Showing 225001 words to 228000 words out of 332834 words

Chapter 76 - Bakar wasika Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

65582

sa akwai yan aiki a gidan. Kamar zata fasa kuka haka ta fita dakin ta nufi inda take kyautata zaton madane, ta tura ta shiga sai ta tsaya daga bakin kofa tana kallon Leila da ita ma tsayen take kamar mai tunanin abun yi. Me zata fara? Fasa kwai? Ko feraye dankali? Ko kuma mai zata fara soyawa? Ko ruwan zafi zata fara dorawa ta tafasa? Dan juyowa tai ta kalli Aminatu dake tsaye jikin kofar tana kallonta, sai tai saurin dauke ido, ta nufi kofar waje ta kitchen din ta bude sannan ta dawo ta dauki roba ta fita zuwa inda ake zube buhun dankalin turawa, ciko robar tai ta dawo kitchen din ta mikawa Aminatu.
 
“Ki fara da wannan, ni zan fasa kwai”
 
Aminatu ta karba ta matsa kusa da fridge ta risina.
 
“Ki bani wuka da wani roba mai ruwa”
 
Leila ta dauki wata robar ta cika ta da ruwa, sannan ta zaro wuka ta mikawa Aminatu. Karfi hali kawai take domin ba sanin tai yadda ake shirya breakfast din gidan ba, ta fi gane yadda ake ci kawai, idan ta gama a kwashe kwanunkan.
 
“Ki dawo daga nan sai na taya ki mu karasa da wuri kamin Momy ta farka”
 
Aminatu bata yi mata musu ba ta dauki komai ta maida inda ta nuna mata kusa da tab. Door bell din falon ce tai kara, sai ta kalli Aminatu fuska a yatsine.
 
“Bari na fadawa Mairo da Zulai yau mu zamu shirya breakfast”
 
Ta fada sannan ta juya tana murmushin keta ta fice daga kitchen din. Kai tsaye kofar falon ta nufa ta bude, Mairo ta fara gaisheta sannan Zulai amman bata amsa musu ba.
 
“Aminatu zata shirya abun karyawa, idan an gama za a sanar muku”
 
Bata tsaya jin abun da zasu ce ba ta rufe kofar tana jan tsaki.
 
“Kullum ku rika damun mutane da farar safiya kamar dole”
 
Daman can tana jin haushin yadda suke zuwa da sassafe a falon, idan kuma ba su shigo da wuri ba Momy zata yi fada. Ko da ta dawo har Aminatu ta feraye dankali uku ta saka a roba. Tsaye tai bakin kofar kitchen din tana watsa mata harara wani hayakin bakinciki na taso mata. Jin motsin shigowar mutum a kitchen din yasa Aminatu ta juyo ta kalleta, sai Leila ta tsuke baki ta karasa kusa da ita ta zari wuka, ta dauki dankwalin ta fara gyarawa. Tsit kitchen din yai kamar ba kowa a ciki, Aminatu na ta aikin gyara dankali Leila kuma ta kasa feraye ko daya sai wasa take da shi tana watsa mata harara kasa kasa, can kuma ta dago tana murmushi ta ce.
 
“Kin ba ni tausayi sosai, Talba ya fada min abubuwan da suka faru, Allah ya jikan iyayenki”
 
Aminatu ta yi shiru for few seconds sannan ta amsa.
 
“Ameen”
 
“Azzaluman mutane ne, gashi suna wulakanta mata ba kadan ba”
 
Aminatu ta tsayar da gyaran dankalin da take ta. Hakan kuma ba karamin dadi yai ma Leila ba, daman burinta ta bakantawa Aminatu.
 
“Akwai zafi ko? Wai ya kika ji lokacin da suka miki fyade?”
 
Aminatu ta dago ta kalleta da idanuwanta da suka cika da hawaye zuciyarta kuma ta hau bugawa da karfi.
 
