Showing 48001 words to 51000 words out of 332834 words
fara tana kallonta.
“Wallahi zaki sha kudi, manyan masu kudin nan suna son fararen mata amsu kananan shekaru”
“Da gaske?”
“Uhm har sai na rantse miki ma, a ciki ma zaki samu wanda zai ce miki aurenki yake so, ko ma be ce ba idan kin ga ya miki sai mu bada sunansa kawai a kama mana shi, dube ki gani fa Wallahi ke matar manya ce Baturiya”
Baturiya ta yi murmushi tana jin wani irin dadi, sannan ta koma ciki ta dauko. Jakarta da karamar wayarta da makulli ta fito.
“Ina Sultan”
“Tun dazun na tura shi makota”
“Aiko kin kyauta, domin yara akwai sa ido zai iya fadawa Babansa na zo”
Suka yi dariya sannan suka fito daga falon kamin su fita daga gidan gaba daya Baturiya ta kulle gidan. Sannan suka nufi bakin titi inda motar Ramlee take, front seat Baturiya ta shiga Ramlee kuma ta ja motar suka kama hanya, suna tafe suna hira har suka shigo cikin gari, gaban wani katon shagon siyar da wayoyi Ramlee ta faka motar, kusan a tare suka fito ita da Baturiya, tana kokarin rufe motar ta hango Alhaji Garba jikin mota yana waya.
“Ramlee bari na gaisa da mijin yayata ga shi can”
“Ba zai ce wani abu ba?”
“Zan ce ke na rako ai, ban sani ba ko zai ba ni wani abun yana da alheri ai”
“Shikenan bari na jira ki daga ciki”
Kai ta daga mata sannan ta nufi gurin da yake tsaye jikin motarsa yana waya, ganinta yasa yai hanzarin yanke wayar da yake ya kalleta yana murmushi.
“Baturiya ina kika fito?”
“Ai kai zan tambaya na sani ko wata budurwa ka rako”
Yayi dariya.
“Zaki bari ne? Ai kin tare kowa ya gida ya kowa ina mijinki?”
“Kowa lafiya kalau, ina Anty”
“Lafiya Kalau take, me kika zo yi nan?”
“Wallahi wayata ta bata kwanan baya shi ne na zo siyen karama”
“Oh haka fa, Yayarki ta fada min Allah maida alheri, ai da na san da zuwanki da na riko miki wani abu gashi bani da enough a mota”
“Uhm Alhajina kenan ai kai babba ne, kuna da kudi sai dai idan ba ayi niyar ba mu ba, tun da alherin zuwa zuwa ne”
Ya sake yin dariya yana kallonta.
“Haka yayarki ta fada miki?”
“Aa yayata bata fada min komai ba, haka dai na gani da idona”
Ya bude motarsa yana dariya.
“Baturiya sarkin rigima ashe dai mijin naki yana fama”
“Kana dai fama zaka ce, ko ka bawa wani ne?”
Yayi dariya mai sauti.
“Zankadediyar mata irinki zan kyautar na dai ara masa shan miya, yanzu dai bari na siye bakin nan naki dan karki je ki fadawa yayarki kin gan ni a gurin siyen waya”
Ya fada bayan ya zauna cikin motar, sannan ya ciro bandir din yan dari dari 10k ya mika mata.
“Gashi na rufe bakin nan kar yayarki ta ji”
Murmushi tai ta karba.
“Karka damu Alhajin Allah, ai ko mutum ka yanke agabana ka bani wadannan ka rufe bakina babu wanda zai ji”
“Da gaske? Ashe za a iya siye ki da kudi?”
“Ba wai za a iya ba, ana ma yi ne”
Ta fada tana wani irin kashe masa ido kamar wata tsohuwar karuwa. Binta da kallon da shi kadai ya san manufarsa yana murmushi har ta shiga cikin gurin. A bakin kofa ta samu Ramlee tana jiranta.
“Yayarki tana da miji kamar wannan kike zaune a talauci?”
