Showing 195001 words to 198000 words out of 332834 words

Chapter 66 - Bakar wasika Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

65630

mutumen.
 
“Kai ba dai har kin fito ba?”
 
“Yace wai mu bari sai gobe”
 
“Lafiya dai?”
 
“Lafiya kalau wai an kira daga gidansa matarsa ba lafiya”
 
“Okay bari na zo na maida ke”
 
“Ni ina gida yanzu, ina kika san shi ni fa ya min”
 
“Hahaha, kuma Wallahi zaki kwashi naira idan ya sake jiki da ke, mutume na ne sosai, ina kawo masa masu kyau sai dai ya fi son farare kuma sirara kin ga ai yana da jiki sosai”
 
“Eh, ashe kun saba”
 
“Sosai ma, ke ma ai labarinki kawai na bashi amman ya takura min na kawo masa ke, kamar zai cinye ni”
 
“Allah sarki yana da kirki”
 
“Sosai ma Wallahi”
 
Sama sama Baturiya ta bugu cikin Ramlee ta ji labarin yayanta sannan sukai sallama. Tun daga lokacin sai Baturiya ta kasa sakewa tana ganin kamar yayanta zai fadawa mahaifiyarta abun da tai ne. Bayan kwana hudu da farar hakan Yayanta ya shigo gidan, abun ka da namiji sai ya murje ido kamar ba shi ba, ita ce ma mai jin kunya, shi kuma sai hararta yake yana jin haushinta, domin a ganinsa bata rasa komai ba a gidan mahaifiyarta balle ace saboda rashi ne take wannan bakar sana'ar. Tana gaishe shi ta shige ciki dakin tana ta chatting dinta Fahat bata fito sai da ya tafi. Tun daga yanayin yadda Umma take watsa mata harara ta san akwai wani abu a kasa, hakan yasa ta fasa zaman a falon ta nufi kofar fita kamar daman can fitar zata yi.
 
“Rafi'a”
 
Gabanta ya fadi sosai ta juyo cikin tsoro ta kalli Umma.
 
“Zo ina da magana dake”
 
Ta juyo ta dawo kusa da Umma ta zauan kan kujera, zuciyar dake raba jini a jikinta na bugawa da karfi.
 
“Ga ni Umma”
 
“Yayanki ya bada sako ya ce a fada miki, ki fitar da mijin aure cikin satin nan ko kuma ya samu miki wani ko ya maidake gidan tsohon mijinki”
 
“Aa ni ina da wanda nake so”
 
“Na fada masa kina da manema, sai ce min yai wai Allah yasa ba mutnen banza ba ne, domin shi ya fara tunanin da laifinki a rabuwarku da Faruk shiyasa be fada ba, so yanzu ina son ki fada min, yayanki ya ganki a wani guri ne da be dace ba ko kuma kin fara tsayuwa da mutanen banza ne?”
 
“Ba ko daya, idan ma mutanen banza ne ni dai ba su zo min da maganar banza ba, dan haka ba zan iya shaidarsu da wannan ba”
 
“Sannan abu na biyu yace akwai wata kawa taki da kike mu'amala da ita ba yarinyar kirki ba ce”
 
“Kawata...”
 
Ta fada da siffar tunani tana kokarin kawar da tunani Umma, ita ala dole bata gane ko wace kawa ba ce.
 
“Ya fada miki sunanta?”
 
“Be fada min ba, ke ai kin san a cikin kawayenki wadanda ba mutanen kwarai ba, sai ki rabu da su tun wuri, kin fi kowa sanin yayanku, ko mahaifinku ba kai shi zafi ba”
 
“To Umma zan gyara”
 
“Cikin samarin wanda kika ji ya fi kwanta miki sai ki gabatar masa da shi”
 
Umma na kaiwa nan ta tashi tsaye ta nufi kicin. Baturiya ta sauke ajiyar zuciya cike da jindadin yayanta be fadawa Umma komai ba.
 
