Showing 75001 words to 78000 words out of 332834 words

Chapter 26 - Bakar wasika Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

65609

ya fada yana murmushi, shi ma murmushin yai ya cigaba da tukin har suka isa asibitin, aka duba kafar aka bashi magani suka rufe ciwon. Sannan ya sake daukoshi a motarsa suka suka nufo unguwarsu, suna tafe suka hira kamar daman can sun saba, be yarda ya bar Faruq a bakin titin ba duk kuwa da kasancewar mota bata shiga har kofar gidansu, sai ya fito ya taka masa har kofar gidan yana masa wasa wai kar madan tace sun buge mata miji, Faruq murmushi kawai yai ya kai hannu ya taba gidan sai ya ji shi a rufe, key dinsa ya dauko ya bude ya shiga ciki.
 
“Ina jin bata nan, daman tace min tana da biki zata je”
 
Fada a kokarinsa na kare matarsa duk da kasancewar mutumen be san Rafi'a balle har ya munana mata zato.
 
“To a gaishe ta, kuma a bata hakuri ga kuma wannan ayi cefane”
 
Ya fada yana mikawa Faruq dubu goma.
 
“Aa haba ai abu ne da Allah ya kawo...”
 
Kamin Faruq ya karasa Mutumen ya saka rantsuwa.
 
“Wallahi sai ka karba, kai shedan kadai ke maida kyauta”
 
Murmushi Faruq yai a karo na barkatai ya karbi kudin yana masa godiya.
 
“Na manta ban tambayi sunanka ba”
 
“Faruq”
 
“Ni kuma Muhammad Fahat na gode sosai Allah ya tsare gaba”
 
“Ameen”
 
Daga haka Faruq ya karaso cikin gidan shi kuma ya juya ya kama hanyarsa. A falo Faruq ya zauna yana kiran Baturiya a waya domin jin inda take, sai dai bata dauka ba daga baya ma sai yaji wayar a kashe, hakan kuma ba karamin bata masa rai yai ba, ba yau ta saba fita ba tare da izininsa ba sai dai ya fi jin zafin fitarta fiye da koyaushe. Cikin karfin hali ya shiga uwar daka ya tube tufafin jikinsa yai wanka ya canja wasu kayan sannan ya kwanta, nan da nan bachi yai gaba da shi. Kiran Allah azahar ne ya tashe shi, ya tashi yai alwala ya fita masallaci a can ya hadu da dansa da yabi yaran makotansu suka tafi masallacin a tare. Kusan kowa da ya gaisa da shi sai ya masa sannu da fatar Allah ya tsare gaba, shi kuma ya amsa da Ameen bayan ya labarta musu abun da ya faru.
 
Sultan na ganin mahaifinsa ya rike shi suka dawo gida tare. Abun ka yaro yana shigowa ya fara tambayar Faruq ina mamansa.
 
“Dady Momy bata dawo ba?”
 
“Ina ta tafi?”
 
“Bata fada min ba, amman na ji tana ta waya da yawa tana ta waya har ta ce ummouy”
 
Ya nuna yadda tai kiss din da bakinsa. Faruq ya hade yawu yana jin wani bakinciki na taso masa. Haka ya wuni a gidan
 
Shin kin san Kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud
Sandal flakes
Sandal wood
Signature
Kajiji
Damboun kajiji
Halud ball
Wardrobe ball
Coconut sandal
exclusive gowe
Black humra
Body milk
Kulaccam
Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin da kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya, domin siye ko sari ku tuntubi Ramla incense ta wannan number 07038392576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa
 
 
*Dan girman Zatin Allah karki karanta idan baki biya ba. Masu sharing Allah yai muku yadda kuke min! Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
 
 
 
AMINATU POV.
 
