Showing 258001 words to 261000 words out of 332834 words

Chapter 87 - Bakar wasika Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

65649

Momy zuwa asibiti, sai dai kamin su isa asibitin suka ji ta yi kalmar shahada ta daina numfashi, sai suka yi zaton ko ta mutu ne, bata min yadda akai suka tabbatar da mutuwar, ta dai fada min cewar hankalinta ya tashi sosai kuma Hajiya tace idan suka kaita asibiti dole za a san sun da maganar, gudun hakan yasa suka binne gawar a tsohon gidan gonar Momy, bata fada min yadda suka binne gawar ba, amman ta fada min cewa a tsohon gidan Momy suka rufe gawar. Tun daga lokacin sai tsoro ya kama Leila har mafarki Baaba take, wani lokacin kirana take ta fada min, and i always told her rai ne dole hakkin rai zai saka ta a haka.. Life goes on... Wallahi ban taba tunanin zan aikata wani abu makamancin wannan ba”
 
Hajiya da jiri ya fara dibanta ta cire hannayenta daga na Madina tana kallonta a tsorace.
 
“Kisan kai kika aikata?”
 
Madina ta yi saurin girgiza kai.
 
“Aa, ban aikata kisan kai ba, sai dai son Talba ya saka na aikata abun da ban yi tunani ba, lokacin da maganar auren Leila da Talba ta matsa kusa sai na ji kamar mutuwata ce take matsowa a kusa da ni, saboda ina son Talba, kuma na san abu ne mai wahala Leila ta yarda na auri Talba idan har ta aureshi. Hakan yasa na yi amfani da wannan damar na shirya yadda zan tsorata Leila saboda na saka hankalinta ya tashi maganar auren ta watse, na so na saka Leila a cilas ta rabu da Talba ta hanyar da ba zai san dalilin rabuwar da tai da shi ba, so that ya kalli hakan a matsayin cin amana, ni kuma sai ya so ni”
 
“Ban fahimci me kike nufi da kin tsorata taba?”
 
“Wasika na shirya aika mata a gidansu, da duk wani gurin inda zata risketa, wasika ta tsoratarwa na abun da ta aikata, bayan na gano inda gawar Baaba take”
 
Wani irin kallo Hajiya take yi ma Madina mai cike da alamar tambaya kala kala, gaba daya sai take ganinta kamar ba yarta. Ta ya ta aika duk wannan abun?
 
“Ya akai kika gano inda gawar take? Ke da wa kika yi wannan abun Madina?”
 
Ganin idon Hajiya ya kawo ruwa ya saka Madina ta fashe da kuka.
 
“Ni kadai, ni kadai na aikata haka, sai kuma mutanen da na biya”
 
“Ina kika same su?”
 
“Na yi magana da, Jamil ne Hajiya ai kin san shi? ”
 
Hajiya ya gyada kai.
 
“Na kira a waya na fada masa, akwai wani neighbor din mu da yake min cin mutunci yana zagina, so nake a dauko min shi a bashi kashi a sake shi, sai yace min ba matsala zai sama min wasu yan unguwarsu yaran yan siyasa ne ya san za su iya wannan aikin, mun yi magana da shi da safe da yamma ya kira ni yace min ga inda zamu hadu mu yi magana. The following day after na dawo daga aiki na saka mask na tafin can na hadu fa su suka fada min zan ba su 20k da address din inda mutumen yake, ba su fake addressees kuma na yi musu kwatancen karya na fuskar yadda mutumen yake, na karbi number wayarsu, sai bayan da na bar gurin kuma na tabbatar Jamil ua tafi sannan na kira su na fada musu ba wacan aikin za ayi min ba, wani dabam ne na fada musu ina son na tsorata wata ne, kuma zan ba su 500k amman yanzu zan fara ba su 200k idan aiki yayi zan cika musu 300k, sai suka ce min ba za su iya wannan aiki ba, amman ba su hada ni da wanda yake yin irin wannan aiki, suka kirashi a waya suka hada mu kai magana da shi, sai ya fada min inda zamu hadu, na je na same shi a gurin muka yi magana na fada masa komai, sai ya fada min dokokinsa cewar zan ba shi 500k a yanzu, idan aiki ya gama zan ba shi 500k kuma dole ne na bude fuskata ya gan ni, a dole na bude fuskar, sai yace min weather na yarda ko ban yarda ba, deal ya fara daga yanzu saboda ya ga fuskata, wai idan ban aminta na aikata ba, zai same mi wadanda nake son aikatawa haka ya fada musu, kuma ta aikata hakan a matsayin ni ce, a dole na aminta wasu abubuwan shi ya shirya yadda za su kasance, ban san yadda akai ya samo abubuwan da yake turawa Leila ba, sai dai idan ya aikata ya kan fada, saboda na sani, amman na fada mishi ya dakata daga lokacin da Momy ta fara zargina”
 
Madina bata karasa ba, Hajiya ya mike tsaye baki sake ta nufi gurin wardrobe dinta tana jin kamar mafarki take. Madina ta daga kai tana kallon mahaifiyarta.
 
