Showing 45001 words to 48000 words out of 332834 words

Chapter 16 - Bakar wasika Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

65568

kishi da ni”
 
“Haba Momy Talba ne zai yi kishi da ke?”
 
“Eh mana, bakisan wasu yayan suna tsanar iyayen da ba su haife su, Idan ba haka ba ai ba zai min kalaman banza ba, ko ba komai ni surukarsa ce right”
 
“Momy yanzu zai ji babu dadi Wallahi ransa zai bace”
 
“Ran nasa ya dade be bace ba, wannan wane irin so ne kike ma Talba wai? Shi fa baya son ki kamar yadda ke kike sonsa, kuma naga ke ma ai kina bata masa ran”
 
“Eh amman Momy wannan ai matsalar mu ce ta dabam ba wai akan ba”
 
“I don't care, idan ke baki san zafin abun da ya fada ba ni na sani”
 
Mikewa tai tsaye cikin yanayin damuwa ta fice daga dakin tana ta sake sake, ko ta kira ta bashi hakuri akan abun da Momy tai ko kuma ta kyale shi, sai dai idan ta tuna cewar saboda ita komai ya faru sai ta ji wani iri.
  Dakinta ta shiga ta dauki wayarta ta kira Madina ta labarta mata abun da ya faru, daman komai na duniyar ba zata iya boyewa Madina ba, no matter how Momy ta kwatseta akan abu sai ta fadawa Madina.
 
“Amman Leila baki taba bata min rai irin yau ba, wai miyasa kike barin zuciyarki tana aikata abun da Talba baya so? Ke baki san yadda zaki faranta masa rai ba? Haba Leila ni kam da baki labarta min wannan abun ba da ban shiga damuwa ba Mtchssssss ”
 
Ta yanayin yadda Madina take mata responding kadai ya isa ya karantar da ita cewar Madina ta fita shiga bacin rai ma.
 
“Ni ma fa ban jidadi ba, that's why na kira ki ko zan samu mafita”
 
“Mafitar me? Ni Wallahi kin bata min rai, i don't think i can eat today, kin bata ran bawan Allah, na sha fada miki haka rayuwarsa take ki bishi a haka mana sai ku samu zaman lafiya amman kin gagara daukar shawarata”
 
“Look Madina na yarda a nan ina da laifi daya janyo aka fada masa magana marar dadi, amman maganar Allah ban ga laifi a abun da na yi ba, Talba yana shigar min hanci da yawa fa”
 
“Yanzu dai na ji, idan kina son mu shirya da ke kije ki bashi hakuri”
 
“Na bashi hakuri fa? Gaskiya ba zan iya ba”
 
“To miye a ciki, ke fa kika ja komai, kuma ba akan abun da yai miki fada zaki bada hakuri ba, akan abun da Momy tai masa”
 
“Zan ga idan zai yiyu”
 
“Please do this for me, tsakani da Allah ko kadan bana son na ji ran Talba ya bace, Mutumen yana son ki Leila kin kasa ganewa ne, kina raina yadda rayuwarsa mata da yawa suna can suna sonsa a haka, ki bi a hankali”
 
“Na ji”
 
Ta fada tana juya ido, bata tsaya jiran abun da kawarta zata sake fada ba ta yanke wayar ta wurgar saman gadonta, sannan ta fadi kwance.
 
 
TALBA POV.
 
A lokacin daya fita daga falon cikin motarsa ya nufa ya zauna, ba karamin taba shi kalaman Momy sukai ba, duk yadda ya so ya ga laifin kansa kan abun da yai ma Leila sai ya kasa, zuciyarsa nata raya masa a daidai yake, hannu ya kai ya dauki wayarsa ya kira Ali.
 
“Hello”
 
“Kana ina?”
 
“Office ya akai?”
 
