Showing 153001 words to 156000 words out of 332834 words

Chapter 52 - Bakar wasika Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

65324

zai haifar muku da matsala ba? Baka ganin hakan zai iya sakawa su can su tsane ta?”
 
Cewar Salamatu tana kallonsa.
 
“Idan ma sun tsane ta, ni dai ina son ta kuma ba zan tana yarda a cutar da ita ba ko kuma ni da kaina na cutar da ita, a kokarin sama mata wasu iyalin na kawo ta nan, a can ma abubuwa da yawa marasa dadi sun faru saboda ni da ita, ina tunanin ko da a mafarki aka ce muku zan cutar da ita ko kuma na yarda a cutar da ita ba zaku yarda”
 
“Wallahi ko kadan, ban kawowa raina Cewar zaka cutar da ita ba, ai babu wanda ya dace ta aura sama da kai, kai da kasan komai nata kuma kake tausayinta, kawai dai ina ji maka tsoron abun da zai faru ne a gaba, kasan za su iya fushi da kai”
 
Salamatu ta sake fada tana kallon Kaka dake jinjina kai.
 
“Wannan kuma ai mai sauki ne, komai zai wuce Inshallahu, ni dai yanzu ina son ku amince min ayi komai tsakanin yau zuwa gobe amman da idan har ta amince domin bana son na cilastata”
 
Kaka ta dafa shi.
 
“Karka damu ita fa bata san so ba, kuma ta sabawa kanta da kuka tun da ka tafi kullum kuka take sai ciwo, bata da wayo amman an mata auren zata yi hankali”
 
Yayi shiru ya sauke kansa kasa can kuma yaja numfashi a hankali ya sauke.
 
“Na yi magana da Kawo Hasan kuma ya nuna min cewar ba wata matsala, amman duk da haka ina son yi sake yin magana da shi, sai a yanka min sadaki kuma idan son samu ne a daura auren nan yau ko gobe kamin Daddy ya canja shawara”.
 
“Ka yi gaskiya saboda bakar matar nan ma zata iya kitsa masa wani yace ya canja shawara ba zaka aureta ba, kuma dan be saka hannunsa ba, sai me ai mu masu yi maka komai ne, ba mu hana ka auri yarsa ba karawa kawai aka ce kai amman sai taya yarsa kishi yake, wannan abun da kai ni ka yi wa Allah ya maka albarka”
 
“Ameen”
 
Ya amsa sannan ya mike tsaye ya saka hannayensa aljihu.
 
“Idan kun yi magana da su, sai ki sanar min domin ina son komawa yau, idan kuma hakan be samu ba, zan jira har sai zuwa gobe idan an daura auren”
 
“To bari na nemo shi yanzu”
 
Kaka ta fada sai ya sa kai ya fice ya bar Kaka da Salamatu kadai a dakin. Salamtu ta kalli sarakuwarta cikin yanayi na damuwa ta ce.
 
“Inna baki ganin hakan zai iya haifa da matsala? Allah ya ma ba aurenta zai yi ya tafi ya barta ba sai an gansa”
 
“Aiko da sun ci ubansu, daga shi har uban nasa, be ma isa ba, idan zai tafi kafarta kafarsa haka zai tafi da ita, idan ma wayonsa kenan ba zan yarda ya barta ba”
 
“Toh sai dai haka nan, kam idan ba haka ba zai iya mana wani wayon kin san halin yaran nn na zamani, amman kam da ta yi miji yaro barakalla da shi gwanin kyau”
 
Kaka ta tashi zuwa neman danta Hassan. A lokacin da Talba ya fita daga dakin Salamatu sai ya koma dakin Kaka, daga bakin kofa ya tsaya yana kallon Aminatu dake kwance rairai idonta a rufe, sai dai jin kamshin turarensa yasa ta shakar kamshi bada ta san yan tsaye bakin kofar ba, idan yaja numfashin da karfi sai ta sauke a hankali.
 
