Showing 297001 words to 300000 words out of 332834 words
rawa ta saka talkamin Umma ta fice daga falon zuwa gate ko wayar bata fito da ita ba, tsabar zumudi da rawar kafa Fahat ya turo mata sako cewar yana waje yana jiranta akwai maganar da zai yi da ita.
*_(Kun ga Labarin Aminatu da Faruk? Wallahi True life ne, amman na canja abubuwa da dama akai, but cikin kankanen lokaci Allah ya canja masa rayuwa)_*
_______________________________
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
Tsaye tai bakin gate din with shock tana kallon Fahat bata yarda da gaske yake ba har sai da ta ganshi. Sai dai ga mamakin sai tana ganin wani mai kama da Faruk a kusa da shi rike da hannun Sultan, ko kadan gabanta be fadi ba domin bata yarda Faruk ne a kusa da shi din ba, ta fi kyautata zaton aljanine yai mata siffarsa, ko kuma idonta ne suke mata gizo saboda halin data shiga na kaunar Fahat. Tafiya ta fara yi a hankali har ta isa kusa da inda suke tsaye but still tana ganin Faruk. Lumshe ido tai ta bude a zatonta zata daina ganinsa ne sai ta ga yana nan a lokacin ne hankalinta ya fara tashi ta maida idonta akansa tana kallonsa kamin ta mika hannu da zimmar taba fuskarsa domin tabbatarwa idan shi din ne ko gizo idanuwanta suke ma. Jin tai an buge mata hannu da mugun karfi, muryar Fahat ta daki dodon kunnenta.
“Da gaske shi ne mijin na ki kenan?”
Ta kalli Fahat sannan ta sake kallon Faruk da sauri, sai kuma ya sauke idonta gurin Sultan dake rike da hannun babansa.
“Far... ”
Ta kasa furtawa, sai ta sake maida dubunta gurin Fahat dake mata kallon tsana da mamaki. Ta nuna masa Faruk, so take ta tambaye shi a ina ya san Faruk a ina suka hadu ya akai sukai hadu amman ta kasa furta komai sabida tsabar mamaki da kidemiwa. Sai hade yawu take da karfi tana tara wasu tana hadewa.
“Faruk...”
Ta furta daker hawaye na saikowa idanuwanta. Sai yai murmushin takaici.
“Rafi'a, ashe baki mantawa ni ba, na dauka sunana ma ba zaki iya furtawa ba”
Faruk ya fada sai Fahat ya dora da na shi.
“Baki ji kunyar kanki ba? Kin boye cewar kin taba aure ashe har da ďa kina da! Kuma a haka kike biyewa rudin zuciya kina zina”
Faruk ya kalleshi da sauri cike da mamakin yadda akai ya sani, Fahat ya daga masa kai.
“Yes na sani, saboda ta yi mu'amala da wani na kusa da ni, a haka kuma take shirin aurena”
Faruk ya bude motar Fahat ya kalli Sultan dake tsaye yana kallon Baturiya kamar ya ga bakonsa.
“Sultan shiga mota”
“Dady ba Momy ce wannan ba”
Baturiya ya lumshe ido hawaye masu zafi na sauko mata. Har cikin zuciyarta ta ji kalmar da ya ambace da ita da Momy. Faruk kuma ya hade abu da karfi ya daka masa tsawa.
“Shiga na ce”
A take jikinsa ya fara rawa, sai ya shiga motar da sauri yana fashewa da kuka. Faruk ya kalleta hawayen bakinciki na taruwa a idonsa.
“Ban tana jin nadamar wani a rayuwata, kamar yadda nake jin nadanar aurenki ba, taya zan kalli mace kamar ke na kirata uwar da na? How? Wani irin kwadayi ne a zuciyarki Rafi'ah? Taya zaki bata rayuwar yaron da be san komai ba? Ta hanyar aikata mummunan aiki irin wannan? Saboda wannan abun na rabu dake, kuma na ki na fadawa kowa dalilina na rabuwa da ke, kin san saboda me?”
