Showing 261001 words to 264000 words out of 332834 words
ba a rasa ba, daman can damuwa ce da rashin abinci mai kyau, yanzu kuma Alhamdulillah”
Mama ta fada tana dariya, shi ma dariyar yai ya kalli Ramla data shigo rike da kula dayan hannunta kuma rike da jup.
“Salamu Alaikum”
Mama ta amsa mata tana murmushi, Faruk ma murmushin yake amman be amsa mata ba. Dukawa tai gaban Mama ta aje kofin tana murmushi.
“Daman na ce yanzu kin isa karyawa, shiyasa soya miki kayan fulawa, na miki lemun kwakwa”
“Maa Shaa Allah, har da saka kanki a wahala haka”
“Ba komai Wallahi, ya jikin na ki?”
“Alhamdulillah”
Faruk kam kallonta yake da mamaki. Ta juya ta kalleshi.
“Ban san ko kana son snacks, even though ba kai na yi ma ba, i did it for Mama amman zata iya sammaka”
Ya dan yi murmushi ya girgiza mata kai.
“No, thank you”
Ta dauki plate din data gani a gurin ta zubawa Mama snack din sannan ta matsar mata da jup din lemun kwakwa hadin gida da tai mata, sannan ta dauki daya ta mikawa Sultan.
“Gashi ka ci, ya ma sunanka?”
“Sultan”
Ya amsa mata yana mika hannu ya karba. Murmushi ta sakar masa sannan ta juya ta kalli Mama.
“An yi hoton?”
“Eh an yi hoto an gwada jini, likita yace komai zai koma daidai da yardar Allah”
“Allah ya kara lafiya, yau ina Rukaiyah?”
“Ta tafi gida, a nan ta kwana shiyasa sai nace ta je ta yi wanka ta kimtsa mana gidan”
“Okay, bari na koma gurin aikina”
“Okay Allah ya taimaka, ba yanzu zaki wuce da kwanukan ba?”
“Aa sai gobe, Sultan ko zaka zo muje”
“No fita zamu yi da shi yanzu”
Faruk ya amsa da sauri yana kama hannun Sultan, sai ta kalleshi. Ganin yanayinsa ya dan canja ya saka ta jin wani iri.
“Okay”
Ta nufi kofa ta bude ta fice. Mama ta yi murmushi.
“Yarinyar tana da kirki, kuma ina ganin kamar duk saboda kai take wannan abun”
“Ta kuwa yi a banza, ni ma na fahimci haka ai yanzu, in ba shi ba miya kawo snacks”
Mama ta yi murmushi tana karo na biyu.
“Kar dai ka ce zaka watsa mata masa a ido, ba dai wani abu ta gani ko ta ji balle ka ce”
“Mama haka suke fa, kin manta Rafi'a ita ai bayan aure ne ta tsiri wannan halin, balle wannan mai rawar kan tsiya”
“Kurciya, kana ganinta ai kasan Rukaiya ta girme ta, wannan ai ba zata wuce 20 ba Idan ta yi da 21, ban jidadi da kaki karba ba, kuma ka hanata tafiya da Sultan”
“Idan ban mata haka ba, gaba zata iya wuce gona da iri, kara dai a tsaya baki nan”
“Zan je na yi magana da abokina Shamsu na ji yadda zamu yi, maganar gidan ina son na siye na miliyan biyu, ni motar ma bata dame ni ba zan iya bari sai nan gaba”
“To ba zan hana ka ba, amman dai abun hawa yana da dadi ko da babur ne ka siye”
“In Shaa Allah”
Ya rika hannun Sultan.
“Sultan zaka zauna a nan ko tare zamu tafi”
“Tare zamu tafi ba zan zauna a nan ba”
Mama ta yi murmushi.
“Mama akwai abun da kike bukata?”
“Aa Alhamdulillah bana bukatar komai a yanzu”
“To sai mun dawo”
“Allah ya tsare”
“Ameen”
Ya ja hannun dansa Sultan suka fice daga dakin. Yana fita asibitin ya nufi gurin sana'ar abokinsa Shamsu, sai da suka gaisa sannan ya gabatar masa da abun da yake tafe da shi. Da mugun mamaki Shamsu yake kallonsa.
“Ashe dai da gaske ne ana samu kudin nan da ake fada, Allah mai iko kuma mai yadda ya so, kai kam Allah ya yaye maka matsala Faruk”
Faruk yayi dariya.
