Showing 246001 words to 249000 words out of 332834 words

Chapter 83 - Bakar wasika Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

65580

ya same shi amman a haka ya bi bayan wanda ya sace ni, saboda kawai ya gane waye ya hukunta shi, Wallahi da zan iya da sai na cire masa ciwon nan gaba daya, musamman a yanzu da nake da labari mai dadi da zan bashi....”
 
Ta karasa hawaye na sauko mata. Wani irin bugawa zuciyar Leila take tana son matsowa kusa da Aminatu ta saka mata hannu Ali ya shiga tsakaninsu, shi kansa mamakin bakin Aminatu yake, he never thought zata iya irin wannan furucin.
 
“Leila karku tada fada a nan, Talba ba a kwance yake kina gani”
 
“Baka jin abun da take fada min, yar kauye da ita jahila, ko kunya bata ji ta tsaya a gaban mutane”
 
Yadda Leila take daga murya ya saka wata nurse shigowa dakin.
 
“Ke da kike da ilmin da wayewa me suka amfana miki? Me suka kareki da shi? Saboda ina yar kauye kina yar birni ba shi yake nufin ki mutum ba ce ni dabba, kuma ke ce ya kamata ki ji kunya kina zuwa jinyar mijin da ba na ki ba, tun da ba a daura miki aure da shi ba”
 
Leila ta kalli Ali tana girgiza kai.
 
“Sai na yi kasa kasa da yarinyar”
 
Nurse din ta rike ta tana kokarin fitar da ita. Ali kuma yana kokarin kwantar mata da hankalin.
 
“Dan Allah Leila ki yi hakuri aje sai ku yi nan asibiti ne kuma a kusa da marar lafiya, be kamata ba ki yi hakurin har ya samu lafiya tukuna please”
 
Ta fisge hannunta daga rikon da Nurse din tai mata ta fice daga dakin bayan ya harari Aminatu sai haki take kamar wanda tai fada da zaki. Ali ma kallon Aminatu yake da mugun mamaki, ashe tana da bakin maida magana haka. Be ce mata komai ba ya fice daga dakin bayan ya fadawa Nurse din ita kadai za a bari ta zauna a dakin. Sai da suka fita sannan ta nufi kujerar dake kusa da gadon ta zauna ta saka hannunta biyu ta rike hannunsa daya ta matsar da kujerar ta kwantar da kanta jikin gadon tana kallon fuskarta.
 
 
 
 
 
_______________________________
 
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
 
FAHAT POV.
 
Sai da ya gama karyawa sannan ya fito bangarensa, ya nufi bangaren Mahaifinsa. Da sallama ya shiga sai ya samu mahaifiyarsa zaune tare da Abbah tana masa hira, kallonsa take har ya zauna a kasa inda suke zaune su duka biyun.
 
“Abbah barka da safiya”
 
“Muhammad an tashi lafiya”
 
“Lafiya kalau”
 
Ya kalli Momy sai kuma ya yi unkurin tashi tsaye, sai dai lura da Abbah yayi da akwai magana a bakinsa ya saka ya dakatar da shi.
 
“Akwai wata magana ne Muhammad?”
 
“Wata kila karata ya kawo”
 
Momy ta fada, sai Fahat ya dawo ya zauna yana kallon mahaifinsa da fuskar damuwa.
 
“Abbah akan maganar aurena ne da yarinyar nan, yanzu haka ta fada min a gidansu ance ta fitar da miji ta fada min na turo”
 
“To akwai wata matsala ne?”
 
Abbah ya tambaya ganin yayi shiru be karasa ba.
 
“Momy ta ki aminta”
 
Abbah ya kalleta.
 
“Saboda me?”
 
“Bazawara ce fa yarinyar, haihuwarta daya”
 
Abbah was so confused.
 
“Bazawara kuma? Daman ba budurwa ba ce?”
 