Iskar dake bakinsa ya busar ya kashe wayar ya aje gefensa sannan yai ma motar key yai reverse ya danna horn, tun kamin ya isa gate suka bude masa sai da ya fito ya ga motar Leila dake waje har lokacin sai dai wannan karon an kullenta amman motar tana kunne, horn ya danna har sau biyu wanda hakan ya saka Bello Police lekowa ya nufo motarsa da sauri, sai ya sauke gilashin motar ya nuna masa motar Leila, Bello na ganin ya nuna motar ya san abun da yake nufi na sai ya masa magana ba. Sai ya nufi motar Talba kuma ya hau titi, driving yake kamar wanda be san inda zai je ba, kadan kadan yake lafiya har ya isa asibitin FMC a inda ya saba fakin ya faka motarsa ya fito yana jin kamar ya juya ya tafi gurin aikinsa sai dai ya san he need someone to talk to, a duk lokacin daya shiga wata damuwa komai kankantarta Ali yake fara fuskanta ya fada masa damuwarsa duk kuwa da kasancewar wani lokacin za su rabu a fada ce ne. Kai tsaye office dinsa ya nufa and he got lucky Ali yana ciki sai dai office din ba shi kadai ba ne tebur biyu ne na dayan abokin aikinsa. Ko kallon gefen da abokin aikin na Ali yake be yi ba  ya nufi teburin Ali ya zauna a kujerar baki. Ali na kallon abokinsa ya fahimci akwai damuwa.
 
“Leila ce ko?”
 
Talba ya dago ya kalleshi, sai kuma ya juya ya kalli teburin abokin aikinsa sai a lokacin ya lura da be shigo ba
 
“No”
 
Ya amsa masa cikin yanayin damuwa.
 
“Na san dai abu ne mai wahala yadda Daddy yake ji da kai abu ne mai wahala ya bata maka rai, sai dai idan wata damuwa ce ta dame shi a san zata iya shafarka”
 
Ajiyar zuciya Talba ya sauke, sannan ya labatawa Ali abun da ya faru. Ali ya kwanta jikin kujerarsa yana kallon Talba duk kuwa ya san kallo na daga cikin abun da abonkinsa ya tsana.
 
“Momy dai ta fusata ne, kuma kai ke da laifi”
 
“Amman Ali ban yi dan taji haushi ba, ba ina nufin bata bawa Leila tarbiya ba, kawai bata fahimci ni ba”
 
Yana fadar hakan ya mike tsaye ya nufi windows din office din.
 
“Kuma na ji babu dadi, na san ba ita ta haife ni ba, amman ban taba mata wani kallo na dabam na bayan uwa, ita ta raine ni a hannunta na tashi na girma”
 
“Kai ka ji zafin abun da ta fada maka balle ita? Yanzu dai ka manta da komai ka dauka cewar kuskure ne irin wanda kowa yake yi”
 
“And seriously ba zan iya zama da Leila da wannan halin ba”
 
“Kai da za a bibiya zata ce ba zata iya zama da kai saboda halinka ba, Talba dan adam duk tara ne be cika goma ba kowa ka ganin yana da inda be cika ba, abun da zai fi kawai ka dauke idonka daga gareta, musamman a yanzu da ka fahimci idan ka taba ta ran Momy yana baci, ka bita a yadda take sai a samu zaman lafiya”
 
“And... ”
 
“And ka koyi bada hakuri Talba, ba zaka ragu ba, mata rarrashi suke so, yanzu duk wannan abun daya faru idan ka koma gida ka yi kamar komai be faru ba, ka samu Leila ka lallabata ka bata hakuri”
 
“Ba a hallici wannan macen da Talba zai bawa hakuri ba, ba ayi mace da zan yi ma yar murya ina lallabata akan tai hakuri ba, matukar tana kasa da ni”
 
“Ya kamata ka sauke wannan nauyin daka dorawa kanka Talba life is very simple”
 
Talba ya juyo ya kalleshi.
 
“Ko?”
 
Sai Ali yai dariya domin ya san halin abokin nasa yanzu zata iya bare musu su fara siyar da hali.
 
“Yanzu dai forget about it, akwai maganar da nake son mu yi da kai”
 
Talba ya juya ya cigaba da kallon harabar asibiti da yadda mutane suka zirga zirga sai dai hankalinsa da ears dinsa suna gurin Ali.
 
