Showing 306001 words to 309000 words out of 332834 words

Chapter 103 - Bakar wasika Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

65569

ce ta saka a sace Aminatu... Saboda tana sonka”
 
Tsanananin mamaki ya saka Talba tsayawa kamar hoto yana kallon Ali ko yatsansa ya kasa motasawa, har na tsawon dakika ashirin sannan ya runtse ido ya matse su sosai.
 
“Wow.... ”
 
“Ko a kotu ba za a yankewa Leila hukuncin kisa ba, domin ba da ganganci ta aikata ba, kuma ta yi nadama”
 
Talba ta bude ido cikin wani irin bacin rai da be taba sanin yana da shi ba.
 
“Ta turo tsohuwar mutane daga sama zuwa kasa, ka kira hakan da kuskure? Ta kyale iyalan matar nan suna ta wahala da nemanta na dare ba rana ka kira hakan da kuskure? Ta dauki gawa su je su binne ta ta dawo ta musa cewar ta aikata hakan kuma ka kira haka da kuskure? Da ace Madina bata yi mata haka ba kana tunanin zata bayyana gaskiya ne? Wanda yai nadamar aikata abun yana fitowa ya nunawa duniya nadamarsa ne, kuma ya karbi hukuncin da za ayi masa ba ya boye gaskiya ba, after that Leila ta sake buga kan Aminatu still kana kiran hakan da kuskure? Ta yi nadama? And you expected me na goya mata baya mu rufe wannan sirrin?”
 
Ali ta ji kamar ya daki Talba, cikin fada ya ce.
 
“Baka taba iya daga mata kafa, baka tana shiga side dinta saboda magancs mata matsalarta, tabbatar da Aminatu ce zaka daga mata kafa ka nuna mata abun da ta aikata kuskure har ma ka sama mata mafita, but you can't do this for Leila even for once!”
 
“Yes i can't do that to her because you love her!”
 
Talba ya fada masa kai tsaye, yana kallonsa kamar yadda Ali ma yake kallonsa irin kai tsaye ni tsaye. Talba ya bude motar ya fita tare da buga ganbun motar da mugun karfi kamar zai ballashi.
 
 
  
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
 
Ali ya bude motar ya fita da sauri ya sha gaban Talba. Sai ta Talba ya kauce ba tare da ya kalleshi ba ya cigaba da tafiyarsa, Ali ga juya ya kalleshi yana fadin.
 
“You can't face her with this face Talba, you can't, ba zaka iya ruguza farincikin Momy ba, macen da ta dauke ka kamar danta, matar da ta raine ka ka girma a hannunta, ka fi kowa sanin yadda take son Leila ba zaka jawa yarta zuwa gidan yari ba, ba zaka saka mata da wannan ba, and Leila ma bata maka komai ba, bata nuna maka komai ba sai kauna, bata cancancin wannan daga gareka ba, and ba zaka iya sakawa Daddy da wannan ba, you can't do this Talba, you can't... Idan ka zama silar kai Leila gidan ka so Daddy ba zai manta da wannan ciwon ba”
 
