Showing 102001 words to 105000 words out of 332834 words

Chapter 35 - Bakar wasika Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

65603

wanda yaga shigarta ko fitowarsa a dakin.
 
“Okay muje na ganta”
 
Leila ta nufi hanyar corridor Madina ta bi bayanta dakin kofar suka fara budewa sai suka hangota zaune a kan wheelchair din ta juyo tana kallonsu.
 
“Kin ga musakar can, daya dauko ya kawo mana”
 
Leila ta fada tana yamutsa fuska, sai Madina ta karasa kusa da Aminatu tana mata murmushi, sai da ta kawar da murmushi a fuskarta sannan ta juyo ta kalli Leila.
 
“Ki daina haka, ke ma baki wuce Allah ya jarrabe ki ba, abun da Talba yayi abu ne mai kyau, kamata yayi ki taya shi sai ku ci ribar tare, taimakon maraya abu ne mai kyau ni kaina ba abun da nake so kamar wannan”
 
Leila taja tsaki ta saki kofar dakin ta juya ta fice domin ta fahimci Madina ba zata gane abun da take nufi ba. Sai da ta fice sannan Madina ta rage murya ta kalli Aminatu.
 
“Idan Talba ya dawo ki fada masa abun da Leila tace miki, da kuma wanda nace kin ji?”
 
Uffan Aminatu bata ce mata ba, kuma bata nuna wata alama dake nuna ta ji ko bata ji ba. Madina ta mike tsaye tana sakar mata murmushi.
 
“Zan dawo gobe na gyara miki kanki, wata kila ma anjima na sake dawowa, Allah baki lafiya”
 
Ta fada sannan ta juya ta fice. Ko da ta fito Leila na zaune a inda suka zauna dazun tana tabin wayarta.
 
“Ina Momy?”
 
“Ta hau sama”
 
Ta amsa mata ba tare data kalleta ba.
 
“Tana sama”
 
“Idan ta fito ki fada mata na tafi”
 
Leila ta mike tsaye ta bi bayanta, rakata tai har gurin motarta, Bayan Madina ta bude motar ta shiga ta zauna ta kalli Leila ta ce.
 
“Ina ganin kamar Talba ba zai iya son yarinyar nan ba, amman komai zai iya canjawa”
 
Leila ta bushe da dariya.
 
“Madina baki da hankali”
 
“Really? Ai tausayi ne silar soyayya tun da har ya fara tausayinta, ba ki ga yadda yake son a kula da ita ba?”
 
Wani irin zafi zuciyar Leila ta fara yi, ba dan ta yarda da maganar Madina ba, sai dan danganta alakar so da tai da Talba.
 
“Madina kamar baki san waye talwba ba, yaran masu arziki basa aure sai masu arziki, amman duk wanda ya gaji arziki ya taso a cikinsa ya ginu a cikinsa ba zai taba son rabar talaka ba, a littafai ne ake wannan ko a fina finai, amman talaka sai talaka mai arziki sai dan arziki kaddara ma yana sonta kina tunanin Momy da Daddy za su saka masa ido yana aureta? Ni kuma yayi ya da ni?”
 
Madina ta yi dariya.
 
“Waya ga Leila da kishiya”
 
“Har abada ba zan taba zama da kishiya ba”
 
“Ko da ni ne?”
 
Ta fada tana dariya, sai ita ma tai dariya.
 
“Kin san wani abu? Taimako daya zan miki, ki yi yadda zaki iya yarinyar nan ta dawo karkashin kulawata”
 
“Ya za'ayi  haka ta faru? Kin san yanzu Talba ba yarda yake da ni ba, balle na bashi shawarar ya kai ta gurinki, tsaya ma me zai saka ya kaita gurinki?”
 
“Saboda ya nisanta da ita, ki kuma ki samu kusanci da shi, amman idan tana gidan nan, kullum sai kun samu matsala da shi, hakan kuma zai ta lalata alakarku ne har ya kai inda ba a so”
 
Leila ta yi shiru tana nazarin maganar, ta san gaskiya Madina ta fada sai dai tana ganin hakan kamar a dabara ba ne.
 