“Karya tai masa, cewar ita budurwa ce, domin har yanzu be gano cewar bazawara ba ce sai yanzu da nake maganar nan, shiyasa na fada masa yaje ya bincike ta domin ba zamu yarda ya dauko mana yarinya ya kawo a family ba daga baya abu ya zame mana matsala”
 
“Kina da gaskiya, ba ma shi ba yaran yanzu ba wata doguwar tarbiya ce da su ba, sai ka ga yarinya karama tana shigewa manyan mutane saboda neman abun duniya”
 
“Shiyasa ai ko wacece zai aura sai na saka amin bincike akanta saboda kar a dauko mana mugun abu akawo mana a gida”
 
“Gaskiya ne, kuma ina ganin Muhammad kamar be dace ka auri bazawara ba a yadda kake da kurciyarka, kuma ace mace har ta haihu, kana saurayinka kuma auta a cikin mazan gidan nan”
 
“Amman Abbah ba haramun ba ne, kuma yarinyar bata da wata matsala ta rashin tarbiya, haihuwa ce”
 
“Kai yanzu kana jin zaka iya zama wanda ta taba aure? Abokanka yan'uwa da mutane duk zaka iya shanye irin kallon sa suke maka”
 
Cewar Abbah yana kallonsa shi kansa be yi na'am da auren bazawarar ba.
 
“Abbah ina sonta sosai Wallahi, akwai mata da yawa a gari da kuma cikin familyn nan, amman ban kamu da son kowa ba sai ita. Amman hakan ba zai saka na yi jayayya da ku ba, idan baku ra'ayinta zan hakura da ita”
 
Abbah yayi gyaran murya.
 
“Aa ba zamu hana ka abun da kake so ba, amman shi lamarin duniya ana bin komai a sannu, bana son soyayya ta saka ka yi abun da zaka yi nadama, kuma ba zamu so mu hanaka abun da kake so ba, auren bazawara ba haramun ba ne dan haka ba zamu hana ka ba, sai dai ina tabbatar maka da cewar ni ma zan yi nawa bincike idan na same ta da irin halin matan zamanin nan ba zan yarda ka aureta ba”
 
“Na yarda Abbah na yarda”
 
Ya amsa da sauri yana murmushi.
 
“To shikenan, yaushe iyayen nata suka ce a turo”
 
“Ba su saka rana ba, ta fada min ne cewar ance ta fitar da miji kuma ta fitar da ni, so ni take jiran na fada mata ranar da zan aiko”
 
“Okay tau zuwa karshen watan nan... Kamin lokacin In Shaa Allah, zan yi abun da ya dace”
 
Fahat ya kama hannun mahaifinsa da sauri ya rike yana murna.
 
“Na gode sosai Abbah na gode Allah ya kara girma”
 
Mommy kam hade rai tai kamar bakin hadari.
 
“Haba haba Alhaji akan me zaka goya masa baya ya auri bazawara yana yaronsa? Kuma mata har ta haihu daya dan Babban mutum kamar Fahat sai kace dai mata sun kare a duniya”
 
“Hajiya tun da har yana so, be kamata mu hana abun da addini be hana ba, ba mu sani ba ko Alheri ne, yanzu ba zamani ba ne da ake yin auren dole”
 
“Amman dai...”
 
Abbah ya daga mata hannu, sannan yai ma Fahat Umarni daya tashi ya tafi. Fahat ya tashi cikin farinciki ya fice daga falon. Sai da ya fita Abbah ya kalli Mommy ya ce.
 
“Idan mutum yana farin ciki da abu baka tsake masa wannan farincikin kai tsaye ko da kuwa illa ne a gareshi, kara kai masa nuna sa illar idan zai iya gani, idan kuma ba zai gani ba sai ka bishi da lalama har ya fahimci komai, amman a yanayin yadda yake a yanzu idan muka hana shi aurenta kai tsaye, zai rika kallonmu a wasu kalar iyaye da basa son farincikinsa, amman yanzu idan aka bashi dama idan ma akwai wata illar a tare da ita shi zai fara ganewa a hankali”
 