Tun da ya fara maganar Talba ya tsaya cak yana saurarensa har sai da ya gama sannan ya cigaba da tafiyarsa ba tare daya juyo ba. A ka'ida idan tafiya ta kama shi a wani gurin direban gidansu yake kira ya zo ya dauke shi, sai dai wannan karon abun hawa ya tara ya hau ya kai har bakin gate din gidan. Knocking yai aka bude masa sai ya saka mai gadin gidan ya sallami mai achaban sannan ya shiga cikin gidan, kallo daya yai ma part din Momy ya dauke idonta ya nufi bangarensa, tura kofar dakin yai ya shiga, sai ya nufi bakin gadonsa ya zauna ya dafe kansa, ba abun da Leila tai yafi ba shi mamaki ba, na Madina ne, domin be taba tsammanin haka daga gareta ba, ko kadan be taba kawowa ransa cewar Madina zata iya aikata wannan abun ba, and he can't believe Ali yana son Talba all this while, sai a yanzu yake fahimtar dalilinsa na bawa Leila gaskiya a ko da yaushe. Ya busar da iskar bakinsa ya mike tsaye ya nufi bandakinsa sai da ya raba jikinsa da tufafi sannan ya sakarwa kansa ruwa ya lumshe ido yana sauraren yadda ruwan ke dukan kansa, zuciyarsa na wani irin zafi kamar ana soyata. Be san ya zai yi ba, zai fuskanci Daddy ne da maganar abun da Leila tai? Ko kuma na Madina? Ko kuma zai rufe duka maganar biyu ne? No taya za'ayi maka sata ka kama wanda yai maka satar sannan ka bar shi ya tafi ba tare da ka hukunta shi. Ya dade a tsaye jikin shower sannan ya fara murza sabulu ya wanke jikinsa ya daura tawul ya fito rike da karamin tawul yana goge jikinsa. Gaban madubi ya zo ya tsaya yana kallon kasan. Jin an taba kofar dakin ya saka shi juyowa sai yai arba da Kabir dake rike da wayarsa.
 
“Na kira Ali yace min ka dawo gida”
 
Talba ya kalleshi kawai ya dauke kai ba tare da yace komai ba. Hakan ya saka Kabir tunanin wata kila abun da Momy ta fada masa ta yi ma Talba ne ya saka shi damuwa. Zuwa yai ya zauna saman gadon Talba
 
“Don't tell me abun da Momy tai maka ne ya saka ka damuwa?”
 
Talba ya sake kallonsa a karo na biyu yana tunanin abun da Momy tai masa domin shi har ya manta.
 
“Look, ni da kai fa mun san halin Momy, be kamata mu rika damuwa da abun da take yi ba, i know ba dadi ace maifiyarka bata son matarka, kuma ta nuna maka a fili har ta musguna mata, domin ni ma na san ba lalle ne yarinyar nake hari Momy ta so ta ba, idan ma ta amincen min na aureta kenan”
 
Talba ya zauna kusa da shi yana kallon wani bangaren na dakin.
 
“Ba abun da Momy tai ya bata min rai ba, na manta da wannan”
 
Da mamaki Kabir yake kallonsa.
 
“Me ke damunka?”
 
Talba yayi shiru kamar ba zai ce komai ba, wanda hakan ya bawa Kabir damar karantar damuwar dake fuskarsa.
 
“Akan Momy ne ko Leila ko Daddy?”
 
“Idan na fada maka cewar Madina ce ta saka aka sace Aminatu zaka yarda?”
 
“Aa me zai saka tai yi haka?”
 
“Shi ne abunda nake ta tunani, soyayya ta iya ta saka ka cutar da wani”
 
Kabir ya nuna da alamar rashin yarda.
 
“Don't tell me Madina son ka take yi?”
 
“Yes, saboda hakan ta saka aka dauke Aminatu?”
 
Kabir ya mike tsaye da sauri.
 
“What...? Taya akai ka sani? Waya fada maka?”
 
Talba ya kalleshi.
 
“Ali”
 
“Ya akai ya sani?”
 
“Saboda ya bugi cikinta ne”
 
“Wane irin kalar bugun ciki? Ban gane wannan maganar ba how?”
 
Talba ya sauke ajiyar zuciya, ya mike tsayen.
 
“Ban canja saka kaya yanzu, idan na fito anjima zamu yi magana”
 
“No please wannan ba maganar anjima ko gobe ce ba, shiyasa ta bada number ta? So that ka zarge ni da sace ta? Daman na dade ina zargin cewa na gida ne kawai zai iya wannan abun”
 
Ya juya ya juyo yana ta mamaki har da rike habarsa.
 
“Na kasa yardar da wannan Wallahi?”
 
“No nima yanzu na sani, kuma ina tunanin barin maganar saboda da wani dalili but sometimes ina jin kamar ba zan iya runtse ido na toshe kunne kamar ba zan ji komai ba”
 
“Wait saboda tana kawar Leila zaka kyaleta? Ko kuma kana zargin da hannun Leila a maganar ne?”
 
