Showing 66001 words to 69000 words out of 332834 words

Chapter 23 - Bakar wasika Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

65587

kalamanta na taba zuciyarsa, misali yake da kansa idan shi ne ya zai ji? Yana rayuwa cikin jindadi lokaci daya ace komai ya tarwatse! Shi kansa maraya ne, amman be san zafin rashin iyaye ba, be san zafin rashin yan'uwa ba, idan wani abun ya same shi da gudu za a kawo masa agaji, tsabanin it. Takurewa tai gurin daya ta jikinta na dan rawa alamar tana jin sanyi ga kuma hawayen har yanzu ba su daina zuba ba, murmushi mai sauti ne ya biyo bayan hawayen.
 
“Inna....”
 
Ta furta tana cigaba da murmushi, sai kuma tai fuskar kuka wasu sabbin hawayen suka zubo mata. Mikewa yai tsaye ya cire Jacket din jikinsa zai lulluba mata sai jikimta ya fara, tana numfashi da karfi ta kara rumgume kanta kana ganinta kasan a tsorace take, a hankali ya lullub mata jacket din sai kuma ya tsaya yana kallonta har lokacin hawayenta zuba suke, wani dogon numfashi yaja ya sauke sannan ya juya ya fara tafiya a hankali zuwa gurin kofar.
 
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un... Taya zan tafi na barki? Ko na gudu harbina zasu yi, ba zan tafi ba tare da ke ba...”
 
Juyowa yai ya kalleta, kana ganinta ka san wani tashin hankalin ne take mafarki, da alama abun da ya faru ya shiga ranta sosai ya zauna, ya kusan minti biyar a tsaye yana kallonta sannan ya fice yaja mata kofar a hankali ya rufe.
 
*Dan Girman Zatin Allah karki karanta idan baki biya ba. Masu sharing Allah yai muku yadda kuke min! Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
 
 
 
Ko kin san kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud
Sandal flakes
Sandal wood
Signature
Kajiji
Damboun kajiji
Halud ball
Wardrobe ball
Coconut sandal
exclusive gowe
Black humra
Body milk
Kulaccam
Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin sa kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya domin siye ko sari ku tuntu Ramla incense ta wannan number +234 703 839 2576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa
 
 
FARUQ POV.
 
Mama ta sauke ajiyar zuciya tana jinjina lamarin Rafi'a.
 
“Faruq ka saka mata ido, duk abun da take tana yi saboda ta bata maka rai ne, kuma komai na rayuwar duniya jarabawa ne, ko da arziki ne Allah ya baka ya ga yadda zaka iya rike su, balle kuma talauci, da muguwar mata”
 
“Wallahi Wani lokacin Rafi'a tana bani mamaki, ita kamar bata san Allah ke yi ba? Shi zai yi ma kansa arziki ne? Sai ta rika abu kamar ba yar'uwa ba?”
 
Aisha ta dana da nata. Sai Faruq ya kalleta.
 
“Wani lokacin ina jin kamar na sake ta na huta, sai dai idan na tuna irin wahalar da mahaifinta yai da ni a karatuna kuma ya dauki yarsa ya aura min duk da a lokacin bana da komai, sai na kamar idan na sake ta ban kyauta masa ba”
 
“Haka ne, wani abu dole a daga mata kafa saboda mahaifinta, domin mutumen kwarai ne, kuma na tabbatar da yana raye Rafi'a ba zata maka wani abun ba, kasan Umma daman ba son auren take ba tun farko shiyasa komai tai bata ganin laifinta, amman kai hakuri Inshallah sauki yana tafe”
 
Ya ja wani dogon numfashi ya sauke.
 
“Ni da har na yanke shawarar na bi Yusufa mu tafi nijar gurin ginar zinarina nan”
 
“Nijar kuma?”
 
Cewar Mama ciki damuwa.
 
“Eh kin ga masu zuwa suna samowa ba laifi, kuma ba kasan inda rabonka yake ba, amman zama haka ba zai yi Mama, hausawa sun ce idan hagu ta ki sai a koma dama”
 
Mama ta girza kai.
 