“Ya dai ba ni, amman yayi matsala gaba daya ai ba ta yiyuwa, dan'adam kullum a cikin jarabawa yake”
“Haka ne, amman kai kam ai kakarka ta yanke saka, yanzu Zinarin yana ina?”
“Yana can gida”
“To amman kasan mai siyen zinarin ne mai tsaye”
“Eh akwai wani can da muka hadu da shi Nijar dan garin nan shi haka yake, idan ya samu sai ya zo nan garin ya saida ma masu siya ya fada min ai nan sun fi tsada sama da can, ya bani number mutumen yace idan na zo nan na kira shi na masa bayani zai siya, domin ya kira shi tun can nijar din ya fada masa sunana kuma ya fada masa cewar zan kawo masa zinarin”
“To ai kamata yai kai hanzarin kai masa, ku yi cikini amman fa ya saka maka kudinka account dinka na banki domin aje kudi a gida yanzu yana da wahala”
“Haka nake so, a account din ma ba dadewa nake son su yi ba, shiyasa na same ka da wannan maganar gida nake so mai kyau kamar na miliyan biyu haka so that ina siyar da zinarin zan siye gidan”
“Siyen gida yanzu ai ba shi da wahala indai ga kudi, zan yi magana da dillalin unguwarmu na fada masa, Allah ya tsare ya saka albarka Faruk muma kuma Allah yai mana wata hanyar, abu kamar wasa ya zama gaske, wai kai ne yau da siyen gidan miliyan biyu, har yanzu fa ina kallon lokacin da ka zo kace min zaka yi sana'ar ginin nan da muke”
Faruk yayi murmushi.
“Ko yanzu ai, sana'ar zan yi saboda aikin ya zama sai godiyar Allah”
“Ko da aikin ma zaka iya sana'a ai tun da aikin nigeria yanzu sai a hankali”
“Wallahi, kasar ce sai kasheta ake kara yi”
Sai kusan azahar ya bar gurin bayan ya bawa Shamsu 5k. Asibitin ya koma bakin gate aka sauke shi ya dauki dansa suka shiga cikin asbitin, kamin su karasa ya ciro wayarsa ya shiga neman number mutumen ya kira shi, wayar na daf da tsinkewa yai picking sai Faruk yai masa sallama yana kara gyara natsuwarsa saboda wanda ya bashi number ya fada masa cewar Babban mutum ne.
“Wa'alaikumussalam”
“Ranka ya dade sunan Faruk, kwanakin baya Ayuba ya kiraka akan maganar siyen zinari har ya bani kai muka gaisa, lokacin ina nijar na fada maka idan na dawo zan kawo maka zinarin ka siya”
Alhajin ya dan yi shiru yana nazari kamin ya ce.
“Oh an yi haka, ka dawo ne yanzu?”
“Eh na dawo, shi ne nake son na ji ranar da kake free sai na kawo maka Zinari na gani”
“Kullum ai ina free indai akan sana'ata ne, zaka iya zuwa gidana yanzu ka same ne zinarin yana tare da kai?”
“Aa yana gida, amman zan iya zuwa na dauko sai na kawo mana”
“Zai kai na nawa?”
Faruk ya juya ya kalli dama da hagu domin ya tabbatar babu mai jinsa sannan ya ce.
“To a yadda aka kiyasta dai zai kai na miliyan shida”
“Okay ba mai yawa ba ne, zaka iya zuwa gida ka kawo min”
“Amman ban san gidan naka ba ranka ya dade”
“Kasan Million quarters?”
“Eh na san gurin”
“Idan ka zo a aje unguwar ka tambaya gidan Alhaji Isma'el Zabarma”
“To ranka ya dade gani nan zuwa yanzu nan”
Ya kashe wayar yana jindadi ya yaba yadda Alhaji yake amsa masa. Cira kafa yai ya karasa cikin asibitin da kuzarin, kai tsaye ya nufi inda Mama take. Zaune ya same ta a dakin tare da Rukaiya da wata kawar Rukaiya suna hira. Sai da ya amsa gaisuwar da Rukaiya take masa da kawarta sannan ya kara kusa da Mama murya kasa kasa ya fada mata yadda sukai da Alhaji.
“Zan je gida na dauko sai na kai masa”
“To Allah ya tsare, ayi addu'a dai”
“Inshallah”
Ya amsa sannan ya saki hannu Sultan.