Daga jiya zuwa yau da aka canja mata daki sai ta ci kadaicin ya karu, domin a can tana jin hayaniyar mutune a wannan dakin komai babu kowa sai ita kadai, sai duk ta ji tana kewar gidansu da rayuwarta ta baya.
Bata san dalilin daya saka aka canja mata daki ba, bata san ranar da wani zai zo nemanta ba, bata san ranar da rayuwarta zata koma daidai ba, har yanzu ji take kamar komai mafarki ne.
 Tana fara tunanin ta ji wani irin tsoro ya taso mata, sai ta ji wani abu yana mata yawo a cikin kai karar bindigogi ya dawo mata hayaniyar mutane da rokon da Baba yake musu ya dawo mata kamar lokacin yake faruwa. Wani irin abu ta rika ji kamar kanta ba zai iya dauka ba, gashi tana son ta yunkura ta sauka saman gadon amman dama domin kafafuwanta basa iya komai a yanzu, bakinta ma ya dantse gam duk yadda ta so tai ihu ko kuka sai ta kasa. Ji tai bata bukatar komai a lokacin sai tafiyar da babu dawowa. Da wani irin karfi ta tashi zaune ta fisgi robar ruwan dake hannunta wanda hakan ya bawa jini hanyar fita ya fara zuba, jiki na rawa ta fisgo robar da karfin da bata taba sanin tana da shi ba sai karfen ya fado gefen gadon, bata tsaya komai ba ta hada robar a wuyanta tana kokarin aika kanta da kanta inda take ganin kamar idan ta tafi ta huta da komai.
 Wannan karon ta samu sukunin bude baki, sai dai ko kadan hakan be bawa muryarta damar fita ba, hawaye kawai take babu kakautawa tana ta yaki da numfashinta, kamar an zare mata lakka haka ta ji wani abu ya sauko mata wanda ya zare duk wani sauran kuzari dake jikinta. Tun tana kallon kofa tana numfashi a hankali har numfashin nata ya fara nisa ta komai ya fara mata dishe dishe alamar ta fara ban kwana da duniya, ga jinin hannunta sai zuba yake.
 
 
TALBA POV.
 
As usual every weekend a falon Momy ko Daddy ake karyawa tare da kowa ciki har da Daddy da matarsa, sai dai mafi akasiri an fi cin abincin safe a bangaren Momy, Daddy zai zo bangarenta aci tare da shi, idan an gama ko kamin a fara duk wani mai wata bukata zai gabatar masa.
Sai dai wannan karon a bangaren Daddy Momy ta saka masu aikinta su kai komai wanda hakan ke nuna cewar a bangarensa za a karya.
Duk abun da ake Talba na zaune dinning yana lasa wayarsa, be dago ba har sai da ya ji saukowa Momy, sannan ya dago ya kalleta.
 
“Momy ina kwana?”
 
“Lafiya kalau an tashi lafiya?”
 
“Alhamdulillah”
 
Ya amsa yana tashi tsaye sai da ya bar dinning din ta kira shi.
 
“Talba”
 
Juyowa yai ba tare daya amsa ba.
 
“Ka yi hakuri da abun da ya faru jiya, raina ne ya bace”
 
“Babu komai Momy, ke ai uwata ce Wallahi ban rike ki da komai a rai ba”
 