“Kawai ki bari sai ina nan shi m yana nan, ki yi mata wani abun da zai zama na magana, daga nan sai ki yi rantsuwa ba zata zauna ba, sai ki bar min sauran aikin”
 
Ta karasa tana kanne mata ido daya, Leila dai ta bita da kallon badan ta gamsu ba, har ta rufe motar tai reverse ta bar gidan.
 
 
 
BATURIYA POV.
 
Kamar an dasata a bakin kofar haka ta zauna tana jin kamar ba da gaske ne Faruq ya saketa ba, idan taje gida tace saboda yaga kudi a jakarta ya sake ta? Ai suma za su tambaya ina ta samu kudin, sai tace musu me? Kawarta ta bata ajiya ba lallai ne su yarda ba.
Tana zaune a gurin har ya gama sallah masallaci ya shigo gida, tana jinsa sai ta saka kuka.
A maimakon ya shigo dakin sai ya zauna falo yana bitar karatu da dansa. Ganin be kula ta yasa ta taso daga bakin kofar dakin ta dawo kusa da shi ta duka tana kuka.
 
“Dan Allah Faruq kai hakuri, ka gafarta min, wannan kudin ajiya aka ba ni, Ramlee ce ta bani, kuma san zaka yi fada saboda baka son tarenmu da ita, shiyasa nace Umma ce ta bani ajiyar kudin, ba zan sake ba karba ba na maka alkawari”
 
Ta hade hannayenta biyu tana rokonsa hawaye a fuskarta shabe shabe. Faruq ya sauke Sultan daga jikinsa ya ciro naira ashirin ya mika masa.
 
“Je ka siyo minti”
 
Sultan ya karba yana kallon mahaifiyarsa dake kuka cikin yanayi na rashin jindadi ya fice. Sai da Faruq ya tabbatar ya bar gidan sannan ya kalli Baturiya ya ce.
 
“Hakan ne ya kara tabbatar da kudin nan ba ta hanyar kwarai suka fito ba, tun yaushe na raba ki da yarinyar nan? Yarinyar da a yanzu haka ba gidan iyayenta take ba? Yarinyar da ake zargin har lesbianism tana yi? Rafi'a ban isa na ce kar yi abu ba sai kin yi? Ban isa nace ki yi ba ki yi? Yanzu ai komai ya kare, na riga na sake ki sai ki tattara kayanki ki fice daga gidan nan”
 
Mikewa tai tsaye ta share hawayenta tana watsa masa harara.
 
“To na rantse da Allah babu inda zan je, zaman dana zan yi, kuma ai ga wani cikin nan a jikina, sai na haife shi dan haka sai na gama idda zan bar gidan nan, ai daman ni na biya kudin hayan ko? Sai ka tattara komai naka ka bar min gida, kuma dole ne ka rika ciyar da ni, idan ba haka ba sai na kaika kotu, kuma Wallahi yau ba zaka kwanar min da gida ba”
 
Wani fusata Faruq yai be san lokacin daya kai hannu ya mareta, sai ta fadi a gurin ta fara masa ihu tana kuka, alaar mutane take son tara masa.
Be bi ta kanta ba ya tsallake ya shiga dakin sai ta tashi ta bi bayansa, ta bude wardrobe dinta ta watso kayanta kasa ta fara tumurmuza gadon tana ta ihu, tsayawa yai kallonta da mamaki ganin zata fara masa abun da bata saba ba.
 
“Wai kina da hankali kuwa?”
 
Bata ko saurareshi ba ta cigaba da ihun iyakar karfinta duk wanda ya ji sai yayi zaton ko dukanta yake.
 
“Dan Allah kai hakuri, Wayyo Allah cikina Faruq ina da ciki ka sani dan Allah kai hakuri”
 
Sai ta sake fashewa da kuka ta dawo falo ta fadi kwance tana ta ihun.
 
Makociyarsu ce ta fara shigowa tana fadin.
 
“Subhanallahi lafiya Baturiya?”
 
Kamin ta karaso cikin falon Baturiya ta tashi zaune da sauri ta nufi bakin kofar sai sukai karo da juna, takenta fada jikinta tana kuka.
 
