Showing 177001 words to 180000 words out of 332834 words
ba, sai mun manta da kai ma a cikin dangi”
Ya dan yi murmushi.
“Hajiya ai, kuma kuma da laifi, ba ku zuwa gidanmu ku maida ni bare cikin dangi”
“Aa kai ne dai baka rika mu da mutunci ba, da ace ka rike mu da kima kuma ita wacan uwar taka ta koya maka ai da yanzu an wuce gurin, amman mutum zai tashi ya tafi can ai sai ace kwadayi da neman wani abu ya kai shi”
“Yanzu dai komai ya wuce Insha Allah za a gyara, ya gida”
“Lafiya kalau ya aiki?”
“Alhamdulillah, daman Kaka ce tace na zo mu gaisa da Aminatu”
Hajiya Laraba ta yi dariya, tana jinjina halin Kaka bayan ta gama fada mata cewar kar a barshi ya ganta yanzu kuma sai ta fada masa yan zo nan ya ganta.
“To bari ta zo”
Hajiya Laraba na mikewa tsaye sai shi ma yai saurin mikewa.
“Bari na jirata a mota”
Kamin ta amsa ya nufi kofar fita, yana murmushin zuci, saboda ya samu cin ma abun da yake so. Fitowa yai ya ya jingina jikin wata mota dake fake a gurin, yana kallon kofar falon. After like 15min ya hango wata kyakkyawar bakar fata mai matukar haiba da cikar zati ta fito daga kofar falon hannayenta duka biyu rike da farantin ruwa dake dauke da gorar ruwan ita kanta sai kuma cup. A hankali take takowa cikin natsuwa da taka tsantsan, gaban gashinta a bude saboda lifayar data nada ta sauka a bayanta. He can't believe Aminatu ce har sai da ta karaso kusa da motar tana zuba wani irin kamshi, zagayawa tai ta inda take hango shi tsaye, Kamin ta karaso ya raba jikinsa daga motar yana mata wani irin kallo na mamaki.
“Assalamu Alaikum”
Ta masa sallama, and yes muryarta ya ji balle yace ba Aminatunsa ba ce, amman ta canja gaba daya kamar ba ita ba. Be amsa mata ba ya kai hannu ya karbi ruwan hannunta ta dora saman motar sannan juya ya duba dama da hadu ya ga babu mai ganinsa, sai ya janyota ya rumgume a kirjinsa, cos he was shocked and surprised wai Aminatu ce a haka, be ma san mi zai fada mata ba. Lumshe ido ta yi, sai tai lamooo a kirjinsa tana jin yadda tai marmarin kashin turarensa, not just his perfume even his voice da ganinsa ta yi kewar komai nasa kuma bata taba jin haka ba sai a yanzu da kanta yake shimfide a kirjinsa, hannunta ya lalabo ya saka yatsunsa cikin nata, because now he believe yayi missing dinta sosai, gashi ya ganta ba a yadda yai tsammani ba. Baya baya yai ya jingina da motar sannan ya saka dayan hannunsa ya shafa kanta ya dago fuskarta ya sumbanci goshinta ya sake sumbatar hancinta da kuma saman idanuwanta biyu da suke rufe, sai kuma ya fara shinshinar wuyanta kamshin turarenta na kai masa har cikin kwakwalwa, be san da ya zurfafa ba har sai da ta daga daga kirjinsa tai taku daya baya biyu kamin tai na uku ya kai hannayensa kan kafadarta sai kuma ya zagaye fuskarta da hannayen nasa, yana shafa lallausar fatar fuskarta da babban yatsansa.
“Shalele... Waya gyara ki haka.... Look at you... Your face....your skin... Wow..”
Ya fada cikin wani irin rada, a wata kasalalliyar murya kamar ba shi ba, idonsa na kan lips dinta da suka sha man lebe.
“Oh God”
Ya sake matsawa kusa da ita ya rumgumeta.
