Showing 216001 words to 219000 words out of 332834 words
ya dade be yi ba ita kanta sai da ta kalleshi domin be taba ganin yayi irin wannan dariyar ba. Aje plate din yai ya kalleta yana tauna naman.
“I love you girl”
Ita dai sai kallonsa take da mamaki.
“Ba sai karami ko jariri ake cewa Babe ba, za ki iya kirana da Babe idan kina so nima zan iya kiranki”
“Kuma ka amsa?”
Ya kai hannu ya fika fuskarta.
“Why not? Dadi ma zan ji”
Ta kawarda fuskarta daga rikon da yai mata ta mike tsaye sai ya rikota ua janyota da karfi.
“I can't believe wai ni mai mata ne a yanzu, ina da aure, matata ce wannan, ban san haka ake ji ba da na yi aure since”
Ya kama hijab dinta zai cire sai ta fara kokuwa da tana son hana shi.
“Ki sake jikin ki idan kina tare da ni, mijinki ne ni, aikina na kula da lafiyarki da komai na ki i feel proud Wallahi”
Ya cire mata hijab din da karfi sannan ya rumgume ta, sai ta saka hannayenta ta rufe fuskarta. Murmushi yai ya kama hannayen nata ya sumbanta sannan ya sake ta ta mike tsaye da sauri ta dauki Hijab din ta saka ta haye saman gadon ta zauna. Kamar hadin baki tana zaunawa Kabir ya shigo dakin rike da wasu files.
“Good morning”
Talba ya mike tsaye ba tare daya amsa ba.
“Ya mai jiki?”
“Ta ji sauki, i think yau zaka sallame ta ai ko?”
“Definitely Yes”
Ya fada yana mika masa takardar sallamar.
“And hoton da akai mata ya nuna bata da wata matsala”
Talba ya dafa shi.
“Thank You Kabir”
“Ur welcome, amman a can zaka zauna da ita?”
“Yes, bana son na musa ma Momy ne”
“Yeah but zan iya magana da ita, no Daddy ma zai iya tsaya maka ai, kana nuna masa baka so zai hana”
“Zata ga kamar ban yi mata biyayya ba, kuma zata jidadi ba, na yi aure a boye yanzu kuma tana bani umarni ina kin yi ba zata jidadi ba”
“Amman baka ganin zai zame mata takura ita?”
Talba ya juya ya kalleta sannan ya kalli Kabir.
“For now ban sani ba, amman idan na ga alamar zata takura ba zan barta ta cigaba da zama haka ba”
Kabir ya gyada masa kai sannan ya karasa kusa da Aminatu.
“Madam, an sallame ki zaki dawo gidanmu da zama yanzu, ina fatar dai kina so ko?”
Ta kalli Talba daya hade mata fuska kamar ba shi ba, ba dan komai ba sai dan baya son ta bawa Kabir din fuska. Da sauri ta sauke kanta kasa. Sai yai murmushi ya juya ya fice.
_______________________________
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
Ba su bar asibitin ba sai da ya kira Momy ya sanar mata ta aiko musu da Zulai saboda ta kwashe kayan da suka yi amfani da su, Zulai ce ta kwashe komai ta saka a motar Talba, bayan ta fita ya kalli Aminatu.
“Ta so muje”
Ta kalleshi kamar zata yi kuka.
“Tsoro nake ji”
“Nooo babu abun da zai same ki gidanmu ne fa, kuma nima ina cikin gidan, ki kwantar da hankalinki kinji”
“Toh”
Ta amsa hawaye na sauko mata sai ya saka hannunsa ya shafe mata sannan ya rika hannun nata suka fito tare, yana rike da hannunta har gurin motarsa, front seat ya bude mata ta shiga ta zauna, ya rufe sannan yai ma Zulai alama data bude back seat din ta zauna. Sai ta mika masa envelop din hannunta.