“Wallahi bana son tafiyar nan nesa Faruq, da dai ka hakura mu ga abun da Allah zai yi”
 
“Mama duk inda rabonka yake sai ka tararda shi, ko kuma ya nemeka, kuma abun da Allah ya rubutawa bawa ko a ina yake zai same shi, na san dai ba zai wuce ki ce kina jin tsoron hanya ba ko abunda zai faru da ni, kawai ki min addu'a”
 
“To Allah ya zaba mana abun da yafi zama alheri, idan tafiyar Alheri ce Allah ya shige maka gaba”
 
“Ameen idan Allah yasa naje ko na siyen fili na samu ai na samu”
 
“Haka ne, amman kudin motar zuwa can fa?”
 
“Har cin abinci da komai zan iya kashe 20k haka Yusufa ya fada min, kuma yace ana kwana uku kamin a samu isa, wannan kudin da ban biya haya ba zan iya cire na mota ciki sai kuma sauran kuma na siya ma Rafi'a abinci na bar mata kamin mu tafi kuma mu ga abun da Allah zai yi”
 
“Toh Allah ya shige maka gaba”
 
“Ameen”
 
Ya fada yana mikewa tsaye sai kanwarsa ta kalleshi.
 
“Ya Faruq ance fa rame ake shiga, ko. Kwanan baya na ji ance rame ya rusga da wasu”
 
Murmushi yai.
 
“Allah shi ke tsarewa ai, ku dai kui ta mana addu'a”
 
“Toh Allah ya tsare, yasa arzikinka na can”
 
“Ameen ya Rabb”
 
Ya amsa sannan yai musu sallama ya fice, ko da ya isa gida har ta gota, a bude ya samu kofar gidan, sai ya shiga da sallama ya maida kofar ya rufe sannan ya shiga falon, sai ya same ta tana waya sai dai ganinsa yasa ta sauke wayar ta kalleshi.
 
“Sannu da zuwa”
 
“Yauwa, ya gidan?”
 
“Alhamdulillah”
 
Sai ta tashi ta nufi inda abincinsa yake ta dauko masa ta aje masa tare da ruwa.
 
“Ina Sultan?”
 
“Yayi bachi”
 
Ta amsa sannan ta zauna kusa da kujerar da yake zaune, kallonta yake har ta zauna din, gaba daya yau ta canja, daman can fara fes amman haskenta and yau ya karu sai wani sheki take tana ta kamshin hummura mai tsada. Dauke kansa yai ya maida dubansa gurin abincin data aje masa yana hade yawu, rabon da wata mu'amalar aure ta shiga tsakaninsu har ya manta, domin bata yarda idan ma ya neme ta, idan ya matsa sai tace ga ciki ba zata iya ba, shi kuma baya son yi mata da karfi hakan yasa ya dauke mata kai ta wannan bangaren ba dan baya bukata ba sai dan ba zai iya ja'inja da ita ba.
 
“Rafi'a ina ta shawara da kuma neman zabin Allah”
 
Ta kalleshi da sauri a tunaninta ko zai fada mata cewar daya faga cikin aikin da yake Applying ne wani ya fito.
 
“Na me? Aikin ka samu ne?”
 
“Aa, ina shawarar zuwa nijar ne?”
 
Wani irin yatsine fuska tai kamar wanda tai arba da abun kyama.
 
“Nijar fa kace? Ba dai gurin ginar zinari ba ko?”
 
“Can mana”
 
“No nonono, Wallahi ba zan yarda ba, so kake ka ja min abun magana a gari? Ace mijina ya tafi gurin ginar zinari? Talaucin har ya kai nan? Aa Wallahi ba zaka je ba”
 
“Shi zuwa ginar zinari zunubi ne? Wace irin magana ce wannan nan?”
 
“Kana tafiya za a ce talauci ya matsa mana har ka bar gari ka tafi nema nijar, ka ja min abun magana, kawaye na mazajensu daga masu aiki a kamfani sai banki sai ma'aikatun gobnati, ni kam ba zan iya ba Wallahi”
 
“To sai na fasa saboda ke nan? Ni na riga na yanke shawara, kuma na zo na fada miki ne saboda na baki hakkinki”
 
“To Wallahi ba zan yarda ka je ba, Wallahi sai dai ka sake ni ka tafi na san ba mu tare”
 
Dubanta yai irin duba na mamaki.
 