Wannan maganar da yai sai ya saka Momy ta dan ji nauyinsa, kasa hada ido tai da shi har ya juya ya fice daga falon. Kai tsaye bangaren Daddy ya nufa a bude ya samu kofar shiga falon, hakan yasa be yi sallama ba kamar yadda ya saba ya nufi gurin da suke karyawa.
Leila kadai ya samu zaune a dinning din ta saka plantain a gaba tana ci, tana sanye da wani jan yadi kanta sanye da bakar hula, fuskarta ta ji hoda sosai sai dan janbakin data shafa, ta yi kyau sosai abu ne mai wahala mace ma tai mata kallo daya ta dauke ido balle kuma namiji. Talba yaja kujerar dake facing dinta ya zauna yana kallonta, shi kansa ya san ta yi kyau, sai dai ba al'adarsa bace fadawa mutum cewar yayi kyau ko yana da kyau, musamman mace, no matter yadda take da kyau ba zai taba iya bude baki ya furta cewar ta yi kyau ba, kuma ba zai zake da yawa gurin kallo ba gudun kar a ankara da shi.
Dauke idonsa yai bayan ya zauna, sai a lokacin ya tuna cewar yau be tura mata sakon barka da safiya ba, kuma ba zai iya tura mata a yanzu ba gudun kar tace saboda ta yi kyau ne.
 Gaba daya ya tattara hankalinsa ya maida gurin wayarsa, sai yai kamar be san da zaman Leila a gurin ba, ita kam daman gaisuwa ba halinta ba ne bata saba gaishe da mutane ba bayan Momy da Daddy, balle kuma shi duk kuwa da irin sanin da tai na son a girmama da yake, sai dai ta kasa dauke idonta daga barin kallonsa duk kuwa da irin bugawar da zuciyarsa take after every blink. Har ga Allah bata iya fadar irin son da take yi ma Talba, da ace ta dauki biro da zayyano irin kaunar da take masa da alkalumman rubutu da takardun duniya sun kare bata gama rubuta irin kaunar da take masa ba. Sai dai har yanzu ta rasa gane manufarta a kanta, miyasa ba zai dauki rayuwa da sauki ba? Ya sauko da kai su yi soyayya kamar sauran masoya? Har yaushe zata yi ta jiran ya canja rayuwarsa? Anya ma zai canja din? Bata raba dayan biyu ba ta ji yana amsa waya, bata iya fadar cewar kiransa akai ba ko kuma shi ya kira domin wayarsa a silent take.
 
“Yeah ni ma na kwana da yarinyar nan a raina”
 
Furucinsa ne yasa ta kara tattara hankalinta tana saurarensa.
 
“Okay”
 
Shine last abun da ya fada sannan ya sauke wayar, ya daga kansa yana kallo Amal data nufo inda suke sanye da riga da wando yan patistan.
 
“Good morning Ya Talba”
 
“Morning Little Sis”
 
Ya amsa yana aikawa PA sa sakon kar ta kwana.
 
‘Ka yi magana da wannan number zai fada maka ko nawa yake bukata sai ka tura masa’
 
Aje wayar yai bayan ya aika sakon. Leila bata fahimci komai a wayar ba, sai dai ta fahimci da Ali yake magana domin yanayin yadda ya amsa wayar ya tabbatar mata da hakan. Sai da kalmar da ita na kauna a raina ya fi tsaya mata a rai.
 
“Wace yarinya ce?”
 
Ta tambayi kanta tana kallonsa, a take ta ji zuciyarta ta buga da mugun karfi, har sai da numfashinta yai sama, da sauri ta dauki cup din dake saman teburin ta zuba ruwan sanyi ta sha, sannan ta mike tsaye ta fice daga gurin zuwa karamin falon Daddy.
Zaunawa tai tana haki, ji take kamar taje ta tambaye shi wace yarinya ce sai dai ba wannan damar domin ba ya hira da ita, da ma dai Amal ce ita kam har sirri yake da ita.
 
“Wace yarinya ce Talba zai kwana da ita a ransa? Ban gane ya kwana da ita a ransa ba, as how?”
 
Wannan karon a fili tai tambayar tana hade yawun bakinta, sai kuma ta mike tsaye.
 
“Ko dai yayi ne dan na ji haushi? Amman kuma be taba min haka ba”
 
Ta dafa kanta tana jin kirjinta kamar zai rabe biyu, ita kamta da akai musu baiko bata tana jin yace ya kwana da ita a rai ba sai wata? Wacece ma? Ba kasafai yake saka mutane a rai ba balle har ya kwana da su amman yace da yarinyar na kwana a raina.
Haka ta sake sake a ranta, wani irin zafi ta ji zuciyarta na mata, irin zafin da bata tana jin irinsa ba, wata kila sabida bata tana jin Talba yana maganar wata mace a gabanta ba, hasali ma ba zata ce ga wata mace da yake so ko take burge shi ba, ko akwai be tana nunawa ba balle har ya fada.
 
“What if wani abun bacin rai tai masa?”
 
