Showing 273001 words to 276000 words out of 332834 words

Chapter 92 - Bakar wasika Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

65653

rigata, Allah dai ya tona asirin wanda ya aikata wannan abun”
 
“Ameen”
 
Aminatu ta fada sannan ta shiga raya Hajiya Laraba aikin. A tare suka gama komai Hajiya Laraba ta zubawa Talba nasa dabam, ta kawo na yaranta da Aminatu a falo, ta saka Aminatu ta tashe su suka fito wandanda za su karya a nan suka karya wandanda kuma za su tafi da abincin makaranta aka zuba musu na su.
Bayan sun gama karyawa suka gyara dakunansu suka gyara falon Aminatu ta gyara kitchen ta wanke kayan da suka bata. Sannan ta koma dakin ta zuba ruwa tai wanka ta fito ta shirya cikin wani chocolate material ta saka bakin Hijab ta fesa turare.
 
“Har zance ki tashi ki shirya Baban su ya wuce da ke idan zai kai yara makaranta ashe kin shirya ma”
 
Hajiya Laraba ta fada tana rike da curtains din kofar dakin. Sai Aminatu ta juyo ta kalleta.
 
“Eh na shirya yanzu zai tafi”
 
“Eh kin san 8 suke zuwa makaranta yanzu zai fito, idan ya aje su sai ya kai ki asbitin daga nan shi ma ya shiga ya duba shi”
 
“Toh”
 
Ta mike tsaye ta fito, ta nufi kitchen din ta dauko abincin da aka zuba masa ta fito falon ta zauna. After like 5 minutes ya fito sanye da jallabiya fuskarsa da murmushi hannunsa kuma rike da keys din motarsa dayan hannunsa rike da hula.
 
“Amarya ce amarya data tada mana hankali”
 
Aminatu ta yi murmushi ta sauke kai masa tana jin kunya.
 
“Ina kwana?”
 
“Lafiya Kalau, ya gajiya”
 
“Alhamdulillah”
 
Ya yi gaba ta bi bayansa, Hajiya Laraba ta fito rike da karamar yarta dake shan nono ta rako mijinta har gurin motarsa. Yaran suka shiga baya Aminatu ta shiga gaba rike da abincin.
 
 
 
 
BATURIYA POV.
 
Tun shekaranjiya da Fahat ya ce mata zai zo, bata sake samun natsuwa ba, idan ta kira shi baya picking, idan ta tura masa sako baya mata reply hakan yasa ta shiga damuwa sosai, domin tana sonsa fiye da yadda komai yanzu a rayuwarta kuma ta ci burin aurensa. Ta bangaren Fahat ba dan komai yake mata haka ba, sai dan ta gane girman laifin data aikata masa ba boye masa sirrin cewar ta taba aure har tana da yaro, domin har yanzu be yi mata maganar ba, ita kuma bata nuna masa komai akan haka ba.
Rashin kulawar da bata samu a gurin Fahat ya saka ta watsar da duk wata alaka dake tsakaninta da Alhaji Idriss Ali, daman can ta shirya watsar da wannan rayuwar saboda auren Fahat da take son yi. Balle kuma yanzu da take tsoron kar ayi wani bincike a gano tana tare da wani, ya kara lalata maganar aurenta da Fahat.
Tana zaune tana cin abincin, wani almajiri ya shigo yana sallama.
 
“Wai an ce ana sallama da Rafi'a”
 
Ba ita kadai ba har Umma da kanwarta sai da suka kalli Almajirin, domin bakon abu ne a gurinta wani ya aiko yana mata sallama, domin duk masu zuwa gurinta suna da number wayarta kiranta suke idan za su zo.
 
“Je ka ce waye”
 
Umma ta fada, sai Almajirin ya juya ya koma, Baturiya bata sake maida hannunta a cikin abincin ba, na bakinta ma kasa hadewa tai saboda tunanin wanda ke kiranta, zuciyarta sai sake sake take mata.
Ba dadewa Almajirin ya dawo ya ce.
 
