Showing 204001 words to 207000 words out of 332834 words

Chapter 69 - Bakar wasika Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

65640

ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
 
 
 
KABIR POV.
 
Murmushi yai ya kalli Doc Hassan.
 
“Ai yawanci haka ake ta fama, musamman masu haihuwar fari din nan, shiyasa bana son ana kirana na karbi haihuwa sai dole Wallahi”
 
“Ai idan ta kama kam dole ake kira, kuma idan kai ne a duty dole kaje”
 
“To ya muka iya, ai dole mu yi”
 
Cewar Doc Hassan, Kabir yayi murmushi tare da saka hannunsa aljihu ya ciro wayarsa tai kara alamar shigowar sako. Ganin private number ya bashi mamaki tun a saman screen din ya fara karanta sakon kamin ya bude shi gaba daya.
 
_Idan ka ga dama ka zo ka dauki matar dan'uwanka a lalan area, akwai wata gona a gurin ta gefen gonar akwai ciyawa ka duba da kyau zaka ganta, amman ina gargadinka karka kuskura ka fadawa kowa, kuma kar ka zo da police a nan gurin, idan ba haka ba gawarta zaka tarar, kuma zaka jefa kanka a matsala_
 
Da farko ji yai kamar  be fahimci sakon ba, hakan ya saka shi sake karantawa, a karo na biyu kuma sai yake ganin kamar be karanta daidai ba. Haka ya bi ya karanta sakom yafi a kirga sannan ya yarda da shi aka turawa shi, amman waya turo? Number a boye take. Da sauri ya saki karfin da yake rike da shi ya juya har Doc Hassan na tambayar lafiya amman be tsaya ya amsa masa ba. Number Talba yai dialing sai ya ji ta a rufe, da sauri ya kira number Leila sai da wayar ta kusa yankewa sannan tai picking.
 
“Hello”
 
“Leila Talba na gida?”
 
“Aa”
 
Ya kashe, sannan ya shiga contact dinsa neman number Ali, ya kira shi bugu daya Ali ya dauka.
 
“Hello Kabir”
 
“Talba na tare da kai?”
 
“Aa lafiya?”
 
Kabir be tsaya ce masa komai ba ya katse kiran, kamin ya karasa office dinsa har da hadawa da dan gudu, yana shiga ya dauki keys dinsa ya fito da sauri kamar gudu gudu. Ya nufi gurin da aka tanadarwa likitocin domin aje motocinsu ya , rumfar da aka rubutawa Doc Kabir Mu'az Shimkafi ya nufa yana isa gaban motar ya bude ya shiga, yadda yai reverse ma sai da ya firgita mutanen dake zaune kusa da parking spot din. Kamar an biyoshi haka ya fara gudu yana tukin da dayan hannunsa dayan hannun kuma sai kiran number Talba yake ana fada masa a kashe take. Sai da ya kusa isa Lalan sannan wani tunanin ya zo masa.
 
‘Idan kuma wani ne yake shirya masa wani abun fa? Ko kuma an fada gurin ne saboda ya zo ayi garkuwa da shi? Ya kamata ya samar da Police’
 
Ya rage gudun da yake ya sauka daga titi da zimmar komawa ya je police station, sai kuma wata zuciyar ta kawo masa wani tunani.
 
‘Idan kuma kamin police din su zo wani abun ya same ta fa? Ko kuma police din su kara bata masa lokaci, idan kuma ya fadawa Momy hana shi zuwa zata yi, Daddy ma zai iya hana shi zuwa saboda tsoro, kuma idan ya kyaleta a can be yi ma Talba adalci ba saboda halin da yake ciki’
 