“Rafi'a me kike son ki zama? Ke kin isa ki yi ma kanki arziki ne, da abu kadan zaki fara cewa talauci?”
 
Sai ta mike tsaye domin ya fahimci da gaske take.
 
“Wallahi Faruq, na rantse da Allah ba zaka tafi nijar ginar zinari da aurena ba, sai dai idan tafiya ce zaka yi ta har abada, wanda babu dawowa, wai kai baka da zuciya ne? Baka san Annabi ya faku ba, na gaji da abun kunya Faruq, na gaji, aurena dole ne? Ni kadai ce mace a duniya nan ne? Ba zan iya ba, ga danka nan yayi wayo amman ka kasa saka shi makaranta, wannan da zan haifa ma na san dan taure zaka yanka min”
 
“Sai ki saki kanki ai, ba saki ba? Ba zan saki ba kuma sai na tafi nijar din ki mutu, ina hakuri ne dake kawai saboda Mama da kuma mahaifinki”
 
Ya fada yana mikewa tsaye, sai ta sa gabansa.
 
“Wato ka fito gurin bakar tsohuwa ta kitsa maka abun da take so a kai...”
 
Bata karasa ba ya wanke mata fuska da mari sai da ta fadi zaune. Ta fashe da kuka.
 
“Faruq ni ka mara?”
 
“Har abun da yafi mari zaki samu, matukar iskancinki da rainon wayo ya kai ki ga taba mahaifiyata, ai ko da ba ta hada komai dake ta cancanci girmamawa saboda tana sarakuwarki balle tana a matsayin kanwar mahaifinki”
 
“Ita bata san da zumuncin bane ta barka kana ta cutar da ni? Ba zan iya ba, na ce bana so ka sauwake min mana”
 
Har yayi kamar Ya bude baki yace na sakeki sai kuma wata zuciyar ta hana shi. Be sake kulata ba ya shiga bedroom din, bakin gado ya zauna yana kallon Sultan dake ta bachi ya kai hannu ya shafa shi, makomar dansa yake zubawa idan har ya sake ta rayuwarsa zata zama abun tausayi, domin zaman zai zame masa a tsakanin gida biyu, gidan mahaifinsa da kuma inda Mahaifiyarsa. Tsabar bacin rai da tunani be ci abincin ba ya kwanta kusa da dansa, Baturiya kuma ta kwana a falo.
Washe gari waina ya siyo musu abun kari kasancewar aljihunsa da dan nauyi irin na masu nema yau da gobe, bata gaishe ba tun da garin Allah ya waye, sai dai hakan be hana shi ce mata zai fita ba, da harara ta bishi babu Allah ya tsare balle addu'ar alheri.
 
“Allah yasa kai hadari ka mutu..”
 
Ta fada bayan ta ji karar rufe gidan, sannan ta tashi ta bude wainar ta zubawa Sultan, ita kuma ta nufi wayarta ta dauka ta kira Fahat, ringing biyu ya dauka.
 
“Fee'at”
 
Sai ga murmushi a fuskarta kamar ba ita ba, bata kula da Sultan ba ta cigaba da wayarta tana masa kalaman soyayya kamar yadda shi ma yake mata. Sun kusa awa daya suna abu daya sannan sukai sallama tana masa kiss a wayar, duk abun da take Sultan na kallonta sai dai ita bata lura da hakan ba. Fitowa tai waje ta fara gyara gidan domin Ramlee ta fada mata karfi goma za su hadu. Ko da tara tai Baturiya ta gama komai har ta shiga ta yi wanka. Sai da ta shirya sannan ta kai Sulta makota ta dawo gidan ta kara daukar wasu kayan matan ta sha daman Ramlee ta nuna mata wadanda zata sha idan tana kusan tafiya.
 Tara da rabi kiran Ramlee ya shigo wayarta, jiki na rawa ta dauka kamar ba ita ce ta gama jin tsoro ba a jiya.
 
“Madam hop kin shirya”
 
“Na shirya, ke kawai nake jira”
 
“Haka na ke so, ba wasa ganin nan nima na kusa karasowa”
 
“Sai kin iso”
 
Ta aje wayar tana murmushi, ita ma kanta ta san ta yi kyau, sai kamshi take zubawa kamar sabuwar amarya, kamin Ramlee ta iso ta shafa hoda ya kai sau shida, turare kan ba adadi irin feshin da take masa.
 Tana jin sallamar Ramlee ta dauki wayarta da jakarta ta fito waje da sauri.
 