“Sultan ka zauna gurin Mama zan je na dawo”
“Aa Dady”
“Ba dade zan yi ba zan dawo yanzu nan, na maka alkawari”
“Idan baka dawo ba zan ta yi maka kuka”
“Na yarda”
Sai Sultan din ya nufi gurin Rukaiya yana bata fuska yana son yin kuka, Rukaiya ta dauke shi ta dora saman cinyarta tana rarrashinsa. Faruk har ya juya zai fice Mama ta kira shi ya dawo.
“Kai kadai zaka je? Ba zaka nemi wani ya raka ka ba? Karbar kudi haka mai yawa Faruk?”
“Babu abun da zai faru da yardar Allah, ai ba a hannu zan riko kudin ba a account za a saka min, kuma yanzu kowa ai ba abun yardar ba ne akan kudi, kara ma kasan kai kadai ka tafi”
“To Allah ya tsare”
“Ameen”
Ya amsa sannan ya juya ya bude kofar ya fita, sauri ya fara yi gudun kar ya batawa Alhaji lokaci. Yana kawowa karshen ward din suka kusa cin karo da Ramla dake cikin shirinta na barin asibitin.
“Wannan saurin duk na minene?”
Ya kalleta sai dai be ce mata komai ba, ya wuce ta fuska ba yabo ba fallasa. Juyawa tai fa bishi da kallo har sai da ta daina hangoshi sannan ta juyo ta cigaba da tafiyarta. Dakin da Mama take ta shiga ta dubata, sannan ta kalli Rukaiya ta ce.
“Dazun nake tambayarki aka ce min kin tafi gida wanka, yanzu kuma na hadu da yayanki yana ta sauri kamar zai hade kafa, na dauka ma ko ciwon Mama ne ya tashi”
“Aa jikin Mama yanzu yayi sauki gaskiya, akwai dai inda zai je”
Rukaiya ta fada tana murmushi.
“Aiki? Ko yana duty Rana ne? Mu gashi yanzu zamu tashi”
“Aa wani abun ne dai ya taso, ai Yaya baya aikin yanzu”
Mama ta dan harari Rukaiya kasa kasa tana jin haushin yadda ta saki magana haka. Ramla ta ce
“Saboda me?”
“Aikin ne be fito ba tukuna, amman muna nan muna ta addu'a”
Wannan karon Mama ce ta amsa mata, sai tai murmushi.
“Kuma yayi karatu ko?”
“Yayi karatu aikin dai ne har yanzu, kin san kasar nan aiki ma yanzu sai kana da gata”
“Haka ne gaskiya, Allah ya kawo babban rabo”
Sai duk suka amsa da amin.
_______________________________
Hmmm idan kaga anzudda Miya to cinikin tuwo yakare.Kowa yace wutar Kara ta kwana to shine baiyi bacciba.Arashin Kira Karen Bebe ya Bata.Ina ma,abuta son gyara Manyan Mata idan nace mata Ina nufin wadanda suka San ciwon kansu sukasan darajar gyara da mutuncin da yake kankarowa👌to kuzu kumatso kusa taku dai dindaice Yar Gidan maifata Yar mutan Zamfara tazomaku da kalar nata ingantattu km gangariyar kayan gyara wadanda suka gwada sungani km sun sani wadanda km Basu gwadaba karkubari abaku labari kayan Basu bukatar dogon biyani sai dai gawadanda Basu sanmuba kayane kala kala iri daban daban, amma munhi gwanewa wurin gyaran matsaloli irin na aure da km gyaran amare da tsofi masu son tada komada Kai abundai sai Wanda ya gwada Don neman Karin bayani ko walwale rashin fahimta za'a iya tuntubata a number waya kamar haka 08169311410 ko km chat 09029891757 Ko km a address Dina dake Nasarawa Gusau wurin masallacin Mai solar Allah yasadamu da alkhairansa🤝🙏🤲
Sai da ya je gida ya dauko zinarin zan dake cikin wata jaka ta ratayawa irin ta maza, sannan ya tari wani mai achaba ya fada masa inda zai kai shi. Suna isa cikin unguwar ya tambaya gidan Alhaji Isma'el Zabarma sai aka nuna masa, mai achaba sauke shi ko'ina ba sai bakin gate din gidan. Hannu ya saka aljihu ya ciro dari biyar ya mikawa mai achaban ya cire kudinsa ya bashi canji. Gaban gidan Faruk ya tsaya yana kallon ikon Allah, wai duk wannan katon gidan da gate dinsa ma abun kallo ne, gidan mutum daya ne.