“Kana da gaskiya, amman idan ba a nuna masa hanya ba, so zai rufe masa ido ya kasa ganin komai, ko zancen zawarcin nan bana jin ya sani har sai da na yi nawa bincike na gano haka, domin daya sani da tun farko zai fara fada min, amman ka ga sai ta boye masa”
 
“Da ya gano hakan ai ya kamata yai yayi tunani akai, amman so ya rufe masa ido baya ganin wata illa ce a gareshi, wannan kadai ya isa ya nuna miki idonsa a rufe yake”
 
“Toh Allah ya sauwake, amman Wallahi sam bana kaunar aurensa da yarinyar nan ko kadan”
 
“Ki yi addu'a kawai, idan Alheri ne Allah ya tabbatar, idan kuma akasin haka ne Allah ya raba tsakaninsu”
 
“Amin”
 
Ta amsa tana mike tsaye ta dauke kwanunkan da suka ci abincin ta fice.
 
 
BATURIYA POV.
 
Ta tabe baki tana maida wayar a dayan kunnenta.
 
“Ramlee ni yanzu matsalar da nake ciki ma ta ishe ni, ba ta neman kudi nake ba”
 
“Wace irin matsala?”
 
Baturiya ta sauke ajiyar zuciya sannan ta labarta mata abun da ya faru tsakaninta da Fahat, amaimakon Ramlee ta tausaya mata sai kawai ta fashe da dariya.
 
“Fee'at kina bani dariya, kamae ba mace ba, iyayen na mu mata ma yanzu suna samun samari su saura balle ke da kike da kurciyarki? Haihu daya fa, kuma yaron ma ba a hannunki yake ba, to miye damuwarki a ciki? Ko cewa yai ya fasa aurenki ai ba wani abu ba ne, ke dai ki tara kudi kawai ki aje, ko tsufa kika yi kika ce saurayi zaki aura zaki samu Wallahi”
 
“Ramlee ba zaki gane ba, ni bana son wannan kazamar rayuwa, kuma kin ga gida tun ban je ko'ina ba am fara saka min ido”
 
“Baturiya ke ce baki iya abun ba, wata yar sana'a zaki samu ki fake da ita, ko kuma ki koma makaranta ki cigaba sa karatu kina fakewa da wannan kina sha'aninki yadda kike so, amman ki ce zaki daina tun yanzu me kika samu a ciki? Ni kaina sa nake da gida da mota naje makka na leka wasu kasashe ai bana jin na gama tarawa balle kuma ke da ko kan akaifa baki tara ba”
 
“Ni yanzu ba wannan ya dame ni ba, burina na samu miji na yi aure kuma babban mutum mai kudi, yanzu kuma na samu sai na bar wannan damar da wuce ni?”
 
“Toh sai miye? Ana lamarin duniya ake yin na kiyama fa, aa Wallahi karki ce zaki takura kanki akan soyayyar wani namijin banza, ke idan kika kware a lamarin nan fa har mutanenda kike mu'alama da su zaki iya aurensu”
 
“Aa ni dai ina son Fahat sai idan ban samu aurensa ba sannan zan hakura”
 
Ta sauke wayarta daga kunnenta ta duba kiran dake shigowa, sannan ta maida wayar kunnenta.
 
“Kin ga ma gashi nan yana kirana, yanke kiran zan kiraki anjima”
 
“Oh wato har ya fini muhimmanci, to ni yanzu ya zan yi da wannan mutumen da na yi ma alkawari”
 
“Ki sama masa wata mata, domin ni idan aurena da Fahat ya tabbata babu wani abun da zan sake yi, saboda dole ne na fara taka tsantsan da rayuwa”
 
“Yar wahala ina nan da ke zaki dawo kina rokon na maida ke ruwa”
 
Ramlee ta fada cike da jin takaici sannan ta kashe wayar. Ramlee na kashe wayar Baturiya ta maidawa Fahat kiran da yai mata bata yi piciking ba, wayar na fara ringing yai picking, sai yai shiru ba tare da yayi magana ba, haka ya saka gabanta faduwa sosai domin be saba yi mata haka ba.
 