Ya cika bakinsa ya iska ya busar. Sai kuma ya hau titi ya cigaba da tafiyar, sai da ya isa unguwar sannan ya tsagaita gudun da yake ya faka motar a kusa da inda suka kwatantan, a cikin motar ya zauna yana kallon ko'ina yaga idan akwai wani mai ganinsa ko kuma mai bibiyarsa, cikin tsoro ya fito daga cikin motar ya nufi gonar har ya isa cikin ciyayin ya fara leke leke yana lekawa yana waiga bayansa, babu mai ganinsa domin gurina da babu mutane sosai manya da kananan motoci dake kai kawo. Kara matsawa yai gaba cikin tsoro da fargabar abun da zai same shi yana dubawa, har zuciyarsa ta fara raya masa cewar karya ne kawai an shirya masa hakan ne wata kila saboda a sace shi, kamar ance masa yi hakuri ka kara gaba kadan yana yin haka sai ya hango mace a kwance tana ta juyo bakinta na motsi, sai dai baya iya jin abun da take fada saboda ta yi nisa da shi sosai, da sauri ya saka wayarsa aljihu ya karasa kusa da ita tana kwance cikin ciyayin idonta a rufe da bakin kyalle bakinta kuma a bude tana fadin.
 
“An kashe Baba...Babana.... Kuma sun kashe Inna... Sun yankan... Ya Saminu... Sun yanka Yaya Ibrahim.. Sun fasa kan Ya Rilwanu, ba ni da kowa a yanzu sun kashe min kowa sun kone mana abinci....”
 
Dukawa yai ya saka hannunsa biyu ya dagata sannan ya kwance kyalen dake idonta. Sai ta ji ta rike shi da mugun karfi.
 
“Tsoro nake ji, kashe ni za su yi....”
 
Idonta a bude suke amman sun juye kamar wanda tai shaye shaye gashi sun mata ja sosai. Daukarta yai ya fito da ita daga cikin gurin da sauri har yana hadawa da gudu gudu. Yana fitowa gurin ya nufi inda ya aje motarsa kasa ya fara ajeta da zimmar ya bude motar sai ta rike masa riga gam.
 
“Tsoro nake ji, gasu nan da fuskoki za su dauke ni”
 
Duk yadda ya so ya daga ya bude motar sai ta ki sakinsa, sai da yai da gaske sannan ya samu ya banbare hannunta ya bude back seat ya dauke ta ya saka ta cikin ya rufe, har lokacin bata daina kalaman da take ba, duk abun da ya zo bakinta fada take tun daga kan abun da ya faru da ita a kauye, sai kuma ta tsakuro wani bangare na sace da mutanenan suka yi. Kabir fuki yake gabansa na faduwa sai kuma ya juya ya kalleta.
Dayan hannunsa ya saka ya ciro wayarsa ya kira asibiti ya sanar musu zai zo da Emergency su shirya masa komai. Yana yi yana juyawa ya kalleta. Cikin kankanen lokaci ya isa asibitin kai tsaye emergency ya nufa yana faka motarsa aka kawo dago da sauri, sai ya fita ya zagaya ya bude motar ya fito da ita daga cikin motar sai ta rike shi da karfi tana kuka.
 
“Dan Allah ka ce karta min komai, dan Allah ka basu hakuri, ban musu komai ba, ban yi ma kowa komai ba, marainiyace ni ba uwa ba uba ba ni da kowa”
 
Fada kawai take domin har yanzun mutanen take gani, kuma abun ya zame mata biyu tana ganin wadannan tana wadancan barayin dajin, shi kansa Kabir din data rike bata sam ko waye ba domin bata iya ganin komai sai fuskokinsu. Wani irin tausayinta ne ya kama Kabir daker ya samu ya kwantar da ita saman gadon sai ta rike masa hannu.
 
“Yankani za su yi, dan Allah ka ba su hakuri...”
 
Dauketa yai daga kan gadon ya nufi main door din emergency da ita. Da kansa ya shigar da ita daya daga cikin dakunan da aka tanada domin bata taimakon gaggawa, a nan ma da yai yunkurin sauke ta akan gadon sai ta ki bashi hadin kai hawaye sai sauko mata suke gwanin tausayi.
 
“Bani allura”
 
Nurse din ta shiga hada allurar ta mika masa, sai ya karba da dayan hannunsa ya ware cinyar hannunta Nurse din ta saka kaďa ta goge mata inda za a ayi mata allurar shi kuma ya soka mata a hankali, sai da ruwan allurar suka fara shiga a cikinta sannan ta soma jin zafin allurar a take ta kara bata fuska ta fashe da kuka.
 