“Akwai wata yarinya da aka kawo last week, tana cikin mutanen da yan bidiga suka raunata”
 
Yana tsaka da maganar sai kuma yai shiru yana duba wata takarda dake gabansa.
 
“To ta ina alakarta ta shafe ni?”
 
Talba ya tambaya ba tare da juyo ba, jin Ali ya dauko masa wata maganar da be san ta inda zata masa amfani ba. Murmushi Ali yai yana jinjina halin abokin nasa.
 
“Tana bukatar taimako ne sosai gaskiya”
 
Juyowa Talba yai ya rumgume hannayensa yana kallon Ali.
 
“Kai ina zuciyar taimakonka ta tafi ne? Ko baka taimako?”
 
Ali yayi dariya.
 
“Talba kasan irin taimakon da na yi mata? Tun da aka kawo su ba Gobnati bata sake waiwayarsu ba, babu wani tallafi da ake kawo musu, mostly yan uwa da iyaye ne suke daukar nauyinsu, sisin kwabo babu daga gobnati komai daga alijunsu dana yan'uwansu yake zuwa, wasu an sallame su sai dai wadanda albarushi ya shiga jikinsu ne kawai suke nan suna jinya har yanzu”
 
Ya hade yawun bakinsa sannan ya cigaba.
 
“But yarinyar har yau babu wanda ya taba zuwa nemanta, babu wani da yazo yace shi babanta ne ko yayanta, komai da ake biya daga aljihuna ya fita na taimaka mata saboda ta bani tausayi sosai”
 
Ganin Ali yana maganar babu alamar wasa a tare da shi yasa shi tambayar abun da yake son ji daga gareta.
 
“Miya same ta?”
 
“Na farko dai she can't walk, she can't talk tun da aka kawo ta bata taba magana ba, idan dare yayi sai na yi mata allurar bachi sannan take iya bachi, kuma na yi na yi da ita ta ki tai magana, babu wata alama data nuna yarinyar tana magana, idan ma kaga ta motsa to na matso kusa da ita ne da allura, sai ta fara kallon allurar tana hawaye, and the most sadness part is an yi mata fyade sun lalatata ko mai haihuwa iyaka kenan”
 
Kusan a lokaci daya komai dake aiki a zuciya da jinin Talba ya tsaya cak na dakiku. Kalmar fyade wata irin babbar kalma ce mai razanarwa da muni a kunnuwan tsabtattacin mutane irin Talba, shi din namiji ne ba mace ba, amman ya tsani jin duk wani abu daya shafi fyade balle kuma fyaden kansa, be taba ganin Aminatu ba, labarin wanzuwarta be taba ziyartar kunnensa ba, kamar yadda zuciyarsa da tunaninsa ba su hasaso masa mai irin rayuwarta ba, wani abu daga cikin cikin tausayinta ya kusa zuciyarsa ya samu guri a kusa da kirjinsa ya zauna, hankalinsa ya kara tashi sosai a lokacin da Ali yake kara fada masa halin da yarinyar take ciki.
 
“I don't think kurma ce, domin idan na ce kee zata kalleni amman bayan haka bata yin komai, na sha jera sunaye ina kiranta da su amman bata taba min wata alama da zan gane sunanta ba, kuma kafanta ya kumbura wanda hakan ke nuna ta yi tafiyar da ta wuce kima kuma ta taka abubuwa da yawa gaskiya yarinyar tana bukatar taimako”
 
“Ta ina ya kamata na taimaka? Irin mutanen kamata yai ace gobnati tana daukar nauyin maganinsu fa”
 
“Wallahi kuwa ni ma abun da nake fada kenan amman sai kaga an barsu kara zube ba a kula su. Yanzu dai tana bukatar a duba lafiyar duka jikinta, a kula da kafafuwanta, private part dinta dai yana samun sauki sai dai da zata samu wanda zai kula da ita da zata fi samun sauki”
 
Ali na kaiwa nan ya mike tsaye.
 
