Showing 249001 words to 252000 words out of 332834 words

Chapter 84 - Bakar wasika Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

65673

Momy domin nata motar yana gida, sannan ta fice ba tare data koma dakin duba Talba ba, ba dan kuma bata bukatar haka ba sai dan bata son tai arba da bakar macijiyar, Momy ma yafe dakin tai saboda sanin Aminatu na ciki. Kamin ta isa gurin motar har da hadawa da dan sauri take tana jin kamar zata yi amai.
 
 
 
AMINATU POV.
 
Bachi ne ya dauke ta daga zaunen sa take tana kallon fuskar Talba. Bata farka ba sai da aka kira Magariba, shi ma ta hanyar Ali ne daya shigo dakin ya duba abokin, sai ya dan buga gafen gadon a hankali. Sai ta dago ta kalleshi tana mitsika ido.
 
“Tashi ki yi sallah ko kin yi?”
 
Ta girgiza masa kai, sannan ta mike tsaye ta tana kallon kofar fita kamar mai jiran shigowar wani.
 
“Ga bandaki can”
 
Ali ya nuna mata sai ta juya tana kallon inda saitin hannunsa yake, sannan ta nufi gurin da kofar take ta tura a hankali ta shiga, fitsari ta fara yi sannan tai alwala ta fito tana gyara Hijabinta. Da kwalinta ta cire ta shimfida ta kabbatar sallah, a sujidarta ta karshe ta rokawa Talba lafiya, Ali na cikin dakin har tai ta gama ta sake daga hannunta tai wata addu'ar ta shafa sannan ta tashi ta nade dankwalin ta rike a hannu, tana kallon Talba, kamar mai jiran wani bayani daga gurin Ali. Shi dai be ce mata komai ba ya juya ya fice daga dakin, ya san zuwanta ne ya hana Momy shigowa ita da Leila da adakin zai tararda da ita, wata kila Leila da Momy sun yi fushi ne shiyasa ko dakin ba su sake shigowa ba.
Hakan kuma ba karamin dadi yai ma Aminatu ba ko ba komai zata samu ta sake, ba kamar idan suna dakin ba. A inda ta zauna dazun wato saman kujera ta sake komawa ta zauna ta kwantar da kanta jikin Talba tana cigaba da kallon fuskarsa, labari ne cike fal a cikinta so take ta fada masa ta ga Ya Bashir amman ba dama, tun da baya cikin hayyacinsa. Lumshe ido ta yi tana maida numfashi a hankali, tunanin fadan da sukai da Leila dazun ya dawo mata, sai ta turo baki tana jin tsanar Leila na karuwa a ranta. Ji tai ana taba kanta dake cikin hijab, da sauri ta bude ido ta juyo ta kalli Talba gabanta na bugawa da sauri. Murmushin karfin hali ne shimfide a fuskarsa yana lumshe ido yana budewa, kamin ya saka dayan hannunsa ya cire Oxygen din dake fuskarsa. Aminatu ta mike tsaye da sauri tana zaro ido tana jarfar da hannu alamar jindadi sannan ta rumgume Talba daga kwance da yake.
 
“Alhamdulillah...”
 
Ta furta cike da annashuwa da farinciki marar misaltuwa.
 
 
 
_______________________________
 
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
 
Ya dan yi yar kara, sai tai saurin daga daga jikinta idonta na cika da hawayen farinciki.
 
“Sannu Sannu Sannu, bari na kira likita”
 
Ta juya da sauri, sai yai hanzarin bude idonsa ya rika hannunta da hannunsa na hagu. Tana jiyowa ya girgiza mata kai alamar aa, sai ya sake lumshe ido. Tsoro ta ji ganin ya rufe idon duk da, duk da kasancewar yana rike da hannunta. Kura masa ido tai tana ta kallon fuskarsa, ganin be bude idon ba har na tsawon lokaci yasa ta matsa kusa da kunnensa ta kirashi a hankali.
 
“Yallabai...”
 
Sannan ta dago ta kalleshi, still idonsa a rufe, sai ta sake maida bakinta sautin kunnenta.
 