“I miss you so so so much”
Ya furta yana jin kamar be taba marmarin wani abu so much a rayuwarshi ba irin Aminatu. Ya dago da ita daga jikinsa.
“Zo muje ki raka ni gate”
Sai da ta kalli kofar falon sannan ta fara takawa, gaba daya idonsa na kan tafiyarta har suka isa gate din, da kasa ya bude mata ta fita sannan ya fito suka nufi gurin motar a tare. Key din hannunsa ya danna sannan ya bude mata front seat.
“Shiga”
Ta kalleshi da kyawawan idanuwanta.
“Aa ban fada mata zamu fita ba, ce min tai zamu gaisa kawai”
Tana maganar yana kallon yadda bakinta ke motsawa a shagwabe.
“Shalele kin yi kyau, kin canja you're so beautiful”
Ya furta yana kallon ilahirin fuskarta, hannu ya kai ya kama hannunta zai yi magana, sai aka haskesu da fitilar mota mai matukar haske, daga ita har shi kallon inda hasken yake fitowa suka yi. Sai a lokacin ya lura da mota ce ta haske su direct, gashi unguwar ba irin mai haske ce a ko'ina ba balle yace ya gane ko waye, sai dai da alama wanda yan shi ne domin an haske su ne da gangan kuma anki kashe fitilar. Aminatu ta kai dayan hannu ta rike rigarsa gabanta na faduwa nan da nan hawaye ya taru mata a ido.
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
“Tsoro nake ji”
Ta fada jikinta na rawa a take idonta ya cika da hawaye. Dauke idonsa yai daga kallon motar ya kalle tare da kai hannunsa ya shafa kumatunta.
“Babu abun da zai same ki, ki kwantar da hankalinki”
Sakinta yai sai ta saka hannayenta duka biyu ta rikoshi tana mai tsananin tsoro, domin tun a wacan lokacin da barayin daji suka sace ta take a firgice abun ya kasa fita kanta, dan abu kadan idan ta gani ko ta ji sai hankalinta ya tashi.
“Karka bar ni nan”
Sake juyowa yai ya kalleta a karo na biyu.
“Babu abun da zai same ki, zan je na duba wanene”
Ta kara kankame shi da karfi.
“Idan suka maka wani abun fa? Karka je dan Allah”
Murmushi yai hakan nan kawai sai ya ji ta burgeshi, ko ba komai ta damu da lafiyarsa, and she hug him a rayuwarsa be san wata mace da ta taba rumgumarsa ba, Aminatu ce ta farko, ko Leila da take wayayyiya bata gigin taba shi saboda bata ga fuska ba.
“Okay”
Ya furta sannan ya kai hannu ya kwantar da ita kirjinsa, yana shafa bayanta a hankali ita kuma tai lamo kamar kyanwa tana kallon motae data kasa daina haskensu. Can kuma ya dago ta
“Zauna cikin mota, ko kuma ki shiga gida ki jirani na zo, ina son naga ko waye, babu abun da zai same ni”
“To kai addu'a amman kar ayi maka wani abu”
Ya fada hawaye na sauko mata, sakinta yai ya fara tafiya sai kuma tai saurin sake rikoshi.
“Zan rakaka”
Hannunta ya rike suka nufi gurin da motar take fake, sai motar ta fara ja da baya, hakan yasa Talba ya tsaya cak, sai motar ma ta tsaya yana kara step daya sai motar taja baya, idan ya kara sai motar ta sake ja baya, idan ya tsaya sai ta tsaya.
“Minno tsaya nan ina zuwa”
“Aa”
Ta fashe da kuka mai karfi tana rike da shi, duk yadda ya so ta sake shi ya karasa gurin motar kiyawa tai sai kuka take masa domin har ga Allah a tsarace take.
