Showing 168001 words to 171000 words out of 332834 words
son yarinyar nan ba zata mata komai ba”
“Ban san da haka ba, idan ba wani abun tai mata ba, ko kuma ya faru da ita miyasa bata fada min inda take ba? Ali na damu”
Ya fada da raunanniyar murya kamar mai shirin yin kuka. Ali ya fada shi cike da kulawa.
“I know amman tun da tace ka bata lokaci ka jira mana?”
“Jira nawa zan yi? Har da mun je garin nan ya fi sau uku, amman kaka ta ki ta fada min inda yarinyar nan take, ban san dalilinta na yin haka ba, idan ma wani abun ne ya same ta ya kamata ta sanar min, kasan ma me kake tunani?”
“No”
“Ko dai an dauke ta kaka ta ki ta fada min?”
“Idan har barayi sun shigo, da ai sai kaji”
“Not just Barayi wani ma zai iya, kuma Kaka ta ki fada min”
“Wani wa?”
Ali ya tambaya yana masa kallon fahimtar inda ya dosa. Talba ya saka saka hannayensa duka biyu ya shafa fuskarsa yana sauke idonsa a harabar Company.
“Dan Allah Talba karka saka Leila a maganar nan, na farko dai Leila bata san ka auri yarinyar nan ba, na biyu ban ga dalilin da zai saka tai haka ba, ka rika kyautata mata zato mana, and yanzu idan akai auren nan haka zaka yi ta kallon Leila tana zalintarta? I don't think zaka iya adalci a tsakaninsu ma”
“Ali Aminatu tana da rauni, not like Leila, ina jin rashin yarda da Leila so many times ban san miyasa ba”
“Ya za'ayi ka ji yarda? Bayan ka dauki rashin yarda ka saka a zuciyarka, haka za ku yi zaman auren kowa na ganin laifin dan'uwansa? Kowa yana ji da kansa? Musamman ma kai kara ma Leila ita mace ce kuma kana saukowa na san zata sauko”
Talba ya daga jikin motar yana kallon Ali.
“Baka tana ganin laifin Leila ba, Ali you're always on her side”
“Yeah saboda tana da gaskiya, just like you and Aminatu, ji yadda ka tashi hankalinka saboda kawai baka ganta ba in few months, kaje kauyen nan ya fi a kirga, ka kasa samun natsuwa ka tashi hankalinka just because of her, ashe da ba kai ka aureta ba da ka samu sabon aiki”
Talba ya mike tsaye yana kallon Ali with serious face.
“Wallahi weather you believe it or not I'm not in love with Aminatu, all what i know is i like her and ina matukar tausayin yarinyar fiye da yadda kake tunani, i marry her saboda Kaka, amman da ace yau Aminatu zata ga wani namijin da take so zan iya sakinta ta aureshi kuma zan zame mata uba wajen ganin komai ya tafi daidai ta samu zaman lafiya da kwanciyar hankali, nemanta nan da nake yi i just want to make sure she's safe kuma tana cikin kwanciyar hankali da farinciki ba wai saboda ina son ta ba”
Kallonsa kawai Ali yake not knowing what to say, ya san abokinsa ba zai masa karya ba, and ya san waye abokinsa son wata mace ba abu ne mai sauki ba, sai dai zai iya bada shaidar cewar Talba mutun ne mai matukar tausayi da taimako.
“Idan kuma ita tana son ka fa?”
“Shi kenan sai na zauna sa ita, idan har zan iya nema mata wanda zai bata farinciki me kake tunanin idan tace ni ne farincikinta?”
Ali yayi murmushi tare ta dan tabe baki.
