Showing 201001 words to 204000 words out of 332834 words

Chapter 68 - Bakar wasika Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

65605

tare da saninta ba. Ajiyar zuciya ya sauke ya zauna gefen gadon da take zaune.
 
“Leila Talba yana da fushi sosai, abu kadan ma zai iya saka shi fushi ko bacin rai, ke kanki kin sani. Wani abun ma zaka yi ne domin ka burge shi amman daga karshe ya dawo yana jin haushinka ko ganin laifinka, saboda ya nuna wannan kulawar ba shi yake nuna cewar yana son Aminatu ba, ina tunanin ya damu ne saboda a yanzu kamar tana karkashin ikonsa ne ta bata, kuma kin san halin gogan naki da tausayi, yana tausayinta sosai”
 
Leila ta yi irin murmushin nan da hausawa ke cewa ya fi kuka ciwo.
 
“Tausayi wani mataki ne ya so ne Ali, duk wanda ke tausayinka yana gudun wani abu ya same, yana gudun abun da zai saka ka kuka ko bakinciki, kuma tausayi kan hana mai yi maka shi cutar da kai, tun daga lokacin da ka hada shi da ita ya ji yana tausayinta sai komai ya canja, idan kana tausayin mutum zaka ji baka son komai ya taba shi, tausayi ya fi so ya fi kauna Ali. Mahaifina yana matukar tausayin Talba, saboda yana ganin ya tashi ba uwa ba uba, Daddy yana ganin Talba ba shi da wani gata a duniyar nan sai nasa, ba shi da kowa sai shi, wannan dalilin ya saka mahaifina baya iya musa a kan komai, kuma yana gudun abun da zai bata masa rai ko kuma ya ji cewar yana kewar iyayensa saboda rashin wani ba... To irin wannan tausayin ne Talba yake yi ma Aminatu, yana gudun bacin ranta, ba shi da budi sai na son faranta mata, ranar daya kawo ta a gidan nan har muka samu tsabani da ita baka ga halin daya shiga ba, bana jin yana tausayin kansa kamar yadda yake tausayin Aminatu, sai dai ka san abun bakincikin? Ni baya tausayina, baya damuwa da damuwata, kin ci abinci miyasa ba ki ci ba? Me yake damunki? Me kike son ki ci? Shirya mu tafi wani gurin, Leila ina matukar kaunarki, me ya same ki? Zamu iya zuwa likita ya dubaki? Zamu tafi gurin shakawata, meet my new friends duk be taba min ba. Shim mu ba masoya ba ne?”
 
Ta karasa tana kallon Ali hawaye na zirya a fuskarta, sai kuma ta sauke kanta kasa tana watsa da yatsunta.
 
“Idan wani abu ya faru ni ce ta farko da yake fara zargi kamin kowa, ashe masoyi ya taba zama makiyi? Wani abun dariya kuma na kasa rabuwa da shi, a duk lokacin da na yi yunkurin yin haka sai na zuciyata ta hana ni, Talba yayi min duk wani abu daya kamata na goge shafinsa a tahirin rayuwata amman na kasa, yayi min komai daya kama ace na juya na bashi baya amman na kasa... Wata kila saboda...”
 
“Saboda baki taba bawa zuciyarki damar gwada son wani abun ba sai Talba”
 
Ya marasa mata sai ta kalleshi, numfashi ya aje sannan ya cigaba.
 
“Leila let me tell you something, ba a mutuwa akanmu mu maza, kuma ba a rayuwa saboda maza. Ke mace ce, mace tana da daraja a ko wane irin hali da yanayi na rayuwa. Ba a zabar mutuwa saboda namiji kamar yadda ba a zabar rayuwa saboda shi. Ki mutu a karan kanki idan kin tashi, mazan da suka ji za su iya mutuwa a tare da ke, za su zo ku mutu tare. Ki zabi rayuwa a lokacin da kike jin kin dace ki yi rayuwar, wadanda suke son ki za su zo ku rayu tare! Ki so kanki irin soyayyar da za ki iya kashe kanki saboda ki raya kanki, karki yaudari kanki ki bar zuciyarki ta raya miki wani namijin zai iya mutuwa saboda ke, kuma karki wulakanta kanki ki ji cewar zaki iya kashe kanki saboda Soyayyar Namiji, karki zurfafa karki tsananta kar kuma hakan ya saka ki yi ma soyayyar Namiji rikon sakaina kashi...!”
 