Ta bude ido sai dai hawayen dake sauko mata sun hanata ganin fuskarsa da kyau.
“Saboda d'ana, bana son a kalleshi ace uwarsa tana aikata wani abun da idan ya girma ya ji zai ji bakinciki, yace mahaifinsa be zaba masa mata ta gari ba. A rayuwata ban taba jin na tsani kowa ba, amman ke na tsane ki Rafi'a na tsaneki fiye da yadda na tsani mutuwata”
Ta busar da iskar bakinsa a hankali, sannan ya cigaba.
“Daman na zo nan ne saboda na tambayi adadin abun da kika kashe na barinki da dawainiyar cikina da na yi, but it seems like kin zubar da cikin ma, har kina shirin auren Fahat.. Kuma... ”
Faruk ba karasa ba Fahat ya tari numfashinsa yana daga hannanyensa sama.
“No no no... A a a, wannan da ne, yanzu kam Allah ya tsare ni da bakar macijiya”
Ta maida dubanta gurin Fahat tana jin kamar ta hade zuciya ta mutu, tana jin kamar kasa ta bude ta shiga, ina ma ace ba a halicce ta kamin zuwan wannan ranar.
“Wata kila nan gaba idan Sultan ya mallaki hankalin kansa zai nemi sanin mahaifiyarsa, amman for now ina son ki nisanta kanki da shi, kamar yadda kika nuna masa baki kaunarsa saboda talaucin ubansa, ina daf da sama masa wata uwar mai tarbiya, kuma zan nisanta ki da shi zan koma da shi a inda na samu aiki Lagos na mu zauna can, cikina kuma da kika zubar na barki da Allah”
Yana kaiwa nan ya juya ya bude motar ya fito da Sultan dake kuka ya dauki ledarsa, ya rika hannun Sultan din suka nufi titi. Fahat ya bishi da kallo har sai da yai nisa sannan ya kalli Baturiya.
“Yanzu kin yi farinciki? Kin guji mijinki da danki saboda abun da ba su suka bawa kansu ba? Kin kyamaci mijinki saboda jarabawa ta talauci? Kenan ki nima saboda dukiyata kike so na”
Ya girgiza mata kai yana murmushi.
“Kin ga wancan mutumen da kike gudu? Ya samu aiki, kuma kamin samun aiki ya tafi nema wata kasar, kuma ina kyautata zaton ya samu abun da zai canja masa rayuwarsa, wace riba kika ci kenan? Kin samu zunubin zina, kuma baki yi hakuri cin jarabawar da Allah yai miki ba na aura miki talaka balle ki kai ga cin ribar hakurin, kuma kudin da zaki samu ba zai amfana miki komai ba saboda ba ta hanyar halal kika samu ba, ba zai taba miki albarka ba”
Ya juya a hankali ya zagaya gurin driver seat ya bude ya shiga ya zauna sannan ya sauke gilashin motar ya kalleta.
“Zaki iya komawa, daman na kiraki ne saboda mijinki yana son magana da ke, i mean tsohon mijinki...”
Ya daga glass din sannan yai reverse ya fisgi motar yana watsa mata kura ya bar line da gudu. A maimakon ta koma gida sai ta cira kafarta da tai mata mugun nauyi ta fara takawa a hankali ta nufi hanyar fita daga layin, wani abu take ji ya tsaya mata a zuciyarta kamar mashi, ta tare mata numfashi dake fita ta hancinta sai ta baki take samun damar numfasawa, wani abu take ji kamar kuda yana mata yawo a cikin kai, karar ababen hawa tana shiga da fita a cikin kunnuwanta da wani kalar sauti da bata taba saninsa ba. Tafiya kawai take badan ta san inda zata je ba. Sai da tai nisa sosai da unguwar sannan ta samu simintin wani gida ta zauna tana ta murda yatsun hannunta hawaye sai zuba suke mata. Ta zauna a gurin har na tsawon awa daya bata komai sai hawaye, maganar da Fahat da Faruk sukai mata yai ta maimaita kansa a cikin kanta. Duk yadda ta so taga komai daya faru ya zama mafarki ta masa.