“Zamu gani, bari ma tafi gida, idan an samu wani information sai ka sanar da ni, so that mu shirya inda za a kai Amarya”
“Why not mu yi magana sa matar da muka bawa kwangilar hada mana lefen nan”
“No Khadeeja Candy bata bada hayar gida, iyakarta hada lefe ko koyan kitchen”
“Wai mu mata magana ko ta san wani wanda yake yi”
“Karka damu, ka bar komai a hannuna, ba dai hayar gida ba ne mai komai da komai a ciki? Zamu samu In Shaa Allah”
“Okay”
Ya amsa yana binsa da kallo har ya shige motarsa yai mata key. Sannan Talba ya nufi Babbar kofar shiga Company, tafiya yake cikin natsuwa da isa, kana ganinsa ka ga babban mutum mai matukar kula da lafiyarsa da kuma jikinsa, annashuwa da murmushi su ne abubun da suka nisanta kansu da shi, sai dai hakan be isa ya saka kai masa kallo daya ka kawar da fuska ba, domin tufafin jikinsa sun karbe shi sosai.
Duk inda ya wuce girmansa ake bashi har ya isa cikin office dinsa, a natse ya tura kofar ya shiga cikin katon Ofis mai kamar daki, an kawata ko'ina gwanin sha'awa ga sanyi ta ko'ina da kuma kamshin air freshener da ya gwaraya da turaren jikinsa suka bada wani kalar kamshin na dabam. Phone din shi ce first thing daya fara dauka sannan ya zauna a kujerar dake gefen teburin ta zaman baki. He's just holding his phone not knowing what to do, all these while Aminatu ce a ransa, be san reason din Kaka na hana sa ganinta ba, kuma zuciyarsa ta kasa natsuwa, har yanzu yana kallon rabuwar su ta karshe da ita, is she safe? Ina ma take? Ko dai wani abun ya same ta ne? Ko kuma dai ta gudu ne? Maybe bata son zama da shi Kaka tai forced dinta. Ya mike tsaye yana rike da wayar ya nufi gurin kujerarsa ya dafa kujerar ya jingina da ita.
‘No ba zata gudu ba, idan ma ta gudu ina zata je? Ai bata da gurin zuwa, kuma bata san kowa ba sai Kaka da shi’
Wani bangare na zuciyarsa ya ayyana masa. Sai ya maida dubansa gurin wayarsa ya shiga muhalin kira ya dannan number Kaka ya aika mata kira. Bugu biyu ta daga tana ra gwada masa sallama amai makon ya amsa sai kawai ya gabatar mata da bukatarta.
“Kaka ki dubi girman Allah ki fada min inda yarinyar nan take, Wallahi hankalina ba kwance yake ba, idan ma sace ta akai ki fada min dan Allah”
Kaka ta tabe baki kamar yana ganinta.
“Ka gama fushin da masifa? Ashe dai zaka iya koma kirana”
“Kaka dan Allah ki fada min inda kika kai yarinyar ko kuma ta tafi”
“Yarinya tana nan lafiya kalau fa, kawai dai bata tare da ni ne”
“Haka kike ta fada min kullum, haka ake aure wai? Ko lefen da kika saka na yi na kawo ban ga yarinyar nan ba, ban san manufar ki ko dai so kike na sake ta ne?”
“Aa A'uzubullahi, miya kawo maganar saki kuma ana zaune kalau?”
“To idan ba shi ba miye ma boye yarinyar nan?”
“Wallahi akwai dan abun da ake ne, ba a gama ba, amman da zarar an gama zan fada maka sai ka zo ka dauki amaryar ka a can gusau ma za a dauke ta a kaita gidanta ba a nan ba, sauran kuma idan an tashi daukar amarya ka zo mana haka nan ba tare da masu biko ba, kamar yadda kai mana a kawo lefe”
Shiru yai yana tunanin dabarar da zai mata ta yarda da shi.
“Shikenan zan yi tafiya next week, kuma ba zan dawo da wuri ba sai na yi wata shida, idan kuna bukatar wani abun sai ki fada min”
“Shikenan ma, ta kwana gidan sauki sai a bari sai ka dawo sai a kawo amaryar”
Ya runtse ido da karfi ya bude yana jin kamar ya shako wuyan Kaka.