“Babu hannun Leila kuma ba dan tana kawar Leila zan kyaleta ba”
 
Da mamaki Kabir yake kallonsa.
 
“No please karka ma kawo wani excuse, idan ma kana ganin kamar baka da evidence ne ita da kanta zata sama mana evidence ai, idan ta ji wahala zata fadi mutanen da ta saka sukai wannan aikin”
 
“No...”
 
Talba be fadi abun da zai fada ba, Kabir ya daga masa hannu.
 
“Ya kake abu kamar ba kai ba, ka manta kalaman da kai cewar sai ka hukunta wanda ya aikata mata haka? Kyaleta kamar wawanci ne, kuma ka bata damar da zata sake yin wani abun, abu na biyu wannan abun ba kai kadai ya shafa ba, ni ma ya shafe ni”
 
Kabir na fadar hakan ya juya ya fice daga dakin cikin bacin rai. Talba ya busar da iskar bakinsa, ba wai baya son hukunta Madina ba ne, sai dai baya son rushe farincikin Momy kamar Ali ya fada, kuma ba Leila kadai za a kama ba, kamar yadda ba ita kadai za a hukunta ba, har da Momy, ya Daddy zai ji? Ace matarsa da yarsa sun aikata babban laifi kamar wannan? Shin zai ba sirrin ya kasance a rufe ne, ko kuma zai dauki wani mataki? Har ya saka tufafinsa ya fesa turare be raba dayan biyu ba.
 
 
Kabir na fitowa bangarensu ya kira Daddy a waya ya fada masa abun da ke faruwa, sannan ya karasa bangaren Momy rai a bace jikinsa har rawa yake, kamin a bude masa kofar falon ya danna door bell din yafi a kirga. Da sauri Amal ta bude masa, ya shiga cikin falon ya doshi inda Momy take zaune saman couch Leila na kokarin mika mata kofin tea yana fadin.
 
“Momy kin ji wani abu? Wai Madina ce ta saka aka sace yarinyar nan saboda tana son Talba”
 
Leila bata san lokacin da ta saki kofin shayin ba, ya fadi kasa ya fashe Momy kuma ta kalleshi cike da tashin hankali, Amal kuma ta karaso kusa da su da sauri tana zaro ido tare da saka hannunta ta rufe bakinta.
 
“A ina ka samu wannan labarin?”
 
“Yanzu Talba yake fada min”
 
“Ta ina Talba ya ji?”
 
“Gurin Ali”
 
“Shi Alin ta ina ya ji?”
 
Kabir ya daga kafadunsa, alamar be sani ba. Sai Momy ta kalli Leila ta daka mata tsawa.
 
“Ya akai Ali ya sani?”
 
Kallon mamaki Kabir yake musu.
 
“That's means kun sani kenan?”
 
Momy ta mike tsaye tana amsawa Kabir.
 
“Yes, amman na bar maganar saboda tunuwar asirin Madina yana nufin na Leila, ina fatar ka gane, saboda hakan dole ne ka rufe bakinka”
 
“Taya abun da Madina ta aikata zai shafi Leila? A tare suka aikata ne? Ko kuma da hadin bakinta aka aikata?”
 
“Babu ko daya, amman bayyanar sirrin Madina cewar ita ta saka a dauke Aminatu shi ne bayyanar sirrin yar'uwarka cewar ta kashe Baaba”
 
Da wani irin karfin murya Momy take magana da Kabir, murya dake bayyana bacin ranta karara. Sannan ta nufi kofar fita kanta babu ko dankwali ta bude kofar ta fita, Kabir da Amal suka bita da kallo, ban da Leila da ta kasa yin kwakkwaran motsi sai hawaye take kuma ta ki ta yarda ta daga kai ta kalli kowa. Zaunawa Kabir yai kusa da inda Momy ta tashi ya dafe kansa yana tunanin maganar Momy, domin har yanzu be gano ta inda tonun asirin Leila ya shafi Madina ba. Tafiya Leila ta fara yi kafafuwanta na hadewa kamar mai koyon tafiyar, ta fice daga falon ta bi bayan Momy.
 