“Kina son turarena amman baki son kusanci da ni”
 
Ta bude idon ta sauri ta juyo ta kalli gurin kofar sai ta ganshi a tsaye, wani irin kwarjini da haifa ya kara a idonta. Idan har tace bata son Talba to ta yaudari kanta kuma ta yi karya, amman tana sonsa? Anya akwai son sa a zuciyar dake cike da damuwa da bakinciki? Anya ma ta gama karantar minene son? Ko kuwa dai sabo ne irin wanda ta ji a wacan lokacin da tafi ya barta, a yanzu ma idan bata amince ba zata sake ganinsa ko kuwa zai tafi ne har a bada ba zai dawo ba?
 
“Tashi ki ci abinci idan ba haka ba zan kira wannan mutun ya zo yai miki allura”
 
Daga inda yake tsaye ya fada, sai ta tashi zaune tana turo baki tana masa wani kallo dake nuna alamar kiris ya rage ta fashe masa da kuka. Sai yai murmushi ya saka kafarsa cikin dakin ba tare da ya cire talkaminsa ba.
 
“Idan kika aminta kika zauna da ni, zamu rika ganin juna kullum, amman idan kika ki ni wata kila ba zaki sake ganina ba Aminatu, amman na san ba zaki bawa Kaka kunya ba ko?”
 
Ta yi shiru sai kuma ta fashe masa da kukan da bata san na minene ba. Cooler ya dauka ya sake budewa ya saka hannunsa ya rika dauko farfesun ya kai mata a baki.
 
“Bude baki”
 
Ta bude bakin daker tana ta kukan shagwaba. Sai ya kai mata a bakin yana kallon kyakkyawan lips dinta.
 
“Pretty girl”
 
Ya furta yana hade yawu, even though be taba kissing lips din wata mace ba, he like her pink lips, dan karamin bakinta nan ya dauki hankalinsa sosai da yadda take tauna abinci a hankali kamar ya mata dole. Da hannunsa yake bata har sai da wayarsa tai ringing sannan ya saka hannunsa na hagu ya karba kiran kawo Hassan sannan ya mike tsaye yana fadin.
 
“Okay gani zuwa”
 
Be ce mata komai ba ya fice daga dakin, a harabar gidan ya kunna bohore ya wanke hannunsa sannan ya nufi dakin wajen, ba Kawo Hassan Kawai ya samu a gurin ba har da wane kanen Hassan din wanda shi na kawo ne a gareshi da kuma Kaka, kusan abun da suka tattauna a dakin Salamatu shine suka sake tattauna da Uncles din nasa, sai da ya tabbatar musu da babu wata matsala sannan suka amince akan gobe idan an sauke Sallah azahar za a daura masa aure da Aminatu a Masallacin kofar gidan. Kawu Hassan sai nuna bacin ransa yake akan abun da Daddy yai yana ganin kamar ya wulakanta kuma ya nuna shi kadai yake da iko da Talba, be jidadin da za a yi komai ba tare da shi ba, amman be tsammaci haka daga gareshi ba, sai dai dukansu sun raja'ah ne aka ce maganar Kaka cewar saboda ya maida su talakawa ne shi kuma yan ganin shi mai arziki ne.
A garin Talba ya wuni har dare, sai guraren tara da rabi Daddy ya kirashi Saboda Momy ta fada masa Talba baya gidan, sai da ya fita waje can nesa da gidan sannan ya amsa kiran Daddy, ya fada masa cewar yana gurin Kaka.
 
“Amman kasan yanayin kasar nan ki? Musamman kauye idan sun ga bakuwar fuska har hada kai ake azo a dauke mutum, sannan taya zaka yi tafiya baka fada min ba?”
 
“Saboda zaka iya hanani da wannan hujojin naka daka zayyano a yanzu, ni kuma ina bukatar zuwa saboda na yi magana da Kaka ka san tana cikin fushin a yanzu”
 
“Na ji ka dawo da wuri, Allah ya tsare, kuma ka yi addu'a sosai Wallahi ina tsoron garin nan”
 
“Inshallahu Daddy babu abun da zai faru”
 
“Toh Allah dai ya tsare, amman ka daina wasa da rayuwarka irin haka”
 
“Inshallahu”
 
Daga haka sukai sallama sannan ya kira Momy ita ma ya sanar mata inda yake ya kuma fada mata ba zai samu dawowa ba sai gobe.
 