“ Na ji kwatankwacin abun da kika ji a lokacin da kika ji Talba ya aure ni, shi ai ya fiki sanin abun da ya same ni ko? Kuma a haka ya aureni ya bar ki, ni da ke muna jin bakinciki daya ne, har kara ni na auri wanda ya san abun da ya faru da ni, ke fa babu abun da ya same ki amman ya barki ya aure ni”
 
Mutuwar tsaye Leila tai tana kallon Aminatu with shock, bata san lokacin data rika kan Aminatu da mugun karfi ta buga a tab din sannan ta jefar da ita kasa da mugun karfi. Wata mahaukaciyar kara Aminatu tai ta dafe goshin tana faduwa kwance.
 
 
 
 
_______________________________
 
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
 
Ihu sosai Aminatu take, daman ita da kuka are 5&6 mai neman kuka an fada masa masa mutuwa, daman can ko ba a taba ta idan kuka ya motsa yi take balle yanzu kuma da akai mai dalili, gashi kalamin da Leila tai mata ya mata zafi fiye da goshinta dake zafi, wannan yasa kukan nata ya karu tana ta ihu kamar wanda aka cirewa ido. Kukanta ne ya saka Amal cire hijab din da tai sallah ta nufi kofa daman ita ake bari baya a kullum gurin sallah asuba, abu ne mai wahala ta farka a lokacin da kowa yake farkawa. Da sauri ta sauko downstairs ta nufi kitchen din da take jin ihun na fitowa tana daf da shiga kitchen din Leila ta fito a fusace har suna shirin yin karo da Amal. Amal ta bita da kallo kamin ta kalli kofar kitchen ta leka a firgice, hango Aminatu tai a kwance tana ta rusar ihu, bata tsaya ta ji dalilin kukanta ba balle har ta san abun da take yi ma ihun ta juyo da gudu ta nufi kofar dage can dayan bangaren falon, kofar dake sadasu da part din Daddy, domin Momy tana bangaren Daddy. Da gudu Amal ta shiga part din ta tura kofar falon Daddy ya shiga kamin ta karasa karamin falonsa har haki take, sai da ta isa kusa da kofar bedroom dinsa sannan tai burki, shi ma ba dan Momy ta hana ta shiga dakin Daddy kai tsaye ba da shiga zata yi, ta tsaya tana kwalawa Momy  kira.
 
“Momy, Momy ki fito Laila da mai sunanki sun yi fada”
 
Da iyakar karfinta take fada ganin babu alamar fitowar Momy yasa ta karasa bakin kofar tai knocking.
 
“Momy Leila ta yi fada da Aminatu, mai sunanki tana can a kitchen tana kuka”
 
Tana fada tana kwankwasawa, tana jin an taba kofar ta dan matsa bawa, a zatonta Momy ce sai tai arba da Daddy sanye da jallabiya.
 
“Daddy ina kwana? Mo... ”
 
Sai kuma tai shiru ta kara karasawa daman gulmarta ce ta saka take son fada, yanzu kuma tana tsoron kar Momy tai mata fada.
 
“Me na ji kina fada?”
 
“Daman Momy na ke nema”
 
“Munafuka, bayan kin gama fadi? Yanzu zaki wani canja magana kina nemana, waya sani ko ke kika haddasa komai”
 
Momy ta fada tana fitowa daga dakin.
 
“Miya faru?”
 
Daddy ya sake tambaya.
 
“Daman Aminatu ce na ji ihunta sai na sauko sai na ga Leila ta fito kitchen ita kuma Aminatun tana kuka”
 
Ta fada tana satar kallon Momy dake hararta. Daddy ya nufi kofar fita daga falon kai tsaye, Momy ta watsa mata harara.
 
“Aku, ke kan kin ji haushin rayuwa, yanzu sauranki Talba da Kabir”
 
Ta karasa tana jan tsaki, sannan ta bi bayan Daddy. Tsaye Amal tai sai da ga sun fice daga karamin falon ta kofar ciki, sannan ta nufi kofar gaba ta bude ta nufi part din Talba da Kabir, madaidaicin falo ne, mai dauke dakuna guda uku, daya daga dama na Kabir sai na Talba daga hagu sai kuma na tsakiya wanda ake sauke bako, idan na musamman ne, an kawata falon da kananan cushion daya bangare kuma an saka karamin teburin cin abincin, sai katon plasma da ba kallo suke da shi ba, domin kowa yana da na shi a dakinsa.
Dakin Talba ta nufa ta kwankwasa masa, ta san baya son ana masa knocked fiye da uku, amman da yake wannan gulma ce sai ba tai kasa a guiwa ba wajen dagewa tana buga masa kofar da karfi.
 