“Ni wai... Ni... Ni... ”
Ta fada tana nuna kanta, sai kuma ta mike tsaye ta juya hanyar data fito ta fashe da kuka.
“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un garin na shigo tara ni Baturiya na lakace”
Ta dora hannu saman kai kamar ta manta a hanya take. Tana tafe tana kuka kamar karamar yarinyar mutane sai kallonta suke.
“Ke lafiya”
Wani mutumen ya tambaya, ko kadansa ba tai ba, ta cigaba da tafiyarta tana fadin ta shiga tara. Haka ta shiga gida da hannu saman kai tana ihu da kokuwar ta shiga uku, a tsakar gidan ta zube ta fashe da sabon kuka.
“Umma na shiga uku na lalace, Umma rayuwata ta kare, Umma na shiga tara na lalace, shikenan na gama rayuwa Umma”
Umma ta fito daga bandakin da sauri ta nufo tsakar gida ta dafa Baturiya cikin tashin hankali.
“Lafiya.... Miya same ki?”
“Komai ma ya same ni Umma ya same ni, Umma rayuwata ta lalace, Umma shedan da zuciya sun kai ni ga halaka...”
“Miya faru?”
“Umma Faruk....Fahat.... ”
Ta kasa furta komai, sai ta kuka take, Umma ta rikata ta mikar da ita tsaye suka nufi falon. Saman kujera ta zaunar da ita ta zauna kusa da ita ta kwanto da ita jikinta.
“Rafi'a kina son wahalar da kanki sa saboda maza, haba dan Allah, ji yadda kike kokarin fita hayyacinki saboda namiji”
“Umma ba zaki gane ba, na sake reshe na rika ganye, Umma duniya ta yi min juyin masa, Umma na rasa komai yanzu, asirina ya to nu, Ramlee ta kai ni ga halaka, zuciya ta kai ni ga nadama da bakinciki....Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un Umma...Umma mutuwa zan yi”
Wani irin kuka take na fitar hankali, jikin Umma yayi sanyi sosai jin ta ambaci Ramlee hakan na nuna akwai wani abu a kasa, domin tun tana budurwa aka rabata da abota da Ramlee.
FAHAT POV.
Har ya isa gida hamdala yake yi ma Allah, da be saka ya auri Baturiya ba, da ya aureta da ya jawa kansa bala'in da be san karshensa ba. Lokuta da dama mutum ka so abu ya zama ba alheri ne a gurinsa ba, ko kuma ya ki abu kuma ya zama alheri a gurinsa. Kamar yadda be zama lallai idan ya ki ya zama alheri ko kuma idan ya so ya zama sheri.
This is the first time da yake jin farincikin rashin auren Baturiya, domin a yanzu nw true color ta ya kara fitowa fili. A harabar gidan ya faka ya bude ya fito, sai kuma ya koma ya dauko ledar turaren da ya siyo sannan ya rufe motar ya nufi entrance din cike da kuzari, tura kofar yai ya shiga, kamshin turaren wuta da sanyi ac suka masa lale marhabun, maida kofar falon yai ya rufe ya nufi dakin mahaifiyarsa, zaune na same ta saman carpet hannunta rike da carji tana sanye da Hijab, da yau ta yi latti sallah la'asar. Kusa da ita ya karasa ya zauna yana kallonta cike da kaunarta
“Mommy sallah kika yi?”
“Eh, yau na yi latti ne, ka siyo surarukan”
Ya matsar da ledar kusa da ita.
“Ga kamshi ma kina ji”
Ta yi murmushi tana jin dadi.
