Showing 150001 words to 153000 words out of 332834 words

Chapter 51 - Bakar wasika Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

65622

zai shige ciki, daker ta kwanci kanta domin a ra'ayinsa ya so ta kwana a gidan ne, sai ta nuna masa tana a karkashin iyayenta ne za su iya zarginta idan ta kwana, sai dai bata yarda ta nuna masa cewar tana da aure ba, sai ma karyar da tai masa cewar mijinta ya rasu ya barta da yaro daya.
 
Misalin hudu da kwata ta fito daga gidansa, sai da ta shiga Napep sannan ta kira Ramlee ta sanar mata cewar yanzu ta fito daga gida, domin bada sanin Ramlee ta hadu da shi ba, kuma ta san idan har taji sun hadu ta bayan fage zata iya zargin Baturiya.
 
“To ki tsaya ta sokoto Road, zan zo a dauke ki”
 
“Okay toh amman karki dade dan Allah”
 
“Okay”
 
Baturiya ta sauke wayar tare da shafa cikinta tana jin irin abun da take ji a duk lokacin da tai yunkurin zubar da cikin, sai dai bata da mafitar data wuce wannan, domin idan bata zubar da cikin ba zai iya bata matsala tsakaninta da Fahat, wanda bata fatan haka.
 A kusa da wani shagon mai Napep din ya sauke ta sannan ta fita ta ciro kudinsa ta ba shi taja gefe ta tsaya sai taunar cingan take tana wani kis kis kis, kamar wata tsohuwar karuwa, dan mayafin dake jikinta ma ba wani abun kwarai ba ne yadda kasan wata yar iskar budurwa haka ta fito, arzikinta daya abaya ce a jikinta ba Atamfa ko lace ba. Ta kusan minti talatin a gurin har ta fara gajiya ta fara takawa gafen titin tana tafiya sannan Ramlee ta kirata sai ta kwatanta mata inda take, tana sauke wayar wata Benz ta wuce gabanta sai kuma ya dawo baya ta faka daidai inda take tsaye. A hankali mai tukin motar ya sauke gilashin motar yana kallonta, suna hada ido sai ta sakar masa murmushi shi kam ya dade da yi ma fuskarsa ado da murmushin.
 
“Hajiya ke ce haka dai?”
 
Ta dauke kai tana fari da ido sannan ta sake kallonsa da kyau, shi din ne dai abokin Faruq da ta taba roka kudi ta WhatsApp a lokacin data saci numbersa a wayar Faruq.
 
“Ni ce dai ranka ya dade, ya akai ka gane ni?”
 
“Kyakkyawar mace irinki ai kowa ya gani zai tsaya, sai dai daga baya mutum zai tantance idan ya sanki ko akasin haka”
 
Ta yi murmushi.
 
“Ka dawo nan ne ko zuwa kai?”
 
“To gani nan dai, Ina zuwa haka? Ina abokin nawa ya barki a rana tana gasa ki”
 
“Abokin ka ai ya dade da yin tazara, duk kyau surar nan da kake gani ya zubar wata zai dauko”
 
“Subhanallahi, lallai da labari a bakin naki mai kyau, da zaki taimaka min da kin shigo motar nan”
 
“Wallahi kawata nake jira, zata zo nan ta dauke ni”
 
“Okay”
 
Ya dauko katinsa ya mika mata.
 
“Gashi a taimaka a kirani, duk dai na san ba a rasa number”
 
Ta yi murmushi bayan ta karba, sannan ta daga kai tana kallon Ramlee data faka a dayan gefen.
 
“Okay zan kira ka Inshallahu”
 
“Na gode kyakkyawa”
 
Ya fada yana kare mata kallon irin kallon nan na yan iska. Sannan ya rufe gilashin motar ya hau titi, ita kuma ta nufi gurin da Ramlee ta faka motar ta bude ta shiga.
 
“Waye wacan?”
 
“Wani abokin Faruq ne”
 
“Okay”
 
Sai da suka hau titi sannan Ramlee ta kalleta ta ce.
 
“Hope dai kin shirya?”
 
“A shirye nake, kawai dai ina gudun a samu matsala ne”
 
“Ba wata matsala, Dr KB kwararen likita ne, ba yau na saba aiki da shi ba, ki kwantar da hankalinki”
 
Ajiyar zuciya ta sauke tana jin kamar kar ta aikata.
 

