Showing 318001 words to 321000 words out of 332834 words
hakurinsa mai girma ne, kuma duk yadda Allah ya jarrabe ka, ka duba na masa da kai wani ya fika shiga uku a rayuwa, sai kai hamdala ka godewa Ubangijinka”
Ya sumbance saman idonta yana murmushi.
“Shiyasa na ke sonki, kina da zurfin tunani da basira”
Ta yi murmushin ita ma tana ta shakar kamshin turarensa. Kamin ya saka hannunsa ya dago kanta a hankali ya hade bakinsu yana sotsar lisp dinta cike da kwarewa da shauki, tun yana yi tana amsar sakonsa jikinta na amsa amo har ya fara kokarin wuce gona da iri, hakan ya saka tai saurin rike hannunsa tana kokarin matsawa baya sai dai ta saka samun damar hakan saboda dayan hannunaa yana rike da kunkurunta ne. Daker ta samu ta cire bakinta daga na shi.
“Kar Mama ta ga na dade”
“Mama ai ta san sallama zaki yi da mijikinki”
Ya fada yana kallon lips dinta da take motsawa a hankali, tun da yake tare da ita be san ya gundura da kissing dinta ba, sai dai ya kawar da kai kawai idan ta kama, amman ba dan baya so ba ko kuma ya gaji. Ta saka dayan hannunta jamye hannunsa daga rikon da yai mata sannan ta bude motar ta fita, bata ko tsaya ce masa komai ba ta nufi kofar falon ta bude ta shige, sai da ya ga haka sannan ya bude side dinsa ya fita ya shiga driver seat yai ma motarsa key ya fice gidan.
Kwana biyu da faruwar hakan, ya shigo falon ya samu Amal zaune ita kadai a falon kwance saman kujera plasma na kunne amman idanuwanta suna ta wani gurin kana ganinta kasan tunani take yi. Sai da ya zauna kusa da ita sannan ta ankarar da shi din ta kalleshi da sauri.
“Laa Ya sannu da zuwa”
“Little Sis me mike tunani?”
Ta kalleshi.
“Momy”
“Miya same ta?”
“I don't want to lose her”
“Waya ce zaki rasa ta?”
“Tun da aka kama Leila bata sake lafiya ba, kullum acikin ciwo take”
“Zata ji sauki, tana kewar Leila ne kawai amman very soon zata daina saboda zata saba kamin a yanke hukunci”
“Amman Ya Leila zata dawo ko?”
“In Shaa Allah, but you have to be strong saboda Momy Okay”
Ta daga masa kai tana share hawayen da suka zubo mata.
“Tashi ki ci abinci na san baki yi lunch ba, zan yi magana da Momy yanzu amman make sure before na fito kin gama cin abincin kin ji yar kanwata”
“Toh”
Ta amsa a shagwabe, sannan ya mike tsaye ya nufi upstairs, ita kuma ta nufi dinning taja kujera ta zauna. A hankali ya tura kofar dakin ya shiga sai ya same ta zaune karbi rike a hannunta tana ja, idanuwanta sanye da farin gilashi. Cire gilashin tai tana kallonsa da idanuwanta da bata iya gani sosai da su saboda kukan da take a kullum yana taba idonta. Kusa da ita ya zauna yana kallon kofin tea dake aljihun gadon.
“Wata kila tea din nan kawai kika saka a cikinki?”
Ta dan yi murmushin karfin hali.
“Kasan bana iya cin abu mai nauyi Talba”
“Momy miyasa mike ta damuwa da Leila ne kawai? Kin manta kina da ni da Amal da Kabir? Dukanmu ba zamu iya jurewa idan wani abun ya same ki, and Leila ma ba zata jidadi ba idan ta san irin wannan halin kike, dubi yadda kika rame, me kike son mu yi ne Momy? Why not ki barwa Allah komai”
“Na barwa Allah komai Talba, amman na kasa cire a abun a zuciyata, ko a mafarki ban tana tsammanin Leila zata yi rayuwar gidan yare ba, kuma ace mahaifinta yana a raye be yi komai ba dan ganin ya ceto rayuwarta”
“Idan kin barwa Allah to ki daina ganin laifin kowa, kuma ki yi ta godiya ga Allah kina neman yafiyarsa”
“Ina ta yi Talba, ina ta kokarin ganin al'amurra sun daidaita ko dan saboda ku, kawai dai na kasa cire abun a raina ne, kuma ina ta jin tsoro ina ganin kamar kashe Leila za'ayi”
Ya matsa kusa da ita ya rumgumeta, irin rumguma ta ďa da uwa, domin ta ba shi tausayi matuka.