“Zo muje ka ganta”
 
“No ba sai na ganta ba, kasan akwai mutane sosai a gurin nan”
 
“Haba dai irin abubuwan nan suna karawa mutum tsoron Allah, Allah kadai ya san halin rayuwar data shiga, ni ba abun da ya fi bani tsoro kamar rashin maganar ta, kuma gashi har yau babu wanda ya taba zuwa nemanta, and bata kallon mutane idan zan shiga inda take har na yi abun da zan yi na gama ba zata kalleni ba sai idan na dauko allura, and wani lokacin sai kaga hawaye na sauko a idonta, idan aka aje mata abinci bata ci yadda ka bar shi haka zaka zo ka tararda shi, idan ka danka mata abu a hannu bata rikewa”
 
“Ya ake take rayuwa bata cin komai?”
 
“Ta hanyar allurar da maganin da muke saka mata a drip”
 
Talba ya lumshe ido ya bude.
 
“Mutanen nan suna ganin rayuwa, farincikin da suke so, kadan ne amman ya gagaresu, a kashe su, a kwashe dukiya a kune kuma wandanda aka raunata a bar su da daukar nauyin kansu, Allah kadai ya san abun da akai mata ko ta gani”
 
“Wallahi ai mu muna ganin abubuwa sosai”
 
Ali ya nufi kofa Talba ya bi bayansa sai suka fito tare suka jera zuwa gurin da ake aje marasa lafiya, suna tafe Ali na masa hirar wasu da aka kawo da yadda sukai ta fama da su, Talba dai be ce Uffan ba har suka shiga female ward din suka doshi gado na 36 da inda Aminatu take kwance. Ko da suka isa sun tarar an ja mata lalube gurin da take, an rufe ta ta ko'ina ta yadda bata ganin kowa kuma kowa baya ganinta. Ali ne ya fara daga labulen ya shiga sannan Talba ya shiga. Kwance suka same ta idonta a rufe hawaye na saukowa ta gefen idonta. A zatonsa babbar mace ce sai da ganinta yarinya mai kananan shekaru yasa jin tausayinta ya karu da kashi talatin cikin dari, domin ya san fyade na daga cikin abun da yake lalata rayuwar ya mace, kuma yana daga cikin abun da mace tafi tsana balle kuma wannan da take karamar yarinya. Ali ya saka hannu ya dauki safar dake gurin ya saka a hannu sannan ya taba kafarta sai ta bude idonta da suka yi ja da alama ta dade tana hawayen ta sauke su akan Talba dake kallonta fuskarsa cike da haiba da annuri. Shi ma kallonta yake ba yabo ba fallasa, daga can cikin zuciyarsa cike take da tausayinta sai dai jinkai da rayuwarsa daya daukarwa kansa ya saka ya kasa barin hakan ya bayyana a kyakkyawar fuskarsa.
 
“Da son samu ne, a ware mata daki daya ita kadai saboda halin da take ciki, so that ta samu kulawa ta musamman kuma tana bukatar ayi mata gwaje gwaje, tana ma bukatar jini”
 
Ali ya fada yana kama hannunta ya tabawa. Har lokacin Aminatu Talba take kallo ji take kamar ta taba ganinsa a wani gurin sai dai bata san ko'ina ba ne, ji take kamar ta bude baki tai magana sai dai bara da kuzarin yin haka, kamar yadda take jin jikinta be da kuzarin riketa balle har hannunta ya jimke wani abu, tabbas yanzu kam ta tabbatar da kalamanta sun kare, kamar yadda take jin komai na rayuwarta a yanzu ya zama tarihi, bata yarda ita ce dai wacan Aminatun dake rayuwa a karkara tare da iyayen da yan'uwa ita ce a nan ba.
Da ace zata iya bude zuciyarta ta sun yi arba da tarin bakinciki da duhu zuci, wanda idan suka karanta wata kila likitan zai tausaya mata ya daina bata taimakon da yake bata na drip da allurar so that ta samu ta huta ita ma tafi sahun yan'uwanta da iyeyenta. Har gobe tana jin karar bindigar da aka kashe mahaifinta da mahaifiyarta a cikin kanta, ta kasa manta yadda yan ta'addan suka rika yawo a jikinta a lokacin da suke kokarin keta rigar mutuncinta, idanuwanta sun ki su goge hoton fyaden da akai ma mahaifiyarta a gaban ido wai shin miya rage mata? Miyasa take a raye har yanzu?
 