“Hello kana jina”
 
“Ina jinki”
 
“An tashi lafiya?”
 
“Lafiya kalau, ya gida?”
 
“Lafiya Kalau, na ji muryar kasa kasa akwai wata matsala ne?”
 
Yayi shiru kamar ba zai ce komai ba, sai kuma yaja dogon numfashi ya sauke.
 
“Akwai abun da nake son mu tattauna da ke, kuma akwai abun da kika yi wanda ya bani matukar mamaki, domin na yi zaton komai da zai fito daga gurinki gaskiya ce kai tsaye”
 
Ta dafa kirjinta gabanta na mara faduwa.
 
“Akwai abun da na fada maka wanda ka bincika ka tarar ba haka yake ba Fahat?”
 
“Ba magana ce da ya kamata mu yi da a waya ba, zan shigo anjima”
 
“Ba zan iya jira har anjima ba, ka tayar min da hankali, dan Allah ka fada min ko ma minene, wata kila zan iya maka bayani ta waya ko kuma idan ka zo anjima din, ko kuma ka shigo yanzu”
 
“Safiya ce, zan shiga office yau idan na fito zan zo gida na same ki”
 
Yana kaiwa nan ya katse wayar, yana mata duk wannan abun ne saboda ta fahimci cewar ransa ya bace na boye masa zancen ta taba aure da tai. Ba dan yana tsananin sonta ba da wannan karyar kadai ta isa ta saka ya rabu da ita, sai dai soyayyar da yake mata ta hana shi aikata haka, sai dai bata rufe masa ido ta hana shi ganin laifinta ba. Safa da marwa ta fara yi a dakin tana ra tunani kala kala, gabanta sai faduwa yake.
 
‘Ko dai ya ji na taba yin aure ne? Ko kuma an fada masa an gan ni a gurin da be kamata ba ne? Ko kuma wani ne ya kai masa sukarta?’
 
Haka dai tai ta sake sake cikin ranta, ta kasa gane dalilin wannan furucin da Fahat yai mata. Gashi kuma ta kasa samun natsuwa, abun ka da marar gaskiya, hankakinta ya tashi sosai domin a yau ta ji shi a wani yanayi da bata saba jinsa ba. Ta san sun rabu cikin damuwa a jiya, sai dai damuwar bata kai kamar ta yau ba.
 
“To ko dai binciken da nake ganin kamar ba za ayi ba ya saka an yi masa ko kuma iyayensa sun gano cewar na taba aure?”
 
Wannan karon a fili tai tambayar, gaba daya ta kasa natsuwa. Sake kiran wayarsa, sai dai be yi piciking ba har wayar ta gaji da ringing ta yake, sake kiran tai sai da ta jera masa miss calls hudu tana kokarin sake yin na biyar ta ji. Ko sau daya a tahirin haduwarta da Fahat bata taba kiransa yaki dagawa ba sai wannan karon. Ji tai kamar ta dora hannu saman kai fara ihu, jikinta har rawa yake nan da nan gumi ya kadyo karyo mata kamar wanda ke gaban alkali.
 
 
 
MADINA POV.
 
Sai da ta gama kukanta da bakincikin sa'insar da sukai da Leila sannan ta sake yi ma motar key ta hau titi tana kai hannunta ta zaro tissue ta goge fuskarta ta gyara hancinta.
 
“I promise myself this, ba zan jefa rayuwata a hatsari ba, kuma na kasa samun abun da nake so, daga karshe kuma ace ni ce zan fada a matsala”
 
Taja numfashi da karfi, ta kai hannunta ta sauke gilashin motar ta jefar da tissue din.
 
“Ya kamata Leila tai min sadaukarwa ai, ko da a munafurci ne, amman ji sai. Barazana take min, tana zagina  ya kamata ta yarda da ni ko sau daya ne, amman idonta ya rufe”
 
Ta fada tana jin tsantsanar nadamar a abun da ta aikata.
 