 
 
AMINATU POV.
 
Kullum sai sun bata abinci mai kyau da ruwa mai sanyi, ko bakar magana basa mata balle kuma duka, ko razanar da ita, sai idan tana musu magiyar su barta ta tafi gida, ko kuma ta dame su da kuka wasu daga cikinsu kan daka mata tsawa. Sai farin mutumen nan ya taka musu burki. Yau kan su biyu suka shigo kawo mata abincin rana, sai suka same ta tana sallah. Tsaye suka yi har ta gama.
 
“Ki fara shan lemun kamin ki ci abinci”
 
Kallon lemun tai dake cikin roba da takeaway, sannan ta kallesu.
 
“Har zuwa yaushe zan yi ta zama a nan? Miyasa kuka kawo nan? Mi na yi muku?”
 
Ta tambaya hawaye na sauko mata. Sai dayan ya amsa mata.
 
“Sakamu akai”
 
“Waya saka ku?”
 
“Mu wawaye ne da zamu fada miki? Kin ce mana baki da kowa gashi nan an baza hotonki a ko'ina sai nemanki ake, a media an saka kuma saka a jarida da gidajen radio, har da tukuicin naira miliyan uku ga duk wanda ya san inda kike ko kuma ya kawo ki”
 
Shiru tai tana tunanin wanda zai aikata mata.
 
“Da gaske nake, bani da kowa, ban san wanda ya saka ayi wannan abun ba”
 
Ba su sake ce mata komai ba suka fice. Hannunta ta kai a kirjinta ta dafa zuciyarta duk duniya mutum daya ta san zai iya mata wannan shi ne Talba, ashe be manta da ita ba? Yana cikin mawuyacin hali amman haka be hana ta murmushi ba hawaye na sauko mata a lokaci daya. Sai dai abun da ya fi tsaya mata a rai waya saka ayi mata wannan abun? Miyasa suka dauke ta? Kudi suke so ko kuma suna da wata manufa ne na yin haka? Da alama ba mutuncinta suke son tabawa ba, somin ta sha jin suna fadar cewar ance kar su mata komai.
Bata taba abincin ba balle kuma har ta sha lemun da suka bata umarnin ta fara shansa kamin ta ci abinci, har suka dawo suka tararda komai a yadda suka barshi.
 
“Baki ci ba?”
 
Ta yi shiru tana kallonsu, wannan karon dukansu fuskarsu a rufe take, har da farin mutumen daya saba bari fuskarsa a bude.
 
“Ki ci abinci yanzu”
 
Ta girgaiza musu kai a hankali.
 
“Dure zamu miki idan baki ci ba”
 
Fadar hakan da dayan yai sai ya saka ta makara jin tsoron, domin ba su taba cilasta mata cin wani abu ba a dole, sai wannan karon hakan kuma na nufin akwai wani abu cikin abincin ko lemu da suke son ta sha.
 
“Karka mata dore, ance kar mu cutar da ita”
 
Dayan ya fada, sai na kusa da shi ya kalleshi ya soma magana cikin daga murya.
 
“Idan ba mu mata duren ba ya zamu mata? Ai ba taba ta muka yi ba ba fyade zamu mata ba”
 
“Dan Allah Karku min”
 
Ta fada cikin kuka hankalinta na mugun tashi.
 
“Dauki ki sha ai ba maganin mutuwa ba ne”
 