Ta share hawayenta tana nazarin kalamansa, sai kuma ta dago ta kalleshi shi ma kallonta yake kamin ya sauke idanuwansa ya mike tsaye. For the 100 time ta kara jin Ali ya burge ta, rayuwarsa so simple ba kamar Talba ba, ina ma ace Talba ne yake nuna mata wannan kulawar!
 
“Idan kin kimtsa zan iya saukeki gida, na fadawa Momy zan kawo ki gida da kaina”
 
Ya fada ba tare da ya kalleta ba, feeling some how. Dan murmushi ta samu kanta da yi sai a lokacin ta dauke idonta daga barin kallonsa.
 
“Matarka ta yi dace Ali, kana da saukin rayuwa, kuma kana da zuciya mai kyau, ka san yadda zaka kwantarwa da mace hankali”
 
“Abokina ma ya sani, Leila Talba yana da hali mai kyau, idan kika samu soyayyarsa zai maida ki sarauniya, domin idan yana son abu yana so ne da duka gaskiyarsa, Talba baya neman mata, ba neman mata kawai ba, Talba ya irin mazan nan ba ne da kowace mace ke burgeshi ba, samu miji irin Talba da ce, ina fadi miki wannan ne from the bottom of my heart”
 
Ya fada yana jin kamar be dace ya dorata a wacan line na farko ba, miyasa ma zai fada mata wasu kalaman da zasu iya sauketa daga line da Talba yake.
 
“Amman...”
 
“Ina jiranki a waje”
 
Ya tari numfashinta tun kamin ta fadi abun da zata fada, be tsaya jiranta ba ya fice daga dakin. Murmushi tai ba wannan karon ba domin kalamansa ba sai dan tunawa da maganar da Hajiya Saratu tai mata. Mikewa tai tsaye ta juya ta kalli ko'ina na dakin sannan ta nufi kofar fita. Tafiya take tana kallon mutanen dake kai da kawo kamar ba ita ba, ba zaka ce tana cikin damuwa ba, kamar yadda ba zaka karancin nishadi a fuskarta ba.
 
 
***    ***    *** 
 
Lokacin da Ali ya ba su takardar sallama ya fadawa Momy ta tafi gida shi zai sauke Leila da kansa saboda akwai maganar da yake son yi da ita. Momy bata musa masa ba, ta Hajiya Saratu da Kawarta kuma aminiyarta Hajiya Murja da kuma mahaifiyar Madina wato Hajiya Aisha.
 
“To Hajiyoyi mun gode fa sosai Allah ya saka da alheri, na gode sosai”
 
“Ba komai Wallahi Allah dai ya kara lafiya, Madina ma ta so ta zo, sai dai kin san halin gogan naki baya son ana masa wasa da aiki, kuma tace wata kila ma Leila bata farka ba lokacin”
 
Momy ta yi murmushin yake.
 
“Allah sarki babu komai ai, idan ta dawo aikin sai ta zo ta dubata”
 
“Eh haka na ce mata nima, na san ai tana tasowa aikin zata fara zuwa”
 
“Uhm”
 
Momy ta fada sannan ta kalli Mairo dake hada kayansu tace.
 
“Ki yi ki hada kar a bar Direba yana ta jira”
 
“To Hajiya”
 
Ganin hakan ya yasa Hajiya Murja mikewa tsaye rike da key dinta na mota.
 
“Hajiya sai idan mun shigo gida, Allah kara sauki”
 
Ta fada tana kallon Ali da dan mamaki. Bayan fitarta mahaifiyar Madina ta fice ita ma, sannan Momy ta kalli Hajiya Saratu ta ce.
 