 
Inshallahu a nan zamu dakata sai kuma bayan sallah idan mai kowa mai komai ya amince mana ganin lokacin cikin koshin lafiya. Fatar Allah ya karba mana ibadar da zamu shiga ya yafe mana kurakuranmu.
 
Ina neman afuwarku. Sai mun hade a Book 2 bayan Sallah inshallahu. Happy Ramadam
 
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
 
AMINATU POV.
 
Tana jin muryar Talba sai ta bude ido da sauri, domin tabbatarwa idan kunnuwanta daidai suka jiyo mata, tsaye ta ganshi a kanta yana ta kallon kyakkyawar fuskarta cikin damuwa. A take ta zabura ta tashi zaune.
 
“Ina wuni”
 
Sai ya zauna kusa da ita yana kallonta cike da kulawa.
 
“Ya jikin?”
 
“Alhamdulillah”
 
Ta fada tana jin kamar an yaye mata ciwon an aje gefe daya. Hannunsa ya kai ya taba wuyanta sai ya ji shi da dan sauran zafi. A nan ya kalli Kaka.
 
“Wane irin magani aka bata?”
 
“Wanda ka kawo mata”
 
Kaka ta fada masa tana wani tsuke baki, ta dauke kai kamar wata yar yarinya wai ita ala dole fushi take da shi.
 
“Haba Kaka”
 
Sai kuma ya kalli Aminatu.
 
“Shalele wani irin magani aka baki?”
 
“Mai dacin nan na malaria da na ciwon kai, sai kuma ya saka min ruwa, kuma ta min allura”
 
Ta fada a shagwabe idonta na cika da kwalla ji take kamar ta fashe masa da kuka tunawa da zafin allurar da akai mata gashi kullum yake mata safe da yamma.
 
“Kin gani ko? Ba ma wani kwararen ba ne, taya zaka baka maganin malaria da allura a lokaci daya, kuma ba a tsaya an auna mutum ba? Maybe ma hawan jini ne tun...”
 
Kamin ya karasa Kaka ta daka matsa tsawa.
 
“Can can ga kanka, sai dai idan kai ka shafa mata hawan jinin, dan dai ina da shi ne shine kake son murdowa ta nan kace ni na saka mata? Daman tun da ka tafi take ciwo tana kuka na kira dan Asabe ya dubata yace malaria ce”
 
“Ba a auna mutun ba za a gano ciwonsa? Ni ban ce kin laka mata ba, daman ya za'ai wani ya saka ma wani hawan jini?”
 
“Wai idan ma manufar ka kenan ai na san ba so na kake ba”
 
Da gaske take maganar, a kokarin juya maganar zuwa wasa yai dariya ya amsa mata da.
 
“Me zan yi da tsohuwa ga sabon jini na samu”
 
Ya fada yana kallon Aminatu. Kaka ma kallonsa take.
 
“Ko Shalele?”
 
Aminatu ta yi kasa da kanta gabanta n bugawa da karfi. Sai yai murmushi
 
“Kin ci abinci?”
 
“Bata ci abincin ba ai gidan yan yunwa ka kawo ta ko?”
 
Kaka ta amsa masa a fusace. Be kula ta ba ya cigaba da kallon Aminatu.
 
“Bari na fita na bincika idan akwai inda ake siyar da abinci mai kyau sai na siyo miki, hankalina ya dauku shiyasa ban tsaya a hanya na siyo miki komai ba”
 
Magana yake mata a hankali kamar mai kokarin fahimtar da ita. Sai ta daga masa kai a hankali tana kai hannu ta share kwalla da suka tarar mata.
 
“Good Girl”
 
Ya mike tsaye sai ta bishi da kallo har ya fice, Kaka kuma ta bita da kallo mamaki zuciyarta na raya mata wani abun.
 
“Ke Auta...”
 
Aminatu ta kalli Kaka da sauri, sai Kaka ta matsa kusa da gadon da take zaune.
 
“Fada min lokacin da kuna can, yana miki wani abu?”
 
Aminatu ta yi shiru domin bata fahimci inda Kaka ta dosa ba.
 
“Yana tabaki ko ya rike hannunki ko ya dan shafa ki”
 
Aminatu ta yi shiru tana tunanin irin amsar da zata bawa Kaka.
 