Ta girgiza kai tana fashewa da kuka, sai biyun suka nufeta tana ganin haka ta mike tsaye da sauri ta fara ihu tana musu magiya, dayan ya rike ta ya kwantar da ita a gurin ya danneta da dukan karfinsa, daman abu ga marar karfi sai ta kaea wani yunkurin kirki sai kuka kawai take, dayan kuma ya dauki gorar ya bude ya saka dayan hannunsa ya matse bakinta ba shiri a dole ta bude bakin saboda azabar matsa da ta ji. Ya zuba mata lemun ta hade dan dolenta sannan ya sake zuba mata wani ta sake hadawa da karfi ya sake zuba mata har sau uku sannan ya sake ta ya mike tsaye da lemun. Wanda ya danneta ya sake ta sai ta fashe da kuka tana kallonsu. Yawu ta fara tofarwa duk da kasancewar bata ji wani canji a cikin lemun ba, lemun mangoro ne bata ji ya canja ba a dandanonsa da kuma kalarsa. Sake nufo ta sukai dayan yana rike da wani bakin kyalle, tana ganin su sake dosota sai ta fashe da wani sabon kuka.
 
“Aa... Aa... Aa.. Dan Allah.... Aa... ”
 
Ba su saurareta ba suka riketa dayan ya daura mata bakin kyallen a ido ya tsuke idon ta yadda ba zata iya gani ba. Sannan dayan ya dauketa suka fice da ita daga dakin zuwa motarsu, tana jin lokacin sa suka saka ta motar suka yi mata key har suka fita daga gidan tana jin komai, sai dai ta yi shiru tana sausaren motar dake tafiya, sai da suka fara nesa sannan ta soma jin jikinta babu karfi wani abu na sauko mata mai kamar bachi kuma ba bashi ba, gaba daya sai ta ji jikinta kamar ba nata ba, babu kuzari ko kadan, a lokacin ne hankalinta ya fada nisan zango, sai ta fara kalaman da bata ma san tana yi ba.
Nisa sukai da ita sosai kamar za su bar garin gusau da ita sai da suka duba inda babu kowa sannan suka faka suka fito da ita suka shigar da ita cikin gonar dake cike da ciyawa suka kwantar da ita, suka cire mata kyalle. Farin mutumen nan ya tsaya daga waje yana tura rubutawa number Kabir sako.
 
_Idan ka ga dama ka zo ka dauki matar dan'uwanka a lalan area, akwai wata gona a gurin ta gafen gonar akwai ciyayi ka duba da kyau zaka ganta, amman ina gargadinka karka kuskura ka fadawa kowa, kuma karka zo da police a nan gurin idan ba haka ba zmgawarta zaka tarar, kuma zaka jeka kanka a matsala_
 
Bayan ya gama rubuta sakon ya tura masa, sannan ya cire line ya saka a bakinsa ya karya shi ya jefar.
 
“Let's go guys”
 
Yana fadar haka sai duk suka nufo motar mai kama da siyana suka shiga daman shi ne mai jan motar sai yai mata key suka kama hanya.
 
 
 
TALBA POV.
 
Yadda ya ga rana haka ya ga dare, banbancin daren da rana a gurinsa dare akwai duhu rana kuma haske ce, kwana yai sallah da karatun kur'ane yana rokon Allah ya bayyana masa Aminatunsa. Sai da asuba ya fita zuwa masallacin dake cikin gidan yai sallah tare da ma'aikatan gidansu da Daddy da kuma Kabir, bayan sun gama suka fito tare da Daddy suna tafiya a hankali Daddy na yi masa kalamai na kwantar da hankali.
 
“In shaa Allah za a ganta, an baza security ko'ina ana bincike yadda ya kamata, kuma kaga ga hotunan nan kace ka saka ga kuma kudin daka saka, a media ma an watsa abun a jarida, za a ganta In Shaa Allah, ko dan gudun tonon asirin ko waye”
 
“Tsoro nake Daddy karsu cutar da ita, ga shi bata dade daga warkewa daga wata damuwar ba ta yan kidnapping yanzu kuma ace ta hadu da wannan Allah kadai ya san wani hali take ciki”
 
Daddy yayi murmushi irin na su na manya ya dafa kafar Talba.
 
“Ka kyautata zato kuma ka yi addu'a, babu abun da zai same ta, yarinya marainiya Allah zai tsirarta ita da yarda Allah”
 
Talba ya daga ma masa kai. Sai da suka isa inda za su rabu sannan Daddy ya ce.
 