“Yes sai na dawo, amman ina son kamin na tafi ki hada ni da ita a waya na yi magana da ita”
“To zan yi magana da Hajiya Laraba tukuna”
“Tana gidan Hajiya Laraba ne?”
“Baka saci kafa ka tafi gidan ba? Miyasa ba ka ganta ba idan har tana cikin gidan? Wai dan baka da kunya har ka iya cira kafa ka tafi gidan Hajiya Laraba, yaushe rabon ka da gidan? Baka san ka taka ka gaishe ta balle ka aika mata da wani abu, sai gashi tana fada min wai kaje har sau biyu neman Auta, Wallahi kai Mu'azu baka san kunya ba”
“To ni dai yanzu zaki fada min inda take ko ba zaki fada ba?”
“Ba zan fada ba, kuma wannan dubun 100k da ka ba ni ta dade da karewa”
“Idan kina son wasu kudin ki hada ni da Aminatu na ganta, Wallahi ba zan ce sai na dauke ta ba, kawai zan tabbatar idan tana lafiya ne”
“Idan bata lafiya zan tsaya ina magana da kai? Na ce tana lafiya”
Ya katse kiran ya daga jikin kujerar yana kofar office dinsa da Sakatarensa ya turo ya shigo tare da Madina. Hannu kawai ya daga masa sai ya juya da sauri ya fice, Madina kuma ta doso gaban teburin cikin wani irin taku na jan hankali tana masa wani irin kallo kamar ta cinye shi, shi ma kallonta yake har ta aje takardun hannunta a teburin sannan ta kalleshi.
“Na kammala aikin”
Ya gyada mata kai alamar gamsuwa.
“Kana bukatar wani abu?”
“Ina da sakatare”
Ta yi murmushi tana sauke idonta kasa kaminta sake kallonsa.
“Na sani, amman hakkina ne, na tabbatar Angon Leila yana lafiya”
Be ce mata komai ba, sai da ta kusa isa kofa sannan ya kirata.
“Madina...”
Ta juyo a hankali ta kalleshi ba tare da ta amsa ba.
“I think mun dauke ki aiki a nan ne, saboda kina so kuma saboda you deserve it, ba a dauke ki aiki a nan dan ki kula da ni ba, wannan ya zama karo na karshe da zaki shigo min office haka nan kawai ba tare da neman izinin satarena ba! Idan wani abun ne ma zaki iya ba shi ba dole sai ni ba, and ki maida hankali akan aikinki ba wai akaina ba, idan ma Leila ta turo ki nan saboda wani plan nata ki aje shi a gefe ki kula da aikinki before you lose it”
Ta yi murmushi tare da kallon yatsun hannunta, kamin ta fara takowa zuwa inda ta tsaya dazun ta kalleshi.
“Talba, ina aiki a kamfanin nan ne, ba da hadin kan Leila ba, ko da wasa Leila bata taba ce min na zo na yi aiki a kamfanin nan ba, ni na ji ina bukatar hakan kuma na gabatar mata da bukatar har ta samu karbuwa, idan ma kana tunanin na shigo nan ne da wata manufa ko ka daina ka kwantar da hankalinka ka samu natsuwa da ni, ban sani ba ko zaka yarda da ni, Wallahi ba zam taba iya yin wani abu da zai cutar da kai ba, ciki kuwa har da abun da zai saka maka bacin rai ko damuwa”
Ta yi shiru sai kuma ta cigaba.
“Ban san miyasa ba, haka nan nake jin kamar na cuta idan na barka ka zauna da yunwa ko kuma bukatar wani wanda na san zan iya yi maka shi, ina jin damuwa da damuwarka sosai, ban taba fada maka ba, ban taba nuna maka ba, kuma ban tana bari Leila ta fahimta ba, har ga Allah ina jin cutuwa idan kuka samu matsala sa Leila, ba dan bana son ku samu matsala ba, sai dai na san hakan zai saka ranka ya bace”
Idonta ya cika da kwalla, sai ta dago ta kalleshi.