“Maman Siyama ki min rai, Faruq ya doke ni kuma ya sake ni saboda budurwarsa na shiga uku Maman Siyama, ga karamin ciki ga Sultan ina zan kai shi?”
 
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un. Subhanallahi wannan abu be yi dadi ba”
 
After shigowar Maman Siyama makotansu uku suka shigo suna tambayar abun da ya faru. Cikin kuka Baturiya take tsara musu karya wanda ta shiga kansu ta zauna das.
 
“Tun kwana baya na ga Faruq ya canja, idan na tambaye shi miya faru sai yace na daina damunsa ko ya mare ni, yau kuma na fita ina dawowa ya samu yana waya da wata a kan gadona, saboda na yi magana ina cewa hakan da kake be dace ba Faruq, idan ma waya zaka yi ka fita can waje mana, amman ba a gaban idona ba, sai ya hau ni da masifa, wai ban isa na hana shi aure ba, na ce masa Faruq ba aure zan hana ka ba, amman ka duba halin da muke ciki muna fama da rashin abinci ga ni da ciki ga yaronka idan ka ce zaka yi aure dawainiyar ai sai ta maka yawa, Wallahi ko kudin hayar gidan nan sai daje gurin Yaya na samo sannan na biya, wani lokacin haka zamu wuni babu abinci sai wahala, dan Allah idan shi mai tunani har yayi zancen aure a wannan yanayin da muke ciki? Akan haka kawai ya hau ni da duka yana marena yana zagin iyayena ga tufafina can ya watsar a wai na tashi na bar masa gida ya sake ni”
 
Ta kara fashewa da kuka. Kusan kowa dake dakin sai da ya cika da mamaki, domin kallon mutumen kirki suke yi ma Faruq sai yanzu suka gane kallon kitse suke yi na rogo.
 
“Wannan maganar ta kai a duka ayi saki? Ya sake ki ne saboda ya kawo wata ne kawai amman in ba dan haka ba, ai gaskiya kika fada masa, kuma Wallahi kina da zuciyar imani, da wata ce ba zata yarda ta zauna a irin wannan talaucin ba, da kurciyarki? Har ki biya masa kudin haya? Haba kai Namiji dai be yi ba”
 
Maman Siyama sai masifa take ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, Sai dai duk fadan da take ita da sauran makotan ba su san Faruq na cikin dakin ba domin a falo suke. Badiya ta tabe baki tace.
 
“Idan kana ganin mutum baka san halinsa ba, ni Wallahi a zatona Faruq ko hannu aka saka masa a baki a zai ciza ba”
 
“Wallahi ni kadai na san irin ukubar da nake sha a gidansa, ga talauci ga rashin dadin hali, shi yai min mahaifiyarsa da kanensa su min kamar ba yar'uwarsa ba, sam basa kaunata ban san abun da na tare musu ba”
 
“Ki yi hakuri jarabawa ce, yanzu ina Faruq din yake?”
 
“Yana daki”
 
Sai duk suka yi tsit kamar basa gurin, abun ka da mata yan gulma, Maman Siyama ce kawai tai karfin halin nufar dakin, kasancewar ta Babba domin tana da yaya har da jikoki ma. Ta daga lalulen tana kallon yadda aka watsa kayan Baturiya a kasa sai.
 
“Baban Sultan taya zaka bari Sheidan ya shiga tsakaninku, shekara nawa kuna zaune a unguwar nan babu wanda ya taba jinku se yanzu?”
 
Kasa daga kai yai ya kalleta, balle har ya iya furta wani abu, ba zai iya kare kansa ba, ba dan ba shi da abun karewar ba, sai dan baya son tona asirinta ne a matsayinta na matar dansa, taya zai fada musu sanoda ta shigo da kudin da ya ke zargin na alfasha ne? Ba shi ko ita abun zai taba ba, dansa Sultan da kuma wanda zata haifa ne abun zai yi effecting. Dole ne ya rufawa yayansa asiri.
 
“Haba Faruq a rika sara ana duban baki gatari, ko dan yara”
 
Sai a lokacin ya kalleta yana kara tsinkewa da lamarin Baturiya domin a yanzu ta wuce da saninsa.
 