“Ya kamata kaje anjima ka duba Leila, ko kuma ka wuce musu da abun karyawa ma idan an gama, na je jiya da rana kuma na koma da dare Momynka ta fada min baka zo ba, nace mata kana tsoro ne kar ta maka fada”
 
“Zan je anjima  In shaa Allah”
 
“Good”
 
Daddy ya fada sannan ya shige part dinsa. Talba kuma ya sauke ajiyar zuciya ya nufi dakinsa yana shiga phone dinsa ce first thing daya fara dauka, sai ya tararda kiran Ali kusan 5, data ya kunna ya shiga social media hoping to see a good news, sai dai har ya gama shawaginsa ya kashe datan be ci karo da inda aka ce masa an ga Aminatu ba, sai dai masu masa repost wasu kuma suna masa addu'a da sharing. Mikewa yai tsaye ya nufi closet dinsa ya cire doguwar jallabiyarsa ya daura tawul ya fito ya nufi bathroom, wanka yai ya fito jiki ba kuzari rabonsa da abinci tun wanda ya ci jiya da safe ban da ruwa babu abun da yake iya ci, ko tea da yake dan sha sai ya ji gaba daya ya fice masa a rai, ga wani zafi zafi da jikinsa yai alamar fever na son kama shi. Karamin tawul ne a hannunsa yana goge jikinsa har ya isa gaban katon madubin dake dakin ya tsaya yana kallon kansa, babu canji a jikinsa shi din nan dai ne, sai dai fuskarsa ta dan fada kamar wanda ya kwana biyu yana ciwo, ga idanuwansa da suka yi ja har yanzu ba su sauya ba farin ya bata. Hakan ya ji baya bukatar shafa komai bayan turaren da ya zame masa rayuwa. Shi kawai ya shafa ya nufi closet din ya saka suit farar riga da bakin wando ya rike jacket din a hannu ya dauki agogonsa ya saka sannan ya saka black cover shoes  ya fito ya dauki turaren tufafi ya fesa ma jikinsa sannan ya dauki wayarsa da wallet dinsa da key mota ya fice domin cika umarnin Daddy.
 
 
 
LEILA POV.
 
A asibitin suka kwana saboda Ali yace a barta ta dan huta in ya so da safe sai ya sallamesu. A dole Momy ta hakura suka kwana a asibitin ta tura Amal gida. Sau biyu Daddy an zuwa dubata, na farkon bayan ya fito daga gurin CP ne ya karaso nan ya dubata a lokacin ma bachi take, bata samu ganinsa. Sai dai Momy ta fada masa komai da Talba yai ban da ita abun da tai ma Talba. A tunaninta Daddy zai nuna bacin ransa ne kan abun da Talba yai sai ta ga tsabanin haka a fuskarsa da kalamansa, sai kokarin wankesa yake a idonta wai kar taga laifinsa, yana cikin rudani a yanzu. Hakan yasa bata sake cewa komai ba ko fitar da yai bata yi masa rakiya ba. Da dare ma ya sake dawowa duba Leila a nan kam ya same ta a farke har yai mata ya jiki ta amsa masa da cewar ta ji sauki. Be yi mata maganar ba gudun kar ya daga mata hankali ita ma Leila bata masa ba, sai dai kana ganinta ka san tana cikin damuwa. Be bar asibitin ba sai da ya tambayi Momy Talba ya zo duba Leila daker ta amsa masa da aa, domin a yanzu ko sunan Talba bata son ji, har Ali da yake abokinsa ya fiye masa shi domin ya nunawa Leila kulawa sosai kamar yar'uwarsa, minti kadan sai ya shigo ya duba lafiyarta. Sai kusan sha daya na dare sannan Momy ta kira Family how dinsu gurin Hajiyarta ta fada musu cewar suna asibiti amman da sauki ba sai sun zo yanzu ba. Hajiya kasa hakura tai sai da aka kawo ta ta duba jikin Leila sannan hankalinta ya kwanta, Momy ta fade mata daga biri har wutsiya na abun da Talba yai, ba laifi ita kan ta ga laifin Talba sosai sai dai tayi ta nanatawa yarta cewar abun da Talba yai ba haramun ba ne. Har guri mota Momy ta rako mahaifiyarta tana kara nuna mata bacin ranta ita kuma tana tausarta.
 