“Duk yadda Allah ya tsara haka zai kasance, ki saka wannan a ranki, kuma ki daure ki rika cin abinci dan Allah Momy”
Ya tsagaita hawayen da take.
“Allah ya maka albarka Talba”
“Ameen”
Ya amsa yana jin kamar yayi kuka, domin har ga Allah baya son damuwar Momy musamman irin wannan da ba asan ranar da zata daina ba.
Wannan karon har da yan jaridu na social media da kuma na newspaper. Daddy ba jidadin hakan ba sai dai babu yadda ya iya domin aikinsu suke yi kuma da Leila bata aikata ba da basu mata haka ba. A wannan ranar kam Leila ta rufe fuskarta da mayafinta ta zauna a inda aka tanadar mata kusa da lawyer dake tare da rakiyar duka lawyers din chamber su. An gabatar da shari'a biyu kamin ayi ta Leila, kasancewar Lauyer kwararen ya gabatar da da kansa a matsayin lauyan da zai tsaya mata. Sannan aka shiga cikin shari'ar. Iyakacin abun da Lauyer yake nunawa Leila ta aikata hakan ne a kan kuskure, wanda hakan ya bawa Lauyan gwanati karyata ta shi da nashi hujojin. Daga karshe Barrister Fatihu ya nemi a bada belin Leila sai dai hakan be samu ba, alkali yayi duba da laifin data aikata ya sake bada umarni tsareta a gidan kaso.
A ranar ma Momy ta dawo gida cikin wani irin yanayi mai wuyar fassara, domin jikinta a kullum sanyi yake tana ganin kamar Leila ba zata samu sassaucin kotun ba, musamman lura da tai da yadda Alkalin yake da zafi.
Yan'uwan Baaba suka tafi gida cikin farinciki kamar wacan karon, domin suna ganin alamun kamar za ayi musu adalci.
Bayan sallah azahar Talba ya shigo dakin Momy domin dubata sai ya same ta zaune kasa tana ta jan carbi. Karaso yai kusa da ita ya zauna al'adarsa a yanzu duba lafiyarta safe rana dare. Kallonsa kawai tai ta sauke kai kasa ba tare da tace komai ba.
“Ina tunanin daina shan maganin nan zaki yi ma Momy kar yaje ya sama miki matsala”
Ta kalleshi sai dai bata ce komai ba har lokacin, fatar idonta har wani baki tai saboda bakinciki da kuka.
“Kina ji lokacin da Kabir ya fada miki cewar shan magani da kike ba zai amfana miki komai ba matukar baki daina tunani ba, haba Momy kalli yadda kika rame abinci ma baki iya ci, kullum sai kuka da tunanin Leila, ba laifi ba ne tunaninta amman zaki iya kamuwa da wani ciwon kin ga an yi ba ayi ba kenan”
“Ina ta kokari amman na kasa, ji nake kamar na mutu na huta Talba, zuciyata har wani zafi take”
Ta fashe da kuka sosai jikinta na rawa.
“Komai zai wuce Momy, ake rasa rai ma a hakura balle ke da Leila take a raye, kuma ina kyautata zaton zata dawo gareki”
“Ban ga alamar hakan ba, tun da gashi ko belinta sun ki bada ba”
“Ba daga nan take ba, Alkali yana bada beli ne idan ya gamsu da hujojin da aka bashi da kuma duba da yanayin shari'ar, Leila tana amsa laifinta a duk inda aka je, kin ga bata wahalar da kotu ba kuma hakan ya nuna ta yi nadama duk kotu zata duba wannan kamin yanke hukunci”
“Allah ya sa hakan ya kasance”
“Ameen, bari na kawo miki wani abu ki ci dan Allah”
Ya mike tsaye sai ta kalleshi tana jinsa kamar dan cikinta, domin kulawar da yake bata da nuna mata damuwarsa ko Kabir da yake danta baya mata shi.