“Na aikata duk wannan abun ne saboda Talba Hajiya, ina matukar son Talba”
 
 
Hajiya ta juyo ta kalleta hawaye na sauko mata.
 
“Ki kaddara baki aikata komai ba, ki rufe wannan sirrin ki aje, bayan shi wannan mutumen waya san da kin aikata haka?”
 
“Leila, saboda ta yarda da managar Momy da kuma hadarin da aka fada min Talba yayi na tafi gurin duba shi ba tare da ta sani ba, mun fadawa juna magana ni da ita, a ciki na amsa mata cewar tabbas ni na aikata hakan amman ba ni na sace Aminatu ba kamar yadda take zargina”
 
Da mamaki Hajiya take kallonta kamin ta dawo ta zauna.
 
“Wa sace ta? Yaushe aka sace ta?”
 
Madina ta share hawayenta ta hade abu da karfi.
 
“Hajiya na taba fuskantar Talba a office dinsa na yi masa kalamai na nuna kauna a gareshi, amman be saurareni ba, sai yai kamar be fahimci manufata ba, a lokacin na san ban yi abun da ya dace ba saboda yana a matsayin mijin da Leila zata aura, amman ganinsa da na yi da Aminatu ya saka na ji a ranar cewar baya son Leila kuma zai iya kamuwa da so na indai har zai so yarinya kamar Aminatu”
 
Ta kai hannu ta share hawayen dake sauko mata.
 
“Ranar da na fita da dare, ban san inda zan je ba, saboda bacin rai ina ta yawo ba dan na san inda zanje ba, na shiga area Igala sai na ga farar motar Talba fake gaban wani gida, har na wuce sai kuma na dawo na koma nesa da inda ya aje motar na faka tawa motar, ban san gurin wa ya zo ba, amman na yi tsammanin ko abokinsa ne ko kuma wani abun na dabam ya kawo shi. Kuma ni burina a lokacin ya fito na yi arba da fuskarsa na samu natsuwa, ba da wata manufa na yi haka ba, amman a mamakina da ya fito daga gidan sai ya fito tare da Aminatu, kuma ya rumgumeta na Wallahi a lokacin na ji kamar na mutu, domin ban taba tsammanin Talba zai iya sumbantar yarinya kamar Aminatu ba, bata da komai a yanzu kuma ita ba yar kowa ba ce, a lokacin zuciyata bata raya min cewar aurenta Talba yai ba, domin babu wanda ya san da maganar auren, cikin kuka na haskasu da motata, idan ya tako zuwa gaba sai na matsa baya, idan ya tsaya sai na tsaya, ganin ina yin baya ya saka ya ciro wayarsa ban san wa yake kira ba, ni kuma sai na ji tsoron kar wani ya tararda ni a gurin sai na baya da gudu na fice daga area gaba daya”
 
Ta hade yawu sannan ta kalli Hajiya.
 
“Idan zaki tuna ranar na fita na dade a waje, har hankalinki ya tashi, na fita ne saboda na samu sanyin zuciya na kalaman da na yi ma Talba a office, amaimakon haka sai bakincikina ya karu, na dawo gida cikin damuwa ina kuka, a ranar na fada miki cewar Talba baya son Leila, domin da yana son ta ba zai kula Aminatu ba”
 
Hajiya ta daga mata kai tana tuna lokacin.
 
“An yi haka”
 
“A cikin dare na yi magana da wannan mutumen da na fada masa ina son ya sace yarinyar, na fada masa yadda zai ce da kuma kalar motar da zai tafi, washe gari kuma muka je na nuna masa gidan da kaina amman na fada masa kar ya mata komai, da farko ita ma na so a tsorarata ne ta yadda zata nisanta kanta da Talba. Amman sai hankali ya tashi a lokacin da Talba ya ji an sace ta ya haukace har yake fadar cewar ya aureta kuma yana zargin Leila da Kabir a hannu a sace ta, a lokacin tabbas na ga irin son da Talba yake yi ma yarinyar a kwayar idonsa, kuma na tabbatar idan wani abu ya same ba zai saurarawa kowa ba, domin yayi ta fadar irin abun da zai yi ma wanda ya saka aka yi mata haka”
 
Hajiya ta rufe baki hawayen idonta ya tsaya cak. Madina ta sauke ajiyar zuciya ta ce.
 