“Yau ya kamata ka tafi ko sai gobe”
“Duk ranar da kika ce Mommy, ni yanzu bana ja da ke, kawai ina fatar wannan zabin da zaki min ya zama alheri”
“Zai zama Inshallah, yarinya ce mai kyau ga natsuwa, sai dai ba wata babba ba ce domin yarinya ce bana zata gama secondary school”
“Indai kin yarda da tarbiyarta bana da matsala ni”
“Gaskiya ban tana jin iyayenta ko su yayanta da wata matsala ba, kuma an manyan mutane ne”
“Ba matsala Mommy, duk yadda kika ce haka za'ayi”
Ta yi murmushin jindadi.
“Allah yai maka albarka Fahat”
“Ameen”
Ya fada yana kwantawa a carpet din ya dora kansa saman cinyarta.
FARUK POV.
Yana janye da hannun Sultan dake kuka yana tafiya, zuciyarsa na tafarfasa kamar zata kona kirjinsa. Ta dayan bangaren kuma yana jin tausayin dansa da be dacen uwa da gari ba. Tafiya yake yana jin kamar ace zai iya dawo da baya ta cire Baturiya daga rayuwarsa. Wata kyakkyawar mota ce ta faka gabansa kadan, matukiyar motar ta fito sanye da abaya ta karaso inda suke da saurinta.
“Miya samu Sultan?”
Sai a lokacin da tai maganar sannan Faruk ya kalleta, ya gane fuskar da ya sani ce.
“Ba komai”
“Ba komai haka kawai zai yi kuka”
Faruk yayi gaba kamar ba zai amsa mata ba, sai ta saka hannu ta rika hannun Sultan, hakan ya saka Faruk juyowa ya kalleta ganin yana jan hannun Sultan tana jansa.
“Sake shi mana”
“Ba zan sake ba, yaro yana kuka kana cilasta masa tafiya haba Faruk”
“Gida zamu je, sake shi na ce”
Bata ce masa komai ba ta saka hannu ta dauki sultan din wanda hakan ya cilasta masa sakin hannun dansa, ya bita da kallo, ta rumgume Sultan tana rarrashinsa, can kuma ta dauke shi ta nufi motarta da shi ta saka shi front seat ta zagaya driver seat ta shiga ta tashi motar tai gaba ta bar Faruk tsaye yana kallon ikon Allah. Da farko abun haushi yake bashi but this time around abun da tai ya saka shi dariya.
“Yarinyar zata kashe ni”
Ta fada with smile, sannan ya karasa gurin titin ya tari abun hawa ya hau. Mama na ganinsa da ledar siyayya ta san ko dai be je ba, ko kuma yaje ba tararda ita ba, ko kuma ya kai ta ki karba.
“Siyayyar da kai mata ne?”
Mama dake zaune Rukaiya na matsa mata kafafuwanta ta tambaya tana kallon ledar da ya aje kusa da shi. Ajiyar zuciya ya sauke yana girgiza kai irin na takaici da bakinciki sannan ya labartawa Mama abun da ya faru, ba karamin mamaki tai ba jin cewar Baturiya tana shirin yin aure, sai dai ko kadan batai mamakin ace Baturiya ta zubar da cikin ba daman can ta ayyana hakan a ranta.
“Amman daman ko da ta fita gidanka tana soyayya da shi ko kuma yanzu daga baya ta same shi?”
“Wata kila tun tana gidan ne, wata kila kuma bayan ta fita ne, amman shi ba san ta taba aure ba ma”
“Allah ya tsare mu da aikin dana sani, kuma ya ba mu ikon cin jarabawa mai kyau ko marar kyau”
Rukaiya da Faruk suka amsa da amin, sannan Rukayyah ta dora da tambayar Sultan.
“To can ka bar mata Sultan din?”
Faruk ya ce.
“Haba dai ya za'ayi na bar mata shi? Matar data gagara takowa ta ga danta ma, kike tsammani ni idan na kai mata shi zan baro shi can? Boye ma fa take bata son asan tana da da, kuma gidan da bana tarbiya ba, bari dan ka ya zauna a can ai sai dole”
Mama ta ce.
“To ya za'ayi tun da an hada jini, sai hakuri da addu'a kawai, ina ka bar shi?”