“Wow yanzu kika fito da sunanki n Baturiya, amman mutumen idan ya ganki sai ya rude”
 
Baturiya ta yi dariyar jindadi.
 
“Da gaske”
 
“Wallahi kuwa, sam sam baki dace da Faruq ba, ke din matar manya ce, amman fa karki fada masa cewar kina da aure domin na ce masa ke din bazawara ce”
 
“Ke ma dai da wata magana, ya za'ayi na fada, Allah dai ya sa inda zamu je ba public place ba ne, domin akwai wadanda bana son su gan ni”
 
“No guest house dinsa ne, muje dai kar mu bata lokaci”
 
“Amman kin san me? Idan na fita da kwaliyar nan haka ina kamshi mutanen unguwa za su fara saka mana ido”
 
“To ya zamu yi? Ke dai ina ruwanki da mutane ne wai?”
 
“Aa bari dai a saka hijab da nikab idan na je can sai na cire a motarki”
 
“Haka yayi yi sauri”
 
Ta juya ta koma dakinta da sauri ta dauko katon Hijab ta saka tare da niqab sannan fito ta rufe gidan.
Tun daga yanayin ginin unguwar da shuke shuken zaka san cewa unguwar manyan mutane ce, a gaban wani katon gate suka faka Ramlee tai horn Mai gadin ya leko tai magana da shi sannan ya bude mata ta shiga, a harabar gidan tai fakin ta ciro wayarta ta kira shi.
 
“Alhaji mun iso”
 
“To yayi Kyau Hajiya Ramlee a barta ta dan huta gani a hanya, garin sauri ma na kade wasu amman dai na gama komai zan iso yanzu”
 
“To yayi Alhaji sai ka iso”
 
Ta aje wayar sannan ta labartawa Rafi'a abun da ya faru da shi.
 
“Kuma ki sake jikinki ki kwashi arziki, domin yana son ki Wallahi na fada miki hotonki kawai ya gani amman duk yabi ya rufe balle kuma ce ya yi arba da ke”
 
“Inshallah ba zan baki kunya ba”
 
“Yayi kyau, haka nake son ji, yanzu mu shiga ciki na nuna miki falonsa sai n fito na bar ku ku sha shagalinku”
 
Ramlee ta fada tana murmushin jindadi. Sai Baturiya ta cire Hijab din da Niqab ta kai hannu ta bude motar wayarta tai kara.
 
“Allah yasa ba mijin nan naki ba ne”
 
Cewar Ramlee tana tabe baki, fasa fitar Baturiya ta yi ta ciro wayar daga jakarta ta duba.
 
“Shi ne kuwa, ban san mi zai ce min ba, ko kuma ya dawo gida ne oho”
 
“Karki dauka dan Allah zai wargaza mana shiri ne”
 
“Ai ba zan dauka ba”
 
Ya fada tana kallon wayar dake ta ringing har ta gaji ta tsinke, sai gashi ya sake kira sai dai wannan karon ta ji gabanta ya dan fadi.
 
“Kai wannan miji na ki da ci yake, gaskiya ki kashe wayarki kar ya zo yana damunki da kira ya lalata mana shiri”
 
“Wallahi kiran Fahat kawai nake jira, saboda yace zai kira ni anjima bana son na kashe wayar ya kira ya jita a kashe zai damu ne”
 
Ramlee ta mata wani kallo.
 
“Da alama dai shi ma dan hannu ne”
 
“Aa Wallahi shi ai son aure yake min da gaske, na nuna Masa ni Budurwa ce”
 
“Amman ke yar banza ce, ya zaki yi da Faruq?”
 
“Haba Ramlee kina min fatar zama da shi? Ai rabuwa zamu yi, kin ga idan ya sake ni ina zubar da cikin nan na cika idda zai na yi aurena”
 
“Kina ganin Faruq zai sake ki ne?”
 