“Saratu zaku wuce gida tare da Mairo, ni zan shiga tawa motar akwai inda nake son biyawa”
 
“Okay”
 
Ta dauki jakarta ta bi bayan Mairo, sai da suka fita sannan Momy ta kalli Ali da Leila tana murmushi.
 
“To ni zan wuce sai kun shigo”
 
Leila ta daga mata kai, alamar to Ali kuma ya amsa mata.
 
“Okay Momy”
 
Sai da ta gyara mayafinta sannan ta fito daga dakin, kadan kadan take tafiya domin bata son ta hadu da su Mairo. Tsaye tai a bakin ward din tana kallon mutane, da gangan ta bata lokaci sai da ta tabbatar sun isa sannan ta karasa gurin da ta aje motarta ta saka key ta bude ta shiga. Reverse tai sannan ta dauki hanyar fita daga fita asibitin. Kai tsaye ta dauki hanyar da zata kaita tsohon gidan gonarta. Daman tun lokacin da aka aiko musu da sakon nan take son zuwa amman bata samu dama ba saboda abubuwa da suke faruwa, ga shi ta nemi number mai gadi ta rasa a wayarta. Tana driving tana kallon motocin dake bayanta, kamar an fada mata wani zai bibiyeta. Hankalinta be kwanta ba sai da ta shiga area babu wata mota dake binta a baya. Farkin tai gaban gate din ta danna horn, tana jiran mai gadin ya fito ya bude mata, sai ta ji shiru, hakan yasa ta sake danna horn din har sau hudu amman ba a bude mata ba, bude motar tai ta fito cike da mamaki, domin ta saba zuwa ta tararda shi kuma horn daya take ko biyu zai fito ya bude mata idan ma yana waje yana ganinta zai tashi ya bude gate din. Rufe motar tai ta fara takawa ta karasa daf da gate din sai a lokacin ta lura da an sakawa kofar gate din padlock har biyu, wani irin faduwa gabanta yai.
 
“Padlock yau kuma a gidan nan?”
 
Ta furta cike da tsananin mamaki, domin ba a taba saka padlock a rufe gidan ba, idan ma za a rufe gidan ta waje sai dai a saka key ba padlock ba. Har hannu ta kai ta taba domin tabbatarwa.
 
“To ina yaje? Ina iyalansa?”
 
Ta tambaya cike da confused, a take zarginta ya zama biyu bayan Madina a yanzu ma tana zargin mai gadinta, maybe shi ma yana da sa hannu a ciki. Tsaye tai tana ta kallon kofar da mamaki da kuma tunanin kala kala a ranta. Can kuma ya juya tana kallon unguwar, mai dauke da manya da kuma kananan gidaje. Gurin wani mai shago ta nufa tana isa tai masa sallama.
 
“Wa'alaikumussalam”
 
Mai shagon da mutanen da suke zaune tare da shi suka amsa mata.
 
“Dan Allah tambaya nake, Sani Mai gadin gidan can nake tambaya baban Rukayyah yana da mata Nafisa”
 
“Oh na gane shi ai mutume na ne, kullum yana nan muna hira, amman kwana biyu na daina ganinsa gaskiya, yaransa ma da suke dan fitowa suna wasa na daina ganinsu”
 
“Ya tashi ne dan Allah?”
 
“To Wallahi bana tunanin haka, domin a yadda muke da shi da ace tashi yai zai mana sallama, kuma zamu ga yana kwasar kaya, amman ko daya ba mu gani ba, kawai dai mun wayi gari mun ga gidan a rufe da kwado, kuma mun kira wayarsa kullum cewa ake a rufe take”
 
“Amman wani abu ya faru ne kamin ku daina ganinsa?”
 
“Aa Wallahi, babu abunda ya faru sai dai ba mu sani ba ko wani abun ya faru ya boye mana”
 
“Kuma ba ku ji labarin inda ya koma ba?”
 