“Gashi wani mutum yace na baka wai ka bawa Leila”
Tsayawa kallon Envelop din Talba yai kamin ya juya yana kallon harabar.
“Waye ya baki?”
“Wallahi ban san shi ba, yana dai sanye da mask da bakin gilashi kuka kansa da hula”
Ya sake kallon Envelop din sannan ya kai hannu ya karba.
“Me yace miki?”
“Sallama yai min na amsa ya mika min wannan yace na bawa mai motar nan ya bawa Leila”
“Ta ina ya bi?”
“Mota ya shiga ya wuce”
Ya karba ba tare da yace mata komai ba ya zagaya bangarensa ya bude ya shiga, sannan ita ma ta shiga. Gaban motar ya aje envelop din wondering miye a ciki, sai da yai ma motar key yai reverse ya fita daga gurin sannan ya kai hannunsa ya kama hannun Aminatu ya rike sai da tai kamar zata fisge hannu saboda ganin Zulai na bayan motar, sai ya girgiza mata kai a dole ta kyale. Zulai kam dadi ta ji ko ba komai ta san za a takurawa Leila ita da Mairo har tsegumin suka yi.
Da hannu daya yake driving hannunsa daya na rike da hannun Aminatu har suka isa gida ya faka dai dai kofar falon.
“Zulai fitar mana da kayan nan”
“To ranka ya dade”
Ta bude motar ta fita sannan ta fara fita da kayan sai da ta aje komai a wajen motar sannan ta rufe motar. A lokacin ne ya kalli Aminatu.
“Ki sake jikinki, ki dauka nan din ma kamar gidanku ne, and idan wani yai miki wani abu ki fada min kinji?”
Ta yi shiru, sai ya daga dayan hannunsa ya nuna mata part dinsa.
“Kin ga bangarena can, kina turawa zaki shiga ciki”
Ta kalli gurin kamin ta juya ta kalli Momy da Leila da Madina da suka fito daga kofar falon suna kallonta, sai kuma ya juyo ta Talba, ya sakar mata murmushi. Ya saki hannunta ya dauki envelop din ya fita, da gangan Aminatu taki fita daga motar ta zauna a ciki tana kallonsu har sai da ya zagayo ya bude mata.
“Fito”
Sannan ta nasa kafarta a waje ta fito ya rufe motar, kana yai mata iso da hannunsa.
“Bismillah...”
Ta fara takawa a hankali Talba yana kallon steps dinta har ta hau saman entrance din. Leila ta hade yawu tana kallon Aminatu zuciyarta na bugawa da karfi, Madina kam ji take kamar data bude baki hayaki ne zai fito saboda yadda wutar bakinciki da kishi dake cin zuciyarta, musamman yadda ta ga Aminatu ta canja ta yi kyau sosai kamar ba ita ba.
“Sannu da zuwa”
Leila ta fada tana kallon Talba, sai ya amsa mata da kai, Madina ta kalleta da mugun mamaki, Momy ma murmushi ne fuskarta.
“Sannu da zuwa sukarmu”
“Ina wuni”
Aminatu ta gaisheta sai ta amsa tana murmushi.
“Lafiya Kalau Takwarata, amman a nan sai su maida ke Ummi ko Meena ko?”
Ta yi kasa da kanta bata ce komai ba. Talba ya mikawa Leila envelop din hannunsa.
“Wani yace a baki”
Tana kallon Envelop din sai tai baya baya kamar wanda tai arba da wani abun tsoro. Madina ta kalleta ta gefen ido kamar zata yi murmushi sai kuma tai saurin batsarwa.
“Wani wa?”
Momy ta tambaya tana kai hannu ta karbi envelop din.