“Allah yasa dai ba gurin yarinyar nan ka tafi ba”
 
Momy ta fada cike da gadara.
 
“Momy kina manta cewar akwai zumunci a tsakanina da ita a yanzu, ko bayan ita kuma Kaka ta tana nan kuma tana raye dole ne na rika zuwa”
 
“Hmmm Talba kenan, a hannuna ka tashi karka ce zaka min wayo, ni dai n gargadeka, kuma na ja maka kunne ka fita sabgar yarinyar nan tun wuri indai har ka dauke ni uwa, ina tunanin zaka ji magana ta”
 
Ya sauke ajiyar zuciya ba tare da yace komai ba, Momy ma bata sake cewa komai ba ta kashe wayar, sai ya koma cikin gidan ya ari wayar Kaka da sunan zai duba wata number yai blocking din number Daddy a wayar Kaka sannan ya goge number gaba daya, gudun kar Kaka tai karabanin cewa zata kira shi.
 Bayan ya gama abun da zai yi ya mika mata wayarta ya fita, Kawu Hassan ya shigo dakin Kaka ya saka Aminatu a gaba yana tambayar idan tana son Talba, sai dai Kaka bata bata damar amsawa da eh ko aa ba, duk inda Kawu Hassan yai sai a tare, tana cewa wai Aminatu bata da wayo bata san ciwon kanta ba, kuma ba san minene so ba. Ita kanta Aminatu da za a bata dama da bata san wace kalar amsa zata bawa Kawu Hassan ba, domin kanta a yanzu a duhu yake.
Daga ita har Talba bachinsu kadan ne, misalin biyu da rabi ta tashi ta shiga bandakin Kaka tai alwala ta fara raya daren na Laraba tana kaiwa Allah kukanta da neman zaba mata abun da zai zame mata alheri da kuma rokin daukinsa a dukan al'amurranta, ta bangaren Talba ma sallah nafila ya kwana yi, a da can sai dai yai raka'a biyu yai karatu da addua ta kwanta sai dai wannan karon har asuba yana zaune a saman carpet din da yai sallah yana karatun qur'ane, bayan ya kamalla ya fadawa Allah bukatarsa da neman daukinsa a abun da yake kokarin aikatawa.
 Washe gari abun kari na musamman Kaka ta saka aka shirya masa, aka kawo masa har dakinsa, ruwan tea kawai ya sha ya kasa cin komai, sai abubuwan da suka faru a jiya suka rika dawo masa, ya sani akwai kalubale mai yawa a gabansa, sai dai yayi ma kansa alkawarin duk rintsi duk tsanana ba zai taba yarda ya cutar da Aminatu da saninsa ba.
Misalin Tara da yan mintuna Kawu Hassan ya same shi da maganar Sadakin da kuma wanda zai masa walicci domin shi zai dauki bangaren Aminatu ne.
 
“Na saka dubu ashiri Hajiya tace yayi kadan zai dai a saka arba'in”
 
“Ba matsala Kawu zan bada 100k,  Inshallahu”
 
Kawu yayi murmushi yana mamaki.
 
“100k fa kace Mu'azu, aa yayi yawa”
 
“No be yi yawa ba, ita kanta Aminatun ina son ta ji cewar na dauke ta da kima”
 
“Duk da haka dai dubu dari yayi yawa”
 
“Be yi yawa ba Kawu, Allah dai ya tabbatar mana da alheri”
 
“To amin”
 
Talba ba mutum ne mai yawo da kudi mai yawa ba, haka ya saka dole sai da ya je POS ya cire wasu kudin sadakin ya bawa Kawu da kuma kudin da za a siye komai na al'ada na daurin auren. Bayan ya dawo ne ya kira Ali ya fada masa komai, at first Ali dariya ya fara masa kamin ya biyo da addu'a sannan ya tabbatar masa cewar da shi za a daura auren nan.
Haka kuwa akai, kamin lokacin daurin auren ya iso garin tare da sabuwar shaddda mai masifar kyau da tsada sai kyalli take kana ganinta kasan ta ci kudi, fara ce sol zagenta ya fito kwar gwanin sha'awa, not just shadda hula da Talkamin da Ali ya siyo masa ma abun kallo ne.
 