“Yana gurin yarinyar nan Ramla”
Mama da Rukaiya suka hada baki gurin cewa.
“Ramla kuma? A ina kuka hadu”
“A hanya kuma ta nuna min fin karfi ta tafi da Sultan”
Mama ta yi murmushi.
“Allah ya hada jininta da kai, kai kuma ka gagara gane manufarta”
“Mama kenan, kai na nunawa mace kauna ya aka kare balle ita ta nuna maka”
“To ai ta nan zaka gane banbancin, idan mace tana sonka to kwanta ka huta kawai, balle wannan da take yar gidan masu hannu da shunu kaga babu abun da zai burgeta, sai da ma ta taimaka maka wani bangaren, kuma ka san dai ba dan ta rasa miji ba, yadda take da kyau nan Maa-Shaa-Allah ga kuma ubanta da kudi ai dole za a so ta kam”
Rukayyah ta kalli Mama dake maganar ta ce.
“Kuma ni dai wallahi tana burge ni, bata da girman kai gata kyakkyawa, ranar da muna hira da ita cewa min tai wai ita duk a cikin samarin da suke zuwa gurinta babu wanda ya kwanta mata, tace wasu yayan manya mutane ne, wasu kuma za su so ta ne saboda kudin mahaifinta ko kyauta, ita tafi son wanda zai so ta tsakani da Allah”
Faruk ya mike tsaye yana fadin.
“Ba daga nan take ba, ba a fuska ko kalamai ake gane mutumen kwarai ba, sai da a kwakwatanta, kuma a kyautata zato, amman mutane da yawa fuskarsu bata nuna abun da ke zuciyarsu har sai an zauna da su”
“Amman dai wannan muna kyautata mata zato yaya, da zaka bada kai da buri ya hau”
Mama ta kara da cewa.
“Ni da zaka bi shawarata da ka auri yarinyar nan, ta kwanta min a rai, kuma kaga faduwa ta zo daidai da zama, tun da ga aiki ka samu sai aure ka tafi da matarka can”
Wannan karon dariya yai yana jin yadda Mama da Rukaiya suke lissafin duna.
“Mama kenan, yarinyar nan fa ba cewa tai tana so na ko ina sonta ba, amman har wani lissafin aure kuke”
Suma dariyar sukai. Mama tace
“Da ka bata dama ai sai komai ya kama, ni da zaka dauki siyayyar nan ka kai mata ma daga can ka karbo Sultan din da ka burge ni”
Yayi murmushi.
“Wannan dai ya zama na ku, ita kuma zan siya mata wani abun idan zan karbo shi”
“Yauwa Allah yai maka albarka”
Ya amsa da Ameen sannan ya fice. Sai bayan sallah Magariba, ya koma Super market din da yai siyayya a dazun ya sake siyen turarukan masu kyau da dadin kamshi, ya siye chocolate masu tsada ya hade a leda daya. Bayan ya biya ya fito ya nufi gidansu, kamar yadda akai masa wacan karon da ya zo wannan ma sai da suka so hana shi shiga, sai ya fada musu Ramla yake son gani. Dayan ya kirata a waya ya fada mata sai da ta bada izini sannan wani yai masa iso har cikin falon gidan, a lokacin ne ya gane wacan karon karramashi tai da ta kai shi a wani falon na dabam da ba wannan ba, domin wacan ya fi kyau da tsaruwa nesa ba kusa ba.
Zaunawa yai ya ciro wayarsa yana ragewa kansa lokaci kamin ta fito.
“Allah yasa dai ba Mahaifina ka zo nema ba, domin baya nan”
Juyowa yai a hankali ya kalli inda Ramla take tsaye tana masa maganar, sai yai murmushi.
“Wannan zuwan ba na Abbah ba ne”
“Okay Sultan ka zo dauka kenan, baya ka gama saka shi kuka?”
Ya sake yin murmushi, sai ta karaso cikin falon ta zauna nesa da shi.
“Ni ai na dauka baka son