Showing 312001 words to 315000 words out of 332834 words
gawarwakin musulmai yan'uwanta, a haka mata rame kamar yadda addinin musulunci ya ce, shim Amina ba ki san ana cutar da dan'adam bayan rai ya fita daga jikinsa ba? Kun cutar da Baaba, kuma kika bar iyalanta cikin zullumi da tunanin inda take wace irin mace ce ke Amina?”
Momy ta saka hannunta ta share hawayenta, sai dai hakan be hana wasu zubo mata ba.
“Ko wace uwa tana son yayanta, ba zata yarda su cutu ba sai inda karfinta ya kare, taya zan zuba ido a tafi da yata a kasheta akan laifin da ta aikata a kan kuskure? Idan ban rufa mata asiri ba wa zai rufa mata a duniyar nan? Zamu iya biyan diyya yallabai, zamu iya biyan diyar rai ka taimaka min dan Allah karka bari a tafi da Leila kotu”
“Kotu zata yanke hukunci idan diya za'a biya ko akasin haka”
Daddy na kaiwa nan ya mike tsaye, sai Momy ta juyo gurin Talba tana rokonsa.
“Talba ka taimaki yar'uwarka ka taimaka min, Daddynka yana jin maganarka ka roko min shi dan Allah, idan wani abu ya samu Leila ban san iya halin da zan shiga ba, Wallahi Wallahi na muku alkawari Leila ko hararar wani ba zata sake yi ba”
Daddy da be karasa shigewa ba ya juyo yana nuna Talba.
“Karka kuskura, rokona wani abun akan maganar nan! Wallahi ko ka aikata wannan laifin sai na hukuntaka, son da nake yi ma yayana be kai son da na ke yi ma Mahallincina ba, kuma be kai ya saka na saba dokarsa ba”
Ya fada sannan ya juya ya karasa shigewa dakinsa, zaunawa kawai yai saman gadonsa ya ciro wayarsa ya kira CP. Ko gaisuwa be tsaya sun yi ya ce.
“Allah yasa kana office”
“Ina Office amman yanzu nake shirin fita”
“Ina bukatar police zuwa gidana”
“Lafiya?”
“Yata ta aikata kisan kai, ina son a tafi da ita ne?”
“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un.... Garin ya?”
“Labari mai tsawo zan same ka office”
“Okay”
“Amman ina bukatar idan sun zo za a tafi da ita a motar gida ba motar yan sanda ba”
“Zan aiko da police yanzu nan, Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un”
Ya katse wayar, a lokacin Leila Daddy ya fashe da wani irin kuka kamar ba shi ba, jikinsa har jijiga yake.
Momy na ganin Daddy ya shige ta tashi da sauri ta fice daga bangaren, part din ta nufo da gudu ta hau stairs ta tura kofar dakin Leila ta shiga sai ta zame ta zaune a kasa ta takure guri daya ta rumgume kanta.
“Tashi Tashi tashi... Ki dauko passport dinki da duk wani abu daya kamata, zan saka a miki transfer kudi yanzu a account dinki, ki tafi.....”
Sai kuma ta kasa karasawa saboda tashin hankalin dake tafiya da numfashinta. Gafen gadon ta rika ta zauna.
“Ki tafi hotel, zan miki visa zaki bar masar nan...”
Leila ta tashi ta zauna kusa da Momy.
“Ba zan iya guduwa ko'ina ba Momy, abu daya nake son ki min, ko da sama da kasa za su hade karki yarda ki amsa cewar a tare muka aikata binne Baaba, ina son ki amsa cewar bakin san komai ba”
Momy ta girgiza mata kai ta rika ta tana girgizawa tana kuka.
“Baki da hankali? Leila baki da hankali? Tafiya fa za'ayi da ke? Leila baki da hankali? Kin fita hayyacinki ne?”
Cikin wani irin kuka mai kamar na fitar rai Leila ta amsawa Momy.