“Dole na idan na bude masa shikashikan rashin mutunci ai dole ya sake ni”
 
“To dan fa ki yi yaya da shi? Ai kin san za a bincike ki musamman yayan manyan mutane basa aure zai sun zurfafa bincike”
 
“Ai idan na fita zan bar Sultan a gurin Faruq ne, ba da shi zan je ba, kuma shi Fahat din ai yace min a Lagos yake aiki, kin ga zamanmu a can zai kasance ba a nan ba, zan iya boye komai”
 
“Ki ce kema kin iya bala'i
 
Sai duk suka saka dariya, kiran Faruq ne ya sake shigowa wayar, wannan karon wani tsaki taja ta kashe wayar gaba daya.
 
 
 
 
TALBA POV.
 
Sai da yai sallah azahar sannan ya karaso gida, tun kamin yayi fakin idonsa suka sauka akan Leila dake zaune a daya daga cikin kujerun da suke balcony rike da wayarta sai cup din lemu a gaban kujerarta tana taunar cingan har wani kis kis take. Yayi kusan five minutes a motar sannan ya bude ya fito ya nufo inda take zaune ya zauna ba tare da yace da ita komai ba, hakan ya bata damar dauke kai daga gefen da yake ta maida wani gurin tana cigaba da taba wayarta.
 
“Can we talk?”
 
Ya fada ba tare da ya kalli inda take ba, sai ta juyo ta kalleshi.
 
“Ta fada maka ba ni ba ce ba kenan?”
 
Shi ma juyowa yai ya kalleta fuska ba yabo ba fallasa.
 
“Daddy ya damu dake ne i want us to talk”
 
“Da gaske?”
 
Sai ta mike tsaye ta dauki cup din lemun ta wuce ta bar masa gurin. Tana kokarin kai hannu ta danna door bell din kofar falon sai ga Kabir ya fito, ko kula shi bata yi ta shige, da kallo ya bita kamin ya juya ya kalli Talba dake kallon harabar gidan, har lokacin tunanin Aminatu yake. Karasa Kabir yai ya zauna a inda Leila ta tashi.
 
“Ya jikinta?”
 
“Da sauki...”
 
Talba ya amsa ba tare daya kalleshi ba.
 
“Ka yi magana da Leila ne?”
 
Ya girgiza masa kai.
 
“Wani lokacin baka sanin damuwar mutane idan baka kusantar su, you see yan gudun hijirar nan da kake gani a hanya wasu a fankon guri, suna da labaruka masu taba zuciya”
 
“Ita ma tana daya daga cikinsu ne?”
 
“Tana daya daga cikinsu ne?”
 
“Yeah they raped her, killed her Father, mother suka gona musu gida, suka kashe yayyunta and raped her mother in front of her, labarinta akwai tsoro da taba zuciya, yanzu haka she can't walk saboda wahalar data sha gurin mutanen nan, and bata da kowa kuma tana bukatar kulawa sosai”
 
Talba ya fada cikin yanayin dake nuna zuciyarsa ta tabu sosai da labarin Aminatu.
 
“You know a lokacin da kake raina ni ni'imar da Allah yai maka, wasu da yawa suna can suna neman kadan, a yadda na fahimta now yanzu farinciki take bukata, saboda ya cire rai daga shi har tana neman kashe kanta, and Ali and wannan likitan sun fada min abun nan ya taba ta”
 
Kabir ma saurarensa yake cike da tausayin Aminatu duk da kasancewar ba taba ganinta ba, sai dai ya san waye Talba duk abun da zai saka shi a damuwa ko tunani ba abu ne kadan ba.
 
“Yanzu a wane matsaya take”
 
“Tana samun kula a asibitin, amman babu mai kwana a inda yake kuma kasan da ace tana uwa ko wata yar'uwa a raye zata fi samun kulawa, tana jin tsoro sosai har magana take idan tana bachi, and likitan ya fada mim idan tana yawan damuwa zuciyarta zata iya bugawa, yarinya ce karama kamar Amal, bata san inda zata je ba”
 
“Haka ne mutane suna cikin hali, sai dai idan baka shiga cikinsu baka sani”
 
Talba ya mike tsaye yana saka hannunsa aljihu. Ya nufi bangarensa, Kabir ya bishi da kallo yana murmushi.
 
LEILA POV.
 
Tana shiga dakin ta dauki wayarta ta kira

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login