“Wai ance Fahat ne”
 
“Fahat”
 
Baturiya ta maimaita sannan ta tashi da sauri ta shiga dakinsu ta dauko hijab dinta ta saka ta fesa turare ta fito da saurinta ta fice Umma ta bita da ido tana dan tabe baki, domin ita bata ga wani abun rawar kai da kafa akan namiji ba. Tsaye tai jikin gate din gidansu ganin bakar motar da bata san Fahat da ita ba, sai Ramlee sai dai ba zata iya shaidar Ramlee ba ce kai tsaye saboda motar ta bata baya, lambar motar ta kalla ta tana kara raya ma zuciyarta cewar Ramlee ce, sai dai sunan Fahat da almajirin ya ambata ya saka gabanta faduwa da tunani, tana tare da Fahat din ne ko kuma ita ce ta ce ace haka saboda ta fito? Da kamar tsoro ta karasa gurin motar ta bude front seat gabanta na mugun faduwa, sai tai arba da fuskar Ramlee tana murmushi.
 
“Daman na san zaki fito da wuri saboda na ambaci masoyinki”
 
“Kina tare da shi ne?”
 
Baturiya ta tambaya tana shiga cikin motar ta leka baya, sai Ramlee ta bude baki.
 
“Wa? Na isa? Saurayin da ko gaisawa da shi baki taba bari na yi ba? Ina zan ganshi? Ko ma na ganshi shi ai ba sanina yayi ba balle har ya shigo motata ya biyo har nan”
 
Bayan Baturiya ta sauke ajiyar zuciya ta kalli Ramlee tace
 
“Idan kina son magana da ni Ramlee ba akwai waya ba? Zaki iya kirana ta waya ai, kin san inda Umma ta ganki a nan zata min fada sosai”
 
“Saboda na zama annoba ko?”
 
“No saboda bata son alaka ta da ke kuma kin sani”
 
Ranlee ta dan taba baki.
 
“Ke kin ga nima dalilin zuwana, magana nake son yi da ke akan shiyasa na zo, magana waya bata yi kuma na san idan na ce mu hadu zaki yi da saka min rana kina dagewa saboda Fahat ya dauke miki hankali a yanzu”
 
“Uhmmm Fahat din da ni kwana biyu ma na rasa gane kansa”
 
“Ban gane ba”
 
“Idan na kira shi baya dagawa, idan na aika masa sako baya mayar min, yace min yana nan zuwa yana son mu yi wata magana mai muhimmanci amman har yanzu shiru be zo ba kuma be sake kirana yace min komai ba”
 
“To Allah ya kyauta, ni na dauka ma magana har ta yi nisa ana ta shirye shirye?”
 
“Ni yanzu ma ban san mi zan fadawa Yayanmu ba, dan nasan sai ya sake min magana tun da yace na fitar da miji kuma ya ji na masa shiru, iyeyen Fahat din basa son aurena da shi, wata kila shiyasa ma ya daina zuwa”
 
“To wai ke har yanzu baki fada masa cewar kina da da ba? Ko dai ya gano ne? Shiyasa suka hana shi aurenki?”
 
“Idan ya gane ai zai min magana amman be ce komai ba”
 
“Allah ya kyauta, ni idan ma ya fasa aurenki ai ya taimaka min domin ban gama samun kudi da ke ba”
 
Sanin maganar da zata iya biyo baya bayan wannan yasa Baturiya ta dauko dayar maganar da tai mata da farko a kokarinta na kawar da wannan.
 
“Maganar me kike son mu yi, wanda ta fi karfin waya?”
 
“Wallahi akan Alhaji Idris ne, mutumen nan ya bi ya takura min da maganarki, kin san su manyan mutane idan suka ji zuma a abu hankalinsu baya kwanciya sai sun gama yayinsa, kuma Wallahi yana sonki sosai Baturiya, ni da a yadda nake gani ma zai iya aurenki”
 
Baturiya ta yi mata wani kallo na mamaki.
 
“Dan Allah daina wannan maganar, taya zan auri tsoho? Ke yanzu na miki kama da wanda zata iya auren tsoho?”
 