Misalin karfe biyu da yan mintuna aka daura aurensa da Aminatu, ba zai iya cewa happy marriage ba ne, and it's not the sad one, sai dai ya samu kasa da farinciki marar misaltuwa, wani irin annashuwa da natsuwa suka saukar masa, fuskarsa sai haiba take kana ganinsa ka ga ango. Ko kadan fuskarsa ko dabi'arsa da mu'amalarsa bata nuna cewar baya son auren ba, domin shi kansa yana jin matsayinsa da kwarjininsa su karu.
 
 
 
 
BATURIYA POV.
 
 
Kamar yadda tai masa alkawari, a ranar ta same shi a gidansa na hutawa, suka aikata masha'arsu kamar wacan lokacin. Sai dai wannan karon bata yarda ta kai dare ba saboda tana son zuwa asibiti ganin likita kamar yadda ta fada a gida da karyar zuwa asibiti ta samu fitowa.
Wannan karon a account ya saka mata 450k a maimakon ya bata a hannu, saboda ta fada masa bata son kudin a hannu. Yadda yake santi yana yabonta har yafi na wacan karon, sai wani narke mata yake a jiki kamar zai shige ciki, daker ta kwanci kanta domin a ra'ayinsa ya so ta kwana a gidan ne, sai ta nuna masa tana a karkashin iyayenta ne za su iya zarginta idan ta kwana, sai dai bata yarda ta nuna masa cewar tana da aure ba, sai ma karyar da tai masa cewar mijinta ya rasu ya barta da yaro daya.
 
Misalin hudu da kwata ta fito daga gidansa, sai da ta shiga Napep sannan ta kira Ramlee ta sanar mata cewar yanzu ta fito daga gida, domin bada sanin Ramlee ta hadu da shi ba, kuma ta san idan har taji sun hadu ta bayan fage zata iya zargin Baturiya.
 
“To ki tsaya ta sokoto Road, zan zo a dauke ki”
 
“Okay toh amman karki dade dan Allah”
 
“Okay”
 
Baturiya ta sauke wayar tare da shafa cikinta tana jin irin abun da take ji a duk lokacin da tai yunkurin zubar da cikin, sai dai bata da mafitar data wuce wannan, domin idan bata zubar da cikin ba zai iya bata matsala tsakaninta da Fahat, wanda bata fatan haka.
 A kusa da wani shagon mai Napep din ya sauke ta sannan ta fita ta ciro kudinsa ta ba shi taja gefe ta tsaya sai taunar cingan take tana wani kis kis kis, kamar wata tsohuwar karuwa, dan mayafin dake jikinta ma ba wani abun kwarai ba ne yadda kasan wata yar iskar budurwa haka ta fito, arzikinta daya abaya ce a jikinta ba Atamfa ko lace ba. Ta kusan minti talatin a gurin har ta fara gajiya ta fara takawa gafen titin tana tafiya sannan Ramlee ta kirata sai ta kwatanta mata inda take, tana sauke wayar wata Benz ta wuce gabanta sai kuma ya dawo baya ta faka daidai inda take tsaye. A hankali mai tukin motar ya sauke gilashin motar yana kallonta, suna hada ido sai ta sakar masa murmushi shi kam ya dade da yi ma fuskarsa ado da murmushin.
 
“Hajiya ke ce haka dai?”
 
Ta dauke kai tana fari da ido sannan ta sake kallonsa da kyau, shi din ne dai abokin Faruq da ta taba roka kudi ta WhatsApp a lokacin data saci numbersa a wayar Faruq.
 
“Ni ce dai ranka ya dade, ya akai ka gane ni?”
 
“Kyakkyawar mace irinki ai kowa ya gani zai tsaya, sai dai daga baya mutum zai tantance idan ya sanki ko akasin haka”
 
Ta yi murmushi.
 
“Ka dawo nan ne ko zuwa kai?”
 
“To gani nan dai, Ina zuwa haka? Ina abokin nawa ya barki a rana tana gasa ki”
 
“Abokin ka ai ya dade da yin tazara, duk kyau surar nan da kake gani ya zubar wata zai dauko”
 
“Subhanallahi, lallai da labari a bakin naki mai kyau, da zaki taimaka min da kin shigo motar nan”
 
“Wallahi kawata nake jira, zata zo nan ta dauke ni”
 
“Okay”
 
Ya dauko katinsa ya mika mata.
 