“Kai mutum mai matukar daraja da kima a idona Talba, kana kula da mutane da yawa, amman kai babu mai kula da kai, kana da tausayi sosai ka san kimar dan 'adam, amman Leila ta kasa tausayinka kuma ta kasa kula da kai yadda ya dace, gashi har kuna neman zama miji da mata, na san zaka ji bakin kalamai a gareni yau, wata kila ba zaka fahimce ni, ban matsa akan ka fahimce ni ba, domin na lura kana kyarata tun a lokacin dana kama aiki a kamfanin wata uku da suka wuce zuwa yau, baka son ina shiga lamarin, amman ina rokon wata alfarmarki daya”
Ta hade hannayenta guri daya tana kallonsa hawaye na saukowa a idonta suna wanke fuskarta gwanin tausayi.
“Dan Allah karka min shamaki da office sin nan naka, saboda ganinka kadai na daga cikin abun da yake kwantar da min da hankali ya saukar min da natsuwa, a duk lokacin dana samu kaina a damuwa, hotunan ka ne abun da yake debe min kewa, kuma ya saka na dawo cikin natsuwa”
Tana kawai nan ta juya jiki a sanyaye ta nufi kofar fita, bata taba samun kanta a irin yanayin data samu kanta a yau ba, a yau kam ta masa rike hashenta daga furta wadansu kalamai da ta san za su iya ja mata matsala ko kuma su datse alakarta da kawarta. Ta san tana son Talba sai dai ba tabbatar da sonsa ya yi tasiri sonsa a zuciyarta kamar lokacin data fara aikin a kamfanin zuwa yau, a kullum wutar sonsa kara ruruwa yake a zuciyarta, saboda kusancinsu ya karu a yanzu fiye da da, kusan kullum tana ganinsa, a kullum kyaunsa karuwa yake a idonta, idan ta kalleshi har jin take kamar ta rumgume shi, Talba na da cikar kyau da siffar da ko wace mace zata so ya kasance a mijinta.
Da ido ya bita har ta fice sannan ya girgiza yana daga kafadunsa.
“Ita da Leila duk hankali be ishe su ba, daman ance show me your friend i will tell you who you are”
Ya furta yana mamakin yadda Madina ta rikide masa a yau take masa wasu zantuka marasa kan gado.
AMINATU POV.
Yau ma da kanta ta daura lifayar ta nada kamar yadda Farida ta koya mata, bayan ta gama ta dauki turare ta kara feshe jikinta da shi, domin Farida ta fada mata kamshi na daga cikin abun da yake karawa mace kima da martaba, karta yarda ta zauna babu kamshi a jikinta. Hakan yasa ta saba mata idan zata yi wanka sai an zuba mata turare a ruwan, idan ta fito tawul din da zata tsane jikinta ma an saka mata turare, kamin ta shafa komai sai an fara lullubeta da da zane an mata turaren jiki ya tsara ko'ina a jikinta kamin a gabatar mata da na tsuguna, idan kuma ta gama shafa mai sai ta bi jikinta da turaren jiki ta shafe ko'ina a jikinta. Hakan yasa kamshin ya kama jikinta sosai ko wucewa tai sai ka ji kamshi na tashi kamar mai yawo da ruwan turare. Sai da ta dauki red lipstick ta shafa a bakinta sannan ta isa gaban katon madubin tana kallon kanta. Dan murmushi tai domin ita ma kanta ta san ta canja, jikinta yayi kyau kamar ba nata ba, bakar fatar nan sai sheki take tana shining kana ganinta ka san an kashe mata kudi gurin gyara, kumatunta ma sun dan ciko jikinta ma ya bayyana cif saboda gumbar kiba da take sha a kullum wanda Yar gidan mai fata ta hada mata. Hakoranta ma tasss Hajiya Laraba ta saka aka wanke mata su, hakan yasa ta kara kyau da haifa, fararen idanuwanta suka haska fuskarta. Gashin kanta ma every week ake kaita gidan Farida ko kuma ita ta zo ta gyara mata shi tana saka mata mayuka masu kyau da tsada idan ta bude kan har wani kamshin dadi zaka ji yana yi. Ba gyara ne kadai abun da Farida take zuwa yi mata ba har da koya mata tafiya da saka wasu tufafin da ba bata saba sakawa ba, kamar saka kananan kaya da daura lafaya. Ita kanta tana jin jikinta na canja sosai idan ta taba fatarta tana jinta so soft saboda gyaran da ta sha har wani tsantsi take.