‘Wasu na tara dukiya kamar ba a mutuwa’
Ya fada a ransa sannan ya karasa gurin gate din ya gaisa da masu gadin dake gurin.
“Dan Allah nan ne gidan Alhaji Isma'el Zabarma?”
“Eh nan ne, waye kai?”
“Mun yi waya da shi yace min na zo na same shi a gidansa”
“To ka kira wayar ka fada masa kana waje, ya aiko a shigo da kai”
“Okay”
Faruk ya ciro wayarsa yai dialing number Alhaji, wannan karon sai da ya jera masa kusan miss calls uku ana hudu ya dauka.
“Salamu Alaikum ranka ya dade gani kofar gidan”
“Kai wa?”
“Faruk wanda muka yi waya da kai yanzu ka ce na zo na same ka gida akan maganar zinari”
“Okay Haka haka, ka tambaya ina Usman ka mika masa wayar”
“Okay. Wai waye Usman?”
Faruk ya tambaya ba tare da ya sauke wayar ba, daya daga cikin mazan da suke zaune a gurin ya mike tsaye ta sauri yana fadin.
“Gani nan”
Faruk ya mika masa wayar. Sai ya karba ya kai kunnesa.
“Ranka ya dade Usman ne”
“Usman a shigo da mutumen nan, a me yake?”
“A kafa ya zo ranka ya dade”
“To a shigo da shi karamin falon baki, ace masa ya jira ni”
“To ranka ya dade”
Ya kashe wayar ya mikawa Faruk.
“Biyo ni muje”
Ya bude karamar kofar gate din, Faruk ya bi bayansa suka shiga cikin gidan, Faruk sai rabon ido yake yana mamaki ace gida mai kyau kamar wannan na mutum daya ne, gida kamar na minister, ko da yake ba abun mamaki ba ne, domin masu sana'ar zinari suna da kudi sosai, su da suke ganowa ma sukai kudi balle manyan dilolin dake siye su siyar. Ko rabin gidan ba su ba aka bude katon gate din wata hadaddiyar mota ta kunno kai a cikin gida, ta doshi filin da aka tana da domin aje motoci ta faka, sau daya Faruk ya kalli motar ya dauke kai yana basarwa kar a ce masa bakauye.
“Abban Sultan mi ka zo yi gidanmu”
Ba a saba kiran da sunan ba, sai dai jin an fadi Sultan din kuma ance me ka zo yi gidan mu ya bayyana masa cewar da shi ake. Hakan yasa ya juyo ya kalli inda detection din motar yake, sai yai arba da Ramla sanye da uniform dinta na ma'aikatan jinya wato Nurse, fuska da annashuwa kamar kullum.
“Gidanku?”
Ya fada yana nuna ta da mamaki, sai ta gyada masa kai tana murmushi daya zame mata al'ada domin abu ne mai wahala kai arba da fuskar Ramla bata sammaka murmushin da take rabo ba.
“Yes”
“Hajiya Ramla sannu da zuwa”
Usman ya fada, sai ta amsa masa tana doso inda suke rike da jakarta.
“Yauwa Usman, ina zaka kai shi?”
“Alhaji ne ya ce a shigo da shi”
“Je ka zan shiga da shi”
“To ranki ya dade”
Usman din ya juya ya koma inda ya fito, ita kuma ta karasa kusa da Faruk tana murmushi dimple dinta har lutsawa suke.
“Daman saurin da kake ta yi nan zaka zo?”
Ya dan yi kamar ba zai amsa mata ba.
“Eh, da gaske nan gidanku ne?”
“Na yi kama wanda zata iya maka karya?”
“Aa kin dai fi kama da wadanda za su iya yin zolaya”
Ta fadada murmushinta, sannan ta nufi hanyar part din Mahaifinta.
“Biyo ni muje”
A tare suka jera suna tafiya, har suka isa bangaren. Hannu ta kai ta tura kofar ta bude masa.
“Bismillah”
Sai da ya fara shiga sannan ta bi bayansa, yana shiga sanyin ac da wani turaren wuta mai matukar dadi yai masa lale marhabun. Ta cire karamin Hijab din da yake kanta ta goge one seater ta sofa.