“Talba”
 
Ta sake dagowa a karo na biyu ta kalli fuskarsa, still be bude idon ba. Sai maida bakinta tai a karo na uku sai dai wannan karon ba saitin kunnensa ba ne, sai tin kumatunsa ta kai bakin ta sumbance da soft pink lips dinta a hankali. A hankali ya fadada fuskarsa da murmushi yai bude idon yana kallon dayya ta saka dayan hannunta tana jiran ya bude nasa idon ta rufe nata.
 
“I love you Babe”
 
Ya furta da kamar rada, sai tai saurin rufe idon tana jin wani kalar kunya ta rufeta. Hannunta dake cikin nasa yaja ya kai saitin kirjinsa yana kallon fuskarta data rufe da dayan hannunta.
 
“Hawo nan mu kwanta”
 
Ta janye hannunta da sauri.
 
“Zan kira likita ya dubaka, wannan Abokanka, ko wani”
 
Ya girgiza mata kai.
 
“Yana zuwa zai fara damuna da magana babu abun da zai min a yanzu, zo mu kwanta”
 
Ya fada yana gyara kwanciyarsa daker  domin har yanzu kirjinsa ciwo yake, matsa mata yai ta yadda zata samu gurin kwanciya a saman gadon. A kokarin na ki gujewa kwantawa gurin ta ce.
 
“Ina da wani labari da zan baka”
 
“To kwanta a nan sai ki fada min”
 
Tsayawa tai kallon gadon sannan ta cire talkaminta ta hau saman ta kwanta gefensa tai matashin kai da gefen kirjinsa zuwa damtsen hannunsa, tana kwantawa sai tai lamooo kamar bata gurin, sai kamshin turarensa ke kai mata hari a hanci. Ya kai bakinsa ya sumbacin goshinta yana kallon saman idonta kasancewar ta rufe idon ne gabanta sai faduwa yake.
 
“Fada min kyakkyawata labarin me?”
 
Ta bude idon ta sauri saboda ya tabo inda yake mata kaikayi.
 
“Da baka dawo ba, sai wannan abokinka likita ya ce matarsa ta kai ni gida....”
 
Daki daki ta tsara masa hadda lamarin ya faru har zuwa inda take son direwa, tana yi tana zane a jikin rigarsa, kana gani kasan tana cikin farinciki da jindadi. Murmushi yai yana ta kallon kwayar idonta, ba zai karyatata ba, amman labarinta be yi making sense ba, after ta fada masa ta rasa duka familynta yanzu kuma tace ta ga yayanta? How? Kallonta tai jin yayi shiru be ce komai ba, yasa ta fara rantsuwa.
 
“Wallahi da gaske nake, ba karya ba”
 
Ya kalli bakinta dake matsawa a hankali, sannan ya sake kallon idonta.
 
“Hug me rumgume ni”
 
Ta sauke nata idon daga nashi tana dan turo baki ganin ba ce komai ba.
 
“Baka yarda da labarina ba?”
 
Yayi murmushi ya lumshe ido, baya son musu da ita a yanzu kuma baya son ya zurfafa a tattaunar, domin jikinsa baya masa dadi.
 
“Hug Babe”
 
Ta dan yi sama kadan ta mika hannunta jikin wuyansa ta rumgume shi tana kallon kyakkyawar fuskarsa,sai ta kai hannu ta taba tsinin hancinsa, murmushi yai ba tare daya bude ido ba, ita ma murmushin tai tana kallon fuskarsa. Kara turo kofar dakin da suka ji yasa ta dago ta leka kofar sai tai arba da Kabir, Talba kam ko motsawa be yi ba, cos to him ba wani abu ba ne dan an tararsa shi yana kwance da ita a gado daya, idan ma akwai wanda zai ji ma kunya Daddy ne ko Momy, amman sauran siblings dinsa ba.
 
“Wanene?”
 
Ya tambaya still idonsa a rufe.
 
Sai tai masa rada tana kallon Kabir dake doso inda suke.
 
“Kabir ne gashi nan yana zuwa gurinmu”
 
Kabir yayi murmushi yana kallonta cike da burgewa.
 
“Ashe kin iya rada, yan matan Talba”
 
Sai tai saurin rufe idonta tana murmushin jin kunya, Talba ya bude idon ya dago cike da karfin hali yana kallon Kabir.
 
“Dan sa'ido”
 
Kabir yayi murmushi ya kai hannunsa ya cirewa Talba drip din dake hannunsa sannan ya zauna yana kallonsa.
 