“Eyeeee matsayi, wasu suna nan suna neman tsohon ba su samu ba, ke yanzu ba ki san Sugar daddy ake yayin aure ba? Indai mutum yana da rufin asirinsa yana da kudi ina ruwanki da tsufa”
 
“Aa ba zan iya auren tsoho ba, koma zan auri tsoho sai na auri Alhaji Idris mutumen da muka gama lalacewa a titi”
 
“To na nawa akai, idan can da ana samu zunubi yanzu ba sai a samu lada ba, ina ce dai muradinki ki samu kudi, shi ma wannan Fahat din ai ba dan yana da kudin kike sonsa, ba dan kurciya ba, tun da be fi Faruk komai ba”
 
“Ni dai yanzu ki fada min abun da ya kawo ki”
 
“Maganar Alhaji ce, ya matsa min yana ta son na lalaba masa ke, har albishir yace na miki zai biya miki maka kuma zai sai miki gida ya siya miki mota idan zaki yarda ki zauna da shi tsawon shekara daya”
 
“Baki fada masa zan yi aure ba? Na fada masa cewar zan yi aure fa ko be yarda ba ne”
 
“Wallahi na fada masa, cewa yai shi ina ruwansa, indai zaki ba shi abun da yake so, kin san manyan masu kudin nan suna daukar kwangilar mata fa, kuma Wallahi kika sake jiki zai miki komai saboda yana son ki, ke da ni ake so haka ai da na warke”
 
“Miyasa ba zaki ba shi kanki ba idan gaskiya ne, sai ni kike turawa kuma na fada miki aure zan yi amman ke da shi kun kasa fahimta, so kike na fasa auren na cigaba da wannan shiriritar ne ko kuma so kike na cigaba da yin abun da nake da aure?”
 
“Na dai babu bako a cikin abun da kika ambata yanzu, kin yi karuwanci a lokacin da igiyar aure take kanki ai, kuma kike dauke da cikin Faruk ma, kuma kin kashe aure kin yi karuwanci kuma kin samu biyan bukata to miye bako a ciki? Ni kina ganin idan ina da value da za so mu'amala da ni zan tsaya ina rarrashinki ne?”
 
Baturiya ta yi mata kallon rashin fahimta.
 
“Ban gane ba”
 
“Uhm. Baturiya shi wannan kasuwancin da kike gani yana da wani limit idan ka wuce wannan limit din,to zaka daina samun riba ne za a daina yayinka sai dai ka laba da rigar wasu kana samun biyan bukata, kamar yadda nake yi a yanzu, ke yanzu tunaninki ba baki cewar Alhaji Idris ya gama yayi na ba ne shiyasa nake kawo masa wasu?”
 
“Amman kuma shi ne ni kike neman ki jefa ni a cikin wuta? Abokin mutuwa kike nema? So kike ni ma na yi expire na dawo  kamar ke na rasa madafa? So that mu zama Magajiya da kawar magajiya? Haba Ramlee!”
 
“Ya kika magana kamar kin manta wacece ni Rafi'a, ni fa na tsamoki daga bakin talaucin da kike ciki a wacan kangon gidan na maida ke mutum har kika hadu da Fahat din da kika min wannan haukar saboda shi”
 
“Aa ni tun kamin aurena ya mutu na hadu da Fahat, baki san inda na hadu da shi ba, ba ki san komai akan alakarmu ba”
 
“Okay fine amman dai ni na wayar da ke har kike wannan rawar kan ko? Har kina fada min na rasa madafa”
 
Baturiya ta sauke ajiyar zuciya.
 
“Amman Ramlee kina ganin ina cikin matsala a maimakon ki sama min mafita sai ki bijiro min da wata maganar ta dabam”
 
“Idan mafita kike nema ai kin san yadda zaki nemita, kuma kin san inda zaki same ni mu yi magana, ba wai ki fito haka kai tsaye ni tsaye ba?”
 