“Ban san shi ba, Zulai ya bawa yace a bani na bawa Leila, ban san miye a ciki ba”
“Oo. Okay... Shi..ga da ita ciki, dakin data taba zama na sakan Mairo ta gyara mata shi”
Har Madina ta kai hannu ta kama hannun Aminatu sai Talba ya rigata rika hannun matarsa ba tare da tunanin komai ba, a ganinsa Leila ma tai haka wa kawayenta maza da ba muharramanta ba balle shi da take matarsa. Yana rika hannun nata yaja ta zuwa ciki juyawa tai tana kallon yadda ya rika hannun nata tana jin kamar tai haniniya tai cikinsu ta fisge hannun Aminatu daga rikon da Talba yai mata. Leila kam bata kula ba sai hawaye take domin gaba daya hankalinta a tashe yake, Momy ce kawai ta tsare Madina da ido tana karanta karantun da ita kadai take gane shi.
“Unko shiga cikin da Envelop din”
Leila ta kasa karbar Envelop din da Momy ke mika mata ta juya da sauri ta shige falon. Ganin haka yasa Madina ta fara takawa zata bi bayan Leila ba tare data juyo ba, sai Momy ta kirata.
“Madina...”
Sai ta juyo sannan ta amsa.
“Na'am”
Momy ta matsa kusa da ita tana mata wani shegen kallo.
“Stop playing this game...”
Madina ta yi ma Momy kallon rashin fahimta.
“Yes kin san abun da nake nufi, ki daina wasa da hankalinmu kina tsorata min ƴa...”
“Ban fahimta ba Momy”
“Kin san me nake nufi, kina wasa da hankalin saboda zuciyarki na raya miki zaki iya lalata alakar Talba da Leila ki kulla taki, kina son Talba Madina na sani”
“You are not make any sense right now”
Madina ta fada with shock. Momy ta yi murmushi.
“Na harbo jirginki, kuma ina gargadinki domin zaki jefa kanka a matsala ne kawai, domin ba zan zuba ido a kai yata a gidan yari ba”
“Momy kina magana da ni kamar kin manta cewar ni kawar Leila ce kuma aniyarta”
“Ban manta ba, shiyasa nake gargadinki, kin hada baki da mai gadina kina kara jefa kanki a halaka, make sure kin dawo da gawar Baaba a inda take if not...”
“Ban san wani mai gadin kika magana akai ba, ban san gawar da kika magana ba, I'm not heartless like you and your daughter da zaku binne gawa na bita na tone ya kamata ki san da wannan, kuma ni ba zan taba blackmailing din Leila ba har abada”
Tana kaiwa nan ta sauka daga entrance din ta nufi motar cikin bacin rai, miyasa Momy zata zarge? Tana kama sa makiyiyar Leila ne? Why her? Bata zargi kowa ba sai ita. Momy ta bita da kallo har ta shiga motar ta fice sannan ta juya ta koma ciki. Har tayi kamar ta shiga dakin da Aminatu take sai kuma ta nufi dakin Leila kai tsaye domin ta san yarta tana cikin tashin hankali a yanzu. Tun kamin ta tura kofar dakin ta shiga ta ji sautin kukan Leila. Da sauri Momy ta karasa kusa da ita ta kai hannu ta dago ta daga kwance da take tana rera kuka idonta har yayi ja.
“Hana Leila so kike ki tonawa kanki asiri? Tun kamin a karaso gurin kofar dakin nan fa ana jin kukanki?”
“Momy na fara gajiya, waye yake min wannan abun? Momy ko waye tona min asiri zai yi, bana son na tafi gidan yari Momy bana son na mutu, Momy ba da gangan na kasheta ba”
Momy ta yi saurin rufe mata baki.
“Ki daina fadar haka, ba zan taba barin haka ta faru ba”
“Momy duba abun da yake cikin takardar nan”
Ta fada tana nuna Momy envelop din, Momy ta juya ta kalli Envelop din, rigar Baaba ce dake kalar dankwalin nan da aka aiko mata wannan karon ma rigar da datti kuma da kasa a jiki. Momy ta karasa ta dauki rigar tana dubawa.