A asibitin Momy ta kwana tare da Leila, Washe gari guraren karfe bakwai Hajiya Saratu kanwar Momy ta doro asibitin cikin wani irin bacin rai da mamakin abun da Talba yai, Momy ta jidadin zuwanta sosai domin ta samu mai kama mata ta yaga. A nan Momy ta baje mata hajar a faifai, wato ta kara fada mata komai bayan wanda mahaifiyarsu ta fada mata. Hajiya Saratu ta daki kirji ta ce.
 
“Dan adam butulu, to Wallahi karki yarda, idan ma kika ce ba zai aureta ba ai ita kika jefa a matsala shi kuma kin ba shi damar yayi rayuwarsa yadda yake so, to ba zata sabu ba bindiga a ruwa, Wallahi Talba be isa ba”
 
Momy ta tabe baki.
 
“Ai ne ya fice min gaba daya”
 
Hajiya Saratu ta ja wani dogon tsaki, tana jin kamar ace Talba yana gabanta ta wanke masa fuska da mari.
 
 
 

 
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
 
*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*
 
 
TALBA POV.
 
Tsaye yai bakin kofar yana jin kamar kar ya shiga. Sai da yaja dogon numfashi ya sauke sannan ya kai hannunsa ya tura kofar dakin ya shiga. Da Momy ya fara hada ido tana ganin shi ne ta dauke kai ta maida wani gafen irin bata ma kaunar ganinsa din nan. Be damu ba ya maida dubansa gurin Leila wanda ta kura masa ido tana ta kallonsa kamar yau ta fara ganinsa. Murya kasa kasa yai sallama daga Hajiya Saratu har Momy aka rasa mai amsa masa, daman ita Leila ba magana take ba sai idan ta kama dole. Karasawa yai kusa da ita ya duka ya aje kwandon dake dauke da ayan abinci.
 
“Ya jikinki?”
 
Da sauri ta Leila ta dauke kai ta juyar zuwa wani gafen tana zuciyarta na mugun kuna kamar ana soyata, wani irin son Talba da kaunarsa ke dibanta, duk yadda take yaki da zuciyarta akansa sai ta kasa samun hadin kanta, a yanzu kam ta gane tana matukar son Talba, domin abun da yai mata ya kai ace ta tsani jin sunansa ma balle ganinsa, amman sai jin take kaunarsa na karuwa a zuciyarta, da ace wani namijin ne yai mata abun da Talba yai mata da tuni ta goge shafinsa a zuciyarta, amman ta kasa komai akan Talba, ko zaginsa da Momy take.bata jindadi a yanzu, balle kuma tai yunkurin cireshi a ranta sai take jin kamar zata rabu da rayuwarta ne. Be damu da kin amsa masa da tai ba ya sake tambayarta.
 
“Zazzabin ya sauka?”
 
Nan ma bata amsa masa ba, daman can idan yan yangarta suka tashi bata amsa masa balle kuma a yanzu da yai mata babban laifi. Hajiya Saratu ta tabe baki.
 
“Kai dan Allah yanzu baka ji kunya ba? Kana tare da yarinya shekara da shekaru sai ka tsallake kaje can wani guri ka auri wata, wai kuma har ka iya zuwa kana zargin Leila da sace yarinyar, yanzu duk abun da Yaya Amina tai maka ka manta kenan har na iya zagayawa ka munafunceta ka ci amanarta”
 
Ko da wasa be kalli inda Hajiya

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login