“Yaya Talba”
 
Be ta ji motsin zai bude ba sai da ta ambaci Aminatu.
 
“Yaya Leila ta yi fada da Aminatu tana can tana kuka sosai”
 
Tana gama rufe baki da dakiku ya iso gurin ya bude kofar yana kallonta jikinsa sanye da pajamas.
 
“Ina take?”
 
“Tana kitchen”
 
A bude ya bar dakin ya fice da sauri, sai ta bi bayansa, kamin ya karasa gurin kofar falon har da saurinsa, sau daya ya murda kofar ya ji a rufe sai ya juyo da sauri zuwa part din Daddy daya hango kofar a bude. Ta cikin falon Daddy ya bi ya shiga part din Momy, da gudunsa ya karasa kitchen din sai ya samu Momy da Daddy tsaye Aminatu kuma na kwance tana rusar kuka Leila na daga gafe.
 
“Daddy zagina fa tai”
 
Leila ta fada tana kokarin kare kanta daga fadan da Daddy yake mata. Da sauri Aminatu ta tashi zaune tana rike da goshin da yayi kololo.
 
“Karya take ban zage ta, ita ta tambaye ni na amsa mata shi ne ta ji haushi ta buga min kai a fanfo kuma ta wulgar da ni kasa”
 
“Ke Aminatu yaushe kika koyi munafurci? Sannan Leila bata girme ki ba da zaki ce karya take, fitina kike son hada mana a gida”
 
Daddy ya jefawa Leila wata bakar harara, kamin ya kalli Momy dake kokarin tare mata.
 
“Kina nan lokacin da komai ya faru? Ko kuma laifin yarki kike kokari karewa? Shiyasa kika ce ya dawo da ita gidan nan saboda ku musguna mata? Idan ma zaginta tai me kai hannunta a jikinta? Yarta da zata daketa? Ke kanki baki dukan yayanki balle wani ya dukar miki yaya, akan mi Leila zata daga hannu ta daki yar wasu? Kuma matar Talba? Ni kuka wulakanta da ni Talba, domin ko yar tsana ďana yake aure be kamata ku wulakanta ta ba, balle mutum”
 
Sai a lokacin Talba ya nufi inda Aminatu take zaune, domin tun da ya shigo kitchen din tsaye yake bakin kofa saboda bacin rai da kaduwa, kasa cewa komai yai ya karasa kusa da ita tana kuka ya rika hannunta yana kokarin duba goshin sai ta fisge hannunta ta sake dafe gurin tana kuka.
 
“Ki bata hakuri yanzu nan?”
 
Leila ta kalli Daddy da sauri, Momy ma kallonsa tai.
 
“Haba Engr, ayi mata hakuri dai, kasan Talba bata iya controlling kanta idan rai ya bace, amman kamata yayi ka bincika abun da ya faru, yaushe yarinyar ta zo? Ba mu gama sanin halinta ba, wata kila ita ta ziga Leila ne da yawa har ya saka ta mareta, kasan kuma Leila da saurin fushi”
 
Daddy ya nuna Momy da yatsansa cikin bacin rai.
 
“Wannan ya zama na karshe da zan sake saka yayana wani abu ki shiga a ciki kina son tsaya musu, kin ga wacan yarinyar da Leila daga lokacin da Talba ya aureta matsayinsu daya a gurina, muna nan da ke wata rana sai na yi mata abun da ban yi ma yaya ba, ko kuma na hana yayana abu na yi mata”
 
Ya juya ya kalli Leila yana daka mata tsawa.
 
“Duka ki bata hakuri”
 
Leila ta resina da sauri idonta na cika da hawaye, muryarta na rawa.
 