“Uhmm yan uwa yanzu ai babu ruwansu da son zumunci idan sun samu daga su sai yayansu”
“Shiyasa nake son ki gina kanki ki yi naki arzikin”
“Wallahi kuwa, babu abun da yake burge ni kamar katon gida da katuwar mota da kayan sakawa da na ci masu kyau masu tsada, Wallahi ko hoto ake turowa a group zaki ga ko wace shegiya da katon falo, haka nake ta ganin friends dina a gida masu kyau da sutura mai tsada, ki duba ko yan'uwana kowa tana auren mai rufin asiri amman ni kullum abushe ko abunda zamu ci wani lokacin gagararmu yake”
“Karki damu kin warke yarinya ke dai ki goge kawai ki iya dadin baki da kwarkwasa da jan hankali”
Haka suka cigaba da nisawa cikin shagon suna ta hira, an tsara shago gwanin sha'awa camera a ko'ina ga gilashi da haske gulob kamar ba rana ba,.kana ganin gurin kasan na manyan mutane ne.
A tare suka jera da Ramlee suka nufi gurin da aka jera wayoyin techno. Ramlee ce ta fara dubawa sannan ita ma ta kai hannu zata dauki wata sai ta ji an riko hannun nata, saurin kallon gefenta tai da tsoro sai tai arba da mutumen daya rage mata hanya a wacan lokacin da ta sauka tasha daga Kano, murmushi ta sakar masa kamar yadda yake mata murmushin shi ma, sai ta janye hannunta.
“Sarki alkawari”
Ta watsa masa wani irin kallon irin na masoya.
“Daman na yi alkawari?”
“Ba ki yi ba amman dai ai ya kamata ki ce min na isa gida lafiya ko?”
Ta yi murmushi, shi ma murmushin yai ya gabatar mata da yarinyar dake gefensa.
“Ku gaisa da kanwata, ya kamata ku san juna tun yanzu ai”
“Sannu”
Baturiya ta fada. Sai ita ma yarinyar dake kama da saurayin ta maido mata.
“Yauwa sannu, sunana Salima”
“Ni kuma Rafi'a amman anfi kirana Baturiya”
“Yeah kin fi turawan kyau ai”
Cewar saurayin sai duk suka yi dariya har shi.
“Me kika zo yi nan?”
“Waya na zo siya kasan wayata ta bata”
“Oh haka ne, amman kin san na tashi koma gidan nan sai kuma wata zuciyar ta bani hakuri ashe rabon zan hadu dake ne a nan, gaba daya na kasa samun natsuwa tun da muka rabu Wallahi nake ta mamarin ganinki har Hajiya na bawa labarinki”
Ta yi murmushi.
“Gashi yanzu, ai mun hadu katin daka bani ya bata ne”
“Ayyah”
Ya fada sai kuma ya kalli Ramlee dake ta duba wayoyi.
“Ko zaki bani aron kawar nan taki mu zagaya gurin masu IPhone”
“Yeah ba matsala, zan jiraki a mota”
Ramlee ta fada tana murmushi, sai Baturiya ta daga mata kai.
“Okay”
Bayan Ramlee ta wuce ya bawa kanwarsa key din motar.
“Je ki jirani a moto”
“Okay sai anjima in-law”
Budurwar ta fada sai duk suka yi dariya, sannan ya nuna mata hanyar da zasu bi su bullo gurin da aka jera iPhone din.
“Fahat sunana duk dai baki tambaya ba”
Ta kalleshi ta yi murmushi, da kansa ya zaba mata iPhone mai kyau, sannan ya nufi wajen biyan kudi ya mika atm dinsa, kamar ance ta juyo, tana juyowa tai arba da Nura tsaye gurin biyan kudin, da alama wani ya rako, suna hada ido tai saurin dauke kai gabanta ya shiga faduwa da mugun karfi. Bayan ya biya ya rakata har gurin motar Ramlee ya sake ciro katinsa ya mika mata.
“Ki tausayawa zuciyar nan tawa ki kira wayata ko zata samu sukuni”
“Karka damu zan kiraka, na gode sosai”
“Nine da godiya yau zan yi kwanan farinciki”
Ya fada sannan ya rufe mata motar Ramlee yaja suka bar gurin.
“Ina kika san shi? Baturiya Allah ya miki farin jini”
Dariya tai kamin ta labarta mata yadda akai ta sanshi, sannan ta dora da na ganin da Nura tai mata abokin mijinta kuma amininsa.