Ali ya kalli Talba dake tsaye ya kalli Aminatu data kafe Talba da ido, a zahiri shi take kallo, a badini kuma rayuwarta bayan take hange a cikin idanuwan mutumen da take jin kamar ba a yau ta taba arba da shi ba. Har lokacin hawaye ba su daina zubar a idonta ba.
 
“Kallon mutane ba dabi'ar bace ko dai ta san ka ne?”
 
Ali ya tambaya, kallonsa kawai Talba yai ya dauke kai.
 
“Kin san shi ne?”
 
Bata dauke ido daga kallon Talba da take ba balle har ta kali Ali ta amsa masa. Ali ya kalli Talba dake kallonta shi ma har lokacin.
 
“Ka yi mata magana wata kila zata amsa”
 
“A canja mata daki idan kana ganin hakan ya dace, idan ka yi list din ko nawa za a ashe sai ka fada min”
 
Shine abun da Talba ya fada sannan ya sakar ma Aminatu murmushinsa mai tsada kadan wanda yafi kama da na yake ya juya ya fice. Yana fita sai ta lumshe idonta kamar mai bachi sak rayuwar da take a gidansu ita da iyayenta da yan'uwanta ya soma kawata idonta dake rufe. Juyawa Ali yai ya fice yana kokarin cire safar hannunsa.
 
Shin kin san Kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud
Sandal flakes
Sandal wood
Signature
Kajiji
Damboun kajiji
Halud ball
Wardrobe ball
Coconut sandal
exclusive gowe
Black humra
Body milk
Kulaccam
Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin da kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya, domin siye ko sari ku tuntubi Ramla incense ta wannan number 07038392576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa
 
 
*Dan girman Zatin Allah karki karanta idan baki biya ba. Masu sharing Allah yai muku yadda kuke min. Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
 
 
BATURIYA POV.
 
Bayan ta gama zazzagawa Alhaji Sule rashin mutunci ta shiga tai wanka. Ta shirya cikin farin lace sai aikin gogawa fuskarta powder take, can kuma ta mike tsaye tana kallon kanta a madubi, sai ta ji ana kwankwasa gidanta, jiki na rawa ta aje soson hodar dake hannunta ta fice daga dakin da sauri taje ta bude gidan domin ta san da zuwan Ramlee.
Rumgume juna sukai ita da Ramlee kowa ne na murnar ganin wani kamar wadanda suka shekara basu saka junan a ido ba.
 
“No no ba dai lace din nan kika saka ba? Ai yanzu kuma kin wuce saka kananan kaya”
 
Ramlee ta fada tana yatsina fuska
 
“Ke mai tsada ne fa, yayata ta ba ni shi, mai kudi take aure fa”
 
“Baturiya kenan yanzu ai kin wuce wata ta kwance ta baki ki daura, sai dai ke ki kwance ki bawa wata ta saka, ga wata abaya nan na zo miki da ita kamin mu fara zuwa siyayen tufafi masu tsada”
 
Ta karashe tana mika mata jakar dake dauke da abayar, wani irin tsalle Rafi'a tai ta dire tana murna.
 
“Amman Wallahi kina da zuciya mai kyau, kamar kin san ina mararin abaya”
 
Ta karba da sauri ta nufi cikin dakinta sai Ramlee ta bi bayanta tana murmushi, a falo ta zauna har sai da Rafi'a ta canja tufafin jikinta daga lace zuwa sabuwar abaya, ita kanta ta yaba yadda bakar abayar tai mata kyau kasancewarta fara, cikin zumudi ta nufo falo.
 
“Allah ya miki sura Baturiya Wallahi kina da kyau”
 
Ramlee ta

Join Our Groups

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login