“Ki yi.... Hakuri....”
 
Ta mike tsaye da sauri sai, sai Daddy ya sake daka mata tsawa.
 
“Duka ki bata hakuri na ce”
 
Leila ta kalli Momy da sauri, sai Momy ta gyada mata kai alamar ta yi, domin ita kanta tana shakkar Daddy idan ransa ya bace. Leila ta duka kasa tana kuka.
 
“Ki yi hakuri ki gafarce ni...”
 
Ta mike tsaye tana jin wani irin wulakancin da kaskanci da bata tana ji ba. Da gudu ta fice daga kitchen din tana kuka. Daddy ya juyo ya kalli Talba.
 
“Ba ka sati daya, ka dauke matarka daga gidan nan ka kaita gidanka ku tare can, ka fadi duk abun da kake bukata zan saka a zuba muku kamin lokacin”
 
Momy ta bude baki da sauri.
 
“Haba Engr, na ga ai Leila ta bata hakuri, kuskure ne ana samun tsabani ma tsakanin halshe da hakori balle kuma dan adam”
 
Uffan Daddy be ce mata ba ya fice daga kitchen din sai ta bi bayansa, Amal dake labe ta fito ta leka kitchen din.
 
“Kai ashe har da kololo bari na kira Ya Kabir ya saka mata magani”
 
Sai da ta juya ta fita daga kitchen din sannan ta tuna ita ma ai ba kaunarta take ba, sai kawai ta fasa zuwan ta nufi upstairs. Amal na ficewa Talba yai saurin rumgume Aminatu ta runtse ido yana jin wani irin tausaynta.
 
“Baby na miyasa kika shigo kitchen din? Ji yadda ta taba min jiki har yayi kololo”
 
“Ita ce ta ce na zo mu yi girki”
 
Aminatu ta fada cikin kuka, sai ya kara rumgumeta yana jin kukanta har cikin ransa.
 
“Bana son gidan nan... Bana son gidan nan....”
 
“Shiiiiiii”
 
Ya fada yana kokarin kai bakinsa kunnenta sannan ya mike tare da ita tsaye, ya dan saketa daga rikon da yai mata yana duba goshin.
 
“Bari na duba kadan”
 
Ta ki bari sai kuka take, hannayensa ya saka ya dauketa cak ya fice da ita daga kitchen din, Kofar fita falon ya nufa ya bude da hannunsa na hagu yana rike da ita ya fita daga falon, be direta ko'ina ba sai gaban motarsa. Be damu da duba waye a gurin ba ya kai bakinsa ya sumbanci hannayenta.
 
“Bari na dauko keys dina na kai ki asbiti, amman ki daina kukan dan Allah”
 
“Ni dain na tsani gidan nan”
 
Ta fada domin har ga Allah ji take ta tsani gidan. Da sauri ya nufi bangarensa ya shiga da sauri, be taba saka tufafi ba tare da yayi wanka ba sai yau a gaggauce ya shirya. Ya dauki keys dinsa da walle da wayarsa ya fice da sauri. Leila na tsaye jikin windows din dakinta tana kallon fitowar da Talba yai har ya karasa gurin motarsa ya bude wa Aminatu front seat ta shiga ta zauna, ya rufe sannan ya zagaya side dinsa ya shiga da sauri ya tashi motar. Juyowa tai ta share hawayenta sai da ta kai karshen dakin ta juyo ya dawo gurin window ta leka kasa, sai sake juyowa ta dawo tana rumgume da hannayenta hawaye na sauko mata. Zaunawa tai bakin gadonta tana jin zuciyarta kamar zata fasa kirjinta ta fito, kamar ance dago tana dagowa Momy na turo kofar dakin ta shigo.
 
“Leila miya kaiki aikata wannan abun?”
 
“Momy kin san abun da ta fada min? Ce min tai wai Talba ya aureta ya bar ni”
 
Momy ta zauna kusa da ita da mugun mamaki.
 
“Ita da bakinta ta fada miki haka? Wato har ta samu bakin fada miki bakar magana?”
 