“Ke kar ya dame ki, idan ma ya fada masa ki bururuce ki ce ki kam sam ba ke bace, idan ya dage ke din ce kice tare da yayanki kika je siyen waya”
“Kuma fa kin kawo shawara, idan ba haka ba kam zai iya fusata sosai domin dazun na ci mutun mai mana maganar kudin haya na san kuma za su fada masa”
“Saboda me? Ai ba haka ake ba, nawa ne kudin hayar?”
“80k”
“Just 80k? Yanzu zan baki 100k da mutumen ya baki sai ki nemi inda mai hayar yake ki bashi gaba daya, wayar da ban siya miki ba zan baki kudin daman na yi niyar kashe miki 50k akan wayar dan haka zan baki su a hannu, gobe kuma zan kawo miki kayan mata masu kyau ki fara shirya kanki kamin lokacin da saku gana da Alhajin”
“Har da wani shan kayan mata?”
“Eh mana, kuma idan kika fara sha karki yarda ki bar Faruq yaje kusa da ke”
“Ni daman bana shan kayan mata ai, mutum yana fama da talauci ko a sha kayan mata me zan samu? Shiyasa ba ruwana da shan su, kuma ba kullum nake barinsa yana damuna ba”
“To ki dai kiyaye, yanzu kina isa gida ki fara neman mai kudin hayar ki bashi hakuri ki bashi kudinsa, kin ga idan ya dawo zai rage jin zafin tun da kin biya kudin hayar”
“Haka zan yi Inshallah na gode sosai kawata”
“Allah dai ya bar mu tare”
“Ameen”
A inda ta faka motarta dazun ta sake tsayawa, ta ciro kudin ta bata sannan sukai sallama, Baturiya ta fita ita kuma ta juya ta hau titi.
FARUQ POV.
Kamin ya isa gida sai da ya kira abokinsa Nura ya fada masa yadda sukai da abun da ya samu kana yai masa godiya. Ya isa gida cikin farinciki, ba zai ce be taba rika 100k ba amman ba kasafai ba, rabon daya rika 10k tashi ta kanshi ma ya manta.
Yana isa ya zare dubu biyu ya bawa Asiya ya ta girka abinci, sannan ya shiga daki ya taba mahaifiyarsa dake zaune tana maida numfashi a hankali.
“Mama ya jikin na ki?”
“Alhamdulillah, Aisha tace ka zo dazun ina bachi”
Ta amsa tana kallon yanayinsa dake bayyana irin farinciki da yake ciki.
“Eh na zo na tararda jikin na ki ne sai a hankali...”
Ya dora mata da labarin yadda komai ya faru ciki har da abun da Malam Musa ya kira shi yana fada masa Rafi'a ta yi, kamar wanda aka cirewa ciwo sai Mama ta nemi ciwon ta rasa zuciyarta tai fal, daman ciwon nata hawan jini ne na tunanin auren Aisha da kuma yunwar da suke wuni da ita su kwana da ita, abu ga talaka bawan Allah kadan ya ishe shi.
“Amman Allah ya saka masa da alheri, Allah ya faranta rayuwarsa ya daummawar da farinciki a cikin zuciyarsa kamar yadda ya faranta ranmu”
“Ameen, ni kaina ina tafe a hanya ina ta masa addu'a, Wallahi na jidadi sosai, domin rashin lafiyar nan naki ya dame ni, yanzu ki tashi ki shirya mu tafi asibiti”
“Aa wace asibiti kuma Faruq? Ai ni yanzu na ji sauki, daman ciwon ai na rashin kudin ne”
Wata kalar dariya Faruq yai wanda ya manta rabon da yai irinta har ya manta.