“Ya isa ba tafiya zan yi ba”
“To mu shiga gida tsoro nake ji sosai”
Ta furta tana kuka hawaye shar wasu na bin bayan wasu. Ya gyada nata kai, sannan ya saka hannunsa aljihu ya ciro wayarsa yai dialing number Ali, yana kara wayar a kunne sai motar tai baya da karfi da mugun gudu ta still tana haskensu har sai da ta kai karshen kwanar sannan ta juya dama ta hau titi da gudu. Ba mamaki ne kadai abun da Talba yake ba, har da tsoro domin be san waye ba kuma be san manufarsa ta yin haka ba, ya san shi ko kuma yayi hakan ne kawai dan ya daga musu hankali? Aminatu kam dukewa tai a gurin ta dafe kai tana kuka.
“Hello”
Ali ya amsa kiran bayan wayar ta dade tana ringing.
“Zan kira ka”
Talba ya amsa masa sannan ya kashe wayar ya duka ya kama hannayen Aminatu yana murmushi mai sauti.
“Sarkin tsoro, ko waye ma ya gudu ai”
Ya mikar da ita tsaye ya rumgumeta, for no reason yake jin dadin jinta a kirjinsa.
“Kukan ya isa Auta, daman kun iya kuka ko?”
Ta dan tsagaisa sai dai bata iya hana hawayenta zuba ba.
“Yanzu zaki kara ni ko kuma gida zaki koma?”
“Gida”
Ta amsa cikin kuka, sai yai murmushi ya shafa kanta yana kara matsar da hancinsa saitin inda gashin kanta ya bayyana yana shakar kamshin da kanta yake yi.
“Waya gyara min ke haka? Kin yi kyau sai kamshi kike ta ko'ina, kin kalli kanki a madubi kin ga yadda kika canja kuwa?”
Ta daga masa kai still crying.
“Oo na shiga biyu, wannan kuka haka?”
Ya dagato ya saka hannayenta yana share mata hawaye, sannan ya sumbanci goshinta, sai kuma ya hade goshinsu yana goga mata hancinsa a hankali, saurin dagawa tai ta dan ja baya saboda numfashinsa dake gwaraya da nata. Murmushi yai ya daga kansa sama ya sauke, shi kansa ya zurfafa da yawa, irin zurfafa da be san lokacin da yai haka ba, kuma be sa ran zai yi haka ba. Gyaran murya yai yana kokarin dawowa ainahin shi amman ya kasa, baya iya daure mata fuska ba ya iya nisanta kansa da taba jikinta he don't know why yake behaving wani kalar Talba dabam a gaban Aminatu.
“Muja na raka ki gida”
Ta juya, kamin tai taku na biyu ya kai hannu ya riko hannun, ko da suka isa gate yana murza yatsunta a hankali.
“Sake ni kar wani ya gani”
“Ba haram mu kayi ba you're my wife, ke matata ce”
Sai kawai ta bata fuska tana shirin fara yi masa kuka, sai ya sake hannun nata.
“Okay na saki, Autar kuka ba sai kin min ba”
Ta juya zata kai dayan hannunta ta tura gate din sai yai saurin rikonta ya juyo da ita, ya kai hannayensa duka biyu ya rike kunkurunta sannan ya dora goshinsa a saman nata yana kallon cikin idanuwanta.
“You're so special Aminatu, i mean so so so special, very special ban taba yi ma wata mace abun da nake miki ba, ban taba ganin mace na ji na rasa natsuwata ba irinki, ban taba tunanin zan zama haka ba, ban tana gwada aikata haka ga wata ba but look at me”
Ta kai hannayenta tana kokarin raba hannanyensa da kunkurunta da yake rike da shi yana murzawa a hankali, kwantar da fuskarsa yai ya raba lips dinaa biyu ya saka lip dinta na sama a tsakiyar nasa, ya tsotsa a hankali, sai kuma ya kama na kasan shi ma ya tsotsa, sannan ya cire bakinsa ya sake ta yai baya baya yana kallonta yana murmushi, for the first time in his life yawun wata mace ya gwaraya da nasa, and her lip is so soft and sweet.