“Wayyo Babana....”
 
Sai ta sake shi domin jikin nata ya kara zama weak. A nan ya samu damar kwantar da ita saman gadon ya soma bata taimakon gaggawa. Sai da ya tabbatar komai ya tafi daidai sannan hankalinsa ya kwanta ya fito ya baro mata dakin. Waje ya fito zuciyarsa da tunani kala kala, waya turo masa sakon miye dalilinsu na yin haka? Ina suka kaita da suka dauke ta yanzu kuma miyasa suka dawo da ita?
 
“Dole ne na sa a bincika min boyayar number idan akwai yadda za ayi ta fito, saboda na gano ko waye”
 
Wannan karon a fili yai zancen, sannan ya sake dialing number Talba, har lokacin a kashe take, hakan yasa ya yanke shawarar tura masa sakon karta kwana.
 
_Na kira wayarka switch off, wani ya turo min sakon inda Aminatu take kuma na je na dauko ta tana nan asibiti_
 
Bayan ya tura ya jingina da karfen gurin, yana kira number wani abokinsa.
 
“Doc Kabir”
 
“Dahiru ya kake ya gida?”
 
“Wallahi Alhamdulillah, kwana da yawa”
 
“Mun gode Allah, tambayarka nake son yi nasan ku ne masana harkar computer kuma kana aiki da kamfanin line”
 
“Okay ina saurarenka”
 
“Wani case ne muke ciki, kuma yau sai aka turo min sako da wata boyayyar number, to shi ne nake son na ji idan akwai yadda za'ayi a gano number da kuma mamalakin line”
 
“Shi ya fi komai sauki, ka shigo gobe domin yau na tashi aiki, and make sure ka zo da police order”
 
“Okay, ba matsala, zan shigo goben In Shaa Allah Thank You”
 
Ya katse kiran tare da sauke ajiyar zuciya, sannan ya dago daga jinginen da yake ya nufi ward din da Aminatu take, a hankali ya mai hannu ya tura kofar dakin ya leka. Sai ya hangota tana ta sharar bachinta drip din da aka saka mata yana tafiya kamar yadda ya saka shi. Sakin kofar yai a hankali ta rufe kanta sannan ta koma office dinsa ya zauna. Sai da yai kamar ya kira Momy ya fada mata sai kuma wata zuciyar ta hana shi, saboda zata iya fadawa Leila kuma ba zama lallai ganinta ya yi musu dadi ba. Jinginawa yai da kujerarsa yana kallon kofar office din kamar mai jiran shigowar wani. Ta wani bangaren kuma yana tuna wasu kalamai da take ta fada wadanda suka shafi tarihin rayuwarta.
Gaskiya ya tausaya mata, a yadda take da matashiya da ita ace ta fuskanci irin wannan kalubalen na rayuwa abar tausayi ce sosai. Be koma dakin ba sai da ya sauke nauyin sallah La'asar, daman ya kwatantan zata farka kamin lokacin ko kuma ta gota 4pm kadan. Da wayarsa ya sake kiran number Talba sai ya jita a kashe a lokacin ne gabansa ya soma faduwa, domin be san Talba da kashe waya ba, ko Meeting zai shiga sai dai ya saka wayarsa Silent, amman ace tun safe har la'asar wayarsa na kashe.
 
“Allah yasa lafiya dai”
 
Ya furta cikin tsoro da faduwar gaba.
 
“Doc Kabir baka wuce ba? Ko kana da da duty dare ne?”
 
Ya juyo yana kallom kashiya dake masa maganar.
 