“Ina da hankali Momy ina da hankali”
Momy ta rumgume ta da karfi tana jin kamar ta fasa cikinta ta saka Leila ta dinki, sai dafa kanta take tana dafa bayanta kamar ta rikice, Leila ma rumgume take da Momy tana kukar fitar hankali, ita da Momy aka rasa mai rarrashin wani.
_Allah ka raba mu da aikin da na sani 😪 ni dai kam yau Leila ta ba ni tausayi_
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
Momy kamar wanda aka tsikara sai ta tashi da sauri ta fice daga dakin zuwa dakinta wayar ta dauka ta hau kiran Hajiya Saratu. Leila kuma ta mike tsaye hawaye na sauko mata ta nufi backyard din gidan tana karewa harabar kallo, domin ta ayyana a ranta cewar idan har ta bar gidan ba zata sake dawowa ba, sai dai gawarta. Ya kai hannu ta share hawayenta ta juyo ta dawo cikin dakin sai kuma ta nufo kofa ta fita tana saukowa stairs a hankali, bankwana take son yi da gidan, ko wane abu ta kalla sai ta tuna yadda take taba shi ko take amfani da shi. Har lokacin Kabir na zaune ya rasa abun da zai yi, dagowa yai a hankali ya kalleta.
“Ina zaki je”
Ta daga masa kafadunta domin bata jin zata iya wata magana a yanzu. Ganin tana kallon kofar kitchen yasa ya tashi ya nufi kitchen din ya dauko mata ruwa ya zuba mata ya mika mata, sai ta karba ta rike tana kallonshi. Can kuma ta dauke kai tana kallon kallon hawaye na sauko mata, ji take kamar bankwana take da komai na cikin gidan. Door bell din gidan aka danna da karfi hakan ya saka Kabir ya nufi kofar ya bude gabansa na faduwa, a tunaninsa Police ne, duk kuwa da bashi da tabbacin Daddy ya hakuri ko kuma yana nan akan bakarsa. Ali ya gani tsaye jikin kofar rike da wayarsa.
“Dan Allah ina son magana da Leila”
“Bata cikin natsuwar da zata iya magana da kai a yanzu”
Kabir ya fada masa yana kokarin maida kofar dakin ta rufe, sai Ali ya rike.
“Please... Na yi magana da Talba ya fada min komai, magana kawai nake son yi da ita”
Kabir ya juyo ya kalleta sannan ya bude masa kofar, sai ya shigo cikin falon da saurinsa sai da ya karaso kusa da ita sannan ya juya ya kalli Kabir alamar yana bukatar privacy. Ganin hakan ya saka Kabir ya bude kofar ya fice daga falon ya tsaya bakin kofar falon ya saka hannayensa aljihu yana sauke ajiyar zuciya.
“Ban yi magana da Talba saboda haka ya faru ba, na masa magana ne saboda ya zama a side dinki, na san yanzu kina jin damuwa marar misaltuwa”
Ali ya mika hannunsa ya karbi kofin ruwan dake hannun Leila ya aje kasa, sannan ya rika hannayenta duka biyu.
“Ina son ki sani, no matter what happens i will always be on your side, and wannan abun zai wuce kamar ba'ayi ba, ba za a yanke miki hukuncin kisa ba, saboda ba ku aikata kisan da ganganci ba, you will be free”
Ta dan sakar masa murmushin karfin hali hawaye na sauko mata.
“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, ki yi ta nanatawa kin ji?”
Ya fada yana jin kamar ace zai iya saka hannunsa ya yaye mata damuwarta, ya maida komai ba komai ba. Ya sake hannayen nata yana jin kamar ba zai iya numfashi ba, yana yin baya kadan sai ga Momy ta sauko da saurinta da mayafi hannunta rike da makullin mota, wata uwar harara ta watsawa Ali domin ganin take kamar shi ya sassa komai.