“Inshallahu hakan ba zai sake faruwa ba, an yi na farko kuma n karshe”
 
“To Alhamdulillah, haka ake son ji, a maida komai ba komai ba, daman shi zaman aure sai da hakuri, a rika kai zuciya nesa ko dan saboda yara, shi auren zumuncin idan ya lalace har zumunci yake tabawa, kuma duk yadda kake ganin kyau matar waje da tarbiya ba tai ta gidanka ba uwar yayanka, dan Allah a gyara kuma ayi ta hakuri”
 
“Inshallahu komai ya wuce, mun gode sosai”
 
“To Alhamdulillah Allah ya muku albarka ya ba ku zama lafiya”
 
“Ameen”
 
Juyowa tai ta dawo kusa da Baturiya dake sharbar kuka ta zauna saman kujera.
 
“Ki kwantar da hankalinki kar hawan jini ya kama ki, kuma cigaba da hakuri sakamakonki yana gurin Allah, Allah ya baku hakuri da zama lafiya, na masa magana kuma ya ji yace za a gyara, ke kuma ki kawarda idonki akan lamarinsa idan ma auren zai yi ya kawo ta a nan falonki ya aje sai ki saka masa ido ki kyale shi, kar na sake jin bakinki kin ji ko?”
 
“To Maman Siyama, Inshallahu ba zan sake ba, na gode sosai”
 
Dayar makociyarsu mai suna Rufa'atu ta tabe baki tana fadin.
 
“Idai kika biye namiji sai ki kashe kanki ya auro wata”
 
Maman Siyama ta bugi hannunta tana nuna mata kofar dakin alamar mijinta na ciki, sai ta daga kafada.
 
“Ina ruwana shi be ji kunya abun da yai ba”
 
Tana rufe baki Faruq ya fito ya nuna mata kofar waje
 
“Malama fata ki bar min gida”
 
“An dai ji kunya Wallahi, ana wulakanta matar gida saboda ta waje”
 
Ta fada sannan ta fice Mamam Siyama na watsarta. Badiya ma ficewa tai tana Allah ya bada hakuri, Maman Siyama kan sai da ta tsaya ta sake musu nasiha sannan ta fita tare da dayar makociyarsu. Komawa Faruq yai dakin ya dauki jakarsa ta littafai ya bude ya dauko takardar da biyu ya rubutawa Baturiya wani sakin sannan ya nufo falon ya jefa mata takardar.
 
“Dazu saki daya nai miki, yanzu kuma kin ja sakin ya zama biyu kuma a rubuce, ki je ki yi duk abun da zaka yi amman zama ni da ke ya kare, ba zan iya zama da mace da bata ganin mutuncina ba, macen da bata iya rufa asirin mijinta ko dan saboda yayanta, Wallahi Rafi'a na rufa miki asiri ne kawai saboda Sultan da kuma abun da ke cikinki, ba dan bani da abun fada ba, kuma wannan abun da kika yi ya kara fito min da halinki yanzu na gane wacece ke?”
 
Mikewa tai tsaye tare da takardar tana karantawa.
 
“To sai me? Ina ce dai ni na biya kudin hayar gidan nan, dan haka ka fice min a gida, kuma gobe goben nan idan na ga dama sai na zubar da cikin nan, daga kawai ka raba ni da wahalar talauci? Ina cika idda zan auri Saurayi, dan gidan masu hannu da miya har da manshanu, kuma ka zuba ido ka gani, sai na baka mamaki Faruq, sai n tabbatar maka cewar ni Baturiya ba ajinka ba ce”
 
Ta fada kamar ba ita ce ta gama kukan munafurci ba a dazun, dauke kai yai ya fice yana taka kafarsa mai ciwo da karfi saboda bacin rai, yana kokarin saka talkaminsa ya hango Sultan zaune bakin kofar bandakin dake tsakar gidan yana kuka. Ajiyar zuciya ya sauke ya saka talkamin ya nufi inda yake ya kama hannunsa, kana ganinsa kasan a tsorace yake, domin be saba ganin Faruq yana fada da Baturiya ba.
 
“Sultan kana son muje gidan Mama my kwana?”
 