“Ki yi hakuri ba zan sake ba”
 
Baturiya ta fada ba dan ranta ya so ba, sai dan ganin yadda ran Ramlee ya bace, gudun kar ta kullace ta da wani abu, domin ta san Ramlee da mugun abu, daman kuma karuwai su gaji cuta da hassada.
 
“Ki je ki yi shawara akan abun da na fada miki, domin ba zaki barki da Alhaji yana damuna da maganarki ba, ya riga ya kwallafa rai akanki”
 
“Shikenan, zan yi tunani akai”
 
Ta bude motar ta fita sannan ta rufe tai tsaye tana kallon motar dake tafiya har ta daina hangota a layinsu.
 
 
 Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
 
“Ba saki hada ni da wata matsala ba, ina fama da ta Fahat ki kara kin da ta wani banzan tsohon mazinaci da be san mutuncin kansa ba balle na iyalinsa, zan yi magana da shi ai, dole na ja masa kunne kuma na shata masa liyi, ai ke dole ki haukace saboda kina samu kudi da ni a wannan bakar sana'ar taki, gashi nan garin bakin kwashe kwashenki kin hada ni da yayana”
 
Sai da ta gama fadanta sannan ta juya ta koma cikin gidan, iyakar kokarin da tai na kawar da bacin dan da yake fuskarta ne gudun kar Umma ta gane wani abu. Da sallama ta shiga yana kirkiron murmushin karfin hali.
 
“Fahat din ne?”
 
Umma ta tambaya.
 
“Eh shine”
 
“Amman fada muka yi ne? Ko kuma me? Na ga idan ya zo ai wayarki yake kira”
 
“Ni ma haka na ce masa, sai yace min yau wai haka ya ga dama, wai yayi zaton ana aikowa kawai zan fito ba tare da na tambaye waye ba”
 
“Ashe kara da aka tambaya”
 
“Wallahi kuwa da na jawa kaina fitina yau”
 
“Toh ya kuka yi da shi?”
 
Umma ta tambaya domin a saninta Baturiya ta fada mata cewar iyayensa basa son aurensa da ita.
 
“Umma bari na dawo mu yi wannan maganar yanzu dai bari na tafi gidansu Maman Ummi ta kira ni a waya wai tana son ganina”
 
“Okay to ki gaishe ta”
 
“Okay zata ji”
 
Ta amsa sannan ta koma cikin dakin ta dauko jakarta ta sakala ciki hijab saboda kar Umma ta gane cewar nesa zata je, sannan ta dauki wayarta ta fice daga dakin ta fito falon tana sakar kallon Umma har ta fice tana fadin.
 
“Sai na dawo”
 
“To Allah ya tsare, tun da na ga fuskar a sake na san akwai labari mai dadi ai”
 
Umma ta karasa tana dan murmushi, domin rabon da ta ga Baturiya a irin wannan yanayin tun daga lokacin data fada mata cewar iyayensa basa son ya aureta. Baturiya na samu ta fito ta ari kafa tana ta zuba sauri, sai ta karya kwana sannan hankalinta ya kwanta ta ciro wayarta ta nemi number Alhaji ta aika masa kira. Few seconds yai picking muryarsa cike da nishadi.
 
“Hello Hajiya, ina ta kira ana min ganya daukar wayar ma sai an ga dama”
 
“Alhaji kana ina?”
 
“Lafiya dai?”
 
“Lafiya kalau yanzu Ramlee ta zo min da wata magana shiyasa nake son ganinki ina son mu yi magana akai”
 
Yayi murmushi mai sauti irin na jindadi.
 
“Kin gan ni nan office yau aiki ya rike mu”
 
“Fada min inda kake zan so na same ka”
 
“Gurin aiki ne fa?”
 