Ita kam tsaye tai kamar hoto tana kallonsa ido kamar za su fito wajr su yi magana, tsabar mamaki da kuma tsoro daya same ta a lokaci daya, sai kuma ta kai hannunta ta taba lips din nata still tana kallonsa. Hannayensa ya daga mata yana mata bye bye.
“Shiga gida na ga tafiyarki”
Ta juya kamar marar kafafuwa ta fara tafiya, sai da ta tura gate din ta shiga sannan ta juyo ta kalleshi yana tsaye gurin motarsa yana kallonta har sai da ta saki kofar ta shige ciki, sannan ya sauke sanyayayiyar ajiyar zuciya bude motarsa ya shiga, yai mata key. Dayan hannunsa ya kai ya shafa kansa yana murmushi, zuciyarsa cike da nishadi da farinciki from nowhere, and now he realized he miss alot, ya dan cika bakinsa da iska sannan ya busar a hankali still smiling. Reaction dinta na dazun yake tunawa yadda ta tsaya tana kallonsa da mugun shock. Driving yake a hankali sai da ya iso gate din gidansu sannan mood dinsa ya canja sam ba zaka ganshi kace shi mutumen dazun a gaban Aminatu. Sau biyu ya danna horn aka bude masa gate sai ya shigo cikin gidan kamin a rufe gate din ya tsayar da motarsa ya sauke gilashin motar ya leko waje.
“Garba”
“Na'am”
Mai kokarin rufe gate din ya amsa da sauri tare nufo inda yake, sai police din dake zaune ya tashi ya nufi gate din ya karasa rufewa.
“Gani ranka ya dade”
“Dazun bayan na fita waya fita?”
“Amal ce kawai ta fita tare da Direba”
“Bayan ita fa?”
“Babu wanda ya sake fita, Sai Kabir daya dawo, ita har yanzu bata dawo ba”
“Da wace kalar mota Kabir da Amal suka fita?”
“Amal baka ce ta Hajiya, Kabir ma Baka ce gata can”
Ya nuna inda motar take, Talba ya dan yi shiru yana nazari, hasken motar ba zai bar shi ya ga kalar motar ba, sai dai da ace fara ce da zai iya gane fararce duk da kasancewar akwai duhu sosai a unguwar kuma inda motar ta tsaya yafi duhu.
“Okay tafi”
Yaja motar ya karasa inda ya saba farking ya aje motar, sannan ya bude ya fito ya nufi main door din shiga falon, wani bangaren na zuciyarsa na raya masa Amal ta wani bangaren kuma yana ganin kamar Amal ba zata iya masa haka ba, idan ma ita ce fitowa za ta yi ta nuna masa ta ganshi, duk wanda ya ganshi yai masa abun da yai masa babba ne ba karami ba, and he's very smart.
Door bell ya danna aka sai Mairo ta bude masa kofar tana masa sannu da zuwa, kai kawai ya daga mata ya shiga cikin falon yana sauke idonta akan Kabir dake hakimce saman kujera yana kallonsa fuskarsa da murmushi, Talba ya nufi dinning.
“Ango...”
Kabir ya fada, jutowa yai sai dai be ce nasa komai ba har sai da Sai da Mairo ta koma kitchen sannan Talba ya sake kallon Kabir.
“Kana tunanin abun da kai abun burgewa ne”
Kabir ya masa kallon rashin fahimta.
“Ban gane ba”
Talba ya bar dinning din ya nufo inda Kabir yake yana masa wani mugun kallo.
“Ba zaka gane ba, you're just fooling yourself, idan ma kana ganin kai mai wayo ne, to baka iya komai ba, stay away from me, babu ruwanka da rayuwata, kuma idan wani abu ya samu yarinyar nan kai ne sila”
“Wace yarinya?”