Kai tsaye Momy bangaren Talba ta nufa, kamar zata balla kofar dakin haka ta tura kofar da karfi ta shiga ciki, Talba dake tsaye yana kokarin saura agogon hannunsa ya juyo ya kalleta, sai ta maida kofar ta rufe kana ta juyo ta kalleshi da wani irin duba dake nuna ko kasheshi zata iya a halin da take ciki a yanzu.
 
“Iyakarta ka ce ka fasa auren Leila, ko kuma ka koma kana yi mata wani kallo na dabam, wata kila musgunawar da kake mata ta karu, amman ba zan tana yarda ka bude wannan sirrin ba, ko da sama da kasa za su hade ba zan aminta a hukunta Madina ba, ba kuma zan bari ka fadawa police komai a kai ba, indai na isa da kai, kuma rainon da nai maka baka dauke shi a banza ba, kuma baka son bacin raina to kabar maganar nan a cikinka Talba! Karka kuskura kace zaka hukunta Madina”
 
Hankali kwance Talba yake kallon Momy.
 
“Saboda kina tsoron kar Madina ta fadawa yan sanda cewar Leila ta kashe Baaba?”
 
Kusan suma Momy ta yi, domin ko kadan tunaninta be kawo mata cewar Talba ya san da wannan maganar ba.
 
“Ba zan bari maganar ta fita Momy, ba dan saboda kowa ba sai dan saboda ke, idan aka ce za a hukunta Leila na san zaki damu, kuma damuwarki zata haifar min da damuwa, amman idan aka ce za a hukunta ki, ban san iya halin da zan shiga ba, ba zan iya jure wani abu ya same ki ba Momy”
 
Ganin hawaye ya cika idonsa ya saka ta tako a hankali ta karaso inda yake, sai kuma ta rasa kalma fada masa, she seat there helpless gaba daya ma ta rasa tunanin da zata yi, jikinta yayi sanyi sosai. Talba ya zauna a kasa ya dora kansa saman cinyarta.
 
“Ina son ki Momy, na bude ido dake, kin min gata kin nuna min soyayya, tun da na bude ido ban san wata uwa ba bayan ke, ko da aiki aka dauke ki a gidan nan na kula da ni, kin cancanci na girmamaki na mutuntaki na karramaki, kuma na nema miki farin ciki a duk inda yake, saboda na girma a hannunki, balle kuma ace kin rike ni a matsayin da, kin rainene har na girma na mallaki hankalin kaina”
 
Ta lumshe ido hawayen da suka zubo mata suka sauka saman kansa, na shi kuma suna sauka a cinyarta, fashewa Momy tai da kuka mai karfi kamar ba ita ba, sai Talba ya dago ya kalleta, Leila kuma dake labe jikin kofar ta turo kofar dakin ta shigo fuskarta da hawaye shabe shabe, ta tako ta shigo cikin dakin.
 
“Na rusa farincikin mutane da dama, bana tunani mai kyau wani lokacin, bana iya yin komai a natse, zuciyata tana saka ni aikata ta abubuwa sai daga baya na dawo ina nadama”
 
Ganinta ya saka Momy ta yanke kukanta a take ta kalleta. Talba ma dagowa yai ya kalleta sai ya mike tsaye yana jin kamar ya saka bindiga ya halbeta.
 