Ta sake tambayar kanta tana cire hular kanta, sam bata taba sanin wani abu wai shi kishi ba sai yanzu, domin Talba be taba yin maganar wata mace a kusa da ita ba, shiyasa kullum hankalinta a kwance yake bata da haufin komai, sai dai a yanzu tana jinta a cikin wani irin yanayi marar misaltuwa saboda ya furta ya kwana da wata a ransa.
 
“Ko dai bata masa rai tai, ai be kamata ya kwana da ita a ransa ba, Indai har macece ko yaya ne be kamata Talba ya kwana da ita a ransa ba”
 
Ta fada tana wasa da wayar hannunta, can kuma ta busar da iskar bakinta ta shiga contact dinta ta nemi number Ali ta kira shi. Kara wayar tai a kunne ta fara safa da marwa, kamin yai picking har ta matsu.
 
“Hello Leila”
 
“Ali ya weekend?”
 
“Alhamdulillah”
 
“Am akan maganar da kuke da Talba ne yanzu”
 
“Okay...”
 
Yayi shiru yana jiran yaji abun da zata ce, sai ta rasa ta inda zata fara ta san duk irin wayon da zata yi ba zai taba fada mata sirrinsa da Talba ba, sai dai idan ba sirri ba ne.
 
“Ban fahimci abun da kuke magana akai ba, kuma na ga kamar ransa a bace”
 
“Leila”
 
“Na'am”
 
“You should feel free to ask when ever kika ga Talba a damuwa ko matsala, shi ne fa mijin da zaki aura a tare zaku gina rayuwa idan kuna irin wannan zaman rayuwarku ba zata taba yin dadi ba”
 
“Na sani, amman ka san halin abunka, zan iya tambayarsa ya ki fada min ni kuma na damu ne kawai”
 
“Ki saka a rayuwarki ba ki da wanda yafi Talba, idan har kin damu da damuwarsa ya kamata ki tambaye shi”
 
“Zan yi haka, amman for now ina jin akan wata yarinya ce da na nuna masa jiya tana bukatar taimako, yar gudun hijira ce”
 
Shiru tai kamar mai tunani.
 
“Subhanallahi, tana ina yanzu?”
 
“Asibitin mu”
 
“Okay Allah ya bata lafiya, amman idan ana bukatar taimako Ali kai na gida ne, ka san yadda komai a Foundation din mu yake, ba sai ka sake yi masa magana ba, domin ba zan taba lamunta Talba ya kwana da tausayin wata a ransa ba, an yi na farko kuma na karshe, bana son ya kwana da kowa a cikin ransa sai ni”
 
“Ameen”
 
Ya amsa addu'ar da tai a farko yana murmushi, sannan ya aje wayar ba tare da ya sake ce mata komai ba domin ya san kishi ne.
Sai ta sauke ajiyar zuciya tana dan jin sauki a ranta.
 
“Ranki ya dade, Hajiya ta ce a kira ki”
 
Ta juyo da sauri ta kalli Mairo, sai kuma ta rufe da masifa domin ba karamin razana ta tai ba.
 
“Wai miyasa komai ba ku iya yinsa a cikin natsuwa ne? Mi yake damunku ne? Wannan ya zama na karshe da zaki sake kira sunana da karfi I'm not your mate”
 
Ta karasa tana jan tsaki sannan ta nufi hanyar shiga babban falon, bata ko tsaya kula Mairo b dake aikin bata hakuri. Ko da ta isa dinning din kowa ya hallara har sun fara cin abinci.
 
“Ina kika je?”
 
Momy ta tambaya tana kallonta.
 
“Waya na amsa”
 
Ta fada sannan taja kujera ta zauna tana mikawa Daddy gaisuwa. Sai da suka nisa da cin abincin sannan Daddy yai gyaran murya ya ce.
 
“Ina son na yi wata magana mai muhimmanci, Shiyasa na bukaci a shirya mana abun karyawa a nan, musamman mahaifiyarku”
 
Jin hakan tasa kowa ya kalleshi har Momy.
 
“Allah yasa ba laifi na yi ba”
 
“Laifi kika yi kuma babba, laifin da ban saka ran zaki yi ba a matsayinki na uwa, sam ban tsammaci haka daga gareki ba, ban yi zaton rana zata zo da zaki dubi dana ki fada masa cewar ba ke kika haife shi ba...”
 