“Me kake yi nan? Bayan halin daka jefata har kana da karfin halin da zaka tako kafarka gidan nan ka zo gabanta ka tsaya?”
Momy na fada tana yin cikinsa kamar zata dokeshi. Leila ta mika hannu ya rika Momy ta riko Momy ta girgiza mata kai. Momy ta kama hannunta tana fadin.
“Zo muje”
Nan ma fisge hannunta tai tana girgiza mata kai. Sai ga Kabir ya shigo da sauri.
“Momy police ne, waya kira su?”
Momy ta kalli Kabir cikin tashin hankali, Leila ma kallonsa take tana jin kamar mafarki take, domin tun da take a rayuwarta bata taba zuwa police station ba, ko da sunan beli ko ganin wani, balle ace yau ita za a kai. Momy ta kalli Ali
“Kai ka zo da police?”
“Aa ba ni ba ne”
Ali ya amsa, ana danna door bell din Momy ta maida Leila bayanta. Kabir da Ali suka kalli kofar aka rasa wanda zai karasa ya bude. Sai kuma Momy ta juyo ta kama hannun Leila.
“Zo nan na boye ki”
Leila ta fisge hannunta tana girgizawa Momy kai, Momya ta mata wani kallon tsoro.
“Karki je Leila, karki bar ni dan Allah, yar'uwarki tana bukatarki... Kabir....Talba... Ni... Leila burikanki....”
Momy ta kasa karasawa sai wani irin rausaya take kamar zata fadi. Cikin karfin hali da dakewar zuciya Kabir ya karasa gurin kofar ya bude falon, sai yai arba da Daddy da Talba sai kuma police guda uku maza biyu mace daya.
“Daddy Police...”
Kamin Kabir ya karasa Daddy ya amsa masa.
“Ni na kira su”
A dole ya matsa baya ya ba su hanya, tun da yake a rayuwarsa be taba jin son yar'uwarsa Leila a ransa ba irin yau, sai ya ji kamar ya dauke ta ya goya a baya yai ta gudu har ya tsirarta da ita. Da hannu Daddy ya nuna musu ita, sai suka nufeta Momy na kara boyeta. Talba ya kalli Daddy da sauri kamar yayi wani abu babu dama.
“Aa dan Allah, haba Yallabai Leila fa yarka ce jininka ce”
Sai kuma ya nufi gurin Talba ta rika shi.
“Dan Allah kar a tafi da ita”
Ta koma gurin Daddy.
“Ka yi hakuri dan Allah”
Ta sake juyowa.
“Kabir za a tafi da yar'uwarka, Amal... ”
Momy ta kwalawa Amal dake dakinta tana kuka kira. Sai ga Amal ta sauko da gudu a lokacin Police din har su saka mata handcuff a hannu, mace ta rika ta za su fara tafiya.
“Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, Leila ki yi ta maimaitawa”
Ali ya fada sai Talba ya kalleshi. Leila kuma ta juyo tana kallon Momy da yan'uwanta, Kabir ya rike Momy da mugun karfi domin so take ta rike Leila ta hana a tafi da ita.
“La'ilaha Illalah... Wayyo Yata... Leila...”
Tana kawawa kusa da Daddy sai ya kai hannunsa ya taba kanta.
“Allah ya miki albarka, kuma ina kyautata zaton kotu zata yanke hukuncin daya dace a bisa adalci, i forgive you Leila”
Ta daga kai hawaye na sauko mata, domin har lokacin bata iya furta komai. Momy ta zube kasa tana kuka kamar ranta zai fita. Daddy ya kalli Talba.
“Muje ka ja mota...”
Talba ya girgiza kai da sauri.
“Daddy ba zan iya ba, ba zan iya tuka mota na kai Leila Station ba”
Daddy ya kalli Kabir shi ma ya girgiza masa kai, sai Daddy ya ciro wayarsa yana kiran direbansa. Amal nufi kofar da gudu ta sha gabansu ta rumgume Leila tana kuka.