Daga shi har Kabir din stairs suka kalla, sai suka ga Momy a tsaye tana kallonsu sai dai bata karasa saukowa ba. Talba be ce komai ba ya juya ya nufi kofar fita daga falon, Kabir kuma ya bishi da kallo mamaki, domin gaba daya be fahimci inda ya dosa ba, saboda kawai yace masa ango? Kawai ya fada ne dan ya zolaye shi, domin a ganinsa shi ango ne shi tun da an saka date din aurensa da Leila, ba kalmar ango kawai ba, wace yarinya yake magana akai?
“Wace yarinya miya faru me ka masa?”
A lokaci daya Momy ta aiko masa da wadannan tambayoyin. Sai ya kalleta ya daga mata kafadunsa alamar be sani ba.
“No dole akwai wani abu, kuma ya san ka sani, da ba zai zarge ka ba, dan haka ina bukatar sanin komai”
“Ban san komai ba Momy ban ma san abun da yake magana akai ba”
Momy ta nuna shi da yatsa.
“Dole ne ka fada min ko minene idan ba haka ba, idan Daddynku ya dawo zan fada masa abun da yake faruwa”
Kabir ya mike tsaye
“Haba Momy sai kace wani karamin yaro? Ban san komai akai ba, ban san wace yarinya ba ce me yake magana akai i know nothing, excuse me”
Ya barta a tsaye gurin ya nufi kofar fita ransa a bace.
BATURIYA POV.
A cikin napep ta cire mask dinta sannan ta sauka ta mika masa kudinsa ta shiga gida. Da sallama ta shiga falon sai Umma ta amsa mata ciki ciki tana mata kallon tuhuma. Abun ka da marar gaskiya sai ta zauna saman kujera tana dan satar Kallon Umma.
“Daga Ina kike?”
“Gidan Yaya mana”
“Aisha a daga can ta fito, kuma tace baki je can ba”
Wani irin faduwa gaban Baturiya yai sai dai hakan be hana ta kankaro karyar da zata saka ta kare kanta ba.
“Aa naje sai dai ban dade ba na fito na tafi gidansu wata kawata!”
“Wace kawar? Ai baki fada min zaki je gidansu kawarki ba?”
“Haba Umma ni fa bazawara ce a yanzu ba budurwa ba, idan zan je gidan kawaye har sai na fada”
“Saboda kina bazawara shi ya baki lasisin yin yadda kike so? Ni fa kwana biyun nan ban ganewa kanki ba, kina yawan fita da sunan zuwa gurin Yayanku sai yawan fitarda kudi da ban san inda kike samo su ba, ina iya bawa yayana lasisin yin komai ban da aron hannu”
“Haba Umma kalle ni ki gani, tsakani da Allah ina da kyau fa, Wallahi kusan kullum idan na fita sai wani ya min magana, ina tsayawa a gidan Yaya ne nai zance da su, saboda yanayinsu yawanci yayan manya ne kuma kin san gidan yaya yafi wannan kyau da tsari, babu wanda zai ga ka fito daga gidan ya raina maka wayo, yan kudin nan ma da kike gani ta hannunsu nake samu”
“Idan haka ne, ai sai ki fitar da na aure, tun da kin cika idda”
Ta yi dariya.
“Karki damu Umma, nan ba da jimawa ba zan fitar da daya In shaa Allah”
“Allah ya nuna mana”
“Aamin, yau ma akwai wanda zai zo ammam shi gidan nan ma zai zo”
Ta amsa tana mikewa tsaye ta nufi hanyar dakinta, ita da Aisha. Umma dai bata ce mata komai ba, ta bita da kallo har ta shige. Tana shiga ta yaye gyalenta ta aje ta ciro wayarta a jaka ta kunna, tana kunnawa kiran Fahat na shigowa wayarta, da sauri ta danna picking ta kara a kunne tana murmushi.
“Dear”
Fahat ya jingina