“Aa ina da patient ne shiyasa ban koma gida ba”
 
“Okay Allah ya sauwake”
 
“Amin”
 
A tare suka jero suna magana sai da suka kawo cikin asibitin sannan suka rabu shi ya nufi gurin harkokinsa, Kabir kuma ya nufo Ward din da zata sada shi da dakin da Aminatu take ciki, wannan karon ma kamar barawo haka ya tura kofar dakin ya shiga, ya karasa har gaban gadonta ya kama hannunta ya cire mata drip din a hankali sannan ya aje hannun yana kyakkyawar bakar fuskarta, ta yi kyau sosai kamar ba ita ba, ba kyau na kwaliya ba, yana mata kallon wacan lokacin ne da Talba ya kawo ta gidansu, a lokaci akwai rama da duhun fata, a yanzu kuma ta yi jiki kuma bakin fatarta ya ragu sai sheki yake. Agogon hannunsa ya kalla sannan ya juya ya fice daga dakin, be wuce two to three steps ba wayarsa dake hannunsa tai kara yana dubawa sai ya ga number Talba.
 
“Tana wane daki?”
 
“Emergency room 7”
 
Yana amsa masa ya tsinke wayar, Kabir ya dan tabe baki sannan ya nufi pharmacy dake asibitin domin karbo mata wani magani, da yake ganin ya dace ta sha shi idan ta farka.
 
 
Fitarsa da kamar minti hudu ta fara motsa kafafuwanta, tana jin jikin kamar ba mata ba, kanta yayi nauyi sosai har bata iya bude idanuwanta, duk yadda ta so tai unkurin bude ido sai ta kasa, ta dan bude baki tana fitar da iska, can kuma ta fara motsa yatsunta. Ta fi karfin minti goma a haka tana son bude idon ta kasa, haka ma ta yunkura ta tashi zaune shi ma ta masa, daker ta samu ta fara motsa hannunta, da kafafuwanta tana jin masalar na dan rage mata. Tana cikin wannan halin ta ji an turo kofar dakin da karfi, da gudun Talba ya karasa kusa da ita yana kallonta da mugun shock numfashinsa har wani rawa yake, a take idonsa suka cika da kwalla, hannu ta kai ta inda iskar dake zirya a hancinta yana shiga da fitar da numfashi ya sanar mata zuwan Talba. Dukawa yai a gurin kamar mai rokon gafara ya kama hannunta ya rike da hannayensa biyu yana sumbata kamar wanda baya hayyacinta, kamin ya dago ya daga ta daga kan gadon ya rumgume ta a kirjinsa tsantsan kamar ance masa wani zai sake sace ta. Lumshe ido yai yana kara matseta a kirjinsa gaba daya sai ma rasa abun da zai yi kuka ko farinciki.
 
“I miss you so much Shalele na i miss you”
 
Ya furta yana dagowata daga kirjinsa ya sumbanci goshinta, ya kai hannunsa ya shafa gashin kanta, ya sake shafa fuskarta sannan ya maida ita a kirjinsa.
 
“I can not do without you, the only one girl i miss”
 
Ya fada yana lumshe ido, ya kara matseta kirjinsa. Wani irin bugawa zuciyarsa take da karfi irin bugun da ya wuce misali. A hankali ta bude idon sai ta soma ganin dishe dishe kamar wanda ta shekara tana bachi, dagowa tai a hankali ta kalleshi sai ya sauko da fuskarsa saman tata yana shakar numshinta kamar yadda take shakar nasa, kallonta yake ido cikin ido hancinsa da nata suna gogar juna, sai hawaye mai zafi ya sauko ta gefen idonta, da sauri ya rumgumeta.
 
“You are safe in this hands of mine, ba zan sake nisa da ke ba, babu abun da zai sake samunki i promise you this”
 
Ya fada try to calm himself.
 
“I love you so much Aminatu, you drive me crazy, dana rasa ki na ji kamar na yi hauka, i miss you more than i did before”
 
I kara matseta a kirjinsa kamar zai fasa kirjin nasa ya saka ta ciki.
 
“I feel you... You're heart in my heart”
 
Ya fada idonsa a rufe hawaye na sauko masa, ba tabbatar haka haka tai marmarinta har sai a yanzu da take gabansa, ya rasa inda zai saka ta a kirjinsa kamar ya hadeta ta zauna a cikinsa haka yake ji.
 