“Kamin ki aikata hakan ya kamata ki yi wannan tunani ba bayan kin aikata ba, kin bata Komai Leila, saboda son zuciya da nuna isa, kowa wulakantattace ne a gurinki, idan zuciyarki ta raya miki abu baki iya hanata sai kin aikata, saboda muguwar zuciyarki da baki iya controlling kika jefa kanki cikin fitina kika jefa Momy da ni, kuma kika jefa iyalan matar nan cikin tunani da zullumi, and i know wata rana gaskiya zata bayyana domin karya fure take bata yaya, kuma duk ranar da gaskiya ta bayyana duniya Daddy zata zarga, za ace matarsa ta boye gawar yar aikinsu a gidan gonarta, mutane da yawa za su ce tsafi akai da ita, ba kowa zai kyautata mana zato ba, all this because of you LEILA”
 
Ya karasa yana furta sunanta a fusace in capital letters, jijiyar wuyansa har tashi take saboda bacin rai. Ba karamin razana tai ba kamin yadda Talba ya taso mata kamar zai dake ta, da sauri tai baya baya.
 
“Wata kila zan iya gyara komai...”
 
Bata karasa ba ya isa gurinta ta rika kafadarta duka biyu da hannayensa yana girgiza zata.
 
“Ta ya? Ta  ya...? Wannan maganar b zata fita ba Leila, ba zaki cusa bakinciki a zuciyar Daddy ba, wannan da kika mana ya wadatar”
 
Momy ta yi saurin karaso gurin ta fisge hannayen Talba ta raba jikin Leila ta hannayensa sannan ta shiga tsakiya tana girgiza masa kai.
 
“Talba... Ya isa... Baka san ya take ji ba.. Ni ma ina ji na a wani yanayi balle kuma ita, don't hurt her please”
 
Ta karasa muryarsa na fita slowly. Talba ya kalleta with angry face.
 
“I hate you”
 
Ya furta, hakoransa na sama suna haduwa dana kasa tsabar bacin rai.
 
“I'm sorry, I'm sorry... I'm sorry...i know this is not easy... I'm sorry ”
 
Ta fada sannan ta juya tana fice daga dakin tana tafiya kamar bata son motsa kafafuwanta, Momy ta rufa mata baya. Talba ya nufi inda yake aje keys din motarsa ya dauka ya fito daga dakin yana jin gidan gaba daya ya fice masa a rai. Yana fitowa ya nufi motarsa ya bude da zimmar shiga heading to gidan Marayu sai gashi an bude gate din Motar Daddy ta kunno kai.
 
 
BATURIYA POV.
 
Tana zaune dakinsu saman prayer mat hannunta rike da carbi tana ja, bakinta kumshe da addu'o'i kala kala, ita kanta bata san ta iya tasbihin da hailala da kyau ba irin yau. Ji take kamar ta runtse ido ta bude ta ji zuciyarta wasai babu son Fahat kuma babu sanin Faruk a cikinta. Tun jiya da abun ya same ta ta saka magana da kowa ta maida lamarinta ga Allah tana ta fada masa bukatarta tare da jero masa matsalolinta da fatar zai mata magani. Tun da take a rayuwarta bata san wani dare da ta taba tsayawa ta hana idonta bachi saboda neman biyan bukata ko kuma kai kukanta ga Allah ba irin wannan. Tsakanin jiya zuwa yau ta yi rama kamar wanda ta kwanta ciwo, daman can ba jikin ne da ita ba ga kuma damuwar Fahat da ta fara yi mata sannu sannu, sai dai bata taba rama da jin tashin hankali irin na jiya ba. Har yanzu wani abun ganinsa take kamar mafarki. Umma ce ta shigo dakin rike da kofin fura da aka dama da kankara ta aje mata kusa da ita sannan ta zauna.
 
“Ga fura na dama miki idan zaki iya sha, tun da komai aka baki ba iya ci kike ba”
 
Ta kalli furar.
 
“Na gode”
 
Sannan ta cigaba da jan carbi. Umma ta ce.
 
“Tun jiya nake son magana da ke, sai dai ganin kina cikin damuwa ya saka ban takura miki ba”
 
Ta dan kalli Umma kadan.
 
“Jiya na ji kina maganar Ramlee, har kina cewa ta cucece, Rafi'a miya hada ki da Ramlee? Yarinyar da aka hana ki abota da ita tun kina makaranta? Kuma har yanzu

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login