“Ina Aminatu?”
Ta fada a yayinda ya kusa isa gurin kofar dakin, sai ya juyo da sauri ya kalli Momy cikin tsananin mamaki yana kokarin tantancewa ko dai be ji daidai ba ne. Sai dai murmushin daya gani a fuskarta tare da hawaye ya tabbatar masa da muryarta ya ji.
“Tana Lafiya?”
Kallonta kawai yake kamar mai shawarar amsawa.
“Lafiyarta kalau Momy”
Ta daga masa kai, sai ya juya ya fita. Downstairs ya sauko ya dauki plate ya zuba mata abinci ya dora a tray ya shiga kitchen ya dauko lemu da cups da ruwa ya dora a tray sannan ya dauka ya nufi upstairs, yana kallom Kabir dake zaune a sofa yana waya da Rukaiya. Sannu sannu yake takowa har ya hauro sama ya shiga cikin dakin ya aje tray gabanta.
“Shimkafa da miya ne, kuma na san kina sonsa”
Ta kalli abincin sannan ta kalleshi.
“Kwanakin baya, Daddynka ya min magana akan matarka yace ya maka maganar tarewa ka nuna masa baka son na shiga damuwa, ka ce ya bari sai gaba”
Ya mika mata plate din abincin yana fadin.
“Ba yanzu ba Momy, muna cikin wannan hali be kamata Daddy yayi wannan maganar da ke ba”
“Amman yana da gaskiya Talba, za a iya daukar lokaci ba a gama shari'ar nan ba, ka ga mun shiga hakkinka da na matarka, karka dubi halin da nake ciki ka hana matarka tarewa a gidan ta, daman ance kana naka Allah na nashi, muna ta zancen aurenka da Leila sai gashi ka auri yarinyar nan, yanzu kuma ana son yin auren sai ga wannan abun ya faru, mu barwa Allah ikonsa mu yarda da kaddara kawai shi ya fi”
Da ya kalleta sai tausayinta ya rufeshi, ya sani da can ba son Aminatu take ba, saboda Leila a yanzu kuma ita da kanta take bashi damar tarewa da ita.
“Shikenan nan Momy zan duba”
“Dan Allah kai yi abun da mahaifinka yake bukata, na san na shiga hakkinku kai da matarka amman duk...”
“Shikenan Momy ki ci abincinki dan Allah, zan yi”
Ya share hawayenta kamar karamar yarinya ta fara kai abincin a baki tana taunawa duk kuwa da kasancewar ta daina jindadin abincin tun daga lokacin da wannan tashin hankalin ya sameta, sai rashin lafiya ga rama da yawan kuka kullum Leila na cikin ranta ga zullum shari'ar da ake bata san yadda karshen zai kasance ba.
FARUK POV.
Sannu Sannu alaka mai karfi ta shiga tsakaninsa da Ramla, har ya fara zuwa Lagos gurin aikinsa yana dawowa gida yayi weekend. Kullum sai ya kirata sun yi hira, idan kuma ya dawo week zai yi mata tsaraba duk kuwa da kasancewar ta nuna masa bata so.
A wani kamfanin siyar da motoci da koyar da tuki ya koyi yadda ake tukin motar, bayan ya kamalla suka ba shi certificate, ta waya ya dauki hoton ya turawa Ramla ta rika masa dariya wai ta ya sani ya bari ta koya masa ai ta iya.
“Ai ko yanzu dare be mana ba, kuma ba a kure lokaci ba”
“Aa yanzu ai ka rika ka je wani gurin ka koya, dan haka ni zan koya maka ba tun da an rigani”
“Ki ce duk abun da ya kwana baki cin dumame kenan?”
“Wani abun ba...”
Ta fada, sai yai dariya ya dauki chocolate ya kai bakinsa.
“Me kake ci?”