“Haba Mama saboda ciwon ki fa naje karbo kudin nan, kuma har ga Allah ni asibitin nai niyar kaiki”
“Aa ai ciwo kuma ya warke, da aje a kashe kudin a banza ai kara a kara ayi hidima, Idan aka karbi kudin lefe aka rage wani abu cikin nan ai sai a dan kara, in yaso sai ka dauki rabi ka ba mai hayar ka bashi hakuri”
“Ai ba za su isa ba, 80k ne muke biya shekara”
“Eh ka bashi ko 50k ne dai ka bashi hakuri kamin Allah ya budo mana wata hanyar samu sai ka cika masa”
“To Allah ya sa ya yarda, wannan matar ta kira min ruwa, Wallahi na gaji da halin Rafi'a Mama kullum da kalar fitinar da take bullo min da ita, bata da wata magana sai ta na sake ta”
“Ka kara hakuri tana maka haka ne saboda tana ganin baka da kudin yin wani auren, da ace ta san kana da kudi da ba zata maka haka ba, koma na rayuwa dan hakuri ne wata rana zaka ga komai ya wuce kamar ba ayi ba”
“Allah ya kara min hakurin domin har ga Allah ta kai kulu, ba wai zan sake ta ba ne bana son shiga hakkinta ne”
“Yanzu dai tashi ka tafi gurin sana'arka in yaso gobe sai ka samu mai hayar na san zuwa lokacin ya huce sai ka ba shi hakuri ka bashi dubu hansin din, Allah ya warwareka yai maka albarka, zuwa da yamma zan tafi gidan Kanen mahaifinku na fada masa yayi ya aiko da kudin lefen sai a hada da dan abun da aka samu”
“Toh Allah ya taimaka ni zan tafi”
“Ka dai baro mata abinci ko?”
“Eh akwai Taliya da wake, da cefane, idan na koma anjima zan siya mana abinci ina son na cire 5k a ciki”
“To Allah ya taimaka yai maka albarka”
“Amin Mama Allah kara miki lafiya”
Ya fada yana mikewa tsaye sai ta bishi da kallo ina na uwa da da tana jin kaunarsa na karuwa a ranta, ta fi kowa sanin cewar idan Faruq yana da mafita da tuni ya share mata hawayenta.
Kudin ya ciro ya cire 50 na mai haya sannan ya cire 5k ya mika mata 43k da suka yi saura, sannan ya fito ya nufi gurin aikinsa.
A hanyarsa ta tafiya ya saye waina sannan ya karasa shagon daman yana da plate da spoon da dan copinsa a shagon bayan ya bude ya wanke plate din sannan ya zuba wainar ya ci, ya siyo ruwa ya sha, tukuna ya hau gyaran shagon kamar yadda ya saba.
Be tashi ba sai 7:30 daman haka yake tashi kamin ya isa gida 8 tayi sai ya tsaya yai sallah a massallacin unguwarsu sannan ya shiga gida. A duk lokacin da zai shiga gida da tunani da fargabar abun da Baturiya zata masa, amman a yau haushin shiga gidan ma yake ji, har be san ta inda zai fara mata ba idan ya shiga.
Kamar kullum sai da ya tsaya yai sallah, sannan ya biya gurin mai siyar da balangon unguwarsu ya siye na dubu daya, ya biya shago ya siye shimkafa da sauran kayan masarufi sannan ya nufi gidansa.
Yayi mamakin ganin kofar gidan a bude domin bata saba barin kofar a bude ba, rufewa take wai a cewarta masu kudi ma basa barin gida bude sai takawa, hakan yasa duk wanda ya zo sai ya kwankwasa mata sannan ta bude. Sai dai yau kofar a bude ya same ta, sai ya shiga rike da ledodin a hannu nan ma sai ya samu kofar falon a bude, be yi sallama ba ya shiga saboda ransa a bace yake. Sultan kadai ya samu a falon zaune yana shan bobo, Sultan na ganin mahaifinsa ya sauko daga saman kujerar da sauri ya nufe shi.
“Daddy sannu da zuwa”
Sai da ya aje ledodin hannunsa sannan ya dauki Sultan yana murmushi.
“Sultan ya keke?”
“Lafiya”
“Me kake sha?”
“Bobo Momy ta siya min Bobo”
Jimmm Faruq yai sannan ya sauke dansa ya bude masa ledar naman daya siyo ya aje masa a gabansa.
“Zauna ka ci”
“To”
Ya zauna da sauri ya fara ci yana ta murna.
“Momy ma ta siya min kifi dazun”
Faruq be sake ce masa komai ba ya nufi kofar dakin tana tabawa ya ji a rufe, sai ya juyo ya kalli dansa.
“Sultan ina mamanka?”
“Tana ciki”
Kwankwasa kofar ya fara yi.
“Rafi'a ki bude kofar nan”
Sai ta amsa masa daga can ciki.