“Shiyasa sai na ce ya aje ta a cikin daji ko gona, kuma ya turawa Kabir sako saboda shi ne namiji kuma zarge shi, na saka yayi masa haka ne saboda zarginsa ya karfafa kansa, ita kuma ita Leila ta ji da wacan plan din, domin rana daya aka aikata komai sace amintun da kuma kai wasikar”
 
Hajiya ta kasa cewa komai sai kallonta take with shock, da ace wani ne ya fada nata yarta Madina zata aikata haka ko kuma ta aikata ba zata tana yarda ba.
 
_______________________________
 
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
 
“Mi ya zo cikin kanki ne Madina? Taya idonki ya rufe kika aikata duk wannan abun? Baki yi tunanin halin da zaki jefa kanki ba? Baki yi tunanin matsalar da zata biyo baya ba?”
 
Ta girgiza ma Hajiya kai.
 
“Duk wannan tunanin be zo min ba Hajiya, har sai da na riga na aikata, a tunani asiri ba zai tonu ba, domin zan aikawa da hakan ne kawai da nufin na tsorata Leila a fasa auren, ita ma Aminatu na tsoratata ta nisanta kanta daga Talba, a tunani babu wanda zai gane, yanzu gashi Aminatu ta ga mutumen har ta fada cewar shi ne ya sace ta, garin nemansa ne ma Talba yayi hadari?”
 
“Be rufe fuska ba a lokacin da zai dauke ta?”
 
“Ya ce min be rufe ba, ban kuma san dalilinsa na yin haka ba”
 
“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un”
 
Hajiya ta furta tana sake mikewa tsaye jikinta har rawa yake.
 
“Shi ne maganar da kika ji ina yi da Leila, ina son na tsoratata ne ta fasa auren Talba da kanta so that ni da ita duk mu rasa”
 
“Ba shi ne matsalar ba Madina, ke kina ganin yadda kika jefa janki a wannan halin Leila da Momy za su zuba miki ido ne kina wasa da rayuwarsu? Kina son cilasta Leila ta fasa auren Talba? Kuma kin riga kin san sirrin da suke boyewa? Momy ba zata yarda Yarta taje gidan yari ba, haka zaki ka saboda ke Leila ba zata fasa auren Talba ba, kuma Aminatu zata yi ta sheidar fuskar mutunen har a gane inda yake ya fadi cewar ke kika saka shi”
 
“Me kenan zai faru”
 
Ta tambaya tana mikewa tsaye tare da zaro ido.
 
“Dole za su shirya miki wata gadar da ba zaki iya tsallakewa ba, ko kuma su kashe kamar yadda sukai ma Baaba, wata kila ita ma akwai wani abu data sani shiyasa suka aikata mata haka. Madina baki san zuciyar mutane ba, kashe rai a gurin wani ba komai ba ne, musamman wannan zamanin da muke ciki, mutane da yawa suna aikata kisan kai saboda cikar burinsu da biyan bukatunsu”
 
“Na san na jefa kaina a matsala Hajiya, amman ba zai zama ni kadai ce a tashin hankalin ba, dole ne ni da Leila mu rasa”
 
Hajiya ta fashe da wani kuka ta bata san ta inda ya zo mata ba.
 
“Miyasa kika aikata Madina? Kin jefa kanki a Matsala, kin san hukuncin da ake yi ma wanda yai kidnapping kuwa? Kuma kin bata budurcinki, kin bata sunan gidan nan, ba ke ba ko yan'uwanki sai ya shafa, kamin ki aikata komai ya kamata ki yi tunani, ba a biyewa son zuciya Madina, zuciya tana kai bawa ga halaka ne, kuma tun ba yau ba na fada miki ki shafa kanki lafiya ki cire son Talba a zuciyarki, amman baki ji ba ana nuna muku abun da ya dace ku yi kuna bin son zuciyarku. Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un”
 
Madina ta hade abun da ya tsaya mata a wuya, hankalinta be taba tashi akan abun da ta aikata ba irin yanzu da Hajiya ya zayyana mata irin matsala da hukuncin da zata fuskanta. Kasa tai da idonta zuciyarta na bugawa kamar zata fado, tafiya ta fara yi a hankali tana nufi kofar fita ba tare da ta sake cewa Momy komai ba, ta fice daga dakin zuwa dakinta gaba daya jikinta ya mutu, tsaye tai a dakin kamar mai tunanin abun da zata yi, kamin ta juya ta kalli wayar ta sako ya shigo, karasawa tai jikin gadon ta kai hannu ta dauki wayar, 8 miss calls ta tarar daga Leila sai kuma sako daya da ya shigo wayarta a yanzu shi ma daga Leila ne, bude sakon tai tana dubawa.
 