“Zo nan ka zauna”
Sai da ya kalli gashin kanta da tai parking ya sauko har bayanta, sannan ya nufi kujerar ya zauna.
“Kalli can”
Ta nuna masa katon hotonta tare da mahaifinta dake tsaye a cikin katon parlor dake cike da kayan alatu na kawata falo.
“Yanzu ka yarda ni ba makaryaciya ba ce ko?”
“Daman ban ce karya kike ba ai”
Ta yi murmushi mai sauti.
“Bari na kira maka Babana idan ba haka ba, sai ya manta da kai ya fita ya barka a cikin gidan kana jiransa”
Ta mike tsaye ta nufi wata katuwar kofa dake dayan bangaren, a lokacin data shiga bata rufe kofar ba, hakan ta bawa Faruk damar hango wani falo dake gurin a tunaninsa daki zata shiga ashe nan ma wani falon da ya ci uban wannan da kyau, ta cikin falon ya hango yadda take taka stairs ta haye sama. Sannan ya dauke idonsa yana ta mamakin ace gidansu ne, sake maida dubansa yai gurin hoton yana kallo kamar mai kwankwanto.
LEILA POV.
Haushin abun da Madina ta fada mata na cewar ta fasa auren Talba a karan kanta ne ya bata haushi har ta yanke wayar ta sauke tana jan saki. Juyowar da zata yi sai tai arba da wata mata ta doso inda take tsaye tana sanye da uniform din masu shara. Kallonta Leila take har ta karaso kusa da ita.
“Dan Allah ke ce Leila?”
“Ni ce”
Leila ta amsa mata bayan ta gama bata mata lokaci.
“Gashi wani mutum yace na baki”
Leila ta leka bayan matar ko wata hango wani amman bata ga wanda take zargi ba.
“Ina yake?”
“Ya wuce, ya dai bani wannan envelop din yace na baki”
“Sanye da me kika ganshi?”
“Facing cap, sai kananan kaya fuskarsa da mask”
“Okay”
Ta fada sannan ta karba, matar ta juya ta koma inda ta fito, Leila ta sake dialing number Madina cikin bacin rai, wayar tai ring har ta katse Madina bata daga ba, ta jera eight miss calls sannan sauke wayar, ta bude envelop din sai ga hakora biyu da hotunan gawar Baaba sun kwado a kasa. Ihu tai taja baya da sauri ta rufe baki, hango Momy da Hajiya Saratu sun kallon inda take yasa tai saurin dukawa ta dauki hakura tana yamutsa fuska ta saka a envelope din ta dauki hoton ta saka, sannan ta doso inda suke gabanta na faduwa.
“Ke lafita?”
Hajiya Saratu ta tambaya, sai da ta kalli Momy sannan ta amsa.
“Ba komai, zan tafi gida yanzu”
“Gida kuma? Anya lafiya dai?”
“Ba komai”
Ta amsa bata jira abun da zata kara cewa ba, ta nufi hanyar ficewa daga gurin da saurinta, jikinta sai rawa yake domin ba a taba aiko mata da wani abu daya data mata da hankali ba irin wannan, inda ta faka motarta ta nufa ta bude motar ta shiga ta jefa envelop din front seat ta fashe da kuka.
“Miyasa abubuwa zasu chakude min haka? Why?”
Ta daki sitiyarin motar da mugun karfi tana jin kamar ta fisge shi ta jefar saboda bacin rai. That's how she is idan ranta ya bace duk abun da ya zo mata aikatawa take. Kwafa tai ta shiga message ta rubutawa Madina sako ta tura mata. Sannan tai ma motar key tai reverse ta fice daga gurin.
*** *** ***
Momy ta kalli kanwarta Hajiya Saratu a kokarinta na kawar da tunanin Hajiya Saratu tace.
“Allah yasa dai ba kuskure kika yi gurin bada suna ba, kin ji tace tana jun warin ja6a nan fa”
“Aa na fada masa sunan Aminatu kuma na fada masa na Leila, har ma sai da ya rubuta a jikin takardar, sai dai idan can shi yai wannan shirmen”
“To gaskiya ki koma masa ki fada masa, har yanzu shiru kuma ita wanda ake son a kulla soyayyar tsakaninsu ita ke warin Ja6a”
“Ai dole gobe zan koma na fada masa, kuma na tambaya dalilin warin da take ji, ko dai shiyasa ya ce sai ta