“Ya jikin?”
 
“Alhamdulillah, kirjina ciwo yake sosai”
 
“Dole ne wannan, saboda kirjin ne ya bugu, amman yanzu tun da ka farka ai sai ayi maka hoton gurin a duba matsalar”
 
He nodded his head
 
“Ina Daddy?”
 
“Tare muka zo da shi, yana waje”
 
“Ya sani?”
 
“Yeah ya zo dazun ma, yanzu kuma ya sake kirana yace na zo muje, i told him ai fa ba zaman lafiya tun danka na asibiti”
 
Talba ya fadada fuskarsa da murmushi yana cin kaunar Daddy har ransa. Aminatu ta fara kokarin tsallaka Talba ta sauka.
 
“Bari na kira Likita”
 
“Ni kuma Nurse ne?”
 
Kabir ya tambaya yana kallonta, sai Talba yai hanzarin riko kwankwasonta, yana kokarin dawowa da ita.
 
“Ai kai ba likita ba ne”
 
“Saboda ban tana miki allura ba ko?”
 
“Aa ai likitoci da an gansu ana gane su, wannan abokin nasa ai shi kowa ya san likita ne, ban san ko wasa kake ba dai”
 
Kabir ya wara ido yana murmushin daya fi kama da dariya.
 
“Wato ni bana da kama da likitoci?”
 
“Aa ina nufi...”
 
“Shiiiiii”
 
Bata karasa ba Talba ya dakatar da ita ta hanyar yi mata alama da tai shirun, sai tai shiru kamar yadda ya bukata.
 
“Kai gawa ta ki rame, daga dawowarka zaka fara damun mutane?”
 
“Talba yayi murmushi, Please je ka shigo min da Daddy”
 
“Ya kamata ka ci wani abu yanzu ba”
 
“Kira Momy ta bani”
 
Kabir ya mike tsaye, sai da ya kalli Aminatu sannan ya juya ya fice daga dakin. Talba ya kalli Aminatu.
 
“Babe bana son kina sakewa da mutane, baki san muryar mace al'aura ba ce?”
 
“No muryar mace ba al'aura ba ce”
 
“To ni a gareni al'aura ce, bana son kina sakewa da maza any how, yanzu kin fada min wani wai kin ga yayanki waya sani ko kama ce kawai? And ya za'ayi ya zama yayanki bayan duka yan'uwanki an kashe su? And now you're sitting next to me kina magana da Kabir kamar wani dan'uwanki i don't like it”
 
“Ai ba wata maganar nake da shi ba, kuma shi din ai dan'uwanka ne”
 
“Dan'uwana ne, amman idan na mutu a yanzu he can marry you, bakin san wani namiji yana kishin aji muryarsa matarsa ba, balle har ace wani yana magana da ita? Ko da mummuna ce balle ke da kike kyakkyawa, muryarki kuma tana da dadin saurare, hakan zai iya sakawa mutum ya jaki da dogon hira saboda yai ta saurarenki”
 
Shiru tai bata ce komai ba, ba dan bata da abun fadar ba, sai dan bata son musu da shi.
 
“Sauko kar Daddy ya iskoki haka”
 
Ta rika hannunsa ta sauko saman gadon, ta nufi inda aka aje flask din ruwan zafi.
 
“Bari na hada maka shayi”
 
Ya kalleta kawai yayi murmushi ya yunkura ya tashi zaune daidai ya jingina da gadon. Tana daukar cup Momy na shigowa dakin tare da Kabir da Hajiya Sadiya da wata yar'uwar Daddy Hajiya Tuni, sai Daddy dake tare da wani abokinsa Alhaji Tukur. Kowane fuskarsa sake cike da farinciki. Ban da Daddy daya matso daf da Talba ya zauna saman gadon yana kallonsa fuska a hade. Talba na ganin yanayin Daddy ya san da magana a bakinsa, sai ya sauke kasan kasa yana amsa ya jikin da ake masa.
 
“Daman ka dade baka kwanta gado ba, yanzu ai ka kwanta yadda kake so, tun da baka da hankali baka san ciwon kanka, balle ka damu da halin da wasu zasu shiga idan wani abu ya same ka”
 
Alhaji Tukur ya tari numfashin Daddy.
 