Sultan ya daga masa kai, sai Faruq ya sakar masa murmushi ya dauke shi suka fice.
 
Shin kin san Kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud
Sandal flakes
Sandal wood
Signature
Kajiji
Damboun kajiji
Halud ball
Wardrobe ball
Coconut sandal
exclusive gowe
Black humra
Body milk
Kulaccam
Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin da kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya, domin siye ko sari ku tuntubi Ramla incense ta wannan number 07038392576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa
 
 
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
 
 
Aminatu na zaune a dakin har kusan la'asar sannan Amal ta leko tana kallonta domin bata nan komai ya faru sai dai Kabir ya labarta mata abun da ya faru, sai kuma ta fita ba tare da ce mata komai. Aminatu ta saka hannu ta share hawayenta sannan ta fara tura keken da nufi shiga bandaki sai taji abun ya mata karfi ba kamar yadda ta ji yana tafiya idan an turata ba, wata kila saboda bata enough kuzari ne, wata kila kuma idan an turo ta baya yake tafiya ne. Leken keken ta fara yi sai ta ji an bude kofar dakin an shigo, dagowa tai ta kalli Mairo dake dauke da plate din abinci da kofin ruwa ta nufota, kamin ta karasa Leila ta biyo bayanta.
 
“Ke waya saka ki?”
 
Mairo ta juyo ta kalleta.
 
“Babu gani na yi an zubawa masu aiki na su, kuma an debar muku na ku, ita ma yanzu ai ta isa jin yunwa”
 
“Okay ashibabba, yar neman suna, abincin na gidanku ne? Daga zuwa aiki har ki fara tunanin sarrafa gida yadda kike so?”
 
“Saboda na zubo mata abinci shine abun sarrafa gida? Haba Leila miyasa kike fadawa mutum magana any how ne? A haife dai kin san na haife ki amman duk maganar da ta zo bakinki sai ki fada min kamar wata yarki? Saboda kawai ina aiki gidanku?”
 
“Kawai ne? Kyauta kike aikin ne? Ba biyanki ake ba? Yanzu uban waye ya baki umarni kawo mata abinci?”
 
“Keeeee karki sake zagina, idan ina aiki a gidan mu to na gama, arziki ai ba hauka ba ne”
 
Mairo na kai aya Leila ta wanke mata fuska da mari.
 
“Mi zaki dakawa tsawa kina ce min ke?”
 
Mairo ta duka ta aje abincin sannan ta mike tsaye ta ware hannunta zata rama marin da Leila tai mata sai Leila ta rike hannunta ya wulgar.
 
“Karki kuskura ki ce zaki taba ni da karamin hannunki, wawuya kawai”
 
Mairo, ya girgiza kai.
 
“Ina tausayin yadda rayuwa zata maida ke nan gaba, ki taka a hannu duniya ba gurin zama ba ce, ban taba ganin mutum mai wulakanta mutune ba irinki”
 
“Wallahi idan baki wuce kin bar dakin nan ba sai na baki mugun mamaki”
 
Mairo ta kalli Leila kawai sannan fice da Mairo ake fadan amman Aminatu ce ta fashe da kuka jikinta ya fara rawa tana yi ma Leila kallon tsoro.
 
“Ke kuma me akai miki da zaki fara yi ma mutane kuka munafuka?”
 
Ta dauki ruwan da Mairo ta aje ta watsa mata a jiki, wani irin zabura Aminatu tai ta kalli jikinta da ruwa ya jika, sannan ta hayayakomawa Leila a fusace.
 
“Mahaukaciya wayuya, baki san darajar dan'adan, ki bar ni da abun da ya dame ni”
 
Ta fada kamar ba ita ba har wani numfashi take da karfi hawaye a sauko mata. Leila kamar mai jira sai tai cikinta ta chakumota ta jefar kasa.
 
“Ni zaki yi ma ihu dan ubanki”
 
Ta kama tsorayen kanta ta rike gam tana fisger kan nata. Wani irin ihu Aminatu ta saka iya kar karfinta tana jin zafin har cikin kanta, sai ta soma jin abu kamar na wacan lokacin yana dawo mata, wani

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login