“Na jefa kaina a halaka, miyasa na aikata tun farko? Hajiya ta yi ta gargadina amman ban ji ba, gashi tun ba ayi nisa ba, ban samu biyan bukata ba, kuma zan jefa kaina a halaka, kuma na saka Talba? Miyasa wani lokacin nake da son kai ne why?”
 
Ta fashe da kuka tana dukan sitiyarin motar. Kai fa girgiza tana jin wata masifaffiyar kaunar Talba na taso mata, ta rasa dalilin daya saka Talba ya kasa ganin kaunar da take masa, wata kila yana duba kusancinsu da tsakaninta da Leila ne, yes ta san abun kunya ne ace tana soyayya da shi, amman ai so be san wannan ba, ita kanta da son ya duba kusanci da kunya da be shiga zuciyarta ya zaauna ba har ya rufe mata ido ta aikata abun da ta aikata a yanzu. Sai da ta kusa isa gidansu sannan ta samu ta kukan da take ya tsaya mata, a inda ta saba aje motarta ta aje faka ta kwantar da kanta jikin sitiyarin ta lumshe ido, wacan daren take ta gani a idonta daren daya hanata samun sukuni saboda arba da tai da abun da bata yi zato ba, daren daya saka tunanin aikata abun da ta aikata a yanzu. Dagowa tai tana kallon harabar gidansu
 
“So babu ruwansa sa kyau, babu ruwansa sa asali, babu ruwansa da hali, babu ruwansa sa waye kai, babu ruwansa da kusanci, babu ruwansa da matsayi, shiyasa ba duba ni lokacin da zai jefa min son Talba, kuma be duba Talba ba ya jefa masa son Aminatu, yarinyar da ko a mafarki ban yi zaton zata samu kusanci da Talba har haka ba”
 
Ta girgiza kai tana lumshe ido, tana lasar bakinta daya bushe.
 
 
***   ***   ***
 
“To laifin waye? Da baki sake mata fuska ba har ta ga damarki ta fada miki magana mai zafi haka? Kamar wannan yarinyar”
 
“Momy laifin Talba ne, shi ya nuna mata bana da wata kima a idonsa shiyasa har ta samu dama”
 
“Yanzu Talban ne a farke da take fada miki haka? Ke dai kin maida kanki wata sakarya, da an yi miki abu sai dai ki ce zaki daki mutum ,amman bakin san ki tsaya me, ki yi abun da ya kamata ba, haka kika dauki yarinyar nan kika maisa ta uwarki, wani sirrinki da Madina ta sani ni da nake mahaifiyarki ban san shi ba, gashin yanzu ta samu damar da zata juya”
 
Leila ta kalli Momy cikin fusace ta ce
 
“Momy idan kika ji irin maganar da Madina ta fada min yau sau mamaku ya kusan kasheki, ashe zargin da kika mata gaskiya ne, ita ce take aikata komai”
 
Da mamaki Momy take kallon Leila, sai dai ganin ba su kadai ba ne a gurin yasa bata zafafa tambayar komai ba, sai kawai ta tabe baki tana kallon Gwaggonsu da ta doso gurin, wato Hajiya Hanne wata kanwar Daddy wanda take zaman cousins a gurinsa.
 
“Ki bar maganar nan, idan mun koma gida zamu yi magana, ki iya bakinki”
 
Leila ta daga kai. Tana juyawa dayan side dinta ta kalli wandanda suke gefenta sai dai suna da nisa da ita sosai, yastinar hanci ta fara tana jin irin warin nan data taba ji a gida yana fitowa a jikinta. Mikewa tai tsaye fana fadin.
 
“Momy zan je gida na yi wanka na dawo”
 
“Okay, ki cewa Amal ba sai ta dawo ba, tun da likitoci sun ce kar a dame shi, bari sai gobe idan Allah ya kai mu sai ta zo ta duba shi”
 
Kai ta dagawa Momy tana yastinar fuska, domin ta tsani warin da take jin jikinta na yi duk da bata san na minene ba. Bayan sun da gaisa da Hajiya Hanne, ta karbi key mota a gurin

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login