“Daddy a gabana komai ya faru, ba da gangan ta aikata ba”
Amal ta fada tana wani irin kuka sosai, Daddy ya saka hannunsa da kansa ya jamye ta daga jikin Leila, sannan yai ma police din alama da su tafi da ita. Motar gida suka shiga sannan Daddy da Talba da Kabir suka shiga mota daya, Ali kuma ya shiga tashi motar, sai aka bar gidan daga Momy sai Amal, daga bisani Hajiya Saratu ta iso ta shiga rarrashin Momy.
Kai tsaye state icd aka wuce da ita, duk wani bincike da ya kamata su yi mata sun mata sannan suka saka ta a cell da sunan Monday za su shiga da ita kotu. Babu yadda CP be nunawa Daddy cewar za a iya canja komai kamar be faru ba, amman Daddy ya ki aminta sai cewa yake a bar doka tai aikinta, duk hukuncin da alkawali ya yanke ya shirya daukarsa. A lokacin ne Daddy yake bada report din Madina a rake Cp ya tashi yaransa aka tura su gidansu Madina. Police suka kira yan'uwan Baaba suka nemi ganinsu station din, wadanda suka garin suka riga na kauye isowa, har cikin office din CP aka shiga da su, saboda Daddy yai magana da su ya kwantar musu da hankali sannan ya fada musu cewar Leila tana gurin kuma zata fuskancin hukunci.
Sannan aka gabatar musu da gawar Baaba da police suka hako a tsohon gidan Momy, a lokacin ne suka fashe da kuka.
Ko da yamma tai na wadanda suka kauye sun samu labarin har sun iso, alfamar da Daddy ya roka daya ce, na hana a fadawa yan jarida.
Sai kuma addu'o'in da yan'uwan Baaba suka rika yi suna tsinewa Leila ko kadan be yi ma Daddy dadi ba, duk kuwa da ya san yarsa mai Laifi ce.
Ba karamin tashin hankali Madina ta shiga ba, ganin Police sun ta ho zasu tafi da ita, da fari boyewa tai aka ce bata nan sai da Police din suka nuna za su shiga su fito da ita da karfi sannan Hajiya ta fiddo da ita, kuka sosai Madina take tana faduwa tana tashi tana rike Hajiya, tana rokon Hajiya tai wani abu kar a tafi da ita. Hajiya kam ban da kuka babu abun da take, suna kasata a motarsu ta kira yan'uwanta da ma mahaifinta da mahaifinta ta fada masa sannan ta bi bayansu tare da direbanta.
Sai da aka saka ta a cell sannan su Daddy suka dauko hanyar gida ko da suka dawo gidan ya cika da yan'uwan Momy, sai taya ta jimami suke, ita kuma tana kwance a dakinta kan tile, babu yadda ba su da ita ba akan ta koma saman gado ko kuma ta tashi a shimfida mata wani abu amman ta ki tai ko daya.
Bayan sallah Isha'i Amal ta fito ta zauna a waje tana ta kuka ita kadai, sai dai abun da bata sani ba Talba na zaune nesa da ita yana nashi tunanin, sai dai ganinta ya saka ya taso ya dawo kusa da ita ya zauna, sai ta kalleshi ta share hawayenta.
“Kai da Daddy zamu iya yin wani abu, Leila ta dawo gida, amman baku ba, yau zata kwana a inda ba gida ba, bana tunanin zata iya yin bachin ma”
Talba ya sauke ajiyar zuciya.
“Ya kike ji a ranki?”
Ta kalleshi tana jin wani sabon kuka na taso mata.