“Gashi a taimaka a kirani, duk dai na san ba a rasa number”
 
Ta yi murmushi bayan ta karba, sannan ta daga kai tana kallon Ramlee data faka a dayan gefen.
 
“Okay zan kira ka Inshallahu”
 
“Na gode kyakkyawa”
 
Ya fada yana kare mata kallon irin kallon nan na yan iska. Sannan ya rufe gilashin motar ya hau titi, ita kuma ta nufi gurin da Ramlee ta faka motar ta bude ta shiga.
 
“Waye wacan?”
 
“Wani abokin Faruq ne”
 
“Okay”
 
Sai da suka hau titi sannan Ramlee ta kalleta ta ce.
 
“Hope dai kin shirya?”
 
“A shirye nake, kawai dai ina gudun a samu matsala ne”
 
“Ba wata matsala, Dr KB kwararen likita ne, ba yau na saba aiki da shi ba, ki kwantar da hankalinki”
 
Ajiyar zuciya ta sauke tana jin kamar kar ta aikata.
 
 
 
________________
 
Inshallahu a nan zamu dakata sai kuma bayan sallah idan mai kowa mai komai ya amince mana ganin lokacin cikin koshin lafiya. Fatar Allah ya karba mana ibadar da zamu shiga ya yafe mana kurakuranmu.
 
Ina neman afuwarku. Sai mun hade a Book 2 bayan Sallah inshallahu. Happy Ramadam
 
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
 
_Fatar mun yi sallah lafiya. Allah ya maimaita mana._
 
 
AMINATU POV.
 
Tun da kalmar an daura aure ta daki kunnenta sai ta nemi natsuwarta ta rasa, a take wani kalar yanayi mai wahalar misaltuwa ya rufeta, zuciyarta ta shiga bugawa da karfi fiye da fitar numfashinta.
Banbancin wacan bugun zuciyar a wacan daren da yau kadan ne, wacan ya kasance na fargaba da tsoro ne, tsabanin wannan da ba zata kira shi na farinciki ba kuma ba na bakincikin ba ne, wata kila bata cancanci auren a yanzu ba ne, wata kila kuma wani tarin bakincikin ne yake kokarin yi mata sabuwar shimfida. Haka tai ta sake sake tana jin kamar tai kuka gashi kuma hawayen ba su shirya ziyartar idanuwanta ba. Duk shigowar da ake ana saka mata albarka a dakin Kaka bata yarda ta daga kai ta kalli kowa ba balle ta san su waye ke kai da kawo a dakin. Ana kusan sallah La'asar Kaka ta shigo dakin da far'arta ta duka gaban Aminatu ta bude kwanon abincin da aka aje mata.
 
“Har yanzu ba ki ci ba? Ki wuni da yunwa tun safe ace har yanzu ba ki ci komai ba, to ko dai a kawo miki fura?”
 
Yunkurin bude baki tai ta amsawa Kaka sai ta ji bakin na ta yayi nauyi kamar wanda kalamanta suka kare, hakan yasa ta girgiza kai, Alamar aa.
 
“Ai dole ki ci wani abu kam ace mutum ya zauna da ciki haka tun safe”
 
Kaka ta fada tana Juyowa ta fita, a nan ma Aminatu ta yi ta kokarin ganin ta bude baki ta fada mata cewar ba zata iya shan komai ba amman ta kasa. Hannunta ta kai ta taba bakinta sai ta ji shi a bushe ba bakin ba har makoshinta a bushe yake, iyakar kokarin da tai na hade yawu ne saboda ta jika makoshinta. Idanunta na kan kofar har Kaka ta dawo dakin rike da kankara a cup ta nufi inda kwayar furarta take ta bude ta debi furar ta zuba a cikin kankarar sannan ta rufe ta aje furar ta nufo inda Aminatu take zaune.
 
“Ta so Mai gida yana son magana da ke”
 
Kamin Aminatu tai wani yunkuri har Kaka ta rika hannunta

Join Our Groups

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login