“Dan gidanki”
“Let me guess i chocolate”
“Yes kin koya min shansa yanzu, na zama kamar wani karamin yaro kullum sai na sha”
“Aa ni fa ba kai na koyawa ba, da na Sultan”
“Ke kika koya min mana, na lura yana cikin favorite dinki, shiyasa ni ma na ko yi ci, kar wata rana ki zo kina ci kina min kori”
Ta yi dariya mai sauti.
“Saboda Chocolate din?”
“Yes, Mama ta fada min duk wani abu da kike so na koyi sonsa, wanda kuma nake so na koya miki sonsa, idan kuma tsanarsa na yi to na koya miki yadda zaki kiyaye aikata abun so that mu samu zaman lafiya”
Ta yi murmushi mai sauti tana ta saurarensa. Sai kusan goma dare suka yi sallama, ba dan ya gaji ba sai dan baya son shiga hakkinta domin ya lura ta fara jin bachi.
Haka suke kullum sai yayi waya da ita da dare, idan kuma yana Gusau Saturday da Sunday yana gidansu sai goma na dare zai dawo. Wani lokacin zata shirya masa abun da ta san yana so ta tarbe shi da shi. Every weekend idan ya zo sai ya bawa Mama kudi ta siya masa wani abu ta aje tana ta tara masa kayan lefa masu kyau da tsada, idan kuma ba shi a gari aka kawo kudin shagon daya bude ya saka wani yaro yana siyar da kayan electric sai ta fada masa a waya ta shiga kasuwa ta siya masa tufafi masu tsada. Ita kanta a yanzu bata daura karamar atamfa sam ba zaki ganta a gidan ita da Rukaiya ba ki ce ita ce, sai ka dauka daman can masu rufi asirin ne. Wannan weekend din ta fi sauran da yake zuwa yi masa dadi domin zai zo ya nunawa Mama da Ramla motar daya siya ne, ba ta iso ba sai yanzu, sai dai be fada musu cewar motar ta iso ba, duk kuwa da irin tambayarsa da Mama take kullum har tana cewa Allah yasa mutumen be gudu masa da kudi ba. Karfe biyar na yamma ya sauka Gusau bayan ya baro Zaria garin daya yada zango ya huta bayan fitowarsa daga Lagos.
A bakin gate din gidan ya faka motar sannan ya bude ya fito da tsararba sa yai musu ya nufo cikin gidan rike da makullin motar da farinciki ya shigo, sai dai yana shiga falon na su da aka kawata da kayan alatu sai fuskarsa ta canja ya nemo farinciki ya rasa, sakamakon arba da yai da Baturiya tana zaune saman kujerar falon da aka kawata da kayan alatu tare da kanwarta, Sultan na zaune saman jikinsa ta rike hannunta kanta a kasa. Tana jin sallamarsa gabanta yayi mugun faduwa wata kalar kunya ta lullubeta sai ta ji da ma ace bata shigo ba.
“Yaya sannu da zuwa”
Rukaiya ta fada sai ya amsa, mata ya kalli mahaifiyarsa dake masa murmushi.
“Faruk ya hanya?”
“Alhamdulillah”
Da gangan ya share Sultan dake masa ayoyo yana saukowa jikin Baturiya ya nufo shi da gudu. Kanwarta gaishe shi sai ya amsa ya dauke kai ya nufi dakin Mama, sai da yai daf da shiga sai kuma ya juyo ya kalli Baturiya da har ta mike tsaye jikinta na rawa, domin bata san zai dawo ba a yanzu ba, domin ta san ba anan yake aiki ba, bayan Fahat ya fada mata ta fara bibiyar rayuwarsa har Ramla da yake da nufin aure ta sani a yanzu.
“Me kika zo yi nan Rafi'ah”
Kamin ta amsa masa Mama ta ce.
“Aa waje ta tsaya ta ce a kira mata Sultan ta ganshi ni na aika na ce ta shigo cikin gidan”
Faruk ya kalleta cike da rashin jindadi abun da Mama tai ya ce.
“Saboda me Mama?”