“Kaddararo ne, ba a isa a kauce musu ba, kuma tun da har ya samu lafiya ai komai mai sauki ne”
 
Daddy ya kalli Alhaji Tukur rai a bace ya ce
 
“An fa fada yadda ya hau titin, duk abun da yai da gangan yai, tun da ya san akwai motoci a fiti ba shi kadai akai wa Titi ba, idan ma wani abun be ba akwai police ba, ce masa akai idan ya kama mutumen tsayawa zai yi? Waya sani ma ko yana da makami yai masa wata illar?”
 
“Daddy I'm sorry...”
 
Talba ya fada sai Daddy ya daka masa tsawa.
 
“Rufe mana baki, daman abun da kuka iya kenan bada hakuri, lokacin da zaku yi abu ba zaku duba kanku ko halin da na kusa da ku zasu shiga sai kawai ku aikata, idan an zo magana ku fara bada hakuri”
 
“Ai ba laifinsa ba ne, laifin wannan yar iskar yarinyar ne, mahaukaciya daga ganin mutum sai ki fara cewa ga wanda ya kamaki can, waya sani ko ba shi ba ne, shi kuma komai ta fada masa sai ya dauka”
 
Cewar Momy cikin tsawa tana watsawa Aminatu data kasa juyowa harara.
 
“Idan ta fada masa, shi ba shi da hankali ne? Ai ba fada masa ne matsalar ba, yadda yake wasa da rayuwarsa ne, taya zaka hau titi kana gudu kamar kai kadai akai wa titin”
 
Daddy ya kara fada, Kabir yayi murmushi.
 
“Wato dai idan mutum yana da uwa da uba a raye ya huta, ji yadda kuka masa fada kamar karamin yaro”
 
Aminatu ta juyo a hankali rike da cup din da bata gama hadawa ba, kanta kasa. Momy ta mata wani mugun kallo.
 
“La la la.... Uban waye ya ce ki taba kayan tea din nan? Da na aje cewa na yi ki dauka ki hada ki sha...?”
 
“Aa daman... ”
 
Bata karasa ba, Hajiya Saratu ta kai mata duka a kafada.
 
“Makira, munafuka”
 
Aminatu ta aje kofin da sauri idonta na cika da hawaye. Talba ya kalli Aminatu da sauri yana jin ba dadi.
 
“Haba Mama Saratu ni nace ta hada min”
 
“Ko ba kai kace ba, ma ai matarka ce, tana da yancin ta taba duk wani abu daya alakantu da kai, weather we like it or no, ta riga ta zama part of us, wannan abun da kuke yi ma yarinyar nan be dace ba Momy”
 
Kabir ya fada cikin rashin jindadi, sai Momy ta watsa masa harara, zata yi magana Daddy ya rigata.
 
“Na dauka na gargadeki akan yarinyar nan? Ita miye laifinta a ciki? Idan zaki huce haushi ki sauke akan Mu'az, ba ita ba. Kuma wannan ya zama na karshe da za ku sake cin mutuncin yarinyar ko ku kai mata hannu”
 
Momy bata yarda ta sake cewa komai ba, ta fice daga dakin cikin bacin rai Hajiya Saratu ta rufa mata baya, kofar bata rufe ba Ali ya shigo, farincikin dake fuskarsa baya boyuwa na ganin abokinsa a zaune. Sai da ya gaisa da su Daddy sannan ya shiga duba Talba, yana tambayarsa abun da yake ji.
 
“Kirjin ne dai kawai yake ciwo”
 
“Za a maka hoto sai a rubuta wasu magungunan, yanzu dai ka saka wani abu a cikinka”
 
“Okay”
 
Daddy ya mike tsaye.
 
“Kai ma Ali kana da kana laifin ai, idan ka ga Talba zai yi wani abu kamata yai ka hana shi, amman ka bar shi yana risking rayuwarsa kamar mai rai biyu”
 
Alhaji Tukur yayi dariya kamar Yadda Kabir da Hajiya Tuni suke. Ali ya ce.
 
