dayan bangaren kuma tana tunanin yadda zata bullowa labarin ta haddasa musu fitina a cikin gida ta hana su zama lafiya, da kuma hanyar da zata bi ta koma gidan Faruk so that a kwashi romon dimukuradiya da ita.
               Washe ta shirya da wuri saboda zuwa asibitin da take son yi domin tsawon da take ya matsa mata sai haifar mata da rama yake ga ciwon jikin dake damumta. Shiga tai ta mutunci ta ta dauki jakarta da wayarta sannan ta fito ta fadawa Umma dake shirya abun karyawa cewar zata je asibiti. Umma ta kalleta sama da kasa sannan ta kira kanwarta tace ta rakata domin a yanzu bata yarda da ita ba, gani take kamar gurin Faruk zata je ko Mamansa. A dole kanwarta ta fasa zuwa makaranta a ranar ta rakata asibitin. Bayan ta samu ganin likitan ne ta fada masa dukan wani abu da yake damunka, sai ya dubuta mata awon jini da fitsari sannan ya dora ta akan wani maganin kamin washe garin ranar da zata dawo ta kawo masa sakamakon gwajin nata.
 Sai da ta fara zuwa gurin dauki jinin sai suka fada mata sai ta zo gobe da safe kamin ta ci komai za su dauki jinin nata, sannan ta siye robar fitsari sauka ce ta kawo fitsarinta na farko da zata fara yi bayan ta tashi daga bachi. A tare suka dawo da kanwarta gida. Washe gari ma sai da Umma da saka kanwarta ta sake rakata har aka dauki jinin nata sannan ta mika musu fitsarin da tai. Sai suka fada ko karfe nawa zata dawo ta karba, cikin asibitin ta dawo ta zauna suna da hira da yar'uwarta har lokacin ya cika sannan taje ta karba, sai da dakin ganin marar lafiya ba wacan likitan na farko ta tarar ba, wani ne dabam yana duba marasa lafiya. Sai da tai masa bayani sannan ta mika masa takardar da awon da kuma takardar maganin da aka rubuta mata.
Ya dade yana kallon takardun sannan ya kalleta.
 
“Kin taba aure?”
 
“Eh na taba?”
 
“Kin dade da yin auren? Kina tare sa mijin ko kun rabu?”
 
“Eh mun rabu”
 
“Mutuwa yai ko kuma yana raye?”
 
Gabanta ya soma faduwa ganin likitan yana mata tambayoyi.
 
“Lafiya Doc?”
 
“Lafiya Kalau, kawai ki amsa min”
 
“Yana da rai?”
 
“Kuma lafiyarsa kalau?”
 
“Aa gaskiya ba shi da lafiya”
 
Ta fada ne kawai saboda ta ji abun da Likitan zai fada, domin hankalinta ya fara tashi.
 
“Kin san abun da yake damunsa?”
 
“Aa be taba fada min ba, gashi har mun rabu”
 
“Okay yanzu zan rubuta miki wani gwajin ki tafi kai tsaye dakin gwaje gwaje na masu cutar HIV za su yi miki wannan gwajin babba ne so that mu tabbatar da abun da yake damunki”
 
Ta dora hannu saman kai tana zaro ido.
 
“Doc HIV fa kace? Na shiga uku na lalace, rayuwata ta kare”
 
Sai yayi kokarin kwantar mata da hankali.
 
“No No no ba mu tabbatar ba tukuna har sai kin yi wannan gwajin, kuma ko da ta tabbata shi din ne zamu dora ki akan magani, zaki yi rayuwa ki samu lafiya fiye da wanda ba shi da shi, ki kwantar da hankalinki HIV ba yana nufin karshen rayuwa ba ne”
 
“An ki a kwantar, tun da ciwon ba a jikinka yake ba ai dole kace na kwantar da hankali, ina kwanciya hankali ga wanda rayuwarsa ta kare? Wayyo Allah ni Rafi'atuuuuuu”
 
Ta fashe da kuka, sai kuma tai saurin share hawayenta ta fito kamar mahaukaciya ta fice fuuu kanwarta ma sai da ta hada da dan gudu sannan ta cin mata.
 
“Anty Rafi'a Lafiya?”
 
“Ba lafiya Ba lafiya....”
 
Ta fada tana kuka, kamar kuma wanda ta tuno abu sai ta share hawayen dake zubo mata.
 
“Sun ce wai dankano ma ne, ya kamani wai sai an yi min aiki idan ban warke ba? To ina lafiya take a nan”
 
Ta sake fashewa da kuka ta dora hannu saman kai.
 
“Wayyo Allah na shiga uku rayuwata ta zo karshe”
 
A cikin satin Asibiti kusan hudu ta tafi ana mata gwanji yana bada result daya cewar tana dauke da cuta mai karya garkuwar jiki. A lokacin ne Rafi'ah ta samun kanta cikin tashin hankali wanda ya amsa sunansa tashin hankali. Da kukanta ta isa gidan Ramlee tana shiga ta rufe ta bakar addu'a da tsinuwa.
 
“Kin kai ni kin baro, daman abokin mutuwa kike nema kuma kin samu, Ramlee kin gama da rayuwata, ba zan tana yafe miki ba, Allah ya isa tsakanina da ke macuciya Azzaluman ko a lahirar wutarki dabam ce Ramlee magajiyar karuwai da kurciyarki kin bata rayuwarki kin bata tawa”
 
Ramlee dai sai kallonta take, a tunaninta Baturiya na mata masifa ne saboda ba je ta tsoke aurenta da Al'Qasim.
 
“Haba Baturiya, ya kike wannan harkowa kamar baki san inda na fito ba?”
 
“Da ace ban san inda kika fito ba, da yanzu ina nan cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali,amman saboda na sanki kin fitine rayuwata kin jefa ni a bala'i da masifa”
 
“Wai me ya faru ne?”
 
Ramlee ta tambaya a tsawace.
 
“Sanadiyarki na kwasowa kaina bakar cutar da bata da magani, hiv Ramlee HIV saboda muguwar hanya da turbar da kika dora ni”
 
Ramlee ta bushe da dariya.
 
“Wai daman baki shirya kwasar Hiv ba kika fito bariki? Ni na dauka ma wani babban abu ne kika ta wannan haniniyar saboda shi? To kwantar D hankalinki ni da ke duk kanwar ja ce, daman duk wanda ya fito bariki ai ya bude mata hanyar shiga ne”
 
“Barikin uwarki? Ai ke kika lalata ni kika dora ni a muguwar hanya marar kyau tsinanniyar Allah ba zan taba yafe miki ba”
 
“Ai kowa ya ga zabuwa da zanenta ya ganta, daman can dama kike nema ba wai ni na lalata ki ba, kuma kudi kike so Baturiya su kuma masu bada kudin suna son abun kudi, sai kuka yi canja to miye kuma na ganin laifin juna a cikin? Taimake ni na taimake ka ne muka yi, kika ba su suka baki, ni kuma kika taimaka min na samu kudi, kuma ni ma da kika ganina ina dauke da cutar nan fa, kawai dai bana wasa da shan magani ne shiyasa kika gan ni haka”
 
“Amman baki tana fada min ba, ba zan biye miki ba shaidaniya, da ba zN bari ki halaka ni ba, kin bar gidan

Join Our Groups

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login