“Wallahi ba zan bude ba, ai na san dokana zaka yi”
“Kin san abun da kika yi kenan?”
“Eh mana, haka kawai muna fama da talauci zai zo ya kara mana da wata damuwar kudin haya shiyasa na karbi number sa na zage shi ai”
“To kin jawa kanki ya bamu kwana daya mu tashi mu bar masa gidansa, Rafi'a mi yake damunki ne wai? Miyasa ke baki son zaman lafiya? Duk wani abu da zai tayar min da hankali shi kawai kike nema”
“Ai na bashi 100k yau, na biya shi kudinshi kuma ya bada takardar ya yarda mu zauna”
Natsuwa yake kokarin yi wai ko zai fahimci inda kalamanta suka dosa, ta bashi kudi haya?
“Rafi'a”
Ya kiranta a hankali, sai ta amsa daga jikin kofar da take, rike da sabuwar wayarta.
“Na'am”
“Maimaita abun da kika fada min”
“Na ce na bashi kudin hayar har na kara masa da 20k sama”
“Ina kika samu kudi?”
“Yaya ne ya ba ni Umma ta cika min sauran”
“Bude kofar nan mu yi magana”
“Ba fa zan bude ba, tufafin ka nan a falo na fitar maka, kuma abinci ka yana nan kusa da kujera, kai da Sultan ku kwana a falo ba zan bude ba”
Ba dukan abun da tai kawai take tsoro ba, har da na sabuwar wayar data siya da kuma kudin data biya hayar domin ta san abu ne mai wahala ya yarda da ita.
“Ki bude kofar nan Rafi'a ba zan dake ki ba, na taba dukanki ne? Duka ai ba halina ba ne ina son nai magana ta fahimta da ke”
Shiru tai masa kamar bata gurin.
“Na samu 100k yau”
“Da gaske? Ko dai dan na bude ne”
“Wallahi da gaske ne, Rafi'a i need to talk to you seriously ki bude kofar nan ko kuma na tafi na barki ki kwana a gidan ke kadai...”
“Wallahi Faruq dukana zaka yi idan na bude ni na san abun da na yi, duk abun da na yi ai dai ina sonka ka san dai ina sonka, bakin talaucin nan ne bana so, saboda farar kafa ce da kai Faruq, aurenka be karbe ni ba, da yanzu na yi arziki”
Ta fada da muryar dake nuna tana daf fashewa da kuka. Murmushi jin yadda ta juya abun zuwa kansa, wato shi ne mai farar kafa ba ita ba.
“Na ji bude mu yi magana”
Ta dade tana tunani sannan ta nufi karkashin filonta ta saka wayar, ta nufo kofar ta bude cike da tsiro sannan tai baya ta haye saman gado, shi kuma ya shigo cikin dakin yana kallonta, yana bude baki yai magana sai wayarta tai ringing, yanayin yadda ta razana kadai ya isa ya nuna bata da gaskiya, saurin nufar inda wayar take ta yi ta dauka ta kashe ta gaba daya.
“IPhone? Ina kika samu IPhone Rafi'a?”
Ta yi shiru sai kallonsa take. Shi ma kallon tsoro yake mata domin lamarinta a yanzu ya fara bashi tsoro ta fara wuce tunaninsa.
“Ko yaya ya siya miki?”
Nan ma shiru tai, at first ya fusata sai dai a yanzu kwakwalwarsa cike take da tunani kala kala. Karasa yai kusa da gadon ya zauna gabansa n mugun faduwa, yana ta kokarin ganin ya kawarta yaye yayen da zuciyarsa take son masa akan Rafi'a. Zaunawa yai bakin gadon yana kallonta.
“Rafi'a ki saka tsoron Allah a ranki, ina son ki san cewa duk abun da aka samu a duniyar nan a nan ake barinsa, ba a zuwa lahira da komai sai aiki da mutum ya aikata, Rafi'a dan Allah ki zama mai tunani ki duba future din Sulta da abun da yake cikinki, na san ni talaka ne ba zan iya miki komai yadda kike so ba, amman da ki je ki aikata wani mummunan abu da aurena kuma kina uwar yayana kara na sauwake miki ki auri mai kudi idan har hakan zai kawo miki mafita”
Yana maganar idonsa ya cika