“Ya...lla...bai.. ”
 
Ta gwada yin magana, sai ya dagota da sauri ya saka hannayensa yana shafa fuskarta cikin wani irin shauki na farinciki.
 
“Talba...”
 
Ya fada nata sannan ya sunbancin goshinsa ya sumbanci saman idonta na dama ya sumbanci na hagu ya sumbanci hancinta, sannan yai masa da bakinsa ya shigar da lips dinsa cikin nata. Kabir na gani haka sai ya saki kofar a hankali ta yadda ba zata yi mara ba, kamar yadda ya bude ba tare da ta yi kara ba, juyawa yai rike da takardar maganin ya nufi office dinsa.
 
 
 
 
 
 
FARUQ POV.
 
Mama ta fashe da kuka, domin tun da ya tafi be taba kiranta ba ko sau daya, tun tana jiran kiransa har ta fara tsarata tana tunanin ko wani abu ya same shi ne.
 
“Haba Mama sai ka ce mutuwa na yi”
 
Faruk ya fada daya dayan bangaren a wayar abokinsa daya ara ya kira da line kasar wato line nijar mai +227.
 
“Miyasa baka kirana? Kasan irin tashin hankalin da nake ciki? Tun da ka tafi baka sake kira mun ji halin da kake ciki ba, kullum hankalina a tashe yake”
 
“Mama Wallahi inda muka je ba a kira, domin daji ne da ba a samun service sai an fito cikin gari, kuma a lokacin da muka isa muna isa aka ce mana ga motar da zata tafi aiki nan, ba mu tsaya komai ba muka bita, kuma tun da muka shiga ban fito daga dajin na Libiya ba sai yanzu”
 
Mama ta share hawayenta.
 
“Kana dai lafiya ko?”
 
“Lafiya kalau Mama, addu'arki ta karbu na samu zinari mai yawa wanda ban taba saka ran samu ba, kuma In shaa Allah cikin satin nan zan dawo”
 
“Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah, haka nake so, Allah ya tsare ya dawo da kai lafiya”
 
“Aamin Mama, Mama ina Sultan?”
 
A take murmushin dake fuskar Mama ya bace, sai dai tana ganin a irin wannan halin da yake ciki na farinciki be kamata ta fada masa abun da zai bata masa rai ba.
 
“Ya fita waje gurin wasa, idan ya dawo zan fada masa kana gaishe shi”
 
“To Mama, ya jikin na ki?”
 
Ta kalli hannunta na hagu da bata iya komai da shi saboda paralyze din dake son kamata na hawan jini.
 
“Alhamdulillah Lafiyata kalau, Allah ya maka albarka ya dawo da kai lafiya”
 
“Aamin Mama ina dawowa zan siya miki gida mai kyau mai tales da gate ki zauna ke kadai”
 
“Allah ya amince, kuma ya sa muna da rabon ganawa”
 
“Aamin Mama, ban mika masa wayar, idan zan taso zan sake kiranki”
 
“Toh Allah ya tsare ya dawo da kai lafiya”
 
“Aamin”
 
Shiru tai tana saurare sai da ya katse kiran sannan ta sauke ajiyar zuciya tana murmushi.
 
“Mai hakuri madawaci, Allah ya kawo ka lafiya dana, dan albarka”
 
Kanwarsa dake kusa da Mama ta karbi wayar tana murmushin jindadi.
 
“Na san yana zuwa zai daukeki ya kai ki asibiti, a baki magani mai kyau”
 
Murmushi Mama tai.
 
“Allah ya kawo shi lafiya”
 
“Amin”
 
Ta amsa cike da jindadi, Mama ma jindadin ne karara a fuskarta.
 
“Je ki kai wayar kar masu ita su aiko”
 
“To”
 
Ta amsa tana mikewa tsaye ta dauki Hijab dinta ta saka sannan ta fice. Da wayar komata ya kira saboda ya kira line Mama ya ji shi a rufe na kanwarsa ma haka ya san ba zai wuce ace sun siyar da wayar ba abu a gurin talaka.
 
 
 
 
 
_______________________________
 
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login