“Shiyasa nake kyautata zatona akan yarinyar Madina ita kadai zata iya haka”
“Momy to ina zata samu kayan Baaba”
“Wata kila ta hada kai da mai gadin ne ta fasa ramen ta dauke gawarta shi ne take amfani da tufafinta take tsorata ki, amman dai ko minene zan je yau zan samu wanda zai yanke mana kwadon bincika gidan”
Ta share hawayenta.
“Kar garin yanke kwadon kuma sirrinmu ya kara bayyana, Momy tsoro nake ji sosai”
“Ki saka a ranki, ko asiri ya tonu ko be tonu ba babu abun da zai faru da ke, kin fi kowa sani ni da mahaifinki ba zamu saka ido a kaika gidan yari ba alhalin muna da kudin da za su iya siye komai, dan haka ki kwantar da hankalinki kamar baki aikata komai ba okay”
Ta gyada ma Momy kai sannan ta kara share hawayenta.
“Ko ma waye zamu gano shi, dan haka ki watsar da wannan damuwar ki maida hankali kan aurenku da Talba okay”
Nan ma kan ta daga ma Momy sannan ta mike tsaye ta nufi bathroom ta wanke fuskarta, ta fito ta je gaban madubi ta shafa hoda saboda ta batar da fuskar kukanta. Momy na kallonta har tai ta gama sannan ta mike tsaye ta dauki envelop din da rigar ta nufi dakinta da ita, a inda ta aje dankwalin ta saka rigar sannan ta fito ta sauko kasa tana kwalawa Talba kira.
*** *** ***
A hankali ya cire bakinsa daga nata ya kurawa fuskarta da idanuwanta dake rufe ido, kamin ya kalli bakinta da take motsawa a hankali. Dagawa yai daga jikinta ya saki hannayensa daga rikon da yai musu. A a lokacin ta samu ta bude idonta ta sauke kasa, hannunta ya riko suka fito daga bandakin ya zaunar da ita gefen gado, shi ma ya zauna ya ciro wayarsa yana kiran Hajiya Laraba yana shafa kansa idonsa na gurin Aminatu dake hawayen, gaba daya abun da yai mata a yau ya tsorata fiye da ko yaushe daga sunan nuna mata bandaki sai ya rike kunkurunta ya hana fita tana mika hannu fa kwaci kanta sai ya mannata jikin tile din dake bandakin ya rike hannayenta gam ya hade goshinsu guri daya ta yadda ba zata iya motsa kanta ba, sannan yai kasa da bakinsa ya kama lips dinta ya fara kissing in a romantic way, ita kanta a yau ta ji ta a wani yanayi da bata taba jin kanta ba. Yana jin muryar Momy ya mike tsaye da sauri yana murza idonsa da dayan hannunsa wai ko idon nasa da suka canja launi za su dawo daidai, ya nufi window ya tsaya rike da wayar a kunne sai wani jan numfashin yake yana ajewa kamar mai yaki da wata dabba.
“Hajiya mun dawo gida, an sallame mu”
“Okay to yara za su shigo anjima za su zo da tufafinta da sauran kayanta, amman dan Allah ka kula da ita Talba kana ganin yarinyar nan marainiya ce kuma bata san kowa ba a gidan nan sai kai”
“In shaa Allah”
Ya sauke wayar sannan ya juyo ya kalli Momy dake tsaye bakin kofar dakin, daman ya ji lokaci data bude kofar dakin.
“Ka fada mata kar tace zata takura kanta da zaman daki ta rika fitowa falo tana zama tare da mu”
Momy ta fada fuska ya yabo ba fallasa, Talba ya kalli Aminatu.
“Kin ji maganar Momy ko? Idan kina so ki rika fitowa falo ko harabar gidan akwai kujeru a ko'ina zaki iya zaunawa ki huta”
Ita dai bata ce komai ba, har ya fice dakin Momy ta bi bayansa. Bangarensa ya koma yai sabon wanka ya shirya cikin wasu tufafin sannan ya fito ya shiga motarsa zuwa office.