Leila ta rumtse ido hawaye na fito mata.
 
“Daddy ya saka na bata hakuri, Momy kishiyata? Na bata hakuri bayan kuma na fita komai, kuma ita ta tararda da ni a gidanmu? Ta auren min miji a yau har tana min alfahari da cewar ya aureta ya bar ni”
 
Ta nuna kanta wasu zafafan hawaye na sauko mata. Tausayinta ya kama Momy.
 
“Duk ba laifinsu ne, laifin Talba ne, da kuma Ali duk shi ya m haddasa komai, da Talba be sake mata ta samu fuska da wuri haka ba, da bata isa ta fada miki magana ba, amman komai zai wuce, na rantse miki da Allah Leila sai Talba ya aureki kuma sai ya rabu da yarinyar, saboda haka ki kwantar da hankalinki ki daina kuka ki bar komai a hannu, ki rika karfafa min guiwa mana, ina fama da mahaifinku ke kuma kina nan kina min kuka? Na samu ya yarda ta zauna a nan ta yadda zamu samu abun da muke so, sai kuma ki rika janta har tana fada miki magana da zaki kasa rike kanki? Leila ki rage wannan zafin zuciyar, saboda wannan zafin kika aikata abun da kika aikata gashi naj ya zame mana fitina, ke kenan idan rai ya bace baki san ki rike kanki ba? Miya kai ki janta har kitchen?”
 
“Ba janta na yi ba, kofi ta shiga dauka, shi ne fa daga na mata maganar Talba sai ta yabo min bakar magana”
 
“Ki daina yi mata maganar mana, babu ruwanki da safgarta, ke dai ki saka ido ki yi kallo”
 
Momy ta karasa tana dafata, kamar wanda aka yayewa bakinciki haka Leila ta ji, a take kukan da take ya yanke ta share hawayenta farinciki ya baibaiye ta, domin Momy ta yi rantsuwa kuma ta san Momy idan tace zata yi zata yi balle kuma yanzu da ta hada da rantsuwa.
 
“Momy karshen kaunar da zaki muna min ita ce ki kori yarinyar, ni Wallahi ko ban auri Talba ba zan fi kowa farinciki idan ta rabu da shi”
 
“Zan yi haka, amman ki yi taka tsantsan da ita, ki kawar da ido ga duk wani abu da zaki gani, kuma ki rika controlling wannan zuciyar taki Leila”
 
“Inshallah”
 
“Bari naje na ji da Mahaifinki shi kuma, kin san idan ya hau be iya saukowa cikin sauki ba, musamman akan Talba nan”
 
“Momy kina jinsa har da cewa wai bata da banbanci da ni”
 
Cewar Leila tana jin haushi.
 
“Ba sai idan ta zauna a gidan ba tuluna, anjima idan Talba ki samu Talba ki ba shi hakuri, kuma ki saka shi gaba ku je gurin mahaifinku ki ba shi hakuri”
 
Ta gyada kai, sannan Momy ta tashi ta fice daga dakin.
 
 
TALBA POV.
 
Faka motarsa yai ya juyo ya kalli Aminatu da har lokacin kuka take kanta yayi wani gummmm kamar ba nata ba. Kujera yaja mata ta kwanta baya. Sannan ya ciro wayarsa, ya kira Ali, sai da wayar tai ring har ta katse Ali be yi picking ba, daman kuma ya san haka zai faru saboda safiya ce wata kila wayarsa ta kwana a silent ne.
 
“Ba lallai ne ace asibiti sun fito ba yanzu, zai kaiki gurin abokina unguwar Yarima ya dubaki okay”
 
Ya fada yana kallon yadda idonta sukai ja.
 
“Ni dai bana son gidan can, ka kai ni gurin Mama”
 
Ko kadan baya son kaita gurin Hajiya Laraba domin ya san wani fadan ne zai ta so.
 
“Shikenan, amman ki daina kukan nan ji idonki”
 
Ya fada cike da damuwa, sannan ya ja motar suka hau titi. In few minutes suka

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login