“Aa Wallahi har yanzu ba su san komai akai ba, amman lafiya ke kike nemansa”
 
“Ni ce wanda yake yi ma gadi, kwana biyu ina zuwa bana tararda shi, ina ganin ya kamata na bincika, domin wayarsa bata shiga idan na kira”
 
“Ah gaskiya dole ne ki bincika kam, amman ke Hajiya ba ki san garin da yake ba?”
 
“Wallahi ban sani ba, wani mai gadin gidan mijina ne ya same min shi, saboda na fada masa ina son na samu mai min gadi saboda ba zai yiyu a bar guri haka ba kowa ba, nace masa ya sama min mai iyali”
 
“To shi ya kamata  ki koma ki bincika gaskiya, wata kila shi ya san inda yake”
 
“Haka za ayi”
 
Ta fada sannan ta juya ta nufi gurin motarta. Bata ji tana iya musu godiya ba dan haka bata musu ba ta koma cikin motarta tai mata key, zuciyarta cike da tunani.
 
“To ko dai shi ne wai? Amman yadda yake dab kauyen nan zai iya wannan abun ma? Ina zai samu kudin hayar mutune da za su kawo sakon babu ko tsoro a tare da su? Ko kuma dai wani ne dabam? Amman taya akai shi kansa ma ya sani?”
 
Haka ta isa gida da sake sake, ta kulla wacan ta kwance wannan. Ba ta labartawa Leila komai ba sai da akai Sallah la'asar sannan ta kira Leila a waya tace mata tana son ganinta dakinta. Azaton Leila Momy zata yi maganar da Hajiya Saratu tai mata ne hakan yasa ta taso da saurinta ta shigo da dakin.
 
“Momy gani”
 
Ta fada bayan ta zauna kusa da Momy sai dai ita ta zauna kan gado ne, yayinda Momy kuma take zaune kan carpet da plate din fruit a gabanta.
 
“Kin ci abinci?”
 
“Momy bana son cin komai yanzu, bana ma sha'awar komai, amman Madina ta zo min da ice cream na sha”
 
Momy ta tabe baki.
 
“Naje tsohon gidan gonata dazun, kuma na tararda gidan a rufe da kwado har biyu, me gadin baya nan.... ”
 
Momy ta fada mata komai ciki har da amsar da mai shago ya bata.
 
“To Momy ko dai shi ne?”
 
“Na yi wannan tunanin, to amman kuma ai be san abun da muka saka a gurin ba, kuma na saka tanki ruwa a gurin an cika shi da ruwa saboda kar ma wani yai tunanin ko akwai wani abu a gurin kin manta”
 
“Amman Momy ke fa kika sa shi ya gina ramin”
 
“Ai na fada masa kudi zan rufe a ciki, ta wani bangaren bana zargin mai gadin nan, domin ko samun wanda zai shirya wannan abun da shi aiki a gurinsa a yadda yake da kauyancin nan, dole dai akwai wani na kusa da mu daya san da wannan abun, kuma Madina nake zargi”
 
Leila ta daga kai sama.
 
“Haba Momy wani irin Madina kuma? Madina ba zata min haka ba, sai dai idan wani ne dabam”
 
“Wai har yanzu ba ki gane cewar Leila tana son abun da kike so ba? Ke yanzu baki gane saboda Talba ta nemi aiki a kamfanin nan ba? Ba ki gane saboda shi take kara kusanci da ke ba? Ko jiya da Talba yake magana baki lura da yadda ta fara kuka ba, ita fa da kanta take tambayarsa ka yi aure? Sannan ta fice tana kuka, na lura neman gindi zama a gurin Talba yasa ta dauki yarinyar nan ta kaita gidansu, amman ke da yake baki da tunani duk hankalinki be kawo miki haka ba”
 
Leila ta yi shiru tana nazarin kalaman Momy da suka soma shigar mata a kwakwalwa.
 
“Kin fada mata inda muka binne Baaba?”
 