Tun da Aminatu ta shiga dakin bata fito ba sai karfe uku na rana, shi ma saboda Momy ta aika Zulai tace ta kirata ta fito falo ta ci abinci rana. Kamar wanda aka cilasta haka ta fito falon tana sanye da short Hijab, sai doguwar rigar abaya brown color kanta a kasa har ta karaso inda suke zaune a dinning din. Amal ta tabe baki tana kallonta, Kabir ma kallonta yake shi da Leila Momy ce kawai bata gurin duk da kasancewar ita ta saka a kirata.
“Sai kin ja kujerar tukuna ki zauna, na san baki taba zaunawa a kujerar cin abincin ba”
Leila ta fada tana watsa mata harara Amal ta fara dariya da karfi sai Kabir ya daka mata tsawa.
“Ke...”
Ta rufe bakinta da sauri, Aminatu ta yi tsaye a gurin tana jin kamar ta juya ta koma dakin. Kabir na ganin haka ya mike tsaye yaja mata kujerar.
“Zauna”
Sai ta zauna amman ta masa daga ido ta kalli kowa. Kabir da kansa ya zuba mata abincin ya zuba mata drinks.
“Ya Kabir ka zuba mata a glass cup ai bata taba sha a ciki ba, zai iya faduwa a hannunta”
Amal ta fada, Kabir ya watsa mata harara.
“Idan na sake jin wata magana marar kyau daga bakinki sai na baki mugun mamaki, kun dauka abun da kuke yi mai kyau ne? Talba kuka muzantawa ba ita ba”
Amal ta mike tsaye sanye da uniform din islamiya.
“Ni dai na tafi Islamiya kar ace na yi wani abun”
Leila ta saka dariya tana cin abincin.
“Ke kike tsoron ace kin yi, mu kam komai ba ma gudu”
Ta karasa tana murmushi, Aminatu ta mike tsaye idonta tab da hawaye, Leila da Kabir suka kalleta.
“Zauna ki ci abincin ki mana”
Kabir ya fada, sai ta girgiza masa kai.
“Saboda ban saba a taburin cin abinci ba, kuma ba mu da kofin gilashi a gidanmu ba shi yake nufin idan na zo gidan wasu a wulakanta ni ba”
Tana fadar haka ta juya ta fito daga dinning area din ta koma dakinta, tana shiga ta maida kofar dakin ta rufe ta jingina jikim kofar ta fashe da kuka marar sauti. Kuka tai sosai har sai da ta gaji dan kanta ta shiga bandakin ta wanke idonta sannan ta hau saman gado ta kwanta.
Sai 4pm Talba ya shigo gidan, sosai ya so ya dawo da wuri gidan sai dai aiki ya rike shi, yana shigowa gidan bangaren Momy ya fara shigo saboda hankalinsa yana gurin Aminatu.
“Sannu da zuwa Babe”
Leila ta fada tana zaune kan sofa rike da remote. Be amsa ta ba ya kalli Mairo dake aikin fesa air freshener ya ce.
“Mairo mai sunan Momy ta ci abinci?”
Kamin Mairo ta amsa masa Leila tai murmushi ta ce.
“Yau kuma kunyar kiranta kake da Shalele? Bata ci ba, Momy ta ci a kira har ta fito sai kuma ta koma”
Dakin ya nufa, sai da ya fara knocked sannan ya tura ya shiga ya maida kofar ya rufe, wani irin abu marar dadi ne ya ziyarci zuciyar Leila, tashi tai taje kofar dakin ta labe ta dora kunnenta saboda ta ji abun da ake fada. Aminatu na ganin Talba ta juya kai daga kwance da take ruf da ciki ta bashi baya. Zagaya yai gefen da fuskarta take yana karantar idonta.
“Kuka kika yi?”
Sake juyar da fuska tai sai ya hau saman gadon gaba daya