Kasa tai da idonta tana kallon tsadaden agogon hannunta, tun da take a rayuwarta bata taba saka agogo ba, sai da Talba ya hada mata lefe kuma Kaka ta aiko mata da abun ta a gidan Hajiya Laraba, hannu ta kai tana tana agogon hankali tana murmushi tuna zuwansa na karshe a gidan nemanta, sai dai Hajiya bata damar fitowa ba sai ta boyeta a dakin dakin yaranta tace masa ba a kawo ta nan ba, har rufe da tai da fada domin be saba zuwa gidan da sunan ya gaisheta ba ko duba lafiyarta, rabonsa da gidan ma har ta manta. Jin motsin turo kofar dakin yasa ta juyo da sauri ta kalli kofar.
“Maa Shaa Allah, Auta an sha kyau ke ma kin iya gyara kanki yanzu haka nake so, kalle ki kamar ba ke ba Wallahi”
Hajiya Laraba ta fada fuskarta dauke da murmushi tana karasowa kusa da Aminatu. Sai Aminatu ta sauke kanta masa tana murmushi.
“Karbi maganinki ki sha, idan kin sha yau kika sha gobe shikenan ya kare”
Ta mika mata kofin dake dauke da garin maganin mata da aka kada da madara, ita kuma ta saka hannu biyu ta karba ta kafa kai ta shanye. Kusan kullum sai ta sha maganin tun tana jin dacinsa tana kyama har ta saba, ya zame mata jiki na safe dabam na rana dabam na dare dabam, bayan na tsuguna dana shafawa set din back to virgin kusan kala uku yar gidan mai fata ta hada mata. Hajiya Laraba ta karbi kofin tana fadin.
“Haka nake so, saboda Talba ya san ba banza muka aura masa ba, ai ko dan yar'uwata zan dage na yi masa abun kwarai, kuma ya san idan shi ya mantawa mu mu ba zai yiyu mu manta shi ba, domin jininmu ne shi, shiyasa ban ji zafin cire kudin nan na bada a miki gyaran jiki ba, kalli yadda kike ta sheki, gaba daya kin canja yan kumatun ma sun taso gwanin sha'awa, ke nan idan kika shekara ai ba za a gane ki ba”
Wannan karon murmushi mai sauti Aminatu tai, sannan ta zauna bakin gadon tana kai hannunta ta dauki tissue ta gyara bakinta, Hajiya Laraba ta fice tana ta yabawa da yadda Farida ta gyara mata jiki. A hankali ta dago ta kalli kanta a madubi, sai tai yi arba da wata Aminatu ta dabam wacan ba, wannan Aminatun kyakkyawa ce mai kwarjini da haiba, mai kwaliya da kamshi mai cikar sura, ba kamar wacan ba wanda wahala da tashin hankali suka hana ta kumari, zaman kauye kuma yana kyauta bayyana, a yanzu kuma tana cikin ac ta kwanta a gado mai kyau ta ci abinci mai kyau ga supplements da magungunan gargajiya da ake bata na gyara jiki tana sha a kullum. Abu daya wannan Aminatun ta rasa irin wanda wacan Aminatun ma ta rasa shine farinciki, ta kasa mantawa da iyayenta, ta kasa mantawa da gidansu, ta masa manta yadda aka rusa rayuwarta, ta kasa goge hoton yadda aka ruguza danginta.
“Inna...”
Ta