“Eh saboda ta tambaye ni lokacin da nake bada labarin kuma na fada mata”
 
“Hmmm Leila baki jin magana, sai da na gargade akan karki fadawa kowa wannan maganar amman baki ji ba, saboda kin dauki Madina kin maida ta uwarki, ba ki da shawara sai nata”
 
“Amman wace riba Madina zata ci idan tai min haka Momy, ko da ace tana son Talba ta yi kokari tun da har ta iya boyewa”
 
“Saboda ta lalata aurenku mana, idan muna cikin wannan tashin hankalin kina ganin zamu iya sakin jiki har mu yi komai cikin kwanciyar hankali? Kuma zata iya tona miki asiri har Talba ya san komai, shiyasa har yanzu ta ki ta kulawa kowa kuma taki ta tsayar da wani”
 
Leila ta kada kai.
 
“Ina jin kamar haka ne, amman Wallahi na kasa yarda Madina zata min haka”
 
“Kin fada mata cewar an kawo miki Envelop da dankwalin Baaba a ciki?”
 
“Eh na fada mata, sai tace min wai akwai mai bibiyata wata kila lokacin da muka rufe akwai wanda ya gani, shi ne zai yi amfanin da wannan damar ya samu kudi, har take ce min wata kila ma shi ne yai garkuwa da Aminatu”
 
Momy ta nisa duniyar tunani tana nazari.
 
“Wani lokacin Momy ina ganin kamar Madina ba zata iya min haka ba, domin ko a yanzu magana take min akan abun da Talba yai har take cemin kar hakan da yai ya saka na gujeshi ko na ce na fasa aurensa kamar yadda kika yi ikirarin aikatawa, tace min idan akai haka ai an bawa ita Aminatun damar da take so”
 
“Makirin mutum babu abun da baya iyawa Leila, munafukin mutum yana da wuyar ganowa, ki yi taka tsantsan da ita, kuma ki daina fada mata sirrinki, Allah yasa ma baki fada mata maganar da muka yi dake da Saratu ba”
 
“Na fada mata, kuma tace kar na yi domin magani dan kwana arba'in ne, kuma zai iya yiyuwa ba asiri suka masa ba, akaran kansa ne yake yin komai, tace min wai duk ranar da maganin ya kare Talba zai ji ba zai iya zama da ni ba”
 
Momy ta yi murmushin takaici.
 
“Ina jin wani sirrinki ma da Madina ta sani ni kaina ban san shi ba, yadda kika zaunawa ki bude mata cikinki ai ita bata bude miki nata haka, ko ta taba yin zancen wani sauyinta da ke? Kin tambayarsa miyasa bata tsayuwa da samari? Amman kin zama sakarya kullum sirrinki na cikin kunnuwanta, ta san komai na ki”
 
“Zan canja mata ai yanzu, idan tana da wata manufar zan gano”
 
Momy ta tabe baki.
 
“Allah yasa zaki iya, je da kanki ki kira min Mustapha ki bude masa kofar karamin falo ta baya ya shigo, kuma ban ce ki bari kowa ya sani ba”
 
“Mustapha kuma Momy?”
 
“Eh mi ya kawo min Sani ai, zan tambaya na ji ko yasan inda sanin yake da kuma garinsu”
 
“Amman Momy kar garin bincike mu tonawa kanmu asiri fa”
 
“Babu abun da zai faru”
 
“Okay”
 
Ta mike tsaye ta nufi kofa kana ganin tafiyarta kasan bata da wani kuzari a jikinta. Tana daf da ficewa sai kuma ta juyo ta kalli Momy.
 
“Momy yaushe zaki yi magana da Mama Saratu?”
 
“Sai mun natsu tukuna, kuma ki kama bakinki idan Amal ko Kabir ya ji maganar nan kin san har Daddynku sai ya ji ta”
 
Ta gyada kai sannan ta kai hannu ta bude kofar ta fice.
 
 
_______________________________
 
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
 
*Littafin nan na kudi ne biya

Join Our Groups

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login