“Eh ai magana kawai zan yi da kai”
 
“Ki Samina naka, kusa da wani gidan sojoji zaki ga wata matuwar ma'aikata kina isowa gurin ki tsaya bakin gate ki kira zan aiko a shiga dake ciki”
 
“Toh”
 
Ta kashe wayar, ta cigaba da tafiya yana yi yana baigawa ko zata samu Napep din data fito daga liyinsu ko kuma wanda zata biyo gaba ba, amman bata samu ba hakan ya sa ta tari mai achaba ta fada masa inda zai kaita ta hau babur din. Sai da su kai nisa sannan ta tuna bata dauko facemask dinta ba, sai dai tunawa da ba wani mugun guri zata je ba yasa hankalinta be tashi sosai ba.
Tafiyar minti talatin da biyu suka isa gurin sai ta sauka achaban ta bude jakarta ta dauko kudinsa ta mika masa, yana kokarin bata canji ta ce.
 
“Bar shi kawai tafi da shi”
 
“Okay na gode sosai”
 
Ta koma gefe tana hango cikin ma'aikatar kasancewar gate din a bude yake kuma irin wanda ke bawa na waje damar ganin na ciki ne, kamar yadda na ciki ke gani na waje. Kiransa rai a waya ta fada masa cewar tana waje gurin gate din.
 
“Okay koma kusa da security ki tsaya wani zai zo ya shigo dake yanzu nan”
 
“Toh”
 
Ta amsa sannan ta kashe wayar, ta koma kusa da su tai musu sallama suka amsa ta fada musu wani ne yace ta jira shi a nan zai aiko a shiga da ita. Bata wani dade tana jira ba wani ya iso gurin da kafa ta gaisa da su sannan ya kalleta ya ce.
 
“Ke ce Baturiya”
 
“Eh ni ce”
 
“Biyo ni muje”
 
Ta bi bayansa yana gaba tana biye kanta a kasa domin bata son ta ga wanda ta sani ko kuma wanda ya santa ya gane ta, bata daga kanta ba har suka shiga ciki, musamman ganin gurin ma'aikata ce mai cike da jama'a. Kasa kasa take kallon kowa har suka haura sama hawa na biyu suka shiga wani karamin office dake dauke da mutum daya, wato Sakatarensa sannan suka ya tsaya daga nan ya nuna mata office dinsa.
 
“Ga office din can”
 
“Okay”
 
Ta fada sannan ta doshi kofar, ta tura ta shiga tun kamin ta rufe kofar ya mike tsaye yana kallonta fuskarsa dauke da annashuwa.
 
“Maraba maraba da zuwa”
 
Maida kofar tai ta rufe, ta karasa inda yake fuska ba yabo ba fallasa.
 
“Gaskiya Ramlee ta kyauta min yau, rabon da na yi arba da fuskar nan an kwana biyu, an bar ni nan sai hade yawu nake”
 
“Na zo nan ne saboda na yi magana da kai”
 
Ya nuna mata kujera.
 
“Zauna mana, zaki iya fadin maganarki, idan ka san wanda zata daga min hankali ce ki rike abun ki sai mu je guest house mun kebe abun mu, saboda nan kowa zai iya shigowa at any time”
 
Magana yake yana wani kashe mata ido kamar tsoron shegen. Sai ta tabe baki
 
“Da yake baka san mutumcin kanka ba, shiyasa zaka lake ka takurawa kanka cewar sai ka yi mu'amala da karamar yarinya sa'ar yarka irina, wai Alhaji ban fada maka cewar zan yi aure ba? Ban fada maka cewar ni a yanzu na daina wannan bakar sana'ar ba? Amman ka nace sai ka yi mu'alama da ni har kana neman haka ni da Ramlee”
 
A take murmushi da annashuwar dake fuskarsa ya gushe. Sai dai hakan be saka ta fasa fada masa abun da tai niya ba cikin daga murya ta ce.
 
“Kana tunanin dan ka yi min albishir da gida da mota zai saka na fasa auren wanda zan aura saboda kawai na cigaba da mu'alama da kai? Ko kuma kana tsammanin zan cigaba da mu'amala da kai bayan aurena ne? Wai kai da tsufanka har da hurhura amman idonka ya rufe baka ganin komai sai...”
 
Bata karasa ba ta tsayar da hannunta ta da take nuna shi da shi, jin an bude kofar dakin

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login