“Saboda mahaifiyarsa”
Mama ta amsa masa tana mikewa tsaye, be sake cewa komai ba ya shige dakin nata ta bi bayansa. Baturiya ta fito da sauri ko sallama bata tsaya yi ma Mama ba, Rukaiya da bita da harara tana tabe baki, daman bata so shigowarta cikin gidan ba saboda kawai Mama ta ce ta kira ta ta shiga ciki ne wai kar ta a fitar mata da Sultan din a waje ta dauke shi ta tafi da shi. Sauri kawai take zubawa gumi na tarar mata a hijab har ta fito gate din, tsaye tai cak tana kallon sabuwar motar Faruk, ko ba a fada mata ba ta san motarsa ce domin ya faka ta daf da gate din gidan wanda ke nuna alamar cikin gidan yake da niyar shiga da ita, wani abu ta hade da karfi sannan ta bi bayan kanwarta wanda tai nesa tana tafiya saboda haushin shiga gidan da sukai daman ita bata so suka shiga ba. Tafiya Baturiya take tana waigen motar kamar wanda bata son tafiya, bata hankaro ba ta ji sanyin hawaye a kumatunta. Hannu ta saka ta share hawayen da sauri ta cira kafa tana tafiyar sauri sai dai duk da haka bata cin ma kanwarta tuni ta tari abun hawa ta hau ta yi gaba ta bar Baturiya a nan. A kafa ta rika takawa har ta isa wata unguwa dake kusa da unguwar wani dan guri ta samu ta zauna tana hawaye. Wani irin bakinciki take ji wanda bata taba jinsa a rayuwarta, ta dade zaune a gurin tana ta aikin kuka kamar wanda akai ma mutuwa. Sai dai abun da bata sani ba tun a lokacin da take tafiya a kafa wani mutumen yana biye da ita da motar har ta iso gurin ta zauna tana aikin kuka. Matashi ne da ba zai rasa mata daya da yara biyu ko uku ba, yana zaune cikin motarsa nesa da ita sai dai ba sosai. Ganin kukan nata ba mai karewa ba ne ya bude motar ya fito ya zari tissue ya nufo inda take zaune. Zuwa yai gefenta ya tsaya yana kallon harabar da take kallo.
“Hey pretty kina kukan rashi ne?”
Ta dago ta kalleshi a hankali still hawaye na sauko mata.
“Ka san zafin rashin wani ne?”
Sai a lokacin ya kalleta.
“Yeah zafi na rashi i lost my son zafi rabuwa i lost my wife”
Wani sabon kuka ya zo mata
“Kuma abun nan akwai bakinciki sosai”
“Sosai ma”
Ya furta da muryar dake nuna tsantsar bakincikinsa, yana kallon wani gurin dabam tsabanin ita da take kallonsa, sai kuma yai murmushi mai kyau ya kalleta.
“Fada min wa kika rasa?”
Ta yi kasa da kanta hawaye na sauko mata.
“Wani ne, mai kyakkyawar zuciya, mai kyakkyawar makoma, mai kyakkyawar fuska amman na rasa shi...!”
Ya mika mata tissue dake boye a hannunsa, sai da ta kalli tissue din sannan ta karba.
“Ya mutu ne?”
Ta share hawayenta.
“A idanuwana ya mutu domin na rasa shi har abada, amman a zuciyata rayayye ne har abada”
Ya zauna kusa da ita yana kallon kyakkyawar fuskarta wanda taja shi zuwa gareta.
“Did you he break ur heart?”
Ta girgiza kai.
“No i break his heart, yana so na nima ina sonsa, amman kaddara ta raba mu”
“Mijinki ne?”
Ta kalleshi kamar zata amsa masa, sai kuma ta ga babu dalilin yin haka ga mutumen da bata sani ba be santa ba. Mikewa tai tsaye.
“Zan tafi gida”
Sai shi ma ya mike tsaye.
“Da zaki ba ni dama da na saukeki gidan”
Ta girgiza masa kai ta fara takawa tana tafiya.
“Please, akwai abun da nake son fada miki”
Ta tsaya sai kuma ta juyo ta kalleshi sai yai mata alama da motarsa, sannan ya jera da ita suka nufi motar da kansa ya bude mata ta shiga sannan shi ma ya shiga driver seat yai ma motar key. Suna tafe yana mata hira yana kokarin kwantar mata da hankali, ciki har da gabatar masa da kanshi