“Karki ji tsoro ko kunya, kin ganshi nan jikana ne, duk yafi soyuwa a raina amman wacan kanen uban nasa da tsinanniyar matarsa da bata nuna masa son yan'uwan uwarsa ba, sun canja shi sun maida shi wani kala, ba san manufarsa a yanzu, na lura sai son shige miki yake kuma bayan ya nuna min shi ba zai aureki ba, har yana wani kiranki Shalele, wannan sunan yan iska ne, karki yarda ya sake ce miki haka kinji ko?”
 
Aminatu ta daga mata kai, alamar eh sannan tai kasa da kanta tana tauna maganar Kaka ba cewar yace ba zai aureta ba, wa yai masa tayin auren tun farko? Amman miyasa zai aurenta bayan ita da shi akwai banbanci da tazara mai girma?
 
‘A'uzubillahi’
 
Ta fada a ranta tare da lumshe ido tana jin kamar ta yi banban sabo saboda zuciyarta na kusanto mata da aurenta da mutumen da ko a mafarki yafi karfinta. Taya mutum mai daraja da tarin dukiya da kyau da iyali kamar Talba zai yarda ya hada jini da irinta? Amman miye manufarsa ta yi mata furucin da yai mata a lokacin da zai tafi? Ta daga idonta ta kalli Kaka.
 
“Tsohuwa ke kika ce masa ya aure?”
 
“Eh, saboda ki samu rayuwa mai kyau, kuma kin ga dan'uwanki ne zai rike ki da amana, sannan ni bana son yarinyar can da zai aura, uwarta sau biyu kawai ta taba zuwa garin nan, ita yarinyar ma ban santa ba, amman suka zaba masa ita saboda sun ga yana da dukiya, sai juya shi suke kamar waina, ni bana son ya aureta ma, kara ya auri yar'uwarsa idan ma a nan zai aje ki ai kin ga dole ya rika zuwa yana duba ki mu ma muna ganinsa, kuma sai na nunawa wannan bakar matar ni ma na isa da shi, amman sai ya juya min baya harbda turo wannan uban nasa a waya yana fada min kabli da ba-adi da shika shikan kin aurenki”
 
“Yana da wanda zai aura Kaka, kuma ba ki ga zubinsa ba? Akwai banbanci rayuwata da dasa, ni fa a kauye na tashi, sannan na rasa abubuwa da yawa da be zama lallai ma wani namijin ya so ni ba, balle kuma shi”
 
“Ai ba wannan za a duba ba, hadin gida da zumunci ba ruwansa da wannan dan haka ki daina ma duba wannan”
 
Kaka ta karasa tana mikewa tsaye ta gyara daurin zanenta.
 
“Bari na yi fitsari”
 
Aminatu ta yi kasa da kanta idonta na cika da hawaye. Kaka na shiga bandakin Talba yai sallama ya shigo, Aminatu ta kasa amsawa kuma ta kasa dago kai ta kalleshi, har ya zauna kusa da ita ya kai hannunsa ya dago kansa sai yai arba da hawayenta.
 
“Kaka ta miki wani abu?”
 
Ta girgiza masa kai alamar no.
 
“Toh miya faru ko kina jin ciwon ne?”
 
Wannan karon ta samu damar amsawa.
 
“Aa”
 
Sai ya saka hannunss biyu ya share mata hawayenta.
 
“Idan ina kusa da ke, hawaye basa da muhallin a fuskarki, ki daina kuka kin ji Shalele?”
 
“Ka daina ce min haka dan Allah”
 
Ya daga kansa sama yayi murmushi ya sauke.
 
“Idan Kaka ta zo ki fada mata ba zan daina ba”
 
Ya fada domin ya san ita ta kitsa mata wannan maganar, domin bata taba masa korafin kiran da yake da Shalele ba sai a yau.
 
“Na bawa wani ya siyo miki abinci mai kyau, yanzu fada min Kaka ta miki gulma ta?”
 
Ta yi shiru kanta a kasa.
 
“Kaka tana fushi da ni, saboda na ce ta aura min ke taki”
 
“Aa ba sai ka boye min ba, ni bana son aure a yanzu kuma na san akwai banbanci a tsakanina da kai...”
 
Bata karasa ba ya kai hannunsa ya rufe mata baki.
 
“Wallahi ban taba ganin wannan banbanci ba, kawai abun da nake tunani yadda zamu fuskanci juna ni da ke, kuma yanzu wannan zuwan da na yi ba zan tafi ba sai da igiyar aurenki”
 
Ta sakar masa ido sai kuma ta matsa baya kamar mai tsoronsa.
 