Talba ya tsaya da cin abinci ya dago ya kalli Daddy dake maganar cikin tsananin bacin rai, Momy kuma tana kallon Talba a tunaninta shi ya fadawa Daddy abun da ya faru.
 
“Again?”
 
Momy ta tambaya tana cigana da kallon Talba rai a bace.
 
“Ba shi ya fada min ba wacan karon ma ba shi ya fada min ba...”
 
Kamin Daddy ya karasa Amal ya karba tana kallon Kabir.
 
“Ni na fadawa Daddy, ni kuma Ya Kabir ne ya fada min”
 
Momy ta kalli Amal kamin ta kalli Kabir.
 
“Na ji na yi laifi amman Amal bata fada maka danka yana wuce gona da iri ba?”
 
Da wani irin karfi da fusata Daddy ya daki teburin cin abinci.
 
“Da na be yi komai ba Amina... Wannan dalilin ne yasa na tara ku duka anan, saboda Leila ba zan yarda ki rika batawa Mu'azz rai ba, ko da rana daya bana jin ya taba miki wani abu da zai banban taki da uwar data haife shi, akan me zaki zabi raba kan yarana? Ko bana da rai shi zai yanke hukunci a gidan nan kuma shi zai dauki dawainiyar komai, na tara ku a nan ne saboda na ja miki kunne kuma. Yaranki su daina kokarin wuce guri ko da mafarki ban tsammaci zaki iya furta kalaman da kika furtawa dana ba, saboda abun da Amal ta fada min jiya ban samu bachi da kyau ba, ko kadan bana son abun da zai raba kan yayana kuma bana fatan Allah ya nuna min ranar da Talba zai ji bakincikin rashin uwa”
 
Yana kawai nan ya mike tsaye a fusace ya nufi dakinsa, kowa shan jinin jikinsa yai har Talba din da Daddy yake masifa saboda shi, domin ya san indai akansa ne tsab Daddy zai iya fushi da shi ko yai masa fada. Amal ma tashi tai da sauri ta bi bayan Daddy, domin ta san sakamakonta gurin Momy.
Momy da hawaye ke sauko mata ta kalli Talba tace.
 
“Mutum baya kuskure ne? Ni kaina na ji cewar ban kyauta ba, na ji cewar be kamata na furta kalaman nan ba”
 
Talba yayi saurin girgiza mata kai.
 
“Haba Momy kamar baki san halin Daddy ba? Yanzu zai hau kuma yanzu zai sauko, be kamata wannan ya dame ki ba, kin mu sanin Daddy fa, muma a tare muka bude ido muka ganku please ki yi hakuri dan Allah”
 
“Ka yi hakuri kai ma, ban kyauta ba na sani, Allah ya muku albarka”
 
Ameen. Duk suka amsa har Leila sannan ta mike tsaye ta nufi hanyar bedroom din Daddy, hakan yasa Leila ma ta tashi ta nufi hanyar fita daga part din gaba daya.
 
“Daddy's Boy?”
 
Kabir ya fada yana kallon Talba, sai Talba yai murmushi kadan.
 
“Har yanzu Daddy be yarda na girma ba, yana ganina kamar jariri”
 
“Maybe sai ka yi aure ka haihu ya ga ka fara bawa yayanka kulawa”
 
Ya dan tabe baki kadan.
 
“Ni ma ina son ganin haka, you know i love children alot, but before then ya kamata ka iya bakinka, Amal parrot ce ba komai ake fada mata ba, yanzu kaga abun da taja mana”
 
“Da gangan na fada mata ai, saboda na san zata tseguntawa Daddy, sincerely speaking Momy bata kyauta ba, she shouldn't say that, we're one family be kamata tai haka ba, rai na be taba baci irin jiya ba”
 
Cewar Kabir with serious face. Talba ya dauki tea gabansa ya sha kadan.
 
“You know mata suna da rauni Kabir, kuma tunaninsu gajere ne, shiyasa ba a zure musu

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login