“Daddy ka san halin ďanka ba jin magana yake ba”
 
“Yanzu dai aikin gama ya gama, sai dai a harari gaba, Allah ya kara tsarewa, kuma ya baka lafiya Talba”
 
Cewar Hajiya Tuni, sai duk suka amsa da Ameen, ban da Aminatu da ta maida fuskarta gefe tana ta hawaye. A tare Daddy ya fita da yar'uwarsa da kuma abokinsa, sannan Kabir ya saci kallon Aminatu.
 
“Ta hada maka wani tea, ko na hada maka”
 
“Zata hada”
 
Talba ya amsa masa, sai yai murmushi ya fice. Talba ya kalli Ali dake kallon Aminatu ya ce
 
“Ali samo min tissue please”
 
“Ayi me?”
 
“Hawayen matata zan share saboda na san zata min kuka”
 
“Kai ka gwada mata ta rika maka kukan kenan”
 
Ali ya fada sannan ya nufi kofa, yana ficewa Aminatu ta juyo ta fado jikin Talba ta fashe da kuka mai sauti riri kamar yar shekara biyu. Talba ya rumtse ido domin ya ji ciwon fado masa da tai.
 
“I knew it”
 
Kuka take masa sosai har wani maida numfashi take da karfi, Talba ya saka hannunsa a bayan hijabinta yana shafata ba tare da yace tai hakuri ba. Suna haka Ali ya dawo dakin, rike da tissue paper ya mikawa Talba yana kallon Aminatu dake ta kuka shagwaba, sai dai ganin Ali yasa ta rage sautin kukan.
 
“Me akai mata?”
 
“Ka san ita da Momy basa shan inuwa daya”
 
Talba ya amsa masa.
 
“Make sure ka ci wani abu kamin na dawo, sai ka sha magani akwai allurar da za a maka”
 
Kai Talba ya daga masa, shi kuma ya juya ya fice. Talba ya dago kanta cikin rashin karfi jiki yana kallon fuskarta.
 
“Duk wannan kuka na fadan Momy”
 
“Ba na Momy kadai ba har da na wannan matar da ta dake ni a kafada”
 
Yayi murmushi yana ayyana yadda kuka baya mata wuya, abu kadan sai hawaye, ko da yake daman masu yawan shiga damuwa kukansu a kusa yake, kana taba su za su fara maka kuka kamar jarirai. Tissue din ya zara ya fara goge mata fuskarta.
 
“Yi hakuri, ba su sake ba ai kin ji Daddy ya musu magana ko?”
 
Ta turo baki gaba wasu hawayen na sauko mata.
 
“Miyasa Momynka bata so na wai?”
 
“Momy tana sonki mana, kawai dai ranta ne ya bace saboda abun da ya faru”
 
Ta kai hannu ta murza idonta.
 
“Ka kira min Mama”
 
Ta fada tana kara kwantawa jikinsa kamar kyanwa, sai ya rumgumeta ya dora wuyansa gurin kanta. Ko bata ce masa Hajiya Laraba ba ya san ita take nufi domin ita take kira da Mama kamar yadda yayanta suke kiranta. Da karfi Leila ta turo kofar dakin ta shigo cikin da annashuwar kiran da Momy tai mata ta fada mata cewar Talba ya farka, hakan ya sa ta dawo asibitin da sauri. Sai dai a yadda ta tararda Aminatu da Talba ya saka hankalimta ya tashi kuma ranta ya bace sosai, sai ta nemi farincikin farkawarsa ta rasa. dan dagowa yai daga jikin Aminatu saboda ya san zata ji ba dadi, shi kuma be shirya batawa kowa rai ba a yanzu.
 
“Talba miye haka?”
 
Ta tambaya muryarta na rawa, sai Aminatu ta juyo ta kalleta.
 
“Taya zaka maida kanka wani iri kana hada jiki da wannan yarinyar? Kalleta ba Wallahi ba ajinka ba ce, gaba daya an bi an magance ka baka ganin komai sai ita, dubi halin daka jefa kanka all because of this stupid girl, yarinya karama ta canja ka Talba jikinka mai tsada kake bari wannan kazamar yar kauyen tana tabawa, gaba daya an canja ka Talba, yarinyar nan ta mallakeka”
 
Aminatu ta daga jikinta daga jikin Talba, tana kallon Leila, daman tana bata gama huce haushin abun da Momy da Hajiya Sadiya sukai mata ba, ita kuma ta zo zata

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login