_Kina tunanin kina da wayo? Karki fasa ki cigaba sa aiko min da sakon da kika, sai na nuna miki na fiki iya game din, tsakanin ni da ke sai an ga waye loser_
 
Ta karanta sakon yafi a kirga bata fahimci komai ba, domin bata san ta saka a sake aikawa da Leila komai ba, wata kila kuma Leila tana kara gargadinta ne akan maganarsu ta farko.
 
“Ba zan ni kadai ce a damuwa da halaka ba, kamin wani abun ya faru ya kamata na dauki mataki”
 
Ta fada tana jin kamar kuka zai zo mata, sai karfin halin tare shi take ta hana hawayen dake idonta zubowa.
 
“Why? Kamar wanda akai wa asiri miyasa idona ya rufe?”
 
Ta zauna gefen gadon tana tambayar kanta, hawaye na sauko mata daga bisani sai ta fashe da kuka.
 
 
 
FARUK POV.
 
Ya karbi kofin da Mama ta gama shan shayi da shi ya aje.
 
“Amman ki daure ki cinye wainar kwan”
 
“Gashi ai ina ci, Allah ya maka albarka”
 
Mama ta fada tana murmushi, sai ya amsa da Amin ya kama hannun Sultan ya rike.
 
“Likitan yace ko da an sallame ki zaki rika zuwa ana miki gashi”
 
“Gashin nan fa ance akwai tsada sosai”
 
“Haba Mama idan Allah ya kawo abu ai sai ayi maka shi, samun lafiyarki ya fi min komai a yanzu”
 
“Duk da haka dai, bana son ka kashe kudin nan, ka samu gida ka siye ka siye dan abun hawa, sai kuma business kamin Allah ya kawo aiki”
 
“Inshallah haka zan yi, yanzu dai so nake ki samu lafiya hankalina ya kwanta, sai na je na kai zinarin na siyar na siye gidan da abun hawa, kuma a saka Sultan makaranta, Rafi'a ma ina son na bincika yawan kudin abincin da ta ci na biya kuma na siye komai na suna”
 
Mama ta dan yi shiru kamin ta kalleshi ta ce.
 
“Anya wai akwai cikin nan kuwa? Tun fa da tafi bata taba waiwayarmu ko sau daya tace a siya mata kaza ba ko ayi mata kaza”
 
“Ba zata yi ba, saboda tana ganin ta bar gidan talauci tana ganin cewar ba ni da komai to me zata tambaya? Amman ni dai zan sauke nauyin hakkina da Allah ya dora min”
 
Mama ta tabe baki.
 
“Rafi'a bata da tunani sam”
 
“Kowa yai na gari dan kansa, komai mai wuce nan yanzu ma ya zama kamar ba ayi ba balle kuma gaba? Shiyasa ni yanzu ba duk mace ke burge ni ba, yawancin matan yanzu kwadayi yayi musu yawa, kuma ba kowa ke tsoron Allah ba”
 
“Haka ne, amman ai ba taru an zama daya ba, kuma duk yadda mutum yake zai samu mai sonsa”
 
“Wallahi ni gaba daya aure ya fita raina Mama, ban sani ba dai ko gaba”
 
“Aiko yanzu ya dace ka yi shi, ka siye gida ka tare kai kadai babu mata?”
 
“Ga ku? Ai mai Part biyu zan siya Mama, ku daya ni daya”
 
“Duk da haka dai, aure cikar kamalar mutum ne, kuma idan kai auren a yanzu ai zata ji haushi ta san cewa akwai masu sonka”
 
“Ya zaka yi ka gane masoyan gaskiya Mama”
 
“Duk yadda zaka yi ba zaka taba ganewa ba, kawai dai ka auri yar gidan mutuncin kuma ka barwa Allah zabi kai ta addu'a”
 
Ya sauke ajiyar zuciya ya saki Sultan ya zuba hannayensa duka biyu aljihu.
 
“Allah ya zaba mana abun da ya fi zama alheri, ya baka mata da gari mai kaunarka tsakani da Allah”
 
“Ameen”
 
Mama ta mika masa plate din bayan ta gama cinye wainar kwan.
 
“Na zaka dauki shawarata, da kaje ka siye gidanka tun yanzu saboda kudi ba a wasa da su, kuma kasan mutane suna da sa ido, wani zai iya maka ture ko ma ya zo da kansa, saboda ana ganin ka dawo ka samu dukiya, kara ma kome zaka siye ka siye shi da wuri, kasan kasar nan kis ake jira kuma mutane na da hassada, wani ma yana ya tsila ido yana son ganin me ka zo da shi, kuma shi irin wannan kudin na zinari mutane suna cewa baya son ajiya fa”
 
“Duk yadda kika ce Mama haka za'ayi, amman dai sai jibi idan na ga yadda jikin na ki ya kara yi tukuna”
 
“Jiki ai yanzu Alhamdulillah, lafiya ta samu sai dan abun da

Join Our Groups

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login