“Kana da wanda zaka aura, Yallabai ka rufa min asiri bana son na sake shiga wata matsalar idan ma Kaka tana fushi da kai ne saboda ka ce ba zaka aure ni ba, na fahimta”
 
Yayi Murmushi ya kalli wani gefen sannan ya sake kallonta.
 
“Yan mata, idan ma kin yi karya zuciya bata iya karya ba, na riga na karance ki kina kokarin hana zuciyarki abun da take so ne, a miyasa kika rika tambayar yaushe zan dawo a lokacin da zan tafi?”
 
“Saboda na sabu da kai ne kawai na kwana biyu”
 
“Miyasa a lokacin dana tafi kika kwanta ciwo sai a yanzu dana dawo kika samu lafiya?”
 
Ta yi shiru.
 
“Kin san saboda me?”
 
Ta girgiza kai.
 
“Saboda na tafi da zuciyarki, a yanzu kuma da na dawo na dawo miki da ita, karki yarda zuciyarki ta raya miki banbanci tsakaninki da wata ko wani, karki yarda ki sake nisa da mutanen da suke da muhimmanci a rayuwarki, domin zuciyarki ba zata iya daukar wani ciwon ba”
 
Har lokacin kanta a kasa yake tana hawaye, shi kuma yana kallonta yana jin kamar ace yana da permission din rumgumarta ya rarrasheta. Kamar daga sama suka ji muryar kaka tana jan tsaki.
 
“Maye ne kai da ka tafi da zuciyata, ka ji wata maganar banza idan son ta kake da gaske ai aurenta zaka yi”
 
Runtse ido Talba yai ya bude ya kalli Kaka da be san tana cikin bandakin ba har sai da ta fito.
 
“Kaka labe kike mana ne?”
 
“Ina ce dai Dakina ne? Kuma ina jinka dazun kana min karya wai na hana ka Auta, ai ban mutu ba da rai na”
 
“Dakinki ne, amman ni ma ina da hakki da shi ko? Kuma ai ban fadi karya ba na fada miki a waya zan zo kika ce ba zaki ba ni ba, kin dauka wasa nake? Wallahi Kaka ba zan bar garin nan ba sai na auri Aminatu”
 
A take Kaka ta washe hakora, gaban Aminatu kuma yai dukan uku uku.
 
“Aa dan Allah dan Annabi Aa”
 
Aminatu ta fada cikin kuka, sai Kaka ta watsa mata harara.
 
“Ke Wallahi baki isa ba ke ma, idan ba haka ba ni da ke ne, wannan abun farinciki da jindadi haka zaki ce wani aa, Mu'azu da gaske kake yi?”
 
“Wallahi da gaske nake yi kaka, amman dan Allah karki cilasta mata ki barni zan yi magana da ita”
 
“Mu can da aka mana aure, zabi aka bamu ne? Ko mazan ma ba mu sani ba sai da aka daura auren, karka biye shashancinta yarinya ce karama bata da wayo”
 
Talba yayi murmushi yana kallon Aminatu dake hawaye. Kamin ya kalli kofar shigowa dakin Kaka na amsa sallamar Aminu baki har kunnen.
 
“Aminu”
 
“Na'am Tsohuwa ya jikin?”
 
“Aa ni ai na warke, abun farinciki ya samu kuma ai”
 
Har Aminu yayi kamar ya tambaya minene domin ya lura Kaka tana son labarta masa sai kuma wata zuciyar ta hana shi, sai ya karasa gaban Talba ya aje masa kular abinci da ledar lemu ya mika masa canji.
 
“No ka rike carjin”
 
“To na gode Allah ya kara sutura”
 
Aminu na fita Kaka ta bi bayansa domin labarta masa, abun da ya kasa boyuwa a ruhinta. Sai da suka fice sannan Talba ya kai hannu ya bude cooler kamshin ferfesun kayan ciki ya daki hancin Aminatu.
 
“Sauko ki ci”
 
“Aa”
 
Ta fada da muryar kuka, domin kukan ne ya zo mata da gasken gaske. Kallonta yai.
 
“Shalele? Kar dai ki ce min baki son auren nan?”
 
Ta daga masa kai.
 
“No please, kar mu yi haka da ke, ba wai zan aureki saboda Kaka ne kawai ba, zan aureki ne saboda na faranta miki rai, ina tunanin zaki so abun da zai faranta min rai kuma ya shirya tsakanina da yan'uwana, idan har ban aureki ba ina cikin matsala ba yar karama ba...”
 