“Da zafi sosai, ina jin kamar kashe Ya Leila za'ayi, kuma idan aka kasheta ba zamu sake farinciki ba”
“Zamu sake, ko da kuwa an kashe ta din kamar yadda kike hasasashe, ballana ina kyautata zaton ba a za a kashe ta ba”
“Ba zan sake farinciki ba, ba zan sake dariya ba har sai ta dawo”
“Zaki sake, na san wata yarinya sa'arki wanda ta rasa iyaye ta rasa yan'uwa ta rasa muhalli, kuma ta jure, aka wulakantata ta dauka kuma a yanzu haka ta maida komai ba komai ba tana rayuwa cikin farinciki”
Ta kalleshi domin ta san kai tsaye wanda yake magana akanta.
“Aminatu?”
Ya daga mata kai.
“Duk wani halin rayuwa da zaki shiga a yanzu ki rika tunawa da ita, ta shiga taskun rayuwa da damuwa fiye da naki, kuma har yanzu bata gama fuskanta ba, kowa da kalar kaddararsa Amal this too shall pass”
Ta kwantar da kanta jikinta Talba tana hawaye.
*** *** ***
At first Madina ta so ta musa cewar ta sace Aminatu, sai dai bincike da police sukai a wayarta sai suka gano akwai alaka a tsakaninsu, duk kuwa da kasancewar tana goge kiran da yake mata ko take masa, sai dai tuntubar kamfanin sadarwa da sukai an ba su duka record calls dinta, sun saurara sai suka gano wanda ta yi da Alfa. Plan aka hada da ita ta kira sukai magana akan kudin da zata ba shi, 30 million, ta fada masa inda za su hadu sannan aka je gidansu aka dauko motarta aka bata ta tuka kanta police na biye da ita cikin hikima da gwarewar aiki har suka isa meeting point din daya zaba. Madina ta yi amfani da wayarta ta kira shi ya sanar masa daidai inda take tsaye, sai gashi ya fito cikin wata farar mota ya nufo motarta, yana bude motar ya shiga ya zauna, sai ya fahimci ba lafiya ba, domin yanayinta da fuskarta ya nuna haka, da sauri ya bude motar ya fita, sai dai kamin yai wani yunkuri police sukai nasarar cafkeshi.
Kamar taron kasuwa haka mutane suka taru suna kallon abun da ke faruwa, domin ya nuna tirjiya sosai na kin son zuwa, har sai da suka masa rauni a jiki. After an kama Alfa aka kama Bestyn wanda ya hada Madina da wadancan mutanen nan da suka hada ta da Alfa, sannan suma aka kama su.
Washe garin ranar aka zo da Aminatu ta shaidi fuskar Alfa mutumen daya sace ta, sai ta amsa cewar shi din tana ta jin tsoro sosai, dan ma Talba yana kusa da ita, kuma ta san a police station suke.
Duk irin tambayar da aka yi na Leila bata yarda da saka Momy a ciki, ta guri daya sunan Momy ya fito inda ta fadi cewar ta taimaka mata ta saka Baaba a mota sai ta koma cikin kamin ta dawo taja motar zuwa asibiti, sai dai kamin ta isa sai ta ji kamar Baaba ta mutu hakan ya saka ta nufi tsohon gidan gonar Daddy ta yi magana da Mai gadinta ya haka mata rame da sunan zata saka zinari da kudi, hakan yasa dole ta saka gawar a zaune ba a saboda yanayin yadda aka gina ramen. Sosai Momy ta so ta daukarwa yarta Lawyer Daddy ya hana, sannan ya gargade ta akan cewa be yarda ta bawa Alkali cin hancin ba ko ta nemi wata alfama ya fi son abar Alkali yai shari'a a bisa gaskiya.
FARUK POV.
Wajen falon ya fito wato harabar gidan ya tsaya yana jiran ta fito masa da Sultan. Ya kusan minti talatin a tsaye sannan ta fito tana rike da Sultan dayan hannunta rike da wata yar jaka mai kyau, dake cike da chocolate. Gafenta Sultan ya tsaya ala dole shi fushi yake yi ba zai je gurin Faruk ba, dayan hannunsa rike da chocolate daya bata