From a to z ya zayyana mata komai ciki har da kudirinsa na boye auren na su na wani lokaci. A nan ne hankalinta ya kara tashi.
 
“Ina jin tsoron abun da rayuwa zata samar min a gaba, komai nawa ya banbanta dana kowa, rayuwata ta zama ba tawa ba, duhu ne ya fara bayyana a ciki, sai iska ya mamaye komai, kamin na ankara taurarin ciki sun tarwatse! Hakan ne silar rushewar duniyata... Talba ba ni da gata, ni fa yar gudun hijira ce kawai...! Ina jin tsoro abun da zai faru”
 
Ta share hawayenta. Yayi saurin kama hannayenta, a cikin yanayin da ke nuna tsantsan tausayinta, fararen idanuwansa masu kamar madara suka rine da ja tsabar bacin rai da bakinciki.
 
“Ashe ba ina kusa da ke ba? Ki daina tunani wannan tunanin Shalele da yarda Allah sai na mai da ke yar lele”
 
“Taya? Kana da wanda zaka aura, kana da rayuwarka da mafarkinka, miyasa zaka rusa komai? Baka tsoron halin da zan shiga? Abun da iyaye basa so akwai hadari a yinsa”
 
“Ki daina damuwa da iyayena ko Leila, ni mijin mace hudu ne, ba san ba zaki yarda alakar dake tsakanina da Kaka ta lalace ba akan abun da zaka iya yi min, zan sama miki wata rayuwar mai kyau mai inganci, zamu gina wata duniyar mai ciki da daula da jindadi mai cike da zuri'a”
 
Ta fisge hannayenta hawaye na ta zirya a fuskarta, mikewa tai tsaye tana masa kallon tsoro.
 
“Ta ya kake tunanin rayuwa zata zama mai sauki a gareni? Ya kake tunanin Leila zata ji idan ta san ka aure ni? Miyasa kake tunanin samun wasu Family a gareni mai sauki ne? Bayan na rasa kowa? Taya mace irina wanda ta rasa komai na kima da mutuncin mace farinciki zai rabeta, ta ya Yallabai...!”
 
Mikewa yai tsaye yana kallon cikin idonta.
 
“Kar bakinki ya sake furta irin kalamin nan, ina gargade ki a kan furucin... Ina son na roki ki wannan alfarmar Aminatu, dan Allah ki yarda ki aureni ba dan saboda kanki ba ko Kaka, saboda ni”
 
Ta runtse ido hawaye na sauko mata, a take ta ji zazzabin ya dawo mata sabo.
 
“Na san akwai wahala amman ki daure dan Allah”
 
Ta bude idon ta kalleshi sai kuma ta sake rufewa sakamakon jirin data ji yana dibanta.
 
“Ina son zan kwanta”
 
Ta fara lalaben gadon tana kokarin kwantawa idonta a rufe.
 
“Wannan maganar zata zama a tsakaninmu, bana son Kaka ta san cewa a boye zamu yi wannan aure”
 
Nan ma bata ce masa komai ba har ta zauna.
 
“Ki ci abinci sannan ki kwanta”
 
“Bana jin yunwa”
 
“Ba zan cilastaki ba, bana son na saka ki a cikin abun da zai haifar miki da damuwa, zan yi magana da Kaka”
 
Bata ce masa komai ba har ya fice daga dakin. Ta inda yake jiyo muryar Kaka ya nufi sai ya tsaya daga bakin kofar dakin yana sallama.
 
“Shigo Mana Mu'azu”
 
Kaka ta fada da far'arta, sai ya cire talkamin kafarsa ya shiga dakin ya zauna kusa da Kaka yana kallon matar kawon nasa dake da far'ar da alama ita ma abun ya mata dadi.
 
“Mu'azu yanzu nake jin abun alheri Allah ya tabbatar ya sanya alheri”
 
“Amin na gode”
 
Kaka ta kalleshi tana fadin.
 
“Salamatu ce ta zo da wata magana wai idan Alhaji ya ji zai iya hanawa, ko kuma ya cilasta sai ka sake ta”
 
“Kaka kar wannan na dame ki, da saninsa na zo nan, kawai dai yace babu ruwansa saboda na dage sai na yi auren, shiyasa nake son kamin ya canja shawara a daura mana aure da ita inya so idan tarewa ne sai a barshi har sai komai ya kamalla